Showing 21001 words to 24000 words out of 27913 words

Chapter 8 - HAMSHAƘIYAR UWA Book (1).

05 Jul 2024

3331

kawo lefe zuwa jibi." Zan dawo ya kuma cewa shiga gida kawai." Dole na wuce ina waiwayen sa. Fatana Allah ya sa ba bashi zai ci ba.
Jamila sai murna su ke yi ita da Ummu za a.kawo lefe, ni kam ba ta wanna na ke ba,ɗaga bikin shine abinda yafi komai bani takaici. Saidai ba ni da damar in yi maganar da wani, tunda duk ba su fahimta ta. Ashoben Walimarmu shi aka maida ashoben biki wannan ɗagawar sai ya bada damar zuwa a siyo musamman 'yan uwa da 'yanmatan lungunmu waɗan da suka bayyana kansu a matsayin ƙawayena harda su Fati. Kullum sai sun shigo muna tattauna yadda za ayi party. Tare da taimakon Jamila na rubuta wa Yaya abubuwan da nake buƙata. Kuɗin lalle da wankin kai. kuɗin Party kuɗin kwalliya. Ina tura masa ya rubuto cewa,kin manta da na gyaran jiki. Na yi 'yar dariya shidai Yaya baya rabo da ɗorawa kansa ɗawainiya. Umma ta tashi hankalinta game da kayan ɗaki da safe ta aiki Jamila a kira mata aminiyar ta Umman Amina. Jamila bata jima da da wowa ba Umman su Amina ta shigo, ina jin su daga ɗaki Umma tana faɗa mata zancen kawo lefe, ta ce tunda sunyi lefe maganar kaya katako muma dole mu dage ko ba masu tsada bane. Ummansu Amina ta ce, "Haka ne, dama abinda yasa na ce abar batun kayan katako a sai ka tifa da kayan girki saboda ya ce ba matsala kuma ba shi halin lefe akwai wata mafita guda ɗaya in har Abban su Baby zai yarda, akwai masu bada taimako na kayan ɗaki wani foundation mai suna Zeena. Umma tace ina jin su a Radio suna yi wallahi. Umman su Amina ta ce Da sai a rubuta takarda a tafi da yarinyar a kai musu in so samu ne yau ɗinnan. Umma tace ai damuwar da ƙyar Abbansu ya yarda Umman su Amina ta ce " Akwai mafita, Baby ba tana nan ba, tazo yanzu in faɗa mata abinda zata rubuta ni sai in sata a gaba mukai takardar." Na ɗan zaro ido a inda nake a laɓe, Zeena sune waɗanda Yaya ke yiwa yaron shago fa. Ƙwalamin kira Umma ta yi, na amsa naje a kace in ɗako takarda da biro na ɗakko. Muka zauna Umman Amina tana faɗamin ina rubutawa. Neman taimako ne dan Allah an saka bikin har ana ta ɗaga wa saboda. ba'a samu kayan ɗaki ba, har ma maganar tana nema ta lalace. Wai in sa cewa ni marainiya ce. Sai na rubuta iyayena basu da hali gashi an saka auren kusa. Da na gama aka sa lambar wayata da ta Umma. Ummansu Amina ta ce shirya maza bari inje in barwa Amina sallahun girki, tana fita nace A
Umma Hajiya Zeena ita ce Uwar ɗakin Yaya fa, Mahaifiyar mai gidansa da muka je. Tace "Tofa!" Wannan shine ga ƙoshi ga kwanan yunwa, bari ta zo inji ya za ayi." Data dawo Umma ta faɗa mata halin da ake ciki, sai ta ce ai mu ofishin su na Foundation ɗin zamu je,baza su sani ba ma bare yaji labari. Muka hau Adaidaita sahu zuwa titin Ɗanbare muka je wata Zeena plaza mun shiga ofishin muka gaida wadda muka samu, sannan muka faɗa mata buƙatarmu tace yaushe ne bikin mukace kwana shabiyu, ta ce shine zaku kawo takarda yanzu? Umman Amina ta ce 'yarnan ku yi haƙuri da muna sa rai cewa zamu iya sayen kayan ne sai kuma muka ga ba wata mafita. Ta amshi takardar ta buɗe ta karanta,ta yatsina baki, ku ba ma marainiya ba ce kenan? Kuma gashi babu sa hannun ta bare na mahaifinta. Umman su Amina ta lankwashe murya kamar marainiya tace mana a taimaka mana. Matar ta ce gashi nan an rubuta iyaye na basu da ƙarfi." Umman Amina ta kalle ni, na sunkuyar da kai, tace Hajiya ita ce ta rubuta bata iya rubutun bane a taimaka. Ta yatsina fuska. "Sai ku haifi yara ku kasa amfana musu komai,Hajiyar bata shigo ba,in ta shigo zan bata amma bana sa ran zaku samu domin an cire list na wannan wata." Ta kalli Umman Amina "Kamar kun bada ajiya sai a ƙurarren lokaci irin wannan." Umman Amina sai haƙuri take bata tana roƙonta, ita kuma sai yaɓa mana magana ta ke yi. Baƙin ciki kamar in fice ko in hau matar da duka,ta kalle ni, wannan ce mayar kenan Umman Amina tace ita ce. Ta taɓa baki. "Kada kiji haushina yarinya laifin iyayenki ne, zan bawa Hajiya takardar ku in ta shigo suma suna da bikine bata zuwa sosai. Nan dai mukayi godiya muka fice.
Na ce da Umman Amina wallahi dama a kyale su, dubi yadda sai wulaƙanci ta ke mana. Umman Amina tace ai haka suke irin waɗannan aiki fa aka ɗauke ta karɓar takardar neman taimako, amma sai kace itace ta ce zata bada sai irin wannan rashin mutunci ta ce yi.
Umma bata faɗa wa Abbanmu ba, musamman da taji rashin tabbacin abin. Umman Amina tace in shirya in raka Amina kasuwa zata sai anko da mayafi. Nace to sai dai muje da kyalle tunda mu namu a gurin Safara aka siya. Tace bana son kayan Safara dan zata bada bashi saita Linka kuɗin ga rashin haƙurin bashi. Nace Umma da da kuɗi da kin bada na Jamila da yadin da kika ce zaki sai wa su Jafar da Habu. Tace sai in bada a kuɗin gudunmawar da 'yan Kurna suka aiko jiya, Allah ya rufa asiri kar in Lodi bashin Safara bayan biki ta uzzira min naji da naki saura dubu biyu da naira hamsin. Nace to maje gobe,ranar da za 'a kawo lefena kenan. Gidan su Zuhra za akai, gidan wan Abbanmu. Na shirya nasa doguwar baƙar riga da mayafi Amina ta zo har zamu wuce Umma tace kije gidansu Zuhra jiya Ummansu ta aiko tana tambayar inda za a samu anko.
Muka biya, nan "yan matan gidan aka taso, amarsu mai magar zuma, yau zamu sha lefe. Na ce ku ta lefe kuke. Ina Umma zamu kasuwane sayen anko. Murja tace Zuhra ce zata siya. Umman su ta fito muka gaisheta,ta taɓe baki, "Kaga 'ya'yan aminai to Zuhra ta baku saƙo ko kuwa ta biku?" Nace ta zo muje mana tafiyar zata fi daɗi. Dama tsararmu ce Tare mukayi Candy sai dai makarantarmu ba ɗaya ba, domin su ta kuɗi suke zuwa kasancewar Abbansu ya fi namu ƙarfi.
Muka hau adaidaita muka nufi kwari nace kai gabana sai faɗuwa ya ke yi, bansan ina ne gefen su Yaya ba, fatan karya ganni,sai ƙara kaɗe ƙura nake. Muna ta yawo sai wani ya amshi kyallen yace wannan kayan Zeena plaza ne. Gabana ya faɗi. Na tsaya cak, nace bari in baku kuɗi kuje ku siyo harda ta Jamila. Zuhra tace "Me yasa?" Nace a ɗaya daga cikin irin waɗannan kantunan ya ke yaron kanti. Amina ta ce to ai ba lallai shi a wannan yake ba. Nace to muje. Muna shiga wanda ya kawo mu ya tambaya ko akwai sauran wanna kayan?" Wani ya amsa ya duba yace akwai, muka shiga ƙaton kantin wani yace mu zauna a kawo mana saboda nan ba a bada ɗai ɗai sai dozin bari ya karɓo a ɗaya shagon.
Shamaki ya ɗaga robar ruwan paro ya sha ya aje yana sake juya katin hannun shi, ko shakka babu wannan katin daga makarantar su Baby aka kawo masa gayyata da kuma takardar neman taimako. Yanzu a yaya zaije, ya mata alƙawarin zaije mata yaga karatunta kuma zata so ta ganshi a gurin ƙila ma har ta nuna wa ƙawayen ta cewa ga wanda zan aura. Sannan a ɗaya gefen Hajiya bata son yana wasa da zuwa irin waɗannan wuraren da ake bawa Allah rance. Ya kuma ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe ido dan neman mafita. Ya buɗe idanu ya zuba a kan fuskar laptop ɗin dake gaban shi wadda ta ke hasko mishi ko ina na Kantin sama da ƙasa. Ya tsura ido akan wasu 'yan mata dake zaune kan wasu kaya. Ya ɗauki wayar kantin ya danna kira Ɗahiru ya ɗaga, yace suwaye zaune akan kayan nan wasu "yan mata su uku?" Yace Atamfar nan mai ganye suke so, Hassan yaje kawo musu. Shamaki ya ce in yazo kace ya zo ina kiranshi kafin ya sallame su.

Zungureriyar motar ta tsaya a ƙofar gidan Yayan Abban su Baby, Bala direba bai manta gidan ba,dan haka ya fito yace bari ya yi sallama. Wani saurayi zai shiga gidan Malam Bala yace, yaro, dan Allah in kashiga ka yi mana sallama da mai gidan. Tare suka fito domin yasan da zuwansu bayan azahar kamar yadda Abban su Baby yazo ya sanar da shi tun jiya, dan haka ma bai fita ba, kuma ya sanar da ƙaninsu da kuma maƙotanshi kamar yadda suka saba duk lokacin da wani a cikinsu zai karɓi kaya irin haka. Suka gaisa da Malam Bala, sannan ya dubi yaronsa da ya yi sallama da shi, yace Halifa a fito da tabarmi ga baƙin sun iso bari kira Malam liman ya danna kiran maƙocin nasa yana faɗa musu sun iso, dama da suka yi azahar ya tuna musu. Ya kira Abban su Baby ya ce,kazo sun iso, ka taho da ruwa da Lemon kar ka manta. Nan suka hallara sai aka buɗe kujerar baya aka soma fito da akwatuna na zamani haka ma but ɗin motar. Guda shidda ne masu kyau daga gani an zuba kaya masu tsada. Abban su Zuhra ya ce, ba sai an buɗe ba, Allah ya sa albarka ya bada zama lafiya. Suka ɗakko ruwa katan biyu Lemo katan biyu suka ce gashi. Har kawun Aliyu yace su barshi,sai Abban su Zuhra ya ce, ko dai ya yi kaɗan ne?" Suka ce a a haba ba haka bane, Liman da suka zo dashi ya ce a karɓa Allah ya sa albarka.
Suna tafiya aka shiga da kaya ciki dama su Umman su Zuhra suna ciki sun ƙosa su gani koda abin arziƙi ita da yaranta. Nan kuwa jiki yayi sanyi domin Atamfa tirmi talatin ce ga lesuna ga Shadda da dogayen riguna abin dai na girma. Suka haɗa kaya suka aje,tace Hajara kije ki cewa Umman su Baby azo a ɗauki kayannan. Abbansu Zuhra ya ce, ina za a kai su tun yanzu, a bari mana 'yan uwa su gama gani." Tace a a kar wani abu ya ɓace gani da 'yar mata a zarge su, gara akai can kowa yaje can ɗin ya gani.
Ta ƙwarzaba dole yace su Halifa su ɗauka su kai. Suma 'yan lungu suna ganin ana shiga da akwatuna, nan da nan labari ya karaɗe kaffatanin lungun an kawo lefen Baby. Umman su Baby ta aika Jafar ta ce ya kira mata Umman Amina. Itace ta saka ido akan kayan saboda maƙota sun tsaya sai sun gani ba iyayen ba ba yaran ba. Kowa ya sha mamakin kayan Umma kasa magana ta yi saboda tunanin ta kayan ɗaki, suma sun fita kunya,ko da yace baya so shi dai a shiryen sa yake.
Bayan mutane sun watse Umman Amina tace, gaskiya wannan kaya babu batun haƙura da kayan ɗaki. Tashi za kiyi mu koma can gurin tallafi in ba haka ba za aji kunya. Umman su Baby ta ce sai gobe dai yanzu su Baby basa nan ga kayan mutane. Umman Amina tace "To goben dai ya zama da wuri fa insha Allah kamar ƙarfe goma.

Jamila ta yi ta murna da ta dawo makaranta ta ga lefe tace amma gaskiya Yaya Aliyu da tanadin sa, dubi kaya kamar kati!" Umma tace gaskiya ya bada mamaki ya yi mamaya.

Muna jiran mai kawo mana zani, jim kaɗan sai gashi muka karɓa muna dubawa,ya faɗa mana kuɗin. Cikin mamaki na kalli Zuhra kinsa Safara dubu da ɗari biyar ta ɗora akan duk turmin atanfa ɗaya. "Amina tace shiyasa Ummanmu bata yarda da siyan kaya a gida." Zuhra tace dubu da ɗari biyar ta isa ayi ɗinki. Yaron ya katse mu ga ruwa. Ya miƙo mana ruwan Paro mai sanyi. Nace harda ruwa ku ke bayarwa? Yace mai gida yace a baku don daga gani kun gaji. Zuhra ta kalli wanda ke kan teburin a zaton ta shine mai gidan ta ce mun gode.Sai nima na dube shi nace Allah ya saka da alkhairi. Na basu baya ina shan ruwan kamar yadda suma suka nutse a shan ruwa.


🖊️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


*Free Page 9*


Na tuna da yadin su Jafar na cire robar ruwan daga bakina, na dubi wanda dai ya kawo mana atamfar nace, don Allah kuna saida yadikan maza masu sauƙi haka ko shadda irin ishirunka maraya ɗin nan? Yace "Bama sai dawa sai kun koma kan wannan layin nan."
Nace wai gashi mun gaji kyanshi daga nan mu fita. Na zaunen ya ce Ɗahiru zo mana. Yaje, jim ya dawo ya ce ƙanwata kawo a yanko miki yadin, nawa ne kuɗin kuma wace kalar kike so? Nace yadi huɗu ne kala kuma irin dai ta maza ƙanne na za a ɗinkawa. Ya amshi kuɗin ya fita. Abinda ya faru shine Shamaki ya tattara duk wani kallonshi ga motsinshi akan Baby data yi magana sai ya bugawa Hassan waya yana tambayar shi metake so, sai ya sanar dashi, sai yace ka sa Dahiru ya amshi kuɗin ko nawa tazo dashi ya je can shagon ya ɗakko mata shadda yadi biyar,amma karya sake ya ce mata komai, ya bata kawai ya amshi kuɗin. Hassan cikin mamaki ya ce,to Allaji. Muna zaune ya kawo shadda mai kyau, nace gaskiya wannan ta yi sauƙi, amma ka duba ko nawa na baka kuwa? Yace "Na gani ita kaɗai ta rage shiyasa aka bar miki a haka." Nace to mun gode. Muna fitowa bakin shagon sai ga wani mai adaidaita kamar mai jiranmu, nace ɗan agundi. Yace "Dai-dai ina?" Amina tace ko bakin ƙofa ma sai mu ƙarasa. Zuhra ta ce nawa zamu baka? Yace "Ku hau muje kawai. Muka kama hanya. Sai dai yana sauke mu ya wuce wai mubar kuɗin. Muka cika da mamaki sannan muka masa godiya tare da hasashen ko wata ya ke so a cikinmu, amma me yasa bai tambayi lambar waya ba. Haka dai muka wuce zuwa gida muna al'ajabin ɗan sahu. Tun da muka shiga lungun yara suke bamu labarin wai an kawo lefena. Gabana ya faɗi, muka shiga gidanmu har su Zuhra. Mun cika da al'ajabin kaya wanda hakan ni ma ya sa na fara tunanin kayan ɗaki ya wajabta aka iyayena.

Hajiya ta kalli ɗan 'uwanta bayan ya gama yi mata bayanin irin karɓar da akayi musu,yace dattawa ne gaskiya Allah ya sa alkhairi. Ta numfasa, "To sannunku da ƙoƙari kuma Allah ya ƙara zumunci." Yace amin ni zan koma,tace babu damuwa sai ka jini. Bayan fitar shi ta jingina tana nazari,ko shakka babu tunda ɗan uwannan nata ya ce dattawa ne ta tabbatar da hakan, domin da akasin hakanne ba abinda zai hana shi faɗa. A yadda ta karanci yarinyar a ranar da ta zo ta fito daga ƙaramin iyali, kuma kamar ba masu ƙwaɗayi bane, tasan cewa daga lokacin nauyin wannan iyalin zai iya hawa kansu, amma bata son abinda zai wuce gona da iri. Gidanta fadarta ce duk wanda ya shigo dole zai zama a ƙarƙashin ikon ta. Rawar kan Shamaki ya yi yawa a wannan auren ko na farko bai rikice haka ba bare sauran abinda ya ke bata haushi ma yadda yarinyar ta ke kamar an daurawa ƙashi fata, yaron ta lafiyayye ne kuma ta jima da fahimtar cewa shi ɗin mabuƙaci ne, ta yarda cewa ya yi haƙuri shi ne ya sa yanzu ta yarda da wannan auren na gaggawa duk idan ta dunƙule damuwar guri ɗaya tambayar ita ce yarinyar zata iya sama masa gamsashiyar natsuwa?" Bata da tabbacin wannan amsar dan haka dole ya sake aure ba da jimawa ba,domin samun ƙarin wadda zata tare wannan matsalar, zata yi tunani akan yarinyar da Maman Umar ta yi magana. Ta tashi zaune ta zuba wa Azima ido wadda ke zuba mata furar da Juma da dama mata aƙaramin firji da ke kusa da ita wadda ta ke sha bayan la'asar. Tana baiwa Azima duk wata kulawa da wasu ciye ciye na zamani domin amfanin ɗanta,amma har yanzu Azima yar shekaru sha huɗu ce, yar ƙaninta ce data ɗakko tun daga bakin yaye. Tana son Azima ta tashi da irin tarbiyyar da take son matar ɗanta ta kasan ce,sannan Malamin su ya faɗa mata cewa Azima ita ce zata haifi ɗa namiji tare da Shamaki. Sanin Shamaki ba zai jira ba shine yasa ta barshi ya yi duk auren da zai yi kafin Azima ta kawo,kuma Azima ce zata zama Hamshaƙiya a cikin matan sa. ƙaran da wayarta tayi ne ya maido da hankalinta ta kalli wayar wadda ta ware ce don yin magana da iya 'ya'yanta kaɗai. Maryam ce ɗaya daga cikin 'ya'yanta, Ta ɗauka sannan ta ɗaga, ta sa a kunne, acan ɓangaren Maryam cikin girmamawa tace,, "Hajiyarmu barka da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login