Showing 18001 words to 21000 words out of 27913 words

Chapter 7 - HAMSHAƘIYAR UWA Book (1).

05 Jul 2024

3326

cewa kana cikin shirin biki lokacin ai na san zaka so ka ga karatu na. Yace in sha Allah zan zo sannan karki saka a ranki cewa dole sai lokacin da muka ce, in basu yarda ba dole mu jira lokacin da suke ganin ya fi." Na ce Ni fa damuwata kada ka zo ka ce ka fasa, wallahi zan iya mutuwa har lahira. Yace Baby in kinga na fasa aurenki wallahi na mutu ne,matsawar ina numfashi bazan fasa ba. Daɗi ya rufe ni, nace Allah na gode maka. Munata tattauna batun soyayyarmu na ga Abba ya zo ya shiga gida. Ya ce bari inje in sallame su, ki koma gida zan dawo nace to. Na shiga gida don inji yadda suka yi. Anan na samu Abba yana ba Amma labari ya zauna genen tabarmar da yake kai har Jamila ta kawo masa abinci. Yana faɗin "Wato Salamatu Allah ya amshi addu'armu ya kawo wa Jamila mijin ƙwarai ba sai mun bincika komai ba sun wanke shi tas. Limamin Unguwarsu inkinji yadda ya ke yabon sa abin zai baki shi'awa ga neman na kansa ga alheri duk sun yabe shi,ƙanin mahaifiyarsa da ƙanin mahaifinsa banda albarka babu abinda suke sa masa. Kuma sun nemi alfarma ko za a sa aure tare da walimar saukar su nace a a saboda yanayi shima kar ya takura kansa muma haka, amma sai suka dage kan cewa gaskiya yana buƙatar aure sosai kafin nan da azumi. Sanna duk abinda ake dashi bashi da wata matsala akai wa yarinyar. Na ƙara kaso kunne inji me Umma zata ce. Sai naji tace, Gaskiya a sa shekara ya yi haƙuri dan shekara kwana ce Abban Baby, bikin 'yar fari ba mu yi mata komai ba ai sai mun shiga bakin duniya. Ban san lokacin da nace Umma zai fasa inhar aka sa shekara,ni dai gara lokacin da yace ɗin dan in ya fasa mutuwa zany.... Saukar ta kalmi da naji a fuska ta shine ya tuna min cewa bai kamata in tsoma baki a zancan aurena da mahaifana su ke yi ba. Na lalle su dan in gane waya jefe ni,sai naga ashe Umma ce, sai huci take ta rasa abin faɗi dan takaici. Shi kuma Abba ya sunkuyar da.kai, sai suka bani mamaki, domin a magabata banga wani abu na tashin hankali ba, na faɗa musu abinda ni nake so ne, kuma dai su iyayena ne wazan fadawa halin da zan samu kaina in an fasa. Sallamar wani yaro ce ta ratsa shirun da gidan ya yi kamar mutuwa ta gifta, Abba ya amsa sai yaron yace "Ance Baby ta zo." Na tashi da sauri na shuri takalma sai da na kai bakin soro sai na waiwayo dan naji a jikina ni suka bi da kallo dama na zargi haka. Na fita ina tunanin ko dai na kuma wani laifin ne? A fili nace garama amin auren in tafi tunda har sun soma gajiya da ni. Na isa gunsa ina faɗin yau Jamila ta ƙi kawo mana tabarma. Yaya sun tafi ke nan? Ya ce "Sun tafi." Nace amma sun faɗa maka komai yadda aka yi? Yace "bakiji ba da Abba ya shigo?" Na ce Banji matsaya ba a maganar na saka musu baki Umma ta jefe ni sai kuma suka yi shiru. Yace "Subhanallah! Me zai sa ki saka bakinki cikin managarsu?". Na ne Yaya Shekara fa Umma ta ce, kuma kai nasan baza ka shekara bada matarka ba. Yace Banda haka Yaya nima ba zan iya ba. Yace "Baby bai kamata ba kina saka baki a maganar manya. Hajiyata tana da zafi in kinje kina mata irin wannan za ku samu matsala wanda hakan zai kawo matsaloli a cikin zaman aurenmu. Ni kuma bana son a ce ni da ke mun rabu, saboda akan Hajiya zan iya komai. To gaskiya in kina son mu daidai ta ni da ke, to sai kin sawa bakinki linzami in manya suna magana babu ruwan ki." Na sunkuyar da kai, insha Allahu na dai na. Nima jiya ne suka fara wannan kukan da ni,amma bana yi, ko yanzu a maganar ka kaɗai suke cewa na canza. Ni kuma banga canjin ba. Ya ce "Nima na gani dan haka ki dawo kan hanya. Nace to, amma kai ai zamu iya tattauna maganar aurenmu ko? Ya ce "Sosai ma kuwa." Nace to yanzu faɗa min yadda aka tsaya. Yace Abba sunce za su yi shawara, domin shima Wan Abba cewa ya yi tunda na ce abinda ake dashi a kawo ki ba matsala to na shi ganin gara a yi bikin kawai. Shine aka ce a shawarci Ummanki. Nace to Umma tana kiran shekara. Yace Allah dai ya zaɓa mana mafi alkhairi. na ce ameen. Yace "Ni ma dai ya kamata in tafi, da har zan wuce, sai kuma nake tunanin ban muyi sallama ba." Nace yanzu sai yaushe? Yace, "Bazan sa lokaci ba gaskiya tunda an bani ke. amma kowane lokaci za ki iya gani na. Zan bada waya a kawo miki saboda za mu ke yin magana akai akai. Nace "To ɗan Allah kar ka manta da Ni kaji. Ya yi yar dariya sannan ya yi ƙasa da murya, ashe zan mantà kai na. Ina mugun sonki Baby. Cikin farin ciki nace ina sonka Aliyuna. Sai kuma naji kunya na saka hannu na rufe fuskata. Muryar Abba naji yana cewa "Malam Aliyu bari in baka saƙo ka faɗawa magabatan na ka.". Aliyu ya ce to shiga gida sai kin ga saƙon na ce to ka gaida su Hajiya da su Anisa. Na laɓe a soro ko zanji me za su faɗa amma banaji. Dole na shige ciki Umma harta kwanta na leƙa ɗakinta ina yi mata sannu, ko dai ta yi banza da ni, ko kuma ta yi bacci. Na fita na je na saka tuwo na ɗebi ruwa a kofi na shiga ɗakinmu na zauna ina ci. Jamila ta shigo da shirin baccin ta, tace Yaya Baby ki sa su Jafar su yi fitsari in kin gama, yau duk ni na yi aikin ki a gidan nan." Na ce me kika yi nawa da zaki faɗi haka?" Ta ce "Ni na tace gasara kuma na kammala komai." Na yi 'yar dariya. Ni da zan tafi ma gidan mijina daga can zan ke zuwa ina miki akin? Jamila ta yi gialala ta na kallona,sannan ta ce, gaskiya Yaya Baby abinki ya soma wuce tunani, kuma ko a jikin ki. Na kalleta Ni Kuma ke kike bani mamaki, ko da yake na miki Uzri bari ki faɗa soyayyar za ki gane abinda ya same ni. Tace haka ɗazu ki ka yi ta rera wakokin soyayya a gidan nan ke da ko wani ya yi waƙa sai kin masa wa'azi." Na suɗe robar ina lashe hannu, na ce duk ba wannan ba, faɗa min abinda su Umma suka yanke da na fita. Abba ya tsorata da yadda ki ka yi,Ya ce Umma ta yi haƙuri ayi bikinnan a haka yadda ki ke yi ya nuna kin matsu da aure,abinda aka samu a kai miki. Daƙyar Umma ta yarda domin har abin sai da ya kai su kamar za suyi sa'insa, daga bisani Abba ya lallasheta. Amma tana ciki da ke,zaku gauraya da safe. Na ɗanyi jim har ga Allah ni banga abin laifi ba amma dole in ke yin shiru dan in samu zama lafiya. Na dubi Jamila wadda ta kwanta tana ƙokarin rufa. Na ce amma ya suka yi matsaya a ƙarshe. Ta ɗago kai zakiji a bakin Umma da safe, shawarar da zan baki kuma ita ce, ki bawa Umma haƙuri, sannan ki daina magana sam in ana zance.Na miƙe tare da faɗin zan kula sosai. Da safe Umma bata amsa gaisuwa ta ba,to nan ne fa hankalina ya tashi na soma kuka ina bata haƙuri, tace haƙurin me zaki ba ni, ni a su wa ɗanwake a Otal ba dai ɗa namiji bane Baby Allah ya bada sa'a." Na ce Umma wallahi ni fa bansan me zance miki ba ne, kiyi haƙuri na tuba don Allah.Abba ku yi haƙuri ni ban san cewa ba a magana ba. Ya ce tashi kije ki yi aikin ki ta haƙura. Na fita ina sharɓen kuka. Ina jiyo Abba yana baiwa Umma baki, tare da nuna mata cewa ƙuruciya ce,kuma mu godewa Allah Salamatu da ya bamu yara masu kamun kai da nutsuwa, duk tsukunnan yaban su ake Allah ya sa musu albarka karki fusata Allah shine mai rufin asiri abar auren a lokacin da aka sa shi. A ranar wani matashi ya yi sallama muna Islamiya anci sa'a Abba yana gida . Suka gaisa yace Aliyu ne ya aikoshi da saƙo ya baiwa Amira. Abba ya amsa waya ce sabuwa a kwali sai layin da kuma kati wanda ya ce ace in ta saka ta kira shi. Abba ya ce to insha Allahu za a bata, taje islamiyya. Na yi murna sosai lokacin da muka dawo. Umma ta ɗan saki jiki harma ta karɓi wayar ta sa albarka. Tace ki kula irin wannan ta shafawar ba wuya ta fashe. Na ce to. Na saka layi na sa katin na shiga ɗaki na kira wata Number ɗaya daga cikin lambobin da ke jikin wani kati da ya sako a ciki kwalin. Wani ya ɗauka, nace Aliyu nake nema. Yace mai gida baya nan ya yi tafiya. Nace Shamaki fa na ke tambaya? Yace nima shi nake magana ya tafi China ɗazu. Na ja tsaki sannan na kashe waya, ina faɗin Ni Aliyu na ko filin jirgi baya zuwa bare wata China. Na sake ɗakko katin don in duba wata Number. Sai naga ya yi wa wata lamba alama da biro a ƙasa ya rubuta ki kira wannan layin. Cikin sauri na saka na kira. Ya ɗaga "Baby zan kira ki kinji?" Na ce to Yaya na gode, ina jira fa ka kira ni fa. Yace karki damu. Haka dai abubuwa suka ci gaba da tafiya, iyayena suka tada hankali gurin neman kuɗin da za a yi min kayan ɗaki aure saura sati uku da 'yan kwanaki. Umma ta sanar da Baba har Kurna taje,Baba tace Allah ya sa hakan ya zama alkhairi, abinda za ayi yanzu zata sa akama Awakinta guda biyar a saida su, a zo a karɓa a sai min kayan kicin kuma zata sanar da sauran dangi. Shi kuma Abba an sanar da dangi sun nuna murna amma da suka keɓe sai ƙanwar Babanmu Saratu wadda dama basa shiri da Umma tace "Shi Abbana su Babyn da ya kama ya sa rana sati huɗu kila ya tanaji kuɗin da zai yi mata kaya da na abinci da za a dafa. Dija tace Nima dai na yi mamaki muna neman gudunmawar sauka mu bashi, shi kuma ya na tataro aure abinda Allah ya ba ni shi zan bada. Saratu tace ita matarsa dan hauka gata da tsohon ciki shine ta yadda da wannan gangancin koda yake ƙila ma ita ce tace a saka dan a ce yar ta ta riga 'yay'anmu aure. Dija tace ko wane kwashe ne kuma zai ɗebi wannan yarinyar kamar taɓarya oho. Matar waliyin ta taɓa baki tare da faɗin jiya da na shiga murna ai na ga 'yar da wata ƙatuwar waya wai saurayin ya aiko, shiko Abban su Zuhra sai rawar kai shi ga waliyyi nace dubu goma dai ya baka abikin Ummi dan haka sai ka nemi shabiyu kar kaji ance waliyyi ka fara neman siyan gado. Suka sa dariya gara dai ki faɗa masa dan ga sunan riɗa riɗa duk wadda ta samu shima hidimar ce a gaban sa. Haka suka yi ta maida zantuka ta re da alwashin zura ido su ga abin da zai biyo baya.
Har kwanaki biyu ina jiran kiran Yaya, Ni kuma inna kira bata shiga. Hankalina duk ya tashi amma babu dama inyi maganar sai Jamila kawai inna faɗa mata sai ta ce bani da aji wai in jira ya kira ni. Ranar kwana na uku ina zaune a kan tabarma a tsakar gida ina rubuta sunayen waɗanda zan kaiwa katin sauka 'yan uwa da yan makarantar bokonmu. Jamila na ke kira ta raka ni. Umma tace to kuma yaushe za ki kai na 'yan Kurna? Nace sai mu kai ranar Lahadi ko asabar tunda bata da Boko sai muje. Umma tace hakan ya yi saura ku kuma zuwa wani gidan nace imsha Allah babu inda zamu ƙara zuwa. Wayata ta soma kiɗan na ɗauka da sauri. Sanyin zuciyata, haka na rubuta a lambarsa. Na tashi na shiga ɗakinmu. Na ɗauka da sauri. Cikin shagwaɓa na ce sanyin zuciyata shine ka ƙi kazo ko? Yace "My Baby ki yi hakuri tafiyar gaggawa ta taso min." Nace na kira wata lamba aka ce ka tafi China . Yace a a Kaduna na je ina can har yanzu aka wasu kayanmu. Nace to Allah ya tsare shiyasa nace ni Aliyuna ko filin jirgi bana zaton ya taɓa zuwa. Ya yi dariya "Na taɓa raka maigada ba so ɗaya ba ma. " Nace Allah ya sa kai ma wata rana in raka ka. Yace "Ameen Allah ya sa mu hau jirgin tare. Na ce ameen. Ya ce "To ya ake ciki menene labari?" Nace wanne zan baka?" Yace "Sabo wanda ya ke tashe." Na ce kati zan kai in raba na sauka in Jamila ta dawo. "To kuma na bikin yaushe za araba?" Ya katse ni. Kaga karka wani damu da katin Biki duk kashe kuɗi ne, karatun saukaramu asabar ne ɗaurin aure Lahadi sai a faɗawa kowa a haka. Yace "Taɓ aurenmu ace ba kati Baby ko bashi ne ni zanci don in buga mana katin biki." Don Allah karka ci bashi a zo ana sallama da kai. Na faɗa cikin shagwaɓa. Yace "Ai misali na yi.
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo evidence ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ɗora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*


*Free Page 8*


Abubuwa sun kankama lokaci yana ta ƙaratowa Munafinci ba ga maƙota ba ba kuma ga dangi ba. Umman su Fati har gida ta zo wai Allah ya sanya alkhairi amma harda cewa Umma ashe ku da tanajin ku,auren Fati sai bayan Babbar salla mu masu ƙaramin ƙarfi. Umma tace Allahn da ya kawo mijin a lokacin da masu gori suke gori shine zai kawo abinda zamu kai mata. Ina jinsu Umman su Fati aka wuce ana borin kunya. Umma tace Allah kai zaka yi mana wannan lamari Allah ka taimake mu. Sauran kwana huɗu walimarmu kwana biyar kuma a ɗaura mana aure. Yaya ya aiko min da katan Lemo guda biyar wai na walima a daran ranar ne ya zo gurin Abba ya nemi alfarmar a ɗaga aurenmu zuwa wani satin. Walimarmu da sati ɗaya kenan. Abba yace ba damuwa, ya shiga ciki ya sanar da Umma sannan ya ce in fito. Mun gaisa yake faɗa min wai gyaran banɗakin gidan za'ayi shine dalili. Na ce to Allah ya kaimu, amma banso haka ba,yace kamar yau ne. Yanzu ki faɗa min me da me kike buƙata a gurina. Na dube shi, kamar na me? Yace "Kuɗin lalle da pati ko baza ki yi ba?" Nace zanyi amma kana da kuɗin ne? Yace Inkinji makaho yana cewa a yi wasan jifa ai ya taka dutse ne ko? Ki lissafa min duk abinda ki ke so na biki zan miki daidai ƙarfina." Nace to kana son mu kira DJ ko baka son kiɗa? Ya yi 'yar dariya. Kinga Baby zan kama miki ɗan wuri ku yi party da ƙawayanki amma banda maza." Na zaro ido karka matsa wa kanka, kila Abba ma ya ce baza a fita party ba. Kawai zan yi DJ na a can filin,na nuno mishi da hannu. Ya kalli gurin "Shikenan zan sa a zo a sa kujeru." Na ce to na gode Ubangiji Allah ya bada yadda za ayi. Yace Ameen ina jin daɗin addu'o'in ki. Zan tafi ki tura min sauran abubuwan ta text,sai in kawo miki ko?" Na ce to yawwa dama zan tambaye ka ko zan iya buɗe Whatsapp? Yace wannan ki bari sai an kawo ki zan buɗe miki da kai na." Na yi murmushin tare da faɗin na gode. Na ce yawa jira ni ina zuwa. Na shiga gida da sauri,na ɗakko katin saukarmu na ɗakko na kawo masa, nace ga shi don Allah ka zo, tunda ma an ɗaga bikin ai dai zaka zo ko? "Insha Allah zan zo, ki shiga gida zan aiko miki da katin auren shima sai na party ki rubuto min yadda ki ke son ya kasance." Zan yi magana ya ɗaga min hannu,kar ki ce komai shiga gida." Na ce to sai da safe.Har na juya yace, yawa na tuna "Baby!" Na waiwayo, ki faɗawa Abba za a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login