Showing 6001 words to 9000 words out of 27913 words

Chapter 3 - HAMSHAƘIYAR UWA Book (1).

05 Jul 2024

3329

Allahu zan baka ina fatan zaka zo ka ga karatunmu? Ya ce "Ai ina tunanin a haɗa bikinmu da saukar ki... Kai! Na katse shi. Na yi ƙasa da murya. Saura sati biyar fa ayi walimarmu yaushe aka shirya? Ya numfasa "Wane irin shiri kike magana a kai?" Na sunkuyar da kai, yaushe ka kawo kuɗi har aka sa rana, kuma ga maganar lefe su Abbanmu ga maganar kayan ɗaki abin da za a ci abiki, kaga duk abin dubawa ne. Yace "Kinyi gaskiya, amma zan ɗauki wani kuɗin dashi na zan bada kuɗi cikin satin nan a kawo dubu hamsin, sannan nasan dai ko ba lefe zaki aure ni ko?" Har a zuciyata zan iya hakan Yaya, sai dai matsalar iyayena basu da halin yimin kayan ɗaki a cikin wata guda, yanzu ma suna ta abinda zasu fiddani kunyar walimar saukar nan da zamuyi. Yace to ke da me za kuyi a saukar? Nace walima ce kawai a gida, ya ce nawa zaki kashe... Na katse shi da A a bazan ɗora maka nauyi ba, kar ka rene ni da haka, kabari in saba da yanayinka na asali,ka koya min yadda zamu rayu a lokutan akwai ko na babu. Ya ɗaga hannunshi ɗaya tare da faɗin kinga dakata kiji. "Inada shine shiyasa, kuma ba roƙona ki ka yi ba, kawai ki faɗa min nawa zai ishe ki ko inje in ɗauki kuɗin da zan kawo miki na aure inyi gaban kai na da su.". Na ce Umma za su min faɗa, duka yau ne zuwan ka na biyu fa, kuma... "Kuma me?" Nace shike nan dubu uku ne. Ya ce "To zan baki sai kuma me?" Na ce shike nan. Yace "Ankon walima da hijabi Lemo da kalanda kinsan dai nima na taɓa saukar nan nasan ya ake yi. Na ce ai duk Abba da Umma sun sai min. Ya ce to shike nan zan kawo miki dubu uku jibi mu koma kan maganarmu in turo a kawo kuɗin ko?"Nace bari in faɗawa su Umma, yace don Allah da kin shiga ki sanar musu,kuma zan kira komai dare yau inji ko sun amince." Na ce to shike nan, amma nima zan nemi wata alfarma a gurinka. Ya tattaro hankalinsa gurina "Faɗi da sauri in har zan iya kin samu." Ina son in ci gaba da karatu ko da makarantar koyon aikin jinya ne. Ya yi shiru can yace "Bazan miki alƙawari ba,saboda wasu dalilai amma mu aje maganar zuwa gaba." Nace to shike nan. Ya kwai kwayi muryata "Na gode Babyna." Na sa hannu na rufe fuska ta. Yace to bari in tafi, nace yau naga baka zo da Kekenka ba? Ya ce tayar ce ta yi faci ɗazu ina hanyar dawo wa daga kasuwa, na ce to Allah ya tsare ya ce "Ameen muka yi sallama cikin shauƙi da ƙauna.
Na samu Abba yana ta faɗa wai ko dai nice nace wa Aliyu zan sha Lemo domin yaran zamani ba abin yarda bane. Na zauna na ce Abba wallahi ban roƙeshi ba yanzu ma dan baku san ya mu ka yi da shi ba ne, cewa ya yi in faɗa masa abinda zan kashe a walima lokacin sauka zai bani kuɗin nace a a ya bari shine ya ji haushi. Umma tace "Abban Baby na faɗa maka ko Jamila bazata yi roƙo ba, bare kuma Baby, duk da ba 'a shedar 'yan zamani akwai abinda zaka shedi ɗanka dashi, yace "To Allah ya muku albarka dukanku har da ke Ummar ta su,domin tarbiyyar ki ce, shi kuma Allah ya saka masa da alkhairi ya jiƙan magabata." Muka ce Ameen ya ce "To sai a yanka aba kowa, ku rage akai gidan Yaya ba ma ci mu kaɗai ba." Jamila ce me yankawa Ni kuma na yi zugum ina tunanin ta ina zan fara sanar da iyayena saƙon shi. Umma ta ce, lafiya ke kuma ai Abban na ku ya gane ba roƙarsa aka yi ba. Nace ba wannan ba ne, haka ya ce wai a satin nan za a kawo kuɗi, kuma wai in kun yarda za a yi biki tare da walimar saukarmu... Tarin Umma ya sa nayi shiru ta ƙware da ayabar da ta ke ci, na tashi da sauri na kawo mata ruwa ina yi mata sannu.Abba ya taso shima cikin sauri yana mata sannu. Bayan ta samu kanta tana maida numfashi tana magana, "Baza a yi gaggawa ba gaskiya sai anyi bincike, kuma bamu da halin biki a wata ɗaya." Abba ya ce ki daina magana kin ƙware ki yi shiru tukunna. Sai da ta samu natsuwa sannan Abba ya ce, "Inda haka zata samu zanfi kowa murna ace na aurar da Baby a ranar saukar ta. To amma hidimar da yawa ga haihuwarki ko yau ko gabe." Umma tace, ta haihuwa mai sauƙi ne, ba taron suna zanyi ba Allah dai ya sauke ni lafiya. Abba ya ce "Ameen, dama tun farko ya faɗa min aure ya zo, sannan ya taɓa aure kinga dole ya buƙaci aure da wuri, ina ga abinda za a yi mu amince su fara kawo kuɗin sai mu yi maganar da ta dace." Umma ta ce to shikenan ke sai ki faɗa masa in yazo. Na sunkuyar da kai na ce yace infaɗa masa a waya zai kira a ta Umma in yaje gida. Abba ya ce to. Sai ki sanar dashi. Da wayar Umma na shiga ɗakinmu ina ta jiran kiransa har bacci ya kwashe ni.

Shamaki ya ƙosa ƙwarai ya sallami mutanan da yakan gansu in an idar da sallar Isha'i, suka tsare shi, yana sauraron buƙatunsu wanda zai yi a gurin kamar kuɗi marasa yawa ya basu wanda sai ya tura su je Zeena Foundation sai ya tura su. Ya ƙagara sosai dan tun jiya ya so jin yadda Baby suka yi da mahaifanta, amma da yaga dare ya yi sai ya barwa yau. Ya dubi Malam Sabitu wanda shi ne limamin masallacinsu da ke jikin gidansu ya ce, Malam zan shiga gidan gobe zan baka kati ka ba mutumin sai a kaishi Zeena Hospital za su min magana game da abinda za' a biya. Ya ce "To Allaji Allah ya ƙara arziƙi muna godiya." Shamaki cikin ƙosawa ya ce ba komai, Malam Aba sauran jama'a haƙuri ina da uzri a ciki. Liman ya ce "To insha Allahu Ubangiji ya rufa asiri."
Kamar ya wuce amma dole ya shiga gurin Hajiya, tana lazimi, Azima tana gefe tana jira ta kammala dan ta mirza mata manta na ƙafa. Ya zauna shima yana jira, zuciyarsa ta tafi matuƙa ga tunanin Baby, nan da wata ɗaya tana gidansa zai bata rayuwa mai kyau, zai maida ita sarauniyar shi.,.. Yaya Shamaki! Muryar Azima ya ji ta kira sunan shi da ƙarfi, a firgice ya waiga ya dube ta tare da faɗin Baby lafiya?" Sai kuma ya dawo cikin hayyacinsa ya dubi Hajiya wadda ta tsare shi da ido, yace sannunku Hajiya. Bata amsa ba sai ta kalli Azima tace je ki dawo. Ta maido duban ta gare shi, "Aliyu." Ta ambaci sunan sa, ya ɗan zaro ido kafin ya zabura ya amsa da cewa na am Hajiya. Cike da Tsoro ya ke Domin a duk ranar da ta ambaci sunansa to ya tabbatar ranar ya kai maƙura gurin ɓata mata rai. Ta numfasa "Faɗa min tunanin me ka ke yi?" Yace ba wani abu bane waya nace wa yarinyar nan zan mata tun jiya to ban samu na cika alƙawarin ba. Ta nuna shi da yatsa shi yasa ka shigo gida da wuri ba domin ka gama jin matsalolin mutanan da ke da buƙata a gurinka ba? Ni kuma ka zo ka tasani ka faɗa kogin tunani, to in na janye amincewa ta da wannan yarinyar ya zaka yi kenan?" Gaban shi ya yi mummunar faɗuwa cikin sauri yace, Nasan baza kiyi haka ba Hajiya! Ta kuma zaro ido cike da mamaki, abinda ta tsammani zataji shine Duk yadda ki ka yi daidai Hajiya. Ta lumshe ido cike da damuwa, can ta ce "Shikenan yau nasan baza muci abincin dare da kai ba,bare muyi wasu bayanai ko wani lissafi,ka tashi kaje ka yi wayar." Ya san gatse ta yi masa,dan haka sai ya ce, za muyi lissafi Hajiya, abincin ne yau cikina duk a cushe ya ke. Ta kuma yin shiru tabbas ko ita yau abincin nan ba zai ciyu a gareta ba, ta numfasa sannan ta kai hannu ta ɗauki wayar ta a gefe ta shiga neman Hassan. Ya ɗauka cikin girmamawa suka gaisa, ta ce dama zan tambaye ka yau da aka kawo abinci kasuwa Shamaki ya ci Hassan ya ce "A'a kayan marmari ya ci sosai yau." Ta ce to na gode. Ta sake maida kallon ta ga Shamaki, tashi kaje za muyi magana da safe, yanzu kam bana zaton kana iya fahimtar duk abin da zan ce maka." Ya ce haba dai Hajiya karki tashi hankalin ki, wallahi abin ba kamar yadda ki ka zata bane. Ta nuna masa hanyar sashensa "Je ka yi waya." Tsam ya miƙe cikin sanyin jiki ya ɗan kuma risnawa tare da faɗin mu tashi lafiya Hajiya Allah ya huci zuciyarku. "Allah ya maka albarka." Ta furta cikin kallon gefe. Ya tafi ta bishi da kallo ranta ya sosu ƙwarai in da ne Shamaki ba zai tafi ba da tace ya tafi, zai tsugunna ne yana bata haƙuri ƙilama sai ya zubar da hawaye har sai ta huce, sannan zai ci abincin ko da baya jin yunwa,haka kuma za suyi lissafin kamar yadda suka saba. Lallai dole ta ɗauki dukkan mataki kafin abin ya wuce gona da iri, ta koma ta jingina sannan ta ɗauki waya ɗaya a cikin wayoyinta. Ta danna kira, suka gaisa da malamin wanda shine yake taya su da addu'o'in neman tsari da samun kariya. Ta ce Malam akwai wata matsala da ta soma tunkarowa cikin ahalina yaron nan Shamaki ya faɗa soyayya da wata yarinya, yadda ya koma kamar wawa abin ya tsorata ni. Ina son amin bincike shin ba wani abu yarinyar ta yi masa ba! Kuma tsakaninsu ina son in sani akwai alkhairi ma kuwa!Malam yace "Insha Allahu Hajiya za kiji sakamako zuwa gobe, za ayi bincike sosai zamu iya samun sunan yarinyar?" Hajiya ta ɗanyi shiru sannan ta ce ina zuwa. Ta katse layin ta soma kiran wayar Shamaki, ya gama shirin kwanciya kenan yana ta sauri dan ya kira masoyiyarsa, cikin sauri ya ɗaga kiran Hajiya gaban shi yana faɗuwa. Tace "Ya sunan yarinyar da kake so?" Cikin sauri yace Baby Amira ko Rabi atu duka suna kiranta da shi. Ta kashe layin ba tare da tace komai ba. Sai da ya gama komai sannan Ya danna kiran layin wayar mahaifiyar ta sannan ya kwanta a kan tsakiyar gadonsa ƙafafun sa na ƙasa.
Na jigata sosai da tunanin abinda ya hana Yaya Aliyu kira na, sai naji kamar in kira shi sai kuma wata zuciyar ta hane ni,har na kasa cin abinci a yinin na kuma shiga kaiwa Allah kuka in har da akwai matsala ina roƙon Ubangiji ya kauda matsalar, yanzu kam na samu tabbacin cewa ina son Aliyu har lokacin da muka je makwanci banji sautin wayar Umma ba, na sadaƙar cewa ya canza ra'ayi. Ƙarar kiɗan Nokia ya tashe ni zaune, na kasa kunne inji ko Umma zata kira ni, har kiran ya yanke, na tashi da sauri na fita, daidai lokacin da wayar ta sake daukan kiɗan na yi sallama a ƙofar ɗakin ba a amsa ba, na shiga Umma bacci ta ke wayar na caji Abba kuma bai shigo ba, na ɗauki wayar da sauri na nufi ɗakin mu ta kuma katsewa kafin in ɗaga, na fara danna lambobin cin bashi amma sai kira ya ƙara katse hakan, da sauri na faɗa kan lamammiyar katifar sannan na manna wayar a kunne tare da sallama. Ya amsa tare da tambayar ko dai har na yi bacci? Na ce masa e bacci ya fara ɗauka na. Ya ce "Ki min afwa abubuwa sun sha kaina ban kira ba kamar yadda na yi alƙawari." Na sauke numfashi hakan kuwa ya yi matuƙar ɗaga hankali na, na yini a damuwa ko dai ba lafiya ne, in kuma na yi kamar in kira ka, sai zuciyata ta faɗa min cewa in kana cikin wani uzri fa, yanzu dai da tunanin haka na kwanta. "Alhamdulillah! Ina da tabbacin kina so na a yanzu, kuma naji daɗi dan Allah karki dinga ɓoye min duk yadda ki ka ji a kaina ko daɗi ko akasin haka ina son wannan kinji Baby?" Nace To zan ke faɗa maka Yaya. ya ce "Yanzu faɗa min ya kuka yi da su Umma?" Na ce sun amince ka kawo kuɗi amma kamar yadda na faɗa maka baza su amince da auren lokacin walimar saukarmu ba, domin yanayi,kuma kai ma bana son ka takura kanka, kuma malamai suna cewa gaggawa yawancin ta daga sheɗan ne, abi a sannu. Ya numfasa "Gaskiya kika faɗa Rabi'atu amma ina son ki gane wani abu, na taɓa aure nasan daɗin shi kuma ina buƙatar shi. Bazan jure dogon zama ba, tunda har zaki iya sadaukarwa game da lefe, me zai hana ni ba zan sadaukar game da kayan ɗaki ba. Ko ba domin ni za ayi ba?" Na ce domin kai za 'ayi mana,amma kasan mutane akwai su da munafinci sosai za ayi ta gulma cewa ko kayan ɗaki iyayena ba su sai min ba. Lefe kuwa zamu iya cewa ankai ajiya. Yayi murmushi mai sauti, "Gadon ma sai muce kafinta bai gama ba." Ya faɗa cikin yanayin nishaɗi. Na ce in har su Umma za su yarda da haka ni bani da matsala kaine abinji nan katifar da nake kwance da kaɗan ta fi tabarmar kauri. Ya saki dariyar da sai kuma naji kunya ta kamani. Yace "Ina da katifa babba kuma Hajiyata ta na da tukunyar girki dan haka ni matata kawai na ke buƙata." Wani daɗi ya tsirga min da ya ambace ni da matarsa. Allah ya nuna min na faɗa a zuci, "Ameen Babyna." Nace kai araina nayi addu'arfa. Yayi "yar dariya,araina na amsa fa ke ma kinji ne?" Nace e mana, yace "A lallai mu na musamman ne gaskiya kunnuwanmu suna iya sauraron abinda zukatanmu suke faɗa kenan gaskiya mu gode wa Allah. Yawwa Baby in tambaye ki wani abu?" Na lumshe ido na sake yin ƙasa da murya domin bacci yana ɗan bibiyata. Na ce tambayi ko me ka ke so. "Zaki iya zama da uwar miji?" Cikin sauri na wartsake, a son zuciyarta shi ne 'a 'a bisa ga yadda na ga Umma tana fama da kiyayyar dangi Abba, kuma ta bamu labarin abin ya fara ne tun daga tsanar da mahaifiyar Abba tayi mata kafin ta rasu. "Kinyi shiru Baby." Yafaɗa da sanyi jiki. Nace mamaki na ke yi da wannan tambayar kuma ina nazarin dalilin yinta. Yace "Kar ki damu da dalili, ki faɗa min me kike mamaki." Nace to ya zaka tambaye ni cewa zan iya zama da mahaifiyar da ta haife ni? Na marairaice murya ina magana cikin yanayi shagwaɓa. Yaya in har yadda nake jin ka a zuciya shine so to tayaya Mahaifiyar ka baza ta zama tawa ba? Sannan in har wani zai tambaye ni cewa zan iya zama da mahaifiyata me zai hana in so jin dalilinsa cikin mamakina? Ya yi shiru Yarinyar ta gama gigita shi ta sukurkuta shi,dan haka ya fara da faɗin "kiyi haƙuri Babyna nasan mata da yawa suna gudun zama da Uwar miji wannan shine farkon matsala ta da matata ta fari Maman Meema, amma ba wai dan wani abu na yi wannan maganar ba." Nayi ɗan murmushi domin ganin na soma gano wasu abubuwa game dashi, kuma rauninsa ba zai min wahalar ganewa ba. Ya katse ni da cewa "Kin lashe babbar jarabawar da na fara miki kuma zan turo ranar Lahadi ni kuma zanzo jibi in kawo miki dubunki uku ta walima." Ba gobe kace min ba a jiya? Na katse shi, Ni ba damuwata kuɗin ba domin sai da na sha faɗa akan Lemon da ka kawo jiya, Abba yana zargin ko dai roƙon ka na yi ka siya min, Ni kuwa ina jin daɗin hirar da kai ne kawai ina son in ganni gani ga ka." Ya katse ni da cewa "Alhamdulillah na ci nasara Baby wallahi kin kamu da sona Baby dan Allah ki furta ki ce Aliyu ina sonka dan Allah! Ki faɗa inji." Na sunne kaina cikin ɗan yamusashshen filo na Na ce wayyo Allah Yaya kamin afwa zan faɗa maka amma banda yanzu. Ciki shagwaɓa yace haba Babyna." Gyaran muryar Abbanmu naji banji sallamar shi ba, nasan zai zo ne ya duba mu kamar yadda ya saba,don haka sai nace Yaya Abba ya shigo sai goben ka yi haƙuri, na kashe wayar ya taɓa ƙofar na yi laf, ya haska sannan ya yi addu'a ya tofa gabas da yamma kudu da arewa na ɗakin, sannan ya ja ƙofar ya fita.


🖊️🖊️🖊️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login