Showing 1 words to 3000 words out of 19716 words

Chapter 1 - ƘURARREN LOKACI (COMPLETE) BY K_SHITU

Unknown   

28 Jun 2024

2869

ƘURARREN LOKACI


KHADIJA MUHD SHITU
WATTPAD@KSHITU.

Ƙirƙirarren Labari Haƙƙin Mallakata ban yarda ayi amfani da shi ko chanja shi ta kowace siga ba tare da sani na ba.

Bismillahir rahmanir Rahim.

(1).
“Ranar da Dr Jabir ya tabbatar min Imaan ba zata ƙara wata ɗaya ba a duniya za ta mutu, Na ji a raina komai ya fita da raina na tsani rayuwata na tsani kowa da komai, Raina ya sosu na bar Asibiti ina kuka bugun zuciyata yana fita da raɗaɗin ɓacin rai”

Ko a mafarki ban taɓa kawo ma Raina Imaan mutuwa za ta yi ba. Zuciyata ta dinga ayyana mun Na kashe kaina, Ilhaam ba zata iya jurar ganin Imaan cikin wannan yanayin ba.

Ban san ina zan dosa ba, Na dawo gidan ko sallama ban iya yi ba sai kuka da na shigo mata da shi.

Hankalinta ya tashi sosai ta ruɗe tana tambayata Ilhaam me ya ya faru ki faɗa min kar zuciyata ta buga.

Na durƙushe bisa gwiwoyina ina raira kukan da nake jin raɗaɗinsa har cikin ruhina.

Ta yi juyin duniya na yi magana na kasa sai kukan da nake yi wanda ya tabbatar mata lallai akwai matsala.

Sai itama ta fashe da kukan Sosai, Muka rungumi juna muna sake fashewa da kuka.

Ita ta fara tsayar da nata kukan ta dinga lallashina da daɗaɗan kalamai. Imaan tana da kyakkyawar zuciya da lafazi mai tasiri.

Kalaman Ummah ne suka dakar mini zuciya, Jikina har kyarma yake yi “Da kika Tasa ta a gaba kina kuka dan Ubanki warkar da ita za ki yi ne?” “Ummah kika ce me?”

Jikina har kyarma yake yi na ce, “Ba zan warkar da ita ba amma zan iya musayar rayuwata da tata”
Cikin tsananin mamaki take dubana dan bata zaci zan iya faɗa mata magana haka ba. Imaan ta dafe kai cike da tsoron uƙubar da zata biyo baya.

“Ilhaam ni kike faɗa wa magana haka dan uban ubanku?”

“Eh na faɗa miki ki yi duk abin da kika ga za ki iya yi, Ke Imaan tashi”. Yanda na yi magana ba sai na faɗa ba ɓacin raina a bayyane yake zuciyata tafasa kawai take.

“Wallahi daga yau ni Khadija Ilhaam ba zan sake bauta a cikin gidan nan ba bare Imaan! Ba zan sake ɗaukar kowane irin cin zarafi ba, Zan iya aikata komai a kan Imaan”.

Ba ita Umman kawai ba hatta Imaan ta girgiza da jin furucina.

Na kama hannunta na miƙar da ita tsaye.

Ban bata damar magana ba na shiga ɗaki na ɗauko mata hijabi na sanya mata. Bata iya ce mini komai bai sai hawayen da suka turu mata a ido.

Na kama hannunta na riƙe gam muryata na rawa na ce, “Umma za mu tafi ba zamu sake dawowa ba har abada kuma ba zan taɓa mantawa da zaluncinki da Azabtarwarki a gare mu ba, zaki yi Nadama a Ƙurarren Lokaci da duk wanda ya lalata mana rayuwa..”

Muka fito ni da Imaan tana kuka sosai.
Ita ba dutse bace dole duk rintsi ta gaza,dan haka bata ce da ni uffan ba. Muka tsayar da Ɗansahu.

Babbar Tasha na ce ya kaimu Cikin Adaidaita babu wanda yay magana daga ni har ita sai ajiyar zuciya da nake saukewa Imaan na kuka sosai.

Lokacin da ya ƙaraso tashar muka sauka sai kuma kallo ya dawo kanmu dan ko sisi babu hannuna.

Muna tsaka da hatsaniya Allah da nashi ikon ya jeho Alhaji Tahir Yusuf Ɗankwangila.

Ya fito cikin danƙareriyar motarsa ya ƙaraso gare mu yana jin ba'asi ya biya kuɗin.

Na sha Jinin jikina ganin sa da na yi amma na dake.
“Ilhaam ya jikin Imaan ɗin ko zamu je na taimaka muku?” Gaba ɗaya a rayuwarmu bama da zaɓin da ya wuce bin sa na ce,
“Mun gode” a hankali cikin sanyin murya. Muka shiga cikin motarsa.

Babu alamun nadama tattare da ni ko fargaba na janyo Imaan muka sauka daga motar dan zuciyata ta bushe.

Madaidaicin gida ne ɗan daidai muka shiga ya nuna mana ko ina. Bamu yarda Zamu zauna ba sai da ya tabbatar mana da babu Sanin Ummah ya kawo nan ɗin.

Alƙawari muka ƙulla na aurenshi, shi kuma zai mallaka mini duk adadin dukiyar da nake buƙata sannan zai bamu damar hutawa har Imaan ta haihu.

Na amince masa kai-tsaye ina jin sanyi a zuciyata. Ko babu komai zan bawa 'yar'uwata lokacina da kulawata irin wacce bamu samu daga iyayenmu ba.

Na sani ba zan taɓa samun matsala akan Masoya ba sai dai matacciyar rayuwa ce bana buri.

Ban sake tada mata kowane zance ba.

09117440993
K_shitu🦋.


ƘURARREN LOKACI

HIKAYA@KSHITU.

(2).
Ban sani ba, a rayuwarmu sa'a ce bama da ita ba ko kuma Ƙaddarar rayuwarmu ce tazo a haka.

Mun ci gaba da rayuwa cikin gidan Alhaji Tahir. Tun da naga hankalinmu ya kwanta babu wata mtsala na ɗan kauda maganar Dacta Jabir a raina tunanina ya ta'allaƙa ga ciwonta. Ban taɓa fita ko ƙofar gida ba haka Imaan har haske ta yi sosai mai ɗaukar hankali da 'yar ƙiba ta samun kwanciyar hankali, Burina bai wuce ta haihu lafiya ba.

Ranar wata Asabar da safe na shirya cikin doguwar riga cikin siyayyar da Alhaji yay mana, Na ce da ita ta kula zan shiga gari na dawo.

Na fito fuskata lulluɓe da niƙabi. Na nufi Asibiti don ganawa da Dr Jabir domin ko da yaushe zuciyata cike take da matsananciyar fargaba da ruɗu.

Mun tattauna sosai akan matsalar Imaan na fahimci inda ya dosa. Sai dai bayaninsa na ƙarshe ne yay matuƙar ɗaga mun hankali.

“Ilhaam so nake ki fahimta Cutar da take ɗauke da ita tana da hatsari ga ciki a jikinta, Baku fara neman magani da wuri ba bata samu kyakkyawar kulawa ba, damuwa ta yi mata yawa sosai jininta ya hau fiye da zato Ubangiji ne ya ƙaddara ba ku da rabon wahala”

“Haba Dr Taya kai ko da yaushe baka faɗin Alkhairi, Shi kenan idan ƙaddara ta sami mutum yana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki a dinga saka masa mutuwa. Babu komai”

Na miƙe cikin ɓacin rai na bar ofis ɗinsa.

Babu inda zan iya zuwa dan ko ƙawa bama da ita daga ni sai 'yar'uwata muke rayuwa.

Na shigo gidan na tarar da ita zaune ta yi tagumi tayi zurfi sosai cikin tunani har na zauna kusa da ita bata motsa ba.

Ban san sa'adda hawaye suka wanke mini fuska ba, Ina tsananin tausayin imaan fiye da zato ko tsammani ƙaunarta a raina da zuciyata ba zata ƙayyadu ba Allah ne ya dasa ta.

Na kama hannunta a hankali cike da matsanancin tausayinta da ke ratsani.

“Ki yi haƙuri, Ki yi haƙuri Imaan! bani da magani sai Allah shi zamu gayawa kukanmu ban san yaya zan yi da raina ba ko da yaushe a rayuwa ke ce fatana ina son ki samu waraka, ina son farin cikinki fiye da nawa bana son kina jefa kanki damuwa, Ki jure don Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe kin ji ko”

Ta share mini hawayen fuskata, Ta ƙawata fuskarta da murmushi mai kyau wanda har duniya ta naɗe ba zan manta da shi ba.

“Ilhaam ina sonki tsakanina da Allah. Zaki yarda da ni? Ban taɓa damuwa da halin da nake ciki kuma ba zan taɓa ba wannan ita ce Jarabtarmu. Ke ce mafarkin rayuwata da komai ina kuka da ne damuwa akan halin da zaki shiga bayan ba ni. Duk yadda ubangiji ya tsara mana rayuwa mu yi haƙurin akwai riba a gaba. Jikina yana bani ba zan rayu ba, Idan har Allah yayi ikonsa na haifi abin da yake cikina na bar miki duniya da lahira Allah ya tayaki riƙo, Kar ƙauna ta rufe idanunki ki kasa bashi tarbiyya Ke ce mahaihiyarsa Ilhaam”

Kuka sosai ya ci ƙarfinta ta dinga shi kamar zata shiɗe tana tari. Zuciyata na mun raɗaɗi sosai na kasa tsayar da nawa kukan.

*
Duk da Zuciyata bata aminta da Alhaji Tahir ba amma ina kyautata masa zato.

Cikin barcin da ya fige ni nake jin ana yamutsa mini kaya amma tsabar nauyin barci ko motsi ban yi ba sai da na ji an kamar an ɗauki sannan na fara mutsu-mutsu. Buɗe idon da zan yi dishi-dishi na ga abin da ya harba mini zuciyata da ƙarfin gaske.

Ya kulle ɗaki da mukulli ya jefa aljihu sannan ya dire ni saman gado.

Na buɗe idanuwana tangaram ƙirjina na duka.
Cikin wani irin ɓacin rai da ɗacin zuciya na ce, “Alhaji miye haka?”

Ya ƙyalƙyale da dariya.
“idan baki gane ba, Ina son fanshe wahalar da na muku, Idan baki bani haɗin kai ba wallahi saina kashe ki kuma na kashe banza”

Ya zaro bindiga ya saito ni da ita cikin tsantsar mugunta.

#Khadija Muhammad Shitu.

#09117440993.
#Free book.

(Ku yi haƙuri da typing ɗin haka, Idan na samu hali zan dinga baku update sau biyu.)


Share Please!♥️


ƘURARREN LOKACI

KSHITU@WATTPAD.

(3).
Irin yanda zuciyata ke bugawa ji nake kamar zata faso ƙirjina ta fito. Jikina ya ɗau karkarwa sosai.

Ya matsoni cike da rashin imani yana nufo ni na ci gaba da ja da baya cikin matsanancin tsoro. Ya yinƙuro cike da kuzari irin na namiji ya damƙo gashin kaina da ƙarfi ya buga ni bisa gadon ya fara kiciniyar raba ni da suturar jikina.

Ba zan iya misalta irin tashin hankalin da na shiga da ruɗu ba jikina ya dinga kyarma bugun zuciyata ya dinga fita da sauti har cikin ƙwaƙwalwata.

Na iya ƙoƙarina wajen son ture shi amma na gaza ƙarfinmu ba ɗaya ba.

Ya riga ya danne ni ko numfashina da ƙyar yake fita. Lokacin da yay nasarar yage mini riga na ɗauke numfashina tare da runtsa idanuna sunan Ubangijina kawai nake ambata.

Imaan ta dinga buga ƙofar da dukkan ƙarfinta tana kiran sunana. Bai dakata ba ya ci gaba da ƙoƙarin cimma nufinsa.

Bugun da ta yi ma ƙofar sosai ne ya sa ta ƙwala ƙara da kiran sunana.
“Ilhaam!!” Tasirin muryarta a zuciyata da ruhina daban ne, Na buɗe idanuna da ƙarfi ina saka dukkanin ƙarfina na ƙarshe na bankaɗe shi gefe ɗaya.

Na waiga gefena cikin kyarmar jiki na ci karo da kwalba na ɗaga ta da ƙarfina ba tare da ya tsammata ba na rotse masa bisa kai.

Ya fasa gigitaccen ihu ya zube ƙasa jini na tsartuwa. Jikina na kyarma na doshi ƙofa da zummar buɗewa, Ya taɗo ƙafata na faɗi ƙasa goshina ya daki tayil na saki ƙara na rarrafa da ƙyar saboda sarawar da kaina ya mini, na ɗauki mukullin da ya ɓille ƙasa na buɗe ƙofa cikin tsananin tashin hankali.

Durƙushe na ganta tana kuka ƙasa ta kasa tashi. Tana gani na ta yi zumbur ta miƙe hannunta riƙe da taɓarya ta faɗa ɗaki.

Ta daddage ta buge masa a kai, Ya saki ihu mai sauti ina ƙoƙarin riƙo ta ta sulale ƙasa jini na bin ƙafafunta.

Numfashina ya fara fita a sarƙe na durƙusa gabanta ina jijjigata na saki kuka mai sauti. Da hasken ɗakin na kalli agogo ƙarfe Biyu da arba'in na dare.

Numfashinta na fita sama-sama, Na fara ƙoƙarin tayar da ita amma na kasa na sake fashewa da kuka mai tsanani cikin tashin hankali gabana na tsananin faɗuwa.

Jini na ga ya biyo ta hancin Alhaji daga nan bai sake shurawa ba. Cikin kyarmar jiki na miƙe Waya na ɗauko ɗakinmu ina tunanin duk duniya wa muke da shi da zai tallafa mun. Dacta Jabir ne ya faɗo mini a zuciyar hannuna na kyarma na danna masa kira five miscalls na masa amma bai ɗaga ba.

Na durƙushe ina raira kuka cikin ɗacin zuciya.

Ƙaran kiran wayar ne ya sa na miƙe da kyarmar jiki na ɗaga wayar muryata na rawa na soma masa magana.

“Dr ka tausaya mana ka taimake mu Dan Allah imaan zata mutu muna Saulawa..”

Yanda maganata ke fizga sosai da ƙaraji alamun Rikici ya sa shi datse kiran ko ɗankwali ban ɗauka ba na jawo Imaan har parlour na datso ɗakin da yake ciki.

Ko mintuna goma ba a yi ba na ji bugun gida, Ban yi wata-wata ba na buɗe masa.

Da taimakonsa muka shigar da ita mota Ya tada ta da gudu Muka shiga asibiti aka wuce da ita emergency room.

Na dinga kai-kawo ina addu'o'i, Sai da Wani likita ya jani ofis ɗinsa sannan na ɗan samu natsuwa.

Maganarsa ta ƙarshe ce ta ɗaga mini hankali sosai.
“Ba zata iya haihuwa da kanta ba, Jininta ya hau sosai sai dai ayi mata surgery idan akwai wani naku namiji muna buƙatar sa hannunsa.”

“Bamu da kowa Doctor ka taimake mu ka saka hannu a madadi don Allah”

Ya amsa mini sannan ya ce na jira sa a office ɗin ya bar ni nan zaune.

Sai da gari ya fara haske sannan ya dawo jiƙe da gumi fuskarsa cike da Alhini. Na jera masa tambayoyi “Yaya Dr an yi nasara tana lafiya me ta Haifa zan iya ganinta?”

Wata Nurse ta shigo Hannunta ɗauke da Jariri lulluɓe da towel. Sai dai fuskarta babu walwala, Ta miƙo mini yaron ta juya ta fice. zuciyata ta buga gabana ya faɗi.

Na sake jefa masa wata tambayar.
“imaan fa zan iya ganin ta??”

Mu zauna zan miki bayani.
Ya zauna bisa kujera nima na mara masa baya.
Na zuba masa idanuna ina kallonsa zuciyata kamar zata faɗo.

“Ilhaam dan Allah ki yi haƙuri kin san..” Na saki jaririn ƙasa ya challara ihu na fice da saurina kaman zan kifa na faɗa Ɗakin da aka shiga da ita na tsaya gaban gadon da take. Dr jabir ya haɗa abin zuƙo numfashi ya danna mata a ƙirji ta ja numfashi.

Yay tsaye hankalinsa a tashe kamar an dasa shi.

“Imaan ki tashi Don Allah Ilhaam tana miki magana, Na roƙe ki” Hannunta da naga ya motsa na kama ina kuka sosai ina jijjigata.

Fuskarta ta yi wani irin fayau sosai.
Ina jin sautin muryarta na fita a hankali, “Ilhaam, Ilhaam ina K’aunarki!!” Kalamin da ba zan manta da shi ba har zuciyata ta daina bugawa.
“La'ilaha illallahu Muhammad..” maganar ta yanke idanuwanta suka rufe ruf hannunta ya sake.

Na jijjigata ina kiran sunanta amma babu alamun zata tashi.

Daga nan ban sake sanin a wace duniya nake ba.

Khadija Muhammad Shitu.
09117440993.

(😰💔.)

Share Please!♥️🌝
ƘURARREN LOKACI

HIKAYA@KSHITU.

(4).
Irin yanda zuciyata da ƙwaƙwalwata suka taɓu abin ya matuƙar girgiza likitocin.

Satina guda a asibitin bana cin komai bana magana sam babu abin da zuciyata ke juya mini
Komaina ya tsaya chak.

*
Yau tun da na tashi zuciyata ke juya min abubuwa da dama, Na miƙe zaune daidai lokacin aka turo ƙofa.

“Sannu Ilhaam” Dacta jabir ya ce yana zama.
Na gyaɗa kaina ba tare da na ce komai ba.

Cikin kulawa yake mini magana.
“Dan Allah ki yi haƙuri komai ya wuce an sallace ta, mun binne ta maƙabarta addu'a ya kamata ki dinga mata”
“Na gode Allah ya biya ka da Aljannah, Allah ya tsaya maka a rayuwa” Na faɗa cikin sanyin murya.

Wata Nurse ce ta turo ƙofar ta shigo hannunta riƙe da yaron na karɓe shi ina ƙare masa kallo.

Wata irin ƙaunar jaririn ce ke ratsa ni sosai, Ba abin a ya raba shi da Imaan tamkar kuma ni na haife shi, Idanuwanmu iri ɗaya sak.

Na sumbaci goshin Yaron fuskata cike da Fara'a na Ambaci Sunan Imraan a hankali. Sunan da imaan ke matuƙar so.

Na juya ga Dr Jabir cikin Girmamawa na jera masa godiya da addu'a, ya cire mini cannular na saka hijabi na rungume yaron na ce zan tafi.

Ba irin magiyar da be mini ba amma sam ban tsaya ba na bashi haƙuri akan garin zan bari. Daga nan na fito yay mini kwatancen Maƙabartar da suka binne Imaan tare da tabbatar mini yaron yana lafiya baya ɗauke da wata Cuta.

Na fito da ɗana Imraan A hannu har wajen asibitin ina tunanin inda zan dosa.
Ko a mafarki ban taɓa zaton rayuwa zata juya mana irin haka ba, Duk da Azabar da muka sha ta rayuwa ban sa ran abubuwa zasu faru haka ba, A ko dayaushe Ina mana fatan alkhairi.

Da ace wani ne zai faɗa mini ana rayuwa haka kuma al'amura na chanjawa cikin ƙanƙanin lokaci ba zan yarda ba sai gashi hakan ta faru a kaina da 'yar'uwata.

Ban san Inda zan dosa ba, Ba mu da kowa dama Mune 'yan'uwan junanmu.

Cikin sauri sosai tsaya gabana ya ɗaura kuɗin hannunsa a Jikin jaririn ya juya ya koma.

Na tsaya ina kallon bandir ɗin 'yan dubu-dubun, Wani Sanyi na ji a raina cikin sanyin jiki na ɗauka ina riƙewa a hannuna na ci gaba da takawa har bakin titi.

Na shiga adaidaita zuwa Tasha.
Na yi sa'a saur mutum ɗaya motarKaduna ta tashi na biya kuɗin mota na siyi abin da zamu ci na shiga.

Tun da muka fara tafiya nake addu'a cikin raina, Wace irin rayuwa kuma zan ci gaba, A da komai ni da 'Yar'uwar tagwaicina muke yanzu kuma Ƙaddara ta sauya al'amura ni ce da ɗana zan ci gaba da fuskantar ƙalubalen rayuwa.

Matar da ke Kusa dani ta ce, “Baiwar Allah naga yaron”Na miƙa mata shi Ta dinga santi Turbakallah.

“Sunana Fa'iza ga d’iyata kuma Afrah”.

“Khadija Ilhaam, sai shi kuma Imraan”

Na bata amsa da ganin matar zata yi kirki na ce, “Dan Allah ke 'yar Kaduna ce?”
“Kwarai kuwa Chan nake aure babana ma d’an chan ne me ya faru ko ke bak’uwa ce??”
Na gyaɗa mata kai daga nan muka yi shiru babu wanda ya sake cewa komai.

Mun yi tafiya sosai mun yi sallah har na ƙosa da zaman motar, dan ma imraan ɗin ba mai rigima ba ne, bawan Allah yaron da ya ɗan yi kuka sai na ba shi ruwa ya yi barci ya tashi har Allah ya isar da mu Kaduna birnin Shehu.

Fasinjoji suka fara sauka na bi layi ina rirriga Imraan da ke kuka na yi hanyar da naga ana ta bi jikina a sanyaye dan ban san inda na dosa ba.

Ta taɓo ni na juya ta ce, “Idan baki da masauki mu je gidana” Nay saurin jijjiga mata kai ina sauƙe ɓoyayyar ajiyan zuciya. Na sani Allah ne ya dube ni da na sha wahala.

Muka hau adaidaita zuwa gidanta tana jana da hira ina amsa mata kaɗan-kaɗan. Muka sauka wata unguwa mara hayaniya ta masu rufin asiri ta sallame shi muka doshi wani madaidaicin gida mai ƙaramin gate da ƙofa. Ta sanya mukulli ta buɗe ƙofar muka shiga ina addu'a cikin raina.

Gidan na da kyau sosai a gyare tsaf muka shiga da yin sallama. Ta buɗe ƙofar Falo muka shiga tare ta zaunar da ni bisa kujera ta haye sama ta bar ni da 'yarta na dinga rirriga Imraan.

Bata jima ba ta dawo hannunta riƙe da Faranti da kuloli biyu da Plate ta ajiye mun da ruwan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login