Showing 6001 words to 9000 words out of 27897 words

Chapter 3 - SAUYIN LAMARI Book 1 HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

40

sa dake motsi koya ya motsa hannun.

Short hair nashi daya tsaya perfect kansa. Wanda yafi yawa daga gaba. Bak'in wando ne a jikinsa mai kaman leather. Hannu sa dake d'auke da agogo da zubuna ya kai ya tura cikin gashin nasa mai shegen laushi ,kafin ya juyo gaba d'aya zaiyi ciki. Ya hayyu ya Kayyumu. Matsanancin kyau da yake dashi abun bazai misiltuba. Manyan ocean Blue eye's ne dashi dake dauke da dogon hanci da gashin gira yala-yala kaman na mace. Full lips nashi da suke pink colour kaman mai shafa janbaki ya tura leben sa na k'asa ciki ya fara tafiya sak yanda yara suke idan suna koyon tafiya.

Yanda yake tafiya yana had'a hanya zai tabbatar maka a buge yake. Yana shiga ya zube cikin kujeru sai sumbatu yake shi kad'ai. Bai jima ba kuwa mugun barci ya yi awon gaba da shi.
































𝐏𝐆 4.





Kiran sunan sa da yaji anayi da wata irin murya mai amo yasa shi buɗe ido cikin matsanancin mamaki. Maimakon ya ganshi kwance kan sofa kaman yanda yake sai ya ganshi cikin wani kungurumin daci mai shegen duhun tsiya da kukan halittu mai ban tsoro ya cika shi. A mugun firgice ya fara waige-waige yana neman tsira amma kaman wanda aka kafar a gurin ya kasa motsa ko yatsan sa sai kawayar idon sa dake waige-waige cikin matsanancin tsoro da firgice. Daga gefen hagun sa yaji wannan murya ta tunkaro shi tana kira da wani irin k'araji. Matsanancin tsoro da firgici Moha ki ciki abun sai wanda ya gani. Runtse ido ya yi ko Allah zaisa ya farka daga wannan mummunan mafarki da yake mai tsananin ban tsoro gashi kaman reality. Mutsu-mutsu ya fara neman k'ubutar da kanshi saboda muryar yanzu da take gab dashi. Moha sam ya manta da kiran mai duka ,hankalin sa da tsoron sa baisa ya nemi taimakon ubangiji ba sai numfashi da yake a guje kaman mai shirin samun heart attack. Ance Allah gafurur rahamin. Daga gefen daman sa iya inda yake gani ta gefen ido, wani irin haske ya bayyana da ya yi sanadin tsayuwar koma mene ne yake tunkaro shi daya kusa cimma.

"Moha"

Yaji wata irin murya mai tsananin dad'i da sanyi ta kira sunan sa da saida gaba d'aya tsigar jikinsa ta motsa. Wani irin hannu mai tsananin taushi da laushi ya sauka kan kafad'ar sa da yasa shi d'an firgita. A hankali yaji muryar ta sakko daidai saitin kunnen sa tana cewa

"Allahumma ajirni fi musibati, wa aklif ni khairan min ha"

Bai san ya akayi ba yaji bakin sa ya fara motsawa ya fara maimaita Addu'ar kaman yanda yaji muryar nayi. Cikin ikon Allah kuwa gaba d'aya jikinsa da ya yi paralysis kaman wanda akayi snap abu jikin nasa ya saki. Da wani irin azama ya yi k'ok'arin juyowa bayansa don ganin wacece. Yanzu tana can nesa dashi ta bashi baya. A guje ya miƙe ya nufi yarinyar dake tsaye cikin wasu fararen kaya masu matuƙar shek'i . Duk taku d'aya idan ya yi don cimma ta sai ta k'ara yi masa nisa. Haka ya yi ta binta tana k'ara yi masa nisa. Ganin babu mafita ya fara kira kaman zai tsaga mokogaro.

"Wait, please. Who are you?"

D'an murmushi yaji muryar tayi kafin ta k'ara kiransa da muryar nan tata mai tsananin dad'i tace

"MUHAMMAD MOHA"

Daga haka sai bat ta b'ace daidai ya farka cikin matsanancin firgici. Ya had'a wata irin zufa kaman wanda aka deb'o ruwa aka watsawa a jiki. A yanzu ma dai big brother ya mance kiran sunan Allah sai hannu daya kai ya dafe k'irjin sa dake harbawa kaman zuciyarsa zata fito fili. Wane irin mafarki ne wannan kaman gaske?. Wacece wannan yarinyar mai murya da take da matsanancin dad'i?. Tazo kuma ta taimake shi?. Wai shin mafarki ne ya yi ko kuwa hallucinations ne?. Yanda heart nashi ke racing kace zata tarwatse. Duk da ya farka bai hana aikin Jalli tab'a shi ba don ji ya yi duniya a yanzu babu inda yake da burin ya ganshi daya wuce NIGERIA. Ko kwana d'aya baya son k'arayi a nan.

Jiki na rawa ya miƙe ya yi d'akin sa muryar nan nata yi masa amsa kuwwa cikin kunne. Hakanan yaji yana son sanin wacece mai muryar nan. Akwai ta a zahiri?, ko kuma mafarki ne kawai?. Yana had'a kaya ya kira mahaifin sa Alhaji Balarabe. Bugu d'aya ya d'aga da y'ar sallama yace

"Muhammadu ya akayi cikin daren nan?"

"Dad. Ina so na koma Nigeria"

Wani irin shiru Balarabe ya yi jikinsa ya yi sanyi matuƙa. Ba wai baison Moha yaje Nigeria bane A'a. Shi kansa ya rasa dalilin da yasa baison Moha ya kasance da Balaraba da ya'yan ta. Tun yana k'arami ta raini Moha. Kuma ya taso kan tarbiya data ginashi da ya'yan ta. Yasan irin mugun rawar data taka wajen lalacewarsa. Musamman ma kan Shaye-shaye. Babu abunda baiyi ba ya raba shi da shan giya amma abu ya faskara. Shi yasa ma ya dawo Italy nan da zama ,don da yana tare da matarsa SUHANA Balarabiyar Dubai daya aura saboda Moha.

Ya samu uwa da zata bashi tarbiya ta duroshi kan tafarki kai kyau. Amma Moha yak'i. Ko kad'an shi kansa baisn zuwa Nigeria saboda Balaraba data zame masa k'arfen k'afa. Babu yanda zaiyi da ita idan yana tare da ita sai yanda tayi dash. Sautari wani lokacin idan yana neman rufeta da tujara idan ta kaishi bango duk irin yanda zuciyar sa take zafi haka zai kasace mata komai saidai ya yi ta bata hak'uri. Numfashi yaja mai zafi yace

"Moha. Bana son komawar ka Nigeria. Idan ka gaji da zaman Italy d'in ne kazo nan Dubai wajen Mom naka mana. Kazo nima ka tayani neman wannan election da nake. Mutanen gari sun zabe ni ina running zabe na zama President. Come home to me my boy. I needed you here"

Stubbornly Moha yace
"No. I'm going to NIGERIA and that's final."

Bai jira abunda Mahaifin nashi zai cebe ya kashe wayar sa. A daren yabi jirgin sa zuwa Nigeria kaman yanda yaci buri.


AZARE.



Tsintsiya ce riƙe a hannun Jadwah dake share compound d'in gidan. Duk da cewa akwai masu aiki wani lokacin saboda yawon shige da fice da ake kafa duk an tako k'asa. A rayuwar Jadwah koya datti yake yana masifar ci mata rai. Duk lokacin da zata share k'ofar d'akin su zata had'a da compound d'in gidan ta share duk irin girman sa. Asiya dake zaune baranda su ta main kofa da ake shiga gidan tana waya taci uban riga da wando sai murmushi take zubawa kayi tunanin da wani saurayin take waya. Cire wayar tayi daga kunnen ta ta kalli Jadwah dake matsowa kusa da inda take tana shara. Wani irin tsawa ta daka mata ke

"Ke baki da hankali baki ga waya nake ba?"

A hankali Jadwah ta d'aga ta watsa mata manyan idon ta, bata ce komai ba ta juya ta koma k'ofar d'akin su. Ran Asiya ya yi matuƙar b'aci. Haka kawai ta tsani yarinyar saboda kyau da Allah ya bata. Kwafa tayi ta cigaba da wayar tana gayawa JJ abunda y'ar iskar yarinyar ke mata. D'akin su ta shiga ta lek'a wajen Baba dake barci saboda ciwon kai daya kwana dashi da kafa ,da kyar suka samu ya yi barci gabanin asuba. Dan yau ko Sallah Asuba da bata wuce shi a masallaci a d'aki ya yi. Duk Abunda Jadwah take tana dauriya ne. Ciwon Mahaifin ta ya dame ta matuƙa tana tsoron shima ya tafi ya barta kaman Mahaifiyar ta. Numfashi taja mai zafi idon ta cike da kwalla ta fito ta kwashi kwanuka tayi waje dasu don ta wanke.

Tana fitowa aka yi horn k'ofar gida don haka jiki a sanyaye tayi wajen gate d'in ta buɗe. Motar Hajiya Suwaiba ta shigo ciki , maimakon ta wuve sai ta tsaya kusa da d'akin su ta fito daga motar taci uwar ado kaman mai zuwa gasa. Murmushi ne kwance kan fuskarta tana kallon Jadwah harta k'arasa rufe gate ta juyo inda take tsaye. Gaban Jadwah ya yanke ya fad'i haka nan kawai taji matar bata kwanta mata a rai ba. D'an murmushi ta kirki da baikai zuciba ta d'an durkusa tana cewa

"Hajiya ina kwana ,an tashi lfy?"

Fuskar Suwaiba ta k'ara cika da fara tace

"Lafiya lau Jadwah. Ya kwanan ki dana Mahaifin ki?"

A hankali tace lafiya tana kallon k'asa. Murmushi Suwaiba tayi ta buɗe motar ta fito da leda ta miƙo mata

"Ga wannan babu yawa y'ar alawa ce ta yara dana gani naga ta dace dake."
A d'an razane da mamaki Jadwah ke kallonta tana girgiza kai. Yaushe ne sukayi sabon da zata karb'i abu gurinta. Ita koda ta sanka ma baka mata kyauta haka kawai ta k'arba.

" A'a wlh Hajiya. Nagode Allah ya saka da alheri "

Murmushi dake kan fuskar Suwaiba ya kai ta zuba mata tace

"Baza ki karb'i abun hannuna ba saboda me?, ko dan baki sanni ba?"

"Aa wlh Hajiya ba haka bane"

"To kina kyamata ne ko kuwa kin raina abunda na baki?"

Wace irin magana ce wannan?. Jadwah ta ce cikin ranta. Numfashi kawai taja ta fesar bazata iya cigaba dayi mata musu ba. Idan bata karb'a ba ,zata fuskance ta da wata manufar don bazata tab'a fuskantar ta ba. Hannu ta miƙa a hankali ta karb'a tana mata godiya.

Zo kaga fuskar Suwaiba kaman anyi mata albishir sa Aljanna tana kallon Jadwah data wuce d'akin su. Murmushi tayi ta nufi cikin gidan inda Asiya ke zaune tana kallon duk abunda ke faruwa. Y'ar dariya Asiya tayi ganin yanda Suwaiba keta zuba Uban murmushi har kunne. Kai kawai ta jinjina Suwaiba ta wuce ta baki har kunne.


Kai tsaye tayi cikin bakkon ta ta tura jakar cikin ta islamiya. Idan ta fita islamiya anjima zata bawa yara. Duk da cewa chocolates ne maisu shegen tsada a ciki haka nan ranta bai kwanta dasu ba. Saida ta k'ara lek'a Baba sannan ta fito tayi wanke-wanke. Ta cimma rabin sa saura kiris ta gama duk dama ba wasu kwanuka bane masu yawa. Aka yi horn a waje. Da sauri ta miƙe tana goge hannu ta nufi k'ofar ta buɗe. Wata arniyar GMC ce ta sawo kai cikin gidan baka wuluk da ita harta glass nata bak'ikkirin ne. Da matsanancin mamaki Jadwah tabi motar da kallo don bata tab'a ganin irinta ta shigo gidan ba tunda tazo. Mahaukacin ihun da Asiya tasa ta miƙe tayi cikin gida a guje kama wacce abun tsoro ya bi. Kirjin Jadwah ya buda kardai ko wasu mugayen ta buɗewa k'ofar cikin rashin sani.

Tana kallon yanda masu tsaron gidan suka matso wajen motar amma babu wanda ya k'asara inda take. Wannan ya k'ara ninka tsoron Jadwah tak'i rufe gate d'in a tunanin ta koma wu waye idan suka ga babu daman da zau aikata abunda suka zo da niyar yi zasu nemi hanyar tsira. Kuma idan mutanen unguwa suka gani zasu kawo agaji. Saida motar ta d'auki minti biyu da fakawa tsakiyar gidan kafin aka buɗe ta da wani irin slow motion. Kaf babu wanda bai riƙe numfashi ba har Jadwah dake raba ido. Saida ya fara Sao k'afar sa dake sanye cikin farin cambas da bakin wando sann ya Sanyo jikinsa dake sanye cikin bak'ar hoodie ya saka hula rigar kan farin P-cab dake kansa.

Had'adden Daimon Rolex dake hannunsa Jadwah ta kalla, da sark'ar data d'an ratso saboda sunkuyowa da ya yi wajen fitowa daga motar. Wani ingarman namiji ne ya fito hannun sa d'aya riƙe da jaka da yake k'ok'arin goyata a bayansa. Da yake ya juya mata baya bata samu damar gani fuskar sa . Yanda masu tsoron gida suka k'ara kamewa kaman basu numfashi yasa ta mayar da idan ta kansu, Ihun Asiya dake k'ara fitowa daga cikin gidan yasa ta mayar da hankali kanta. Ta canza kaya zuwa wata fitat doguwar riga harda d'an kwalliya kan fuskar ta. Har gwanda k'ananan kayan dake jikin ta da wannan data chanza. Baki Jadwah ta tab'e tana kallon wannan ikon Allah. Yanda Asiya tayi kansa gadan-gadan zata d'ane , ko me ya yi mata taci wani uban burki ya wuce ta da wata irin tafi ta kasaita da izaa zuwa d'aya sashen da ba'a tab'a buɗe shi ba.

Yana shiga Balaraba da Suwaiba na fitowa tana cewa

"Ina Mohan yake?"

Kaman Asiya itama ka kasa b'oye farin cikin ta. Tabbas kuwa Jalli karshe ne wajen tsubbu. Sai yanzu Jadwah ta fara ganewa. Wannan shine Big Brother data ji ana masa inkiya. Numfashi taja tana cewa a ranta tunda ba mugu bane bari ta rufe gate d'in. Rufe gate d'in tayi tana kallon Asiya da Balaraba da Suwaiba da sukayi b'angaren da Moha ya shiga.

Haka ta k'asara wanke-wanke taba tunani a ranta. Shi kuma ko da wane irin hali yazo? . Kayan ta kwashe bayan ta gama ta kai d'aki ta dawo tayi wajen y'ar tsalanta data ajiye a rana ko ta tashi. Tayi kuwa yanda take don haka ta d'auko ta koma k'ofar daki ta kunna risho ta d'ura tanda ta fara suyar y'ar tsala dataji Albasha ga had'edd'en kuli data daka musu a gefe. Tana gamawa ta juye flask ta durawa Baba kunin tsamiya. Saida ta gama ta gyara gurin sannan ta shiga d'aki ta d'auko tabarma ta shimfiɗa a baranda da d'an turaren wuta ta jera kayan abincin, kafin ta koma don tashin Baba , sai ta tarar ma ya farka. Ita ta taimaka masa ya shiga banɗaki ya kimtsa ya fito bayan ya yi brush.

Baba ta fara zubawa abinci sai murmushi yake mata yana saka mata Albarka. Taso ta gaya masa kyautar da Suwaiba tayi mata, amma tasan idan ya sani bazai bari ta bayarba, zaice mata babu kyau maida kyauta. Suna cin abinci tana kallon yanda Asiya da Balaraba keta zirga-zirga da kayan abinci sashen Moha. Jiki Asiya sai uban rawa yake ta kasa nustuwa. Kai kawai Jadwah ta girgiza tana yiwa bayani bakon daya zo. In banda shirme wan nata take yiwa wannan rawar jikin kaman wani saurayi?. Wai to shi menene dashi haka da Amina ma ke sonshi?. Daga inda ta hango shi tasan ingarman namiji ne ga uban tsayi. Banda wannan bata ga komai tattare dashi ba da yake zuzuta mata.

Hmm Allah ya kyauta. D'urawa kai wahala. In bata manta ba har sark'ar ta hango a wuyan sa. Allah ya shirya mana zuri'a. Sanin tarbiyar gidan yasa bata ji komai kan sark'ar dake wuyan sa. Domin tasan dukkanin su babu tarbiya daga uwar har ya'yan. Shi yasa wani lokacin rufin asiri alheri ne ga wasu.







𝗦𝗔𝗨𝗬𝗜𝗡
𝑳𝑨𝑴𝑨𝑹𝑰.




𝔸𝘚Η𝔸𝑵𝚃Ⲩ 𐐛૦𝚅𝞔.♡︎




𝐏𝐆 6.





Yau ya kama ranan asabar, kwana biyu kenan da had'uwar ta da Moha. Tun ranan da suka had'u bata k'ara ganinsa ba. Itama kuma dama bata damu da k'ara had'uwa dashi. A gurguje ta fito sanye cikin kayan makaranta da nik'af a hannun ta tana k'ok'arin sawa tayiwa Baba sallama ta fito daga gida. Saboda saukar su dake matsowa yasa kwana biyu ake musu interview mai zafi. Tana k'ok'arin buɗe gate taji kaman ana kallonta. Da sauri ta juya inda take tunanin idon na binta. Tsaye ta hango shi bakin barandar sa sanye da bakin singlet mai yankakken hannun da bakin wando. Wuyansa irin ear pod d'innan ne na turawa da suke sawa.

Gashinsa dake jike ya d'an zubo goshin sa zuwa idon sa. Suna had'a ido taji wani irin shock ya ratsa ta tayi saurin buɗe k'ofar ta fice k'irjinta na harbawa da sauri. Tana fitowa bak'ar motar Camry ta faka gabanta Amina ta fito daga cikin motar. Da d'an mamaki ta kalli Amina tace

"Au kema wai baki tafi ba?"

"Eh shigo mu k'arasa"

Bata musa ba ta shiga motar ta zauna tana juyowa idan ta ya fad'a cikin na Junaid dake kallonta ta mirror. Da azama ta d'auke idon ta tana tunanin inda ta sanshi. Murmushi Junaid ya yi yaja motar suka bar k'ofar gidan. Har suka k'arasa gate na makaranta ,Amina da Junaid na hira ita ta kasa tankawa saboda kallon da yake mata ta mudubi. A hanzarce ta buɗe motar ta fice Amina itama ta fito da sauri tana cewa

"Wai saurin me ki ke ne? Ki tsaya mana mu tafi tare"

Batace komai ba ta juya ta shiga ⁰⁰⁰⁰makaranta Amina ta bi da sauri. Da ido Junaid ya bisu har suka shiga makarantar kafin ya ja motar yana murmushi. Tunda suka shiga aji Amina ke neman hanyar da zatayi wajen ganin ta fara kafa gwamnatin Junaid wajen Jadwah kaman yanda tayi masa alkawari, tunda ita ba waya ce da ita ba. To ko bayan da suka tashi k'arfe 11 suna fitowa suka samu Junaid jingine jikin mota yana jiransu. D'an bata rai Jadwah tayi don ta lura da take taken su shida Amina. K'ok'arin wucewa tayi ta tafi Amina tayi saurin riƙe ta ta b'ata rai

"Wai me ki ke nufi ne? Yayan nawa ne ya zama abun gudu ko me?"

Kallon Amina tayi taga yanda ta b'ata rai sosai. Ajiyar zuciya taja badan taso ba ta juya suka shiga motar. Tunda ta shiga takejin idan Junaid kanta, amma taki kallon inda yake zaune har suka k'arasa k'ofar gida. Da sauri ta fice daga motar babu ko sallama, Amina ta sauke glass tana k'ok'arin yi mata magana aka buɗe k'ofar k'aramin gate aka fito . Ido suka zubawa Moha daya fito sanye cikin k'ananan kaya. Ash d'in riga mai gajeren hannu da blue Jean's. Rigar ta kama k'irjin nan ta kwanta ko ya ya motsa sai kaga jijiyoyin hannun sa. Kar kuso kuga idon Amina yanda ya buɗe kaman wata horror. Baki hangame take kallon Moha dake tsaye bakin gate d'in hannu zube cikin aljihun wando, fuskarnan a mugun turb'une.

Ido suka had'a da Jadwah da k'irjin ta ya fara harbawa da k'arfi itama ta tamke fuska. Juyawa tayi ta kalli Amina dake kallonsa kaman wadda ta warke makanta. Dariya ta kusa kwacewa Jadwah tayi saurin danneta tana kallon Junaid daya fito daga cikin motar da saurin yana kiran Moha.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login