Showing 15001 words to 18000 words out of 27913 words
taɓa baki. "Allah ya bada Sa'a. Ta dube shi, ka yi magana da Juma a kwashe musu kayan marmarin nan su yi tsaraba. Da sauri na ce a'a Hajiya ki yi mana afwa za a yi mana faɗa. Ta ce "Haka ne domin ba'a san kunzo ba ki ka ce ko? " Ya kalleni cike da mamaki kuma da alamu bai ji daɗin hakan ba, ni ko da a kalli iyayena ƙanana gara ace ni ce bani da mutunci. Tace "Ba haka kika faɗa ba?" Na ce haka ne amma yanzu in har muka je da wannan kayan iyayenmu baza su haƙura da haƙurin da zamu basu na laifin ƙarya da muka yi ba, domin za su zargi ko mun canza hali ne mun zama kwaɗayayyu." Ta tsira min ido, sannan ta kalli Aliyu. "Sai ku sake yin ƙaryar da kuka yi a farko ku faɗi wani wanda in shine ya baku baza'ayi faɗa ba." Ai bamu da shi a dangin mu kaf, kuma ba mu yi nasarar ƙaryar farko ba kenan. Ki yafe mu Hajiya watarana zamu sa da kanmu mu ci insha Allahu. Yace gaskiya ne ranar da na kai musu Lemon ɓawo Abbansu yana ta faɗa. Tace "To shike nan Allah ya yi muku albarka za ku iya tafiyar ku yanzu." Sai lokacin ya kalle ni, muje ko? Na ce to na miƙe ina gyara mayafina Hajiya kuwa idanunta ƙyar a kaina. Jamila ta mata sallama ya nuna mana ƙofar da muka shigo ku bi nan muje. Muka fita har falon ƙarshe bai fito ba. Jamila tace gaskiya baki da hankali wallahi Yaya Baby. Daga zuwa gidan mutane kinji sanyin AC kin kama kina ta zuba,to meye sai kin faɗa mata cewa ba'asan munzo ba,ina ruwan ta da sanin su?" Na ce Dalla banza baki san mekefaruwa ba,amma zan wayar miki da kai bari mu hau keke napep. Yace fito Muje in kaiku can inda zaku ta bani mota aro." Yace in hau gaba Jamila ta hau baya. Maigadin yana faɗin adawo lafiya ranka ya daɗe Allaji. Na kalle shi. Ya yi saurin faɗin su wai mutane suna ƙaunar su kai mutum inda bai je ba, daga zuwa wurin ta wai raina ya daɗe kullum haka ya ke faɗa in dai Nazo gidannan." Na sauke ajiyar zuciya nace ai fatan alkhairi ya yi maka.
Ya canza maganar "Kinji daɗin hira da Hajiya?" Na ce sosai kuwa tana da kirki. Ya saki fara'a sai ma kin zauna da ita zaki sha nasiha da albarka. Na ce umm haka ne kam. azuciyata kuwa sai ina faɗin taɓ zama da wannan ai gara in haƙura da auren. Jamila ta sako baki, amma tana da tambayar ƙwaƙwaf wai! Na waiwayo da sauri wa ta tambaya? Ke mana harda kuka fa ki ka yi a gurin bada amsa. Sai ji mukayi mota ta yi ƙuu kamar zata faɗi sannan ya gungura gefen titi, me ta tambaye ki har ya saki kuka?" Nace kar ka damu ba wani abu bane, ki faɗa min don Allah.Jamila ta zayyana mishi komai, ya sauke ajiyar zuciya to kiyi haƙuri kinji ko?" Nace to ai ba ita ta sani kuka ba,ƙaryar da na yi wa iyayena ita ce ta sani kukan, na ci amanar su, zan faɗa musu gaskiya in mun koma. Yace ba wata matsala ko da baƙi faɗa ba,amma zaki iya faɗa in kina ganin haka zai fi sama miki kwanciyar hankali. Kuma za a turo gobe,sai ki sanar dani nan gidan zan kawo su ko kuwa wani gurin ne daban." Nace zan yi magana da Umma sai in faɗa maka duk yadda suka ce. Ya sauke mu ƙofar gidan Baaba ya bamu dubu ɗaya ya ce ku ba Baaba ɗin kafin inzo. Jamila ya miƙawa ta amsa tana godiya Nima na yi masa godiya muka shiga ya juya.
Hajiya ta jingina ta lumshe ido duk wanda ya kalleta zai yi zaton bacci ta ke yi,amma kogin nazarin yarinyar ta faɗa. Ko shakka babu ta lura yarinyar ta na da kafirin wayo, ta goge laifin dana so ɗorawa iyayenta ta maida shi a kanta,har da wani kukan kirsa wai ita ga mai imani, sannan ta bata mamaki yadda ta ƙi amsar komai dan haka ta fasa bata kyautar da ta yi niyya. Ba shakka ta cinye jarabawar da take son yi mata saidai tsaron ta wayon "yar ya girmi shekarunta.Kome ma Shamaki ya gani ita ba sharaɓa ba, ba ƙirjin kirki ba, kuma a fuska ba wata mai kyawun a zo a gani ba. Ta ke ta tuna da dabino da ya ci ta tashi zaune da sauri,a zuciyarta tana rayawa tasan ba matsala tunda yace dan ita aka yi shi.Amma dan ta kore kokwanto sai ta ɗauki waya dan taji ta bakin Malam.
Suka gaisa ta sanar da shi matsalar da aka samu. Ya ce "Subhanallah Hajiya ya ki ka bari ya ci." Tace ban ankara ba malam sai da ya kai na biyun kuma gashi a gabanta ba dama ince ya zubar,dole zata tuhume ni akan me yasa ita na bata. Malam yace sunansa da nata aka yi aikin gashi aikin mai ƙarfi ne, sirrin Ya wadudu ne aka haɗa da basmala ƙafa dubu talatin da wasu haɗe haɗe. Wani mutum da muka yi masa irin aikin nan matar bata son shi Allah da ta ci Dabinon duk inda zashi binsa ta ke, kuma da Allah ya yi masa rasuwa a maƙabarta ta tare. Gaban Hajiya ya faɗi, to kenan gara da bata ci duka ba, yaushe zan so ta zame masa jela ko ina ya saka ƙafa ta mayar. Damuwa ta yanzu shima kenan zai ƙara sonta? Malam yace mu dai jira muga hukuncin Allah,amma dai ki yi addu'a aike mahaifiya ce harshen ki yafi komai. Tace to shikenan, addu'a a kai muke Allah ya yi mana mafi alkhairi. Suka yi sallama ta miƙe domin yin alwallar azahar.
Jamila ce ke baiwa Baba labarin Yaya Aliyu, sai murna take. Ta bata dubun daya aiko mata,tana ta addu'a muka yini har la'asar list munyi mata wanki da kwalemar gidan taji daɗi tace dama ko yaushe ina ta fatan kuzo duk cikin jikoki na kune kaɗai masu yi min irin wannan ƙoƙarin Allah ya baku miji na gari. Mun tarar umma har ta gama tuwon dare nan na amshi aikin miya Jamila ta kama shara ranar dai munyi fashin Islamiya. Da dare muna cin tuwo Jamila ta ce ""Yaya Baby ina ta tunawa da kayan alatun nan yawuna har tsinkewa ya ke." Nace ko ni wallahi amma ke baki so ci bane, ni kinga ba dama inci. Tace "Itama Hajiyar bata so mu ci ba, ai da ta so muci sai ta bamu guri ko ta sa a kai mu falon farko. Na ce taɓ wannan kinga ta yi kama da wadda zata tashi?"Umma ta katse mu da faɗin wacece? Muka kalli juna. Na ce Umma dama zanzo in kawo kaina, na yi muku babban laifi,dan Allah ku yafe min. Na tsame hannu na a tuwon na zo gabanta na zauna na zayyana mata duk yadda abin ya faru. Ta min faɗa sosai kuma ta jamin kunne akan kar mu sake aikata makamancin irin wannan kuskuren. Tace bazata faɗawa Babanmu ba,har ma ta ce gashi munja mata tana yiwa mahaifinmu rufarufa. Na ɓoye mata wasu tambayoyin da Hajiya ta min wanda nasan zata ji babu daɗi.
Cikin dare ina tsaka da bacci sai naji kamar an tasheni, ina farkawar sai na tsunduma tunanin Yaya take na samu kaina da tashi na nufi ɗakin iyayena na tura ƙofar na kalli gurin da nake zaton wayar Umma na ganta kuwa a caji na ciro Abba da ke kwance a ƙasa kan tabarma yace "Waye nan." Take na firgita nace Abba ni ce ban ɗaki zanje haskawa zanyi da wayar Umma. Yace kwan dake banɗakin ya mutune? Nace babu haske dai. Yace "Ɗauka kije." Banɗakin na shiga na kashe hasken sannan cikin rawar jiki na soma neman layin Yaya. Sai a kira na shida sannan ya ɗaga. "Baby lafiya?" Ya tambaya cikin yanayin bacci da kiɗima,. Na ce lafiya lau Yaya, na kasa bacci ne tunaninka ya dame ni. Goben za'a turo ɗin? Cikin matsanancin mamaki yace kije ki kwanta zamu yi magana da safe,na samu kaina da faɗin Yaya ina sonka sosai kaji? Ya ce "Naji Baby na yarda." Nace to kana sona? Yace sosai Baby. "Kije ki kwanta." Nace to Yaya. Na fito na je na maida wayar sannan na kwanta. Ji nake in har banga Yaya ba zan iya rasa rai..A wannan ranar dai ban samu bacci ba. Shamaki ya zauna cike da mamaki yana son ya ƙaryata kanshi cewa Baby ce, kodai ta gane shine Aliyu Shamaki,inhar ta gane to ba shakka zai fasa aurenta duk da irin son da yake mata. Ya soma tunanin abinda ya faru tun daga zuwanshi gidan har tafiyar shi,shin ko yayi wani abu ne ba daidai ba har ta gane. Yakasa tuna hakan,to ko Hajiya ta faɗa mata. Koda ya dawo kai su abinda Hajiya ta ce mishi kawai ka sanar da Alhaji Umaru da kawunka gobe za a tura kamar yadda kake buƙata. Harya tambaye ta ko yarinyar ta cinye jarabawar ne? Tace "Kayi abinda na ce kawai." Ya numfasa bayan ya gama tuno da komai.To
🖊️🖊️🖊️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*
_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a tura shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_
*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_
*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Free Page 7*
Nayi sallar asbahi duk na rasa me ke min daɗi na koma na kwanta sai bacci ya kwashe ni. Jamila ce ta tashe ni tana cewa, baza ki makaranta bane Yaya Baby. Umma tace kar a tashe ki ƙila bakya jin daɗi ne, saboda ta tabbatar in har ki ka koma bacci baya sallar asbahi to baki da lafiya. Na yi miƙa Yaya yazo ne? "Wanene kuma Yaya?" Ta tambaye ni cikin mamaki. Yaya Aliyu mana ko mafarki nake yi ne? Har ma yace a ɗaura aurenmu kawai. Jamila ta saki dariya "Don Allah Yaya Baby ki tashi nikam." Na tashi naje na gaida Umma ta ce Abba ya fita, na ce kuma kin faɗa masa yau ne 'yan gidan su Yaya zasu zo?" Ta ce "Na faɗa masa tun juya da kika faɗa min,.amma kin faɗa masa cewa gidan su Abban Zuhra za su kai kuɗin ko? Kuma Abbanku ya ce,ki tambaye shi ƙarfe nawa zasu zo?" Nace to bani wayar ki in faɗa masa. Jamila ta fito ɗauke da jaka tana faɗin Wallahi bazan jira ki ba,gara ke jarabawa ki ke yau ne ma ƙarshe. Sai lokacin na tuna da batun makaranta. Nace dan ma dai daga yau na gama. Sai da na shirya sannan na ɗauki wayar zan kira amma ba kati,gashi bashi ne cankas a wayar. Na Umma ko kati za'a siyo? Tace "Wa zai siyo kunyi latti ki tafi in kin dawo kya kira shi,abinda nasan bai wuce da daddre za su zo ba, tunda gari ɗaya ne." Na ɗauki biro bana zuwa da jaka tunda jarabawa ce muka wuce.
Hajiya ta kalli Shamaki, "Ƙarfe nawa zasu je su kawun naka?" Ya saki fara'a sai da dare in kowa ya gama sabgar sa bayan sallar Isha'i. Tace "To nawa za a kai?" Yace dubu Hamsin kinsan bana son ta san komai da wur ne. Tace "Akwai gejin da dole su sani, tunda za su yi bincike." Yace haka ne,amma kafin lokacin na samu abinda na ke so. Bayan sallar Isha'i Shamaki ya kwashi su Ƙanin Hajiya da kuma ƙanin mahaifinsa sai limamin masallacin gidansu suka nufi kai kuɗi, saidai tun a hanya ya ce musu ba zai ce suyi ƙarya ba, amma yana son kar su nuna shi mai arziki ne ya faɗa masu komai a taƙaice da kuma dalilin sa. Suka ce insha Allahu za su yi yadda ya ke so. Ya ɗauki waya zai kira layin Ummarsu. Sai lokacin yaga miss call da yawa, ya yi mamakin ina ya jefar da wayar har da Baby ta yi masa wannan kiran haka. Ta ɗaga wayar ya ji muryarta can ƙasa, ta gaishe shi, ya amsa tare da tambayar lafiya ya ji muryarta haka. Tace banajin daɗi ne, yace ashsha sannu, kin sanar da Abba mun kusa zuwa kuma nan gidan zamu zo? Ga mamakin sa sai ya ji tace dan Allah kun taho?" Ya ce kinsan abinda za ayi wasa daban ya ke ko?" Tace dama kiran da nake maka kenan ɗazu dan in faɗa maka Abba ya ce gidan wansa za a je,amma babu nisa daga nan gidanmu bari in kira Abban a waya ya fita yanzu." Yace "To faɗa mishi gamu tafe a hanya. Naje da gudu gurin Umma,nace Umma Yaya sun taho da iyayensa. Tace I kon Allah! Wai kuwa Baby lafiyarki ƙalau yau wane irin hali kika canza ne?" Na ce yi haƙuri Umma. Na koma gefe na tsaya. Umma ta ce sai ki kira Abban naku ki sanar da shi. Jiki na ɓari na kira Abba na faɗa masa. Yace gashi nan dawowa gidan.
Shamaki ya sanar da su wakilan nasa cewa su faɗawa iyayen yarinyar nan yana son auren ne a lokacin walimar saukar karatunsu. Direba ya sauke su bakin lungun ya tambayi Shamaki ko ya jira su? Ya ce e ka jira mana sai ka kai kowa gida sai ka dawo ka ɗauke ni. Yace "To" Abbansu Baby ya fito ƙofar gida ya tari su Shamaki yace ku zo muje can ayi mai gabaɗaya. Suka juya har shamaki. Ƙatuwar tabarma aka shinfiɗa a barandar ƙofar gidan inda dama anan suke salla kuma ana ɗaukar karatu daga gurin limamin da ke jan su sallar maƙocin shi ne. Annan ne Dai suka gaisa cikin mutunta juna sai Shamaki ya miƙe ya ce to bari ya dawo. Tun da aka ce ga su nan na hau ɓare ɓaren gyaran jiki, ina ta kwalliya sam ban damu da yadda Ummanmu ta haɗe fuska ba. Jamila kanta sai da ta tambaye ni wai kuwa lafiya na ke irin wannan abin? Nace me nayi dan kawai na yi kwalliya laifin ne,kar ki manta da daga yau ya zama mijina,kuma kinsan dai matsayin yiwa miji kwalliya ko?
Cikin
"Matsananci mamaki Jamila ta ce "Yaya Baby wai ina kunyarki da kawaicinki suka tafi ne?" Wallahi karki fara kice za ki ke irin wannan rawar kan, wai baki lura ma da yadda Umma ta ke jin haushin canzawar ki tun jiya ba?" Na ce ni banga wani canzawa da na yi ba. Kafin Jamila ta ce wani abu Muryar wani yaro ta ratso cikin kunnuwanmu yace ana sallama da Baby, cikin rawar jiki na ɗauki mayafi na zira takalmi ina faɗin Jamila ki kawo mana tabarma. Umma tace "Baby ki zo nan." Na nufi gurin ta a ƙofar ɗaki kan tabarma na ce ga ni. Ta ce, "Kinsan daga Allah ba wani in har baki haɗa min hankalin ki guri ɗaya ba zamu samu matsala da ke, tun jiya sai wani shashanci kike yi girma hauka ne? Wato kin riƙa kin so aure shine ki ke wannan rawar kan, dama rashin samun saurayin ne ya sa ki ka nutsu kamar ta Allah ko?" Na sunkuyar da kai ina faɗin Umma dan Allah ki yi haƙuri ni ban fahimci me nake yi ba,yanzun ma Jamila ta gama min faɗa wai na canza. Na daina Umma. Bari inje yana jira. Ban jira me Umma zata sake faɗi ba na yi waje da sauri har ina tintiɓe. Umma da Jamila dai abin har tsoro ya ba su. Ina fita yana jingine inda ya saba tsayawa, na isa da sauri ina faɗin sannu Yaya da zuwa. Yaya ce "Sannu Baby " Na gaida shi ya amsa. Na ce Yanzu sun can ana maganar aurenmu? Ya ce e na rungume hannuwana tare da ɗan tausaya wa ina faɗin Alhamdulillah Naji daɗi Yaya zan iya bacci in aka ɗaura mana aure kuwa? Mamaki ya hana Shamaki magana,duk da cewa shima fa yana jin wata ƙaunarta a zuciyarsa wadda bazata misali ba. Ta katse mishi tunani da faɗin lokacin walimar tamu za a saka ko? Yace ban sani ba gaskiya haka dai nace su tambayar min." Nace Kaga Yaya, asa hakan wallahi na yafe lefen, kuma kayan ɗàkin ma zan faɗawa Umma ba takura ko? Yace "Sai ki iya faɗa mata haka baza ta ga cewa kinyi rashin kunya ba?" Nace to wai me na ke yi ba daidai ba? Tun jiya ake cewa wai na canza ina ta zumuɗi, kuma ni ina jin wani sonka ne bansan ya zan fassara maka abin ba. Ina samun nishaɗi da jin daɗi ne kawai in naji muryarka, da na kira baka ɗaga ba har kuka fa na shiga ban ɗaki na yi, sai ina ji a jikina kamar zaka fasa. Yace "Gaskiyar magana kin canza gaba ɗaya kamar ba ke ba. Nima dai ina mamaki." Nace to Allah ya sa dai su amince shine damuwata. Yace "Ya maganar walimar ku?" Na yi ɗan jim sannan nace tana nan, amma gaskiya dai zaka zo min ko,duk da masana