Showing 27001 words to 27913 words out of 27913 words
a jikina za mu zauna na har abada da ita domin ta iya duk wasu dabaru na riƙe zuciyar miji, to sai Hajiya ta hango aibun wannan kular da ta ke bani, tace ni ne jigon gida kuma ni ne sirrin gida babu wani dalili da matata zata san komai na gidan dan haka in tsuke baki na kar ta na jin komai daga gare ni. Haka na yi wa Hajiya alƙawarin ta dai na sanin komai, to amma na kasa daina faɗa mata musamman in ta sani farin ciki na rasa labarin da zan bata kuma ni labarin kasuwa nafi sani. To Hajiya ta zafafa akan hakan kuma ita bata nemi saki ba,Hajiya ta nemi a sahale mata tare da bata tukwaici irin wanda aka ba 'yan uwanta na baya. To Ni kunji damuwa ta Yarinyar nan da zan aure na ɓoye mata ko ni waye, 'yar talakawa ce, kuma ƙarama ce bata kai shekarun Matana na baya ba. Sannan wata babbar matsalar ina yi mata wani irin so wanda bazan iya fassara shi ba. Ta kai bani da control ɗin kai na game da ita, har yaran Kantina su Hassan sun fara yi da ni akan soyayyar ta. Bana son mu samu wata damuwa da Hajiyata amma nasan zata yi ƙorafi game da soyayyar Baby. Haka ga matsalolin farko dana lissafa muku, ba lallai yarinyar nan ta na da wannan budurcin ba kuma hakan ba yana nufin ta bi maza ba ne, likitoci sunyi bayani zai iya tafiya da kanshi sakamakon cima da wasanni na makaranta tsalle tsalle da guje guje to in aka yi wa yarinyar hukunci da cewa ta bi maza ai bamu yi mata adalci ba. Wannan shi ne kukana. Maman Umar ta numfasa ta kalli sauran ta ce "Ni a nawa ganin Hajiya ba ta yi wannan bane domin ta takurawa rayuwarka, tana yi ne domin ta inganta rayuwarka da mu gaba ɗaya, ka taɓa tambayar dalilin da ka samo suna Shamaki? . Sannan ita ta ba mu kulawa mai tsanani da lallaɓa rayuwarmu domin ganin mun kai mutuncin mu gidan miji, in ka fahimce ta to zaka gane dalilin da take yi maka kiwon Azima. Ta fannin rufe sirri ga mace kuma shima sai inga cewa hakan shima daidai ne, domin kai ne kan komai na gidan dukkan wata dukiya da muka mallaka kai ne ka san komai,lauyoyinmu ma su kula da dukiyarmu kai ne suka sani. Duk wani kaya dazai shigo da kuma wanda zai fita sai ka amince na dukkan rassanmu na jihohi. To mai ɗauke da irin wannan nauyi dole ne ya zama baya cikin shagala ko wani abu mai kama da ɗauke hankali. Ina fatan kun fahimci me nike nufi. Duk suka ce haka ne Shamaki ka yi nazarin maganar Maman Umar.
Maman Nana tace kuma gida kamar namu ba zai kyautu ace marowaciya ce matar gidan ba, akwai hikima cikin gwaje gwajen da Hajiya ta ke yi wa matanka, kuma zaka gane haka nan gaba. A'isha ta ce "Ya kamata dai ta janye maganar budurci nan saboda dalilan da Shamaki ya bada gaskiya haka ne, inzan bada misali da kai na, kwanaki Afra ta faɗi a banɗaki har ta yanke ta gabanta mukaje asibiti damuwata kar dai ya taɓa mata matanci likita yace ko da ya taɓa ba bu wata matsala ya kuma yi min bayani irin wanda Shamaki ɗin nan ya yi. To in kun kula da maganar likita kwalbar nan ta yanke wa yarinyar wannan yanar da ake magana to sai aure ya kai ta inda ake irin wannan al'adar ta ya zata wanke kanta?" Duk suka haɗa baki gurin cewa babu. Shamaki ya yi zugum yana tunanin amsar da Baby ta bashi, "Ni budurwa ce amma bani da wani tabbaci akan budurcina." Ya numfasa, daidai lokacin da Maman Iman ta ce "Ina ganin tun da yanzu duk mun yarda cewa Hajiya ta na kan gaskiya sai dai ɗan gyara kaɗan ta yaya zamu sha kan hakan?" Shamaki yace Yawwa an zo inda nake son a zo, gyara nake so ya kasance in nayi aure na yi kenan kamar yadda ku ke da mazajenku. Ba shakka ina son nima in zama cikakken mutum in kare mutuncina ku sani baya ga karewar Ubangiji matan da suke kawo kansu gurina da yanzu na canza layi na shiga bin matan banza tunda kuɗi suke buƙata ni kuma bani da matsalar kuɗi. Suka ce haka ne Allah ya ƙara karewa. Maman Umar ta ce "To ni a matsayi na na babba a cikin ku kuma wadda in aka samu kuskure a zaman nan laifin zai iya dawowa kai na ina son in baku dama ku kawo na ku shawarwarin sai in haɗa da nawa sai mu tunkari Hajiya. Sai dai amma ina son ku tuna wasu abubuwa kafin ku kawo shawara. Wacece Hajiyarmu? Ya kaifin basirarta yake? Kuma me zata iya amincewa dashi? Ina sauraronku mu fara da Maman Nana tunda ke ce mai bina sai mu gangara har zuwa Shi Shamakin namu.
*Alhamdulillah a nan na kawo ƙarshen free Pages, waɗanda basu biya ba sai suyi ƙoƙari su biya dan samun cigaban labarin,zaku turo ₦600 ta wannan account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn shima ta wannan number 08140004302*
🖊️🖊️🖊️