Showing 12001 words to 15000 words out of 27897 words

Chapter 5 - SAUYIN LAMARI Book 1 HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

41

ihun su da hayaniyar su basuji bugun ba. Hankalina duk ya tashi na rasa inda zanyi a guje nayi b'angaren Moha. A haukace nake bugu ina kira kaman tab'abbiya. Babu zato aka buɗe k'ofar Moha ya fito sanye cikin kayan barci doguwar riga da wandon ta mai mad'auri. Ido ya d'an ware cike da matsanancin mamaki yana kallona. Ina kuka sosai na fara k'ok'arin yi masa magana muryar Asiya ya katseni

"Honey waye?"

Ido na zubawa Asiya data bullo ta bayansa sanye da kayan barci. Saurin kyifta ido nayi ina girgiza kai na juya da sauri zan bar gurin. Babu zato naji an rik'o hannuna . Wani irin shock ya ratsani ba juyo a razane ina kallin hannun Moha dake riƙe da nawa kafij na mayar kan manyan Blue eye's nashi daya kafeni dasu. Da wannan deep voice nashi yace

"What happen?. Menene?"

Tuni na manta da Asiya dake gefensa tana jifana da wani irin kallo, bare na tsaya tunanin abunda take sashen sa yanzu da daddare. Muryar ta na wani iri rawa nace

"Don Allah a taimaki Babana bashibda lfy"

Ido ya d'an ware damuwa naga ta bayyana kan fuskar sa kafij ya wuceni da sauri ya yi b'angaren mu na bishi da gudu. Ina jin Asiya na kiransa da wani irin b'acin rai.

"Moha ina zakaje?"

Dagani harshi babu wanda ya juyo inda take .ya rigani shiga d'akin mu. Yanda muka iske Baba na k'ara rushewa da wani irin matsanancin kuka don yanzu da kyar yake fisgar numfashi. A hanzarce Moha ya ciccibi Baba muka fito ina kuka sosai . Muna fitowa ya bawa d'aya daga cikin masu tsaro ya d'auko masa mukullin mota. A guje ya shige b'angaren sa bai jima ba ya fito da gudu da mukulli a hannun sa. Motar Moha ya buɗe ya saka Baba a ciki na zagaya jiki na rawa na shiga na rungume Baba. Ina jin ya fisgi motar a guje ya fice daga gidan.

Har mukaje asibiti kuka nake rusawa rungume da Baba da yanzu jikinsa ya saki gaba d'aya. Sai ka k'asa kunne sosai kake jin fitar numfashi sa. A hanzarce Moha ya faka motar ya fito da gudu ya zagayo inda nake riƙe da Baba ya sureshi ya yi cikin asibitin da gudu na rufa masa baya. A gaggauce aka karb'i Baba zuwa emergency. K'ofar d'akin na durkushe ina kuka sosai. Motsin mutum da naji gefena yasa na d'ago a hankali na kalli Moha dake durkushe kusa dani kaman yanda nayi. Numfashi ya sauke fuskar nan tashi d'auke da damuwa sosai kanta. Saurin d'auke ido nayi daga kansa. Har yau ban manta abunda ya yiwa Mahafina ba. Mun jima a durkushe k'ofa d'akin har sama da awa d'aya kafin likita ya fito . Da sauri na tashi nayi kansa jikina na rawa. Wani irin kallo ya watsamin na tsantsan pity kafin yace

"Ki shiga yana buƙatar ki. Kece Jadwah y'ar sa ko?"

Kai kawai na d'aga na kasa cewa komai saboda kuka dake cina. Da kai ya min nuni na shiga. A guje nayi d'akin da suka kwantar da Baba. Yana kwance kan gado cikin d'an k'ank'anin lokaci ya lashe ya yi wani fari kaman wanda bashi da jini a jiki. Ina gunjin kuka na na rungume Baba dake murmushi na tsantsan ciwo. Da kyar ya d'aga hannu ya rungumeni. Murya a shak'e yace

"Yi shiru ki daina Kuka. Naji sauki "
Sosai na k'ara matse shi ina kuka sosai. Ina ji aka buɗe k'ofar d'akin aka shigo. Ban damu da d'agowa naga waye ba na k'ara matse Baba ina sheshshek'a. Bansan ya akayi ba barci ya yi awon gaba dani na tsantsan wahala.

A hankali Baba ya d'ago ya kalli Moha dake tsaye gefensa fuskar sa cikin matsanancin damuwa. Murmushi Baba yace

"Nagode sosai d'ana"

Wani irin d'agowa Moha ya yi jin sunan daya kirashi dashi. Hawaye suka tarar masa a fuska. Hannu Baba ya mik'o masa Moha ya yi saurin motsawa ya kama a hankali yana kallon Jadwah dake barci sai ajiyar zuciya take ja.

"Nasan kai yaron kirki ne Muhammadu. Wannan hali da dabi'u naka ,nasan akwai mak'asudi da yasa kake aikata su. Ko wane irin bawa da kaddarar sa. Ina so ka riƙe Allah ,Muhammadu inshaAllahu komai zaizo maka da sauk'i. "

Wani iri sanyi jikin Moha ya yi kaman an zuba masa k'ank'ara. Rana ta farko a rayuwar sa yaji wani irin kunya da nadama Shaye-shaye sa yake .

"Ina son wata Alfarmar guda d'aya a gurinka Muhammadu. Ban sani ba ko ina da sauran kwana a gaba, amma ina neman taimakon ka saboda Allah "

Jikin Moha na rawa ya k'ara matse hannun Baba cikin nasa. Murmushi Baba ya yi ya d'ago d'aya hannun sa da akewa k'arin jini ya shafa kan Jadwah kafin yace

"Wannan yarinya ita kaɗai ce Allah ya mallakamin a wannan duniyar. Mahaifiyarta ta rasu watanni da suka wuce. Ita ce rayuwar mu. Ita d'in alheri ne a garemu nida mahaifiyar ta da bazamu tab'a samun sama da hakan ba. Alfarmar guda d'aya nake so kamin saboda Allah"

K'ofar d'akin da aka buɗe hankalin su gaba d'aya ya yi kan k'ofar. Wani kyakkyawan mutum ne ya shigo magidanci fari tas dashi,kana ganinsa kaga Moha. Tamkar ya yi kaki ya tofar. Murmushi Baba ya yi cikin ransa yana hamdala. Yasan komai zaizo masa da sauki.





Wane Alfarma ne ku ke tunanin Baba ke nema gurin Moha?





𝗦𝗔𝗨𝗬𝗜𝗡
𝑳𝑨𝑴𝑨𝑹𝑰.




𝒜ɱαȥιɳɠ ★'★ ɯɾιƚҽɾʂ ϝσɾυɱ
( 𝒜, ★ ʂƚαɾ'ʂ ,ɯ ★ ϝ)





𝔸𝘚Η𝔸𝑵𝚃Ⲩ 𐐛૦𝚅𝞔.♡︎






𝐏𝐆 8.





Numfashi naja a hankali na fara buɗe idona. Bansan sanda barci ya d'auke ni ba. Kallon Baba nayi dake barci cikin nutsuwa fuskar sa d'auke da murmushi. Wani Numfashin na k'araja na janye a hankali daga k'irjinsa na miƙe in salati. Mamaki ne ya kamani ganin rana tayi a hanzarce na shige banɗakin da nake tunanin cikin d'aki na d'auro alwala na fito. D'ankwalin dake kaina na cire na shimfiɗa na tada sallan asuba. A hankali na shafa Addu'ar dana gama na miƙe ina k'ok'arin d'auke d'ankwali na aka buɗe k'ofar aka shigo. K'irjina ya wani irin harbawa lokacin da idona ya sarke cikin nasa. Sanye yake da manyan kaya wata dakakkiyar farar shadda da tayi masa masifar kyau babbar rigar tasha surfani. Kanshi sanye da bak'ar hula data k'ara fito da ainihin kyansa. Kamshin da yake mai tsananin dad'i da sanyaya gabba ya yimin sallama naja dogon numfashi. Yaune fa d'aurin auren sa ko? Zuciyata ta tunatar dani.

D'auke idona nayi daga kansa na mayar kan k'ofar da ya k'ara buɗe ta sosai. Ido waje nake kallkn Gwagwo data bullo ta bayan nasa tana cewa

"Ina suke ne Muhammadu?"

A guje na tashi nayi kan Gwagwo ina kuka da kira. Wani irin d'ane ta nayi har muka kusa fad'uwa.

"Subhanallahi Jadwah zaki kadani. Yi a hankali kinsan ba lafiyar k'afa ce dani ba."

Bance komai ba na k'ara matse ta ina kuka sosai. Ban damu da idan Moha dake tsaye bayana saida Gwagwo ta janye ni daga jikinta da sauri ta shiga d'akin tana kiran Baba da har zuwa lokacin bai motsa ba. Barci yake mai tsananin nutsuwa da wani irin annuri da murmushi kwance kan fuskar sa. Numfashi naji Gwagwo taja mai k'arfi murya tana d'an rawa ta juyo ta kalleni kafin ta mayar kan Moha dake tsaye har zuwa lokaci.

"Kira Likita Muhammadu "

Bai musa ba ya juya da sauri ya fice Gwagwo ta juyo ta rungumeni sosai cikin k'irjin ta tana faman maimaita Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Rikicewa nayi na d'ago ina kallonta nace

"Gwagwo menene? Ko na tashi Baba ne ya ganki?"

Kai ta girgiza " barshi ya huta Jadwah. Yana samu hutun da bazai k'are ba"

Cikin rashin fahimtar maganan ta naja doguwar ajiya zuciya. Dr ne suka shigo da sauri da Moha. A hanzarce naga ya yi kan Baba yana tab'a k'irjin sa zuwa hannun sa kafin yasa abunnan kaman dutsen k'arfe ya fara tab'a k'irjin sa dashi. A yanzu na fara gane inda maganan Gwagwo ta dosa k'irjina ya fara wani irin harbawa da k'arfi numfashi ya faramin wahalar fita. Banyi zato ba naji wasu hannu masu tsananin laushi da kauri suka sauka kan kafad'ata. Luu nayi baya sai jina nayi cikin faffaɗan k'irjinsa. Muryar Gwagwo naji sama-sama tana salati Dr na cewa a fita dani daga d'akin. Cak naji ya d'auke kaman y'ar tsana ya yi waje dani daga nan idona suka rufe ruf.



"Muhammadu "

Gwagwo ta kirashi tana nufo inda yake tsaye bak'in gadon daya kwantar da Jadwah ana mata k'arin ruwa. Baisan wane irin yanayine yau yake ciki ba. Abubuwa da bai tab'a zato ba sun had'u sun chunkushe. Har yanzu he don't even know what his feeling a kanta .bai sonta haka kuma bai k'inta. Bazai tab'a iya watsawa mutum kaman Baba dake neman alfarma ba wajen sa yana kwance kan gadon tafiya Alfarma da yake nema gurinsa. A ganinsa karb'an wannan alfarmar da ya yi ,ya yi ta ne saboda abunda ya yiwa Baba. Gani yake amincewa da buƙatar Baban ita ne zaisa ya daina saka masa da rashin kunyar da ya yi masa. All this is to much for him. Asiya da Balaraba na can sun tada fitina tun da sukaji abunda ya faru. Asiya sai hauka take , Balaraba kuwa Alhaji Balarabe tasa a gaba tana gaya masa duk irin bak'ar maganan dake fitowa daga bakinta. Daya gaji da masifar ta yace mata

"Idan har kina insisting kan wannan abun daya faru saboda munyi taimako. To ki sani yanda ki ka ce ya aikata abunda ki ke umarta ce shi, itama Asiya hakan ne zai faru a gareta. So choose wisely"

Shi kanshi Balarabe matsanancin mamakin mayar mata da martani da ya yi yake ,bare Balaraba data zuba masa ido cikin matsanancin mamaki baki a hangame tana kallonsa. Yau ita ne take magana Balarabe ke mayarwa?. Kafin tayi wani yunƙuri ya fice daga falon gaba d'aya. Tsayawa ya yi bak'in k'ofar yana sauke wani irin numfashi. Ji yake kaman an yaye masa wata jijiya data d'aure masa harshe. Zai k'ok'ari yaga ya taimakawa Moha wajen ganin sun riƙe wannan amana da aka basu. Jikinsa na bashi kasancewar yarinyar da Moha babban alkhairi ne a garesu.


K'afad'ar sa Gwagwo ta d'an dafa tana cewa

"Har yanzu bata farka ba Muhammadu?. Y'an uwa kowa yana son ya ganta. "

A hankali yace "eh Gwagwo "

Numfashi taja ta cigaba da cewa" yanzu ya batun wannan magana. Da wane ido Jadwah zata d'auki wannan batun?"

Juyowa ya yi sosai ya fuskance ta yace

"Kiyi hak'uri Gwagwo amma ban shirya sanar da ita hakan ba yanzu. Bazanyi miki karya ba Gwagwo dagani har ita babu wanda yasan yanda d'an uwansa ke cikin ransa. Tabbas ita d'in amana ce a gareni kuma nayi alk'awari riƙe ta na tsawon rayuwata. Amma nida da ita muna buƙatar lokaci da zamu koyar da zuk'anta mu san juna har ya kaimu ga zama inuwa d'aya "

Murmushi Gwagwo tayi na manta "kana nufin na tafi da ita can Jordan ko A'a "

Wani irin shaking voice ya sauke a hankali yace

"Ina ganin hakan shine best dayafi dacewa. Muna buƙatar mu fara koyar da zuk'anta mu son juna. Zanyi k'ok'ari na koyawa kaina sonta kaman yanda zan koya mata sona"

" ni nasan kai yaron kirki ne kuma tabbas MUSTAPHA yaga hakan tattare dakai har ya iya damka maka y'ar tsa guda d'aya tak da duniya ta sheda so da kauna da yake mata. Ubangiji ya taya mu rik'o baki d'aya. "

A hankali ya amsa da Amin kafin ya juya ya fice daga d'akin. Kai tsaye gida ya nufa. Tun daga bakin gata ya hango Isma'il dake safa da marwa bakin gate rai a matuƙar bace. Numfashi yaja ya fesar ya tsayar da motar yana kallo Isma'il daya nufo shi kaman bijimin sa. Wani irin buga glass d'in window d'in ya yi yana maga da kumfar baki.

"Har ka isa kaci amanata. Wlh baka isa ba Jadwah tawa ce. Baka da right a kanta. Nike sonta kuma ni zan aureta. "

Kallo ya watsa wa Isma'il dake huci baice komai ba ya buɗe motar ya fito rai a matuƙar bace. Gate d'in ya buɗe ya koma mota ya shige gida. Isma'il ya biyo shi yana ihu. Hayaniyar Isma'il ta fito da Asiya da Balaraba da suke ta fama da ita saboda kuka da take ta rusawa. A hankali suka yo kanshi ya k'ara sauke wani ajiyar zuciyar kafin ya wuce ya yi b'angaren sa. Yana shiga suka shigo.

"TAHEER "

Balaraba ta kirasa da ainihin sunan sa na yanka. MUHAMMAD TAHEER. sunan mahaifin mahafiyar sa. Chak ya tsaya tsakiyar d'akin kafin ya juyo yana kallonsu fuskar na a turb'une.

"Wane irin magana nake ji haka?, wane irin cin mutunci ne wannan?wannan mara mutuncin mutumin duk irin kyautata masa da muke a gidan nan da abunda zai saka mana dashi kenan?, kuma ka amince da hakan saboda tozarci?"

Rai a matuƙar b'ace yake kallonsu baice komai. Balaraba ta cigaba da tsananin b'acin rai

" in har na isa da kai na baka umarni ina so yanzu nan ka cika shi"

"Are you done?"

Baki suka hangame Asiya ta k'ara rushewa da kuka. Wai what is happening ne? Mene ya jawo wannan SAUYIN? mene tayi ba daidai ba?.

"Idan har kina so nayi abunda ki ke so. Zanyi but da sharad'i she needs to go itama. I don't care if we just get married "

Ya k'arasa maganan yana jifan Asiya da wani irin kallon tsana. Gunji kuka kawai take Balaraba ta zuba masa ido cikin matsanancin mamaki abunda ke faruwa. Matsawa ya yi ya d'auki y'ar takarda daga cikin memo nashi ya ciro biro daga aljihun wandonsa. Wani irin kururuwa Asiya ta saki ta nufo shi aguje ta riƙe hannun tana kuka sosai . Baki Balaraba ta cije idonta ya yi wani irin ja na tsantsan bacin rai kafin ta juya fuu ta fice daga d'akin. K'ara riƙe shi Asiya tayi

"Na amince zan zauna. Kar ka sake ni don Allah "

In all honesty ya yi wishing su amince da sharad'in nan nasa ko ya saukewa kansa wannan nauyi. Numfashi kawai yaja ya fisge ya shige d'aki ya barta a nan. Zama ya yi gefen gado ya dafe kansa. Yanzu yake dana saninsa na zuwa Nigeria. He wish bai dawo ba wata kila da duk wannan dramn baza ta same shi ba. Shi kansa baisan mene ya dawo dashi ba in the first place. Suna ta hauka kan yarinyar da batasan menene ke faruwa ba. In all honesty shi kansa baisan mene zai faru ba next. Ta ina ma zai fara?.

A guje Asiya tayi b'angaren su ta sami mummy nasu da Suwaiba suna magana rai a matuƙar b'ace. Allah kad'ai yasan irin abunda ke cikin ran Suwaiba. Bak'in ciki da bacin rai abun har yafi na Asiya da Balaraba. Duk da haka bata cire kudurinta ba gani take hakan ma wata damace da zata cimma manufarta ta hanyar amfani da Asiya. A guje tayi wajen Mahaifiyar ta da tayi bene tana k'ok'arin kiran waya gabanta tasha tana nunata da hannu tace

"Laifin ki ne. Tuntuni saida nace ki sallame su ki ka k'i. Wlh in har ya sake ni sai nayi abunda sai ran kowa ya b'aci a gidan nan"

Tas Balaraba ta d'auke ta da mari tana huci. " ni zaki dinga yiwa maganan banza?. Kin fini jin zafin abunda ya faru ne?"

Da k'araji Asiya da bak'in ciki tace " eh na fiki. Yau rana ce ta farin ciki a gareni amma ta zama ranan bakin ciki saboda ke. Saboda kinsa cin masu gadi a gaba baki d'auki maganata da muhammanci ba. Ko kin d'auka bansan dirty little secret naki ba na kwanciya da masu..."

"Asiya " Balaraba ta kirata da wani irin k'araji ta kai hannu zata d'auke ta da mari Asiya ta riƙe hannun. Ita kanta bata san me yazo kanta ba da k'arfin ta gaba d'aya ta hankad'a Balaraba . Ihun Suwaiba dana Balaraba baisa Asiya taji d'ar abunda tayi ta ba, ta zubawa maifiyarta dake wuntsulawa kan bene tana huci. Gani take duk laifin tane. A guje Suwaiba ta tare Balaraba data sume saboda buguwa da kanta ya yi .

Fuuu Asiya ta wuce d'aki tana hucu. Suwaiba tayi saurin kira suka fita Balaraba daga gidan cikin gaggawa. Isma'il shima tuni ya fice daga gidan ya yi mashayarsa dake cike da y'an matansa.

Kwana d'aya Moha bai k'arayi ba a gidan ya bar gari bayan ya k'ara zuwa wajen Jadwah da har zuwa lokacin bata farfado ba. A daren ya shirya su gaba d'aya suka bar azare. Shi ya wuce UK wajen mahaifin sa daya rigashi tafiya. Jadwah kuma suka wuce JORDAN da Gwagwo.



Bayan kwana biyu.


Lokacin dana farka a gigice ina kuka da kiran Baba. Gwagwo ta shigo da sauri ta rungume tana lallashi. Ina kuka sosai nace

"Gwagwo ya mutu ko?"

Kai ta girgiza ta k'ara rungumeni. " ki kwantar da hankalin ki. MUSTAPHA yana nan da rai inshaAllahu. Wannan yaron da mahaifin sa mutanen arziƙi sun fita dashi waje don a bashi kulawa daya dace dashi"

Wani irin numfashi na sauke ina jin wani iri relief. Hawayen fuskata na goge ina kallon d'an k'aramin d'akin da muke cike mai d'auke da gado da kwaba. Sai kafet da aka shimfiɗe cikin sa. D'akin tsabtsab dashi sai kamshin turaren wuta ke tashi. Gwagwo badai tsabta ba. A hankali na mayar da ido na kanta

" su waye suka fita dashi?. Meke damun Baba ne Gwagwo "

"Wannan ubangidan naku. MUHAMMAD da mahaifin sa. Yaro d'an Albarka. Tunda suka fita dashi suke d'awainiya damu. Yaushe rabon dana ga nasa nama a baka?. Yanzu ki duba kitchen d'ina. Nama babu irin wanda babu"

Ta k'arasa maganan tana yar dariya. Shiru nayi ina kallon ta cikin rashin fahimta. Saboda me za suyi d'awainiya damu kuma?. Yaushe mahaifin nasa yazo?. Tambayoyi kala-kala cikin raina Gwagwo tace

"Likita yace ciwon cancer ke damunsa ya dade masa kuma a jiki har ya kai matakin da suke tunanin lokaci kad'an ya rage masa. Amma inshaAllahu da yardar Allah zai bashi lafiya tunda har wannan yaron ya tsaya masa . Alkwarine ya d'aukar miki wajen ganin ya yi duk abunda zaiyi dan samawa Baban ki lfy,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login