Showing 27001 words to 27897 words out of 27897 words
shigowar mota gidan tayi wuf ta tashi a mugun gudu tayi hanyar d'akin data kulle kanta a ciki. Harta gifta idonta ya hango mata k'aramar pose nata dake zaune kan tebir. Bata san sanda tayi wani irin tsalla ta suri jakarba ta yi d'akin da mugun gudu da banko k'ofar, daidai Suwaiba na sawo kai ciki. A guje tayo wajen k'ofar tana kiran Jadwah amma ina tuni ta garkame ta.
Jiki na rawa ta zazzage jakatar wayarta ta fad'o. D'an k'aramin ihun kuka ta saki ta d'auko wayar sa saura kad'an ta mutu. Babu wani tunani ko jinki ta dannawa Moha kira.
Numfashi ya k'ara saukewa yana kallon Lameen dake ta amsa gaisuwa da murna da ake yi masa a matsayin sa na ango daya angwance yanzu. Gaba d'aya babu wani farin ciki ko annushuwa kan fuskar sa. Kana kallonsa zaka san yana cikin matsanancin damuwa. Zaka san dan dole yake tsaye a gurin badan san ransa ba. Wani Numfashin ya kara saukewa yana kallon kawun sa dake gaisawa da dangin amarya. D'an tsaki yaja ya buɗe motar da yake jingina a jiki ya shiga ya zauna. Gaba d'aya ya matsu yaje yaga Jadwah ya san ya ta tashi. Zamansa ke da wuya wayar sa ta fara ringing. Wani tsakin ya k'ara ja ya karkata ya ciro wayar daga aljihun wandon sa. Ido ya d'an zaro ganin Jadwah ke kiransa a hanzarce ya d'aga harda sauke wata y'ar k'aramar ajiyar zuciya. Kukan ta ne ya fara dukan dodon kunnen sa . Tuni ya firgice
"Baby what's wrong? Kukan me ki ke.? Amina tayi miki wani abu ne"
Tana kuksa sosai tace " kataimake ni ya Moha. Bansan inda nake ba"
"What?. Me ki ke cewa ne? I don't get you"
"Hajiya Suwaiba ce ta sa...."
Dididid wayar ta mutu. Wani irin dukan sitiyarin ya yi ya buɗe motar ya fito kaman mahaukaci yana kwalawa Lameen kira. A hanzarce Lameen ya matso yana tambayar sa
"Lfy, meya faru?"
"Wani abu ya faru da Jadwah muje gidan su Amina"
A guje auka shige mota Lameen ya fisge ta da mugun gudu suka harba kan titi. Suna tafe yana k'ara kiran number amma ana ce masa Switch off. Suna isa k'ofar gidansu Amina ko fakin bai bari Lameen ya yi ba ya buɗe motar a guje ya fice ya yi cikin gidansu Amina duk uban mutane dake cikin sa. Kai tsaye ya yi falonsu yana kwalawa Jadwah wa kira. Hajiya Fati da kawayenta kowa ya miƙe yana kallon Ango cikin matsanancin mamaki. Tuni labari ya jewa Amina ta fito a sukwanne cikin dakakken leshi Maroon. Yana ganin Amina ya yi kanta harta fara murmushi tana d'an kwakwasa.
" ina Jadwah? Me ki ka yi mata?"
Ya watso mata tambayar dukkanin wani annuri fuskar Amina ya b'ace hawayen bak'in ciki suka wanke mata fuska. Wannan wani iri cin mutunci ne gaban iyaye da y'an uwa yana kiran sunan matarsa?. Me ya kamata ya yi yanzu da ta kasance tashi. K'ara matsowa ya yi yana huci da karaji ya k'ara cewa
" ina Jadwah?"
"Dude"
Lameen ya yi saurij dafe k'afad'ar yana kallon yanda mutane ke kallonsu cikin dumbin mamaki. Juyawa ya yi kalli Hajiya Fati da fuskarta ke d'auke da matsanancin b'aci rai. Ko wace uwa aka yiwa y'ar irin wannan wulak'anci dole ranta ya b'aci. Da sauri Lameen yace
"Kiyi hak'uri Mummy. Hankalin mune a tashe. Jadwah ta kira ne tana ce mana bata san inda take ba kafin tayi mana bayani kuma wayar tata ta mutu"
Jin wannan furucin fuskar Hajiya Fati ya chanza zuwa tsananin damuwa. Da d'an k'arfi ta furta "Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Me ka ke nufi?, kana nufin an sace Jadwah a gidan nan"
" ke Amina ba tana tare da kuna jiya?"
Baby dake kusa tayi saurin matsowa tace " A'a Mummy jiya sun d'an samu matsala da Amina. Iya sanina bayan fitarsu Amina ta bi bayansu. To kuma har yanzu bata dawowa. Munyi tunanin ko wani d'akin ta kwana shi yasa bamu fad'a ba"
Aikuwa gaba d'aya d'akin ya kaure da salati. Amina kaman ta had'iye zuciya. Moha kuwa sai ka tsorata da yanda jikinsa ke rawa .realisation ya yi down a kansa. Their is a possibility an sace Jadwah, babu wanda yasan inda take. But waye zai sace ta.? Saboda me.. wait..
"Hajiya Suwaiba ce..."
Last sentence nata ya dawo masa kwanyar kansa. Ina yasan sannan wannan sunan?. Suwaiba ya k'ara maimaitawa a fili. Da sauri Hajiya Fati tace
"Wace Suwaiba ba?, Suwaiba dana sani?"
Yana jin ta furta wannan sunan ya wani irin juyawa da mugun gudu ya fice daga falon Lameen ya rufa masa baya. Amina ta zaune a gurin dabar ranta na matuƙar suya. Hallau dai Jadwah ta k'ara cin galaba a kanta.
End of Free page's.
Tafiyar tamu yanzu ta fara zafi. Kuna ganin Moha zai k'ubutar da Jadwah kan lokaci?
Ya zaman aurensa zai kasance da Amina da Jadwah, ga kuma Asiya?
Jadwah zata amince da Moha har tayi zaman aure dashi?
Wai shin Baba yana nan da rai ko kuwa ya mutu?
Taya akayi Moha ya auri Jadwah ranan da Baba ya nemi wannan alfarmar ?
Duk wad'annan amsoshi na cikin book2 namu da zamu fara nan kusa inshaAllahu. Kudai ku biyoni. Kunsan alkalami na babu na banza ba cika baki ba. Duk wanda yasan books na Ashanty love yasan daban take wajen rubutu. Ko hanzarta ku fara saka kudin ku cikin wannan asusun bankin
👇
3078293374
Aisha sani danjuma
First Bank.
@500N kacal.
Domin neman k'arin bayani a tuntu'bi wannan number.
08140754777.
Ashanty love ce.❤🤟