Showing 21001 words to 24000 words out of 27897 words
pls kisa wanda na baki"
Kasa musawa nayi a hankali nace " to" Murmushi naji ya saki ta cikin wayar
"I will see you tomorrow. Good night "
Bai jira amsata ba ya kashe wayar. Numfashi naja mai k'arfi na ajiye wayar gefe ina Addu'a. Washegari babu wanda ya tashi sai wajen shad'aya sannan aka fara sabgogi bayan an karya. Har d'akin Hajiya Fati naje na gaisar da ita da manyan mata dake gurinta. Da zan fito naci karo da Junaid. Sosai naga mamaki kan fuskar sa muna gaisawa da d'an murmushi kan fuskata na wuce wajen au Amina. Sanda na shiga hira suke sosai suna ganina ko wacce ta b'ata fuska. Ban damu ba tunda ba gurinsu nazo ba nayi wajen Amina dake danna waya. Zama nayi gefenta ina murmushi nace
" Amarya kinsha kamshi barka da safiya"
A takaice ta bani amsa " yauwa" kawayenta suka rushe da dariya da nasan dani suke. Ido kawai na zubawa Amina ina tunanin menene nayi mata haka mai zafi daya sa ta SAUYA min haka cikin d'an k'ank'anin lokaci. Wajejen azahar aka fara shirin tafiya dinner. Nima na miƙe don naje na shirya. Ina fitowa daga wajen Amina na tsaya turus ina kallin Hajiya Suwaiba da suke tare da Hajiya Fati suna magana tsakiyar falon. Gabana ya yanke ya fad'i kafin nayi saurin wucewa ta ganni da mamaki sosai naji ta kira sunana
"A'a Jadwah. Kece"
Yake na d'anyi na d'an rankwafa ina gaisheta. Wani irin farin ciki ne naga kan fuskarta ta nufoni da sauri tana amsawa.
"Saukar yaushe Jadwah babu labari ?"
A hankali nace jiya . Kai ta jinjina ta k'ara cewa " Kina nan har sai an gama bikin kenan? "
Kai kawai na jinjina. " to MashaAllah. Ai kuwa kin kyauta da ki ka zo duk da sanin matsayin ki dana Amina yanzu. Amma zakije duba Balaraba ko?. Kinsan ta dade gadon asibiti bata da lafiya sakamakon faduwa da tayi daga bene. Ta samu karya duka kafuwan ta"
Da d'an mamaki na kalli H Suwaiba ina d'an girgiza kai nace " wlh ban sani ba. InshaAllahu zan dubata kafin na tafi"
"To ya yi. Sai kiyimin magana idan zakije don har yanzu tana asibiti. Saboda gidan babu kowa Asiya tana can UK"
Kai kawai na d'aga mata na wuce da sauri ta ina jin idon ta kaina. Murmushi Suwaiba tayi .shikenan fad'uwa tazo daidai da zama.
A gurguje nayi wanka na fito na fara shiryawa. Allah ya taimake ni d'akin babu kowa saini kad'ai magan duk sun fice an fara tafiya wajen dinner. Agogo na kalla naga yamma tayi sosai ana gab da shirin sallan Magriba. Ina shiryawa na k'ara kiran Gwagwo muka gaisa kafin na kashe ma d'auko jakar daya bani. Wata arniyar silver gown ce mai shegen kyau da taci adon duwatsu kaman diamonds harda sark'ar ta. Ajiyar zuciya nayi na d'auko rigar ina juyata a hannuna. Anya kuwa zan iya saka wannan rigar. Zuciyata tace mun yau d'aya saboda Amina. Numfashi naja na saka rigar data shigeni da kyar tsam ta kamani tabi dukkanin shape d'ina ta kwanta. Tufke gashin kaina nayi da ribon na saki jekar ta sauka bayana. D'an mayafin rigar na yafa shi a wuyana na saki jelarsa ta baya. Had'addiyar sark'ar kansa mai shegen tsafa data zauna tsam saman k'irjina daya d'an fito ta saman rigar data matseni.
Allah ya taima takarmin ba mai tsini bane sosai shima Silver ne haka ma y'ar purse d'in ta. Ni kaina nasan nayi kyau dukka banyi waya kwalliya ba. Tsayawa nayi bakin k'ofar na kasa fitowa har na tsawon minti biyar kafin naja ajiyar zuciya na fito ina Addu'a cikin raina. Numfashi na sauke ganin an watse sai daidaikun mutane dake fitowa wanda suka zo da motocin su. Ina tafe ne ina hardewa saboda abune da ban saba ba gashi duk inda na had'u da wani sai ya bini da kallo.
Harabar gidan na tsaya ina tunanin abunyi don duk an watse babu kowa sai wata mota guda d'aya da ina karasowa ta fice da y'an mata a ciki. Numfashi naja a hankali na juya zan fice naji an saki wani uban horn daya firgitani na juyo da sauri. Wata dankareriyar LAMBO ce fake can gefe da ban lura da ita ba baka wuluk da ita harta glass nata bakine. Ina juyo dalla motar ta haskeni nayi saurin kai hannu na rufe fuskata. Tada motar naji anyi da saida tayi kuwwa tsakar gidan a hankali ta matso gabana ta tsaya glass nata ya sauka a hankali. Moha ne zaunw cikinta sanye cikin wata arniyar dark ash d'in suit three pieces data kamashi tsam necktie d'in nan ya zauna wuyansa. Tsaban yanda kayan suke so dark sai suka zama kaman silver . Fad'ar irin kyan da ya yi abun b'ata bakine. Wani irin kallo ya watsomin da wannan manyan Blue eye's nashi yace
"Get in"
Murfin motar ya d'aga sama. A hankali na shiga na zauna ina tunani abunda ya hanashi tafiya wajen dinner tuntuni Amarya kuwa ta dad'e da hallara a wajen. A hankali yake tafiya kan titi kaman baya so ga wani irin kallo da yakemin da duk sai naji na tsargu sai Mutsu-mutsu nake na discomfort.
Alright. Free page's na gabda zuwa k'arshen. Zaku iya fara payment ga duk masu buƙatar karin bayani chat me up.
08140754777
Kar a manta 500 ne kuɗin SAUYIN LAMARI.
𝗦𝗔𝗨𝗬𝗜𝗡
𝑳𝑨𝑴𝑨𝑹𝑰.
𝔸𝘚Η𝔸𝑵𝚃Ⲩ 𐐛૦𝚅𝞔.♡︎
𝐏𝐆 12.
AUTHOR POV.
Numfashi Jadwah ta sauke a hankali saboda wani irin nauyi da take jin k'irjinta ya yi. Hakan nan kawai zuciyarta ke bata akwai wani gagarumin abu da zai faru matsawar taje gurin dinner d'in nan. Tunda tazo ta fuskanci kaman Amina na fushi da ita wanda ita kanta bata san fushin na menene ba bare kuma yanzu a ganta tazo tare da ango shida ya kamata ace tare suke da Amarya. Batayi tsammani ba saboda zurfi da tayi cikin tunani bata lura da sanda ya sauka daga kan titi ba ya faka motar, saida taji sun daina motsawa sannan ta juyo a hankali ta kalli Moha daya kwantar da kai jikin sitiyarin motar yana mata wani irin kallo mai kashe sassa da gabban jiki. A hanzarce ta d'auke kai bugun k'irjin ta na k'aruwa. Wai meke damun Moha ne?. Murya na rawa tace
"Me ka ke haka?, lokaci na tafiya ka sani "
Baice komai ba saima k'ara gyara kwanciya da ya yi jikin sitiyarin yana k'are mata kallo. Dukkanin wasu sassa da kofofi na jikin sa dake motsa sha'awa sun buɗe. Ji yake kaman ya yi jumping nata ya yi duk yanda yaga dama da ita a wannan lokacin, amma duk da cewa ita d'in halaliyar sa ce, dole ya jira har na d'an wani lokaci. Yana so ya koya mata son shi kaman yanda ya fara gina kansa kan Soyayyar ta da kishin ta. Yanzu yake dana sanin sata saka kayan don wani iri kishi yake ji har yana tunanin ya juya motar su koma gida. Bai tab'a sanin cewa haka ta had'u ba. Dole ta dinga b'oye kanta cikin hijabi don had'uwar ta ya wuce yanda yake kissimawa. Wani irin k'asa ya yi da idon sa yana kallon saman k'irjin ta da sark'ar nan ta kwanta lum a kansu. Koya tayi nishi kota motsa sai sun taso. Baisan sanda ya wani lashe lab'b'a ba da yake jin sun bushe lokaci guda tsabar ishi.
"Kaji"
Wannan muryar ta ta mai tsananin zaki da taushi ta k'ara dukan dodon kunnen sa. Wandonsa ya k'ara tighten jikinsa . Oh he cannot wait for ranan da wannan muryar zata dinga ihun kiransa idan yana pleasuring nata. Ranan da zata kasance k'arshesa tana sumbuta yana rikitata da salon sa. Numfashi ya k'ara saukewa mai k'arfi dake shaking. Maida idonsa ya yi ya lumshe don saisaita nutsuwar sa kafin ya buɗe idon a hankali kanta. Har zuwa lokacin kanta na k'asa tana wasa da yatsun hannun ta . Kasa jurewa ya yi ya d'ago da hannun sa a hankali ya kai fuskarta yana k'ok'arin tab'awa wayar sa ta fara ringing. Numfashi ya sauke a hankali ya mayar da hannun nasa daya tsayar bisa iska ya kara wayar a kunne. Daga d'aya b'arin muryar Amina ta doki dodon kunnen sa tana gab da fashewa da kuka. Dogon nishi ya k'ara saki na rashin jindaɗi. Ya mutsu abubuwa su warwarewa Jadwah tasan matsayinsa yanzu a gurinta dana Amina. A takaice yace
"I'm coming " bai jira amsar taba ya kashe wayar ya fara k'ok'arin tada motar. Duk abunda yake Jadwah na jinsa jikin ta ya k'ara wani irin sanyi ganin ya tada motar sun hau titi. Anya kuwa baza tace ta fasa zuwa gurin dinner d'in nan ba?.ya sauke ta kawai ta samu mota ta koma gida?. Hakan bai samu ba don yanzu sosai yake gudu kan titi basu jima ba suka k'arasa event d'in da akayi booking saboda dinner d'in. Tun daga wajen events d'in zaka san an kashe dukiya bare kuma cikin sa. Hannu ta kai a hankali ta dafe k'irjinta dafe saitin zuciyar ta dake wani irin bugawa kaman zata tarwatse. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un ta fara maimaita da take tunanin cikin ranta takeyi. Ido ya zubawa d'an k'aramin bakin nata dake ta salati yasha man leb'e sai shek'i yake. Tsintar kansa ya yi shima yana maimaitawa a hankali kan l'eben sa sai ka kula da kyau za kaga motsin su. Wata irin nutsuwar zuci yaji ta fara ratsa shi ya sauke ajiyar zuciya yana kallon yanda take kallon k'ofar Hall d'in daya faka motar mutane nata shige da fice ga masu tsaro. Gashi sanda ya faka motar hankalin kowa ya yi kanta ana jiran aga waye zai fito daga cikinta. Murmushi ya yi na gefen baki ya buɗe motar ya fito majestically ya zagayo inda Jadwah ke zaune ya buɗe mata. Babban aminin sa LAMEEN,daya kasance shi kad'ai ne nasa a gurin dake zaune a Dubai, ya nufoshi da sauri don shina zuwansa kenan bai dad'e sauka Nigeria ba.
"Dude. What ?sai yanzu kazo wai?"
Yace yana kallon sa cike da tuhuma. Moha bai kalle shi ya ya matsa ya buɗewa Jadwah motar ya d'an rankwafa a hankali ya miƙa mata hannun sa .kallon hannu tayi ta d'ago ta watsa masa kallo ta fito daga motar. Y'ar dariya Lameen ya yi yana kallon Jadwah dake rarraba ido ya mayar da kallonsa kan Moha. Ido suka had'a kaman masu yin magana da ido. Kai Lameen ya jinjina da sauri yace
"Sannu Madam "
Da sauri ta d'ago ta watsa masa innocent eyes nashi yar kunya ta kama Jadwah a hankali tace
"Ina wuni?"
Wow Lameen ya furta cikin ransa. "A'a Aunty na ni ya kamata na gaishe ki. Sannu da zuwa. And you mu hanzarta kai kad'ai ake jira"
Ya k'arasa maganan yana kallon Moha daya kafe Jadwah da ido ko kyiftawa baya yi ga wani iri kishin ta dake cinsa. Gani yake kowa ita yake kallo. Hannun sa Lameen ya kama yaja yana kallon Jadwah yace
"Muje ko?"
Bata musa ba ta wuce da sauri suka rufa mata baya. Da d'an rad'a Lameen yace saitin kunnen Moha
"I see why your so wip. Ka ajiyr Amarya gefe ka tafi wajen uwargida"
Dariya Lameen ya fashe da ita Moha ya d'an kai masa duka na wasa ya kauce. Murmushi shima ya yi yana kallon Jadwah dake takawa a hankali kaman baza ta taka k'asa ba. Da sauri ya fisge daga hannun Lameen ya matsa kusa da ita suka jera daidai suna shiga Hall. Ido ta zaro tana kallon Moha daya matso sosai kusa da ita kafin tayi wani yunƙurin kaucewa sun shige Hall. Ai kuwa Hall ya d'auki wani irin shiru kace babu mutane. Jikin Jadwah ya fara rawa saboda yawon idon da ya yi kansu. Maimakon ya matsa sai ya k'ara matso ta har k'afad'ar sa na gugan tata. Cak ta tsaya da tafiyar da take tana kallon Amina dake zaune can kan high table ta miƙe tsayi wani irin kishi da b'acin rai kwance kan fuskar ta. Fuskarnan data sha makeup duk ta ya mutse tana shirin fashewa da kuka. Muryar Lameen dake bayansu tace
"Muje mana kunci burki"
Jikin Jadwah na rawa ta matsa da sauri ta samu guri ta zauna. Kallo Moha ya watsa mata ya wuce gurin Amina dake kallonsa kaman tayi bindiga. Wannan wane irin tozarci ne da cin fuska?. Duk irin cin amanan da tayi mata bai isheta ba sai ta nunawa duniya ita cikakkiyar butuluce mai cin amanar abota?. Har Moha ya k'araso inda Amina ke tsaye tana kallonsa da jan ido. Wuceta kawai ya yi ya samu guri ya zauna abunsa bai damu da yanayin Amina ba. A sanyaye ta zauna kar tozarcin ya yi yawa .suna zama kuwa guri ya kaure da hayaniya. Tambayar kowa a gurin shine wacece wannan suka zo da ango mai mamakon a ganshi da amarya?.
B'angaren Jadwah abun ba'a cewa komai kaman tayi tsuntsuwa ta bar gurin. Tana ganin yanda mutane suka kasu kashi kashi. Wasu na zaginta wasu na ganin sun dace ita da ango, wasu na jifan ta da mugun kallo da harara. Kujerar dake gefenta Lameen yaja ya zauna yana d'an murmushi yace
"Karki damu da abunda suke cewa. Babu wanda ya isa ya hanaki zuwa da Moha wajen bikinnan don kin fisu right dashi"
Maganan sa ta d'aure mata kai amma batace komai ba. Zuwa wani d'an lokacin aka cigaba da sabgogi na harkar biki. Koya ta juya idonta sai ya tsarke dana Moha ,sai tayi maza ta sauke idon ta. Banda Moha harda Amina da kawayenta dake jifanta da wani mugun kallo na tsantsan tsana. Minti talatin da zuwansu aka fara ci dasha kafin a fara cashewa. An kira ango da amarya suzo su d'an taka. Amina ta k'anannade Moha suna bin slow music da aka saka musu yana tashi a hankali an rufe su ana musu likin kuɗi. Bayan sun gama suka koma inda suke zaune. Jadwah ta fara gajiya da kallo da ake binta dashi. Tana kallon yanda maza da dama suke son suzo suyi mata magana amma Lameen ya kasa ya tsare kaman mai bata tsaro. Da zarar wani ya yunƙuro zai jefi da mugun kallo dole ya koma inda yake zaune. Karfe shad'aya aka gama dinner aka fara k'ok'arin tafiya. Da sauri Jadwah ta miƙe ta fito daga Hall d'in Lameen ya biyo ta da sauri. Fita tayi ta tsaya harar gurin tana kollan yanda kowa ke shiga motar daya zo. Tunani ta fara na yanda zata koma gida. Shawara ta yanke tayi hanyar waje Lameen yasha gabanta.
"Ina zaki kuma? "
A hankali kanta na k'asa tace " zanje na samu mota ne a waje"
"Aa wace irin mota kuma ga wanda ku ka zo da ita?"
Kafin tace wani abu muryar Moha ta doki dodon kunnen ta. " meke faruwa?" A hankali ta juyo suka had'a ido da Amina dake gefen sa kaman zata shige masa ciki. Kallon data watso mata yasa ta sauke ido kasa da sauri. Sabad'in d'azu, yanzu wata dankareriyar Audi ce jeep baka ta faka gabansu. Moha ya matsa ya buɗe motar. Amina ya fara kalla murya a dake yace
"Get in"
A hanzarce ta shige motar babu musu. Juyowa ya yi ya kalli Jadwah kafin ya shiga bayan suka had'a ido da Lameen. Da sauri Lameen ya matso kaman zau turata yace
"Oya shiga- shiga muje we don't have all day"
Yanda yake matso ta yasa babu shiri ta shiga motar a hanzarce. Sanyi da kamshin motar ya ratsa ta ta sauke ajiyar zuciya. Ko kad'an bata juya ta kalli Moha da Amina dake gefenta ba duk idansa da take ji kansu. Idona nuwa da d'aya ke d'auke da burning hate d'aya kuma da wani burning lust.
B'angaren Balaraba tafi kowa takaicin abunda ke faruwa. Tunda taji zancen auren Moha da Amina ta d'aga hankalinta matuƙa. Bakin ciki kaman zai kashe ta. Ta lura Asiya Sam bata damu ba don yanzu ta fara watsar da LAMARIn Moha tunda tana tare da Jojo da sauran y'an harkallanta suna bad'alarsu. Randa ta kirata saboda Auren baran baran suka rabu a waya. Bakin ciki goma da ashirin ga rashin k'afa gashi yanzu komai ya daina tafiyar mata yanda take so. Balarabe tun kwanciyar asibiti sau biyu yazo dubata don shima ya fara gajiya da ita. Duk da haka yana bata kulawa yanda ya dace .Komai yanzun ya daina tafiya mata daidai. Allah Allah take ta samu lfy ta koma wajen Jalli. Ita ta tura Suwaiba gidansu Amina don ta tabbatar da zancen auren shine sanadin data ga Jadwah a gidan bikin.
𝗦𝗔𝗨𝗬𝗜𝗡
𝑳𝑨𝑴𝑨𝑹𝑰.
𝔸𝘚Η𝔸𝑵𝚃Ⲩ 𐐛૦𝚅𝞔.♡︎
𝐏𝐆 13.
Basu jima ba a kan titi saboda gudu da motar take suka isa k'ofar gidansu Amina. Motar na fakin Jadwah ta fara k'ok'arin buɗewa ta fice saboda yanda take jinta tension da ya yi yawa cikin motar, kaman an kunna mata wuta duk uban Ac dake aiki. Ta gefen idanta take lura da Amina dake kwance kan k'irjin Moha kaman zata koma cikinsa. A hanzarce ta buɗe motar ta fice tun kafin wani daga cikin su ya yi yunƙuri. Tana fitowa wasu motocin na fakin k'awayen Amina da sauran mutane suka fito. Dukkaninsu da kallo suka bi Jadwah data wuce da sauri cikin gidan kaman wata barauniya. Da ido ya bita harta b'ace ciki gate ya d'an sauke ajiyar zuciya a hankali. Amina dake kallonsa kaman tayi bindiga tsabar kishi tace
"Wai me ka ke nufi dani ne Dear? Wane irin cin mutunci ne wannan ranan farin cikin mu ka mayar dashi na bak'in ciki. Ko ba komai ai ka nunawa duniya nima ina da matsayi mai girma a wajen ka tunda yau ranan mu ce. Amma shine don cin fuska ka barni ka tafi gurin tsohon hannu?. Yanzu da wane ido ka ke tunanin zan fuskanci irin wannan cin mutunci?"
Uffan baice mata ba saida ta gama b'ab'atun ta taja neman rushewa da kuka ya bata amsa da kalma d'aya.
"Saida safe"
Kaman zuciyarta zata fashe haka Amina taji wasu hawayen bak'in ciki suka suka mata fuska. Juyawa tayi k'ofar gidan su ta hango su Saudat tsaye suja juran fitowar ta. Dole ne ta nuna musu itama tana da