Showing 15001 words to 18000 words out of 27897 words
sai dai kuma hukunci na ubangiji idan ya yi kwanan nasa ya k'are "
Numfashi naja a hankali na fesar ina hamdala cikin raina. Amma na kasa gane dalilin da yasa Moha yake taimaka mana yanzu.
๐ฆ๐๐จ๐ฌ๐๐ก
๐ณ๐จ๐ด๐จ๐น๐ฐ.
๐ษฑฮฑศฅฮนษณษ โ
'โ
ษฏษพฮนฦาฝษพส ฯฯษพฯ
ษฑ
( ๐, โ
สฦฮฑษพ'ส ,ษฏ โ
ฯ)
๐ธ๐ฮ๐ธ๐ต๐โฒจ ๐เซฆ๐
๐.โก๏ธ
๐ต๐ถ๐ป ๐ญ๐ผ๐ณ๐ณ๐ ๐ฌ๐ซ๐ฐ๐ป๐ฌ๐ซ.
๐๐ 9.
๐ฝ๐พ๐๐ด/๐ท๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐
๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐บ๐จ๐ผ๐๐ฐ๐ต ๐ณ๐จ๐ด๐จ๐น๐ฐ. ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ . ๐บ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐
'๐๐ ๐ท๐จ๐ฐ๐ซ ๐๐. ๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐
'๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐
๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐.
๐ช๐๐๐ ๐๐ ๐๐ ๐๐
๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐.
Watana d'aya a Jordan na samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Y'an uwa da abokan Arziฦi duk sunzo yimin jajen jikin Baba. Damuwa da nake da ita yanzu ta d'an ragu dan Gwagwo kullum na k'ara kwantarmin da hankali jikin Baba na kyau. Tace saboda yanayin jikin nasa yasa ko waya bazai samu damar yi mana sai lokacin daya dace. Da farko na d'auka ko tana fad'an hakanne don ta kwantar min da hankali, amma ganin yanda take yi komai babu damuwa da yanda take gayamin Baba na nan da ransa ,zatona ya d'an kau. Wata d'ayan nan da nayi iyayen Amina da yayanta Junaid sunzo sun dubani ,nayi mamaki da naga babu Amina. Kafin su tafi ne muka d'an keb'e da Junaid k'ofar gida. Babu laifi na d'an sakar masa fuska. Mutumin daya b'ata tsawon awanni yazo duba ka bai cancan wulak'anci ba.
Numfashi yaja a hankali ya d'an kalleni kafin ya kawar da kai gefe ya bayan ya kira sunana. Kallon sa nayi nace "Na'am " Numfashi ya k'araja yana cewa "bazan miki k'arya ba Jadwah. Tun ranan dana fara ganinki na kamu da sonki. Saidai nauyin bakina daya hanani furtawa da wuri ya jawomin har ki kamin nisa. Hak'ika nayi bak'in ciki da faruwar wannan abu, amma hakan bazai hanani yi miki fatan alkhairi ba. Allah ya bad...."
"Yauwa Jadwah ,zo maza ki d'ura d'ura mana kunun madara Hajiya Fati na sha'awar sa"
Muryar Gwagwo ta katse Junaid bai k'arasa kalaman da yake furtawa. Numfashi naja na juya ina kallom Gwagwo dake tsaye bakin k'ofa. Kai na d'an girgiza kafin na juya kan Junaid da shima ke kallon Gwagwo ya juyo da idon sa kaina. D'an murmushi nayi masa da baikai zuci ba na wuce da sauri ina juya kalaman sa cikin raina. Kwata-kwata ban fuskanci inda ya dosa ba. Ina jin Gwagwo biye dani har kitchen saida taga na d'ura kunun sannan ta wuce falo suka cigaba da hira mahaifiyar su Junaid. Sosai Gwagwo ta had'a musu shatara ta arziฦi sai godiya suke ana ta raha. Da zasu tafi ne nake jin dalilin daya hana Amina biyo su. Wai bata jindaษi ne kuma tana tsakiyar jana jarabawa. Numfashi naja na fesar. Har cikin raina banji dad'in hakan ba. Dan dai kwana d'aya Amina ai tazo ta dubani ko babu komai tsakanin mu naci albarkacin zumunci.
Washegari bayan tafiyar su na fito daga wanka d'aure da zani da d'an hijabi. Ina shiga d'aki na samu Gwagwo zaune kan kujera riฦe da y'ar k'aramar wayarta torch kare a kunnen ta. Tana d'an d'aga murya tana magana
"to shikenan TAHEER hakan ma ya yi. To babu komai "
Kai Gwagwo da kwashe-kwashe take wlh. Waye kuma TAHEER?. Tunda nazo Jordan nasan Gwagwo ta jama'a ce. Kullum gidan cike yake da mutane. Samari ,manya da yara. Ko dan tana da barkwanci ne da faran faran. Gata Sam bata da rowa. Kusan samarin layin a nan suke cin abincin rana .ko duk lokacin da suka bushi iska zasu shigo neman abinci. Nima zama a gidan na fara sabawa da wasu. Mai na d'auko ina shafawa ina sauraran Gwagwo dake waya da wannan Taheee kafin ta kashe. Kallona tayi kaman zatace wani abu sai kuma ta girgiza kai ta juya ta fice na bita da d'an kallo. Baki na tab'e na cigaba da harkar gabana. Kafin zuwa azahar gidan ya fara cika da hayaniyar mutane dake ta safa da Marwah cikinsa.
Majina ta k'ara sharewa tana kallon kawarta Saudat. Tsaki Saudat tayi tana cewa da Amina
"Ai saida na gaya miki kiyi hankali da wannan yarinyar simi-simi kasauce. Kina ganin ta hakan wai ita saliha munafukace. Yanzu ba gashi nan taci amanarki ba. Tasan kina san Moha amma ta zagaye ta aure. Ke kuma da yake banza ce kin zauna kina ZUBDA HAWAYE kan wanda bai sani ba. Nace miki a kawai hanya da zaki same shi a saukake number nashi kawai zaki samo kiga aiki da cikawa. Idan ita bataji komai wajen butulci ba ke me yasa zakiji idan kin mayar mata da abunda ta aikata miki?. Wannan rayuwar fa kowa kanshi ya sani. Tun wuri ki newa kan ki mafita"
Majina Amina ta k'ara facewa idon nan sunyi jazur .har wani rama tayi saboda sawa kai damuwa. Tsana da k'iyayyar Jadwah sunyi mata katutu a rai. Sam bata damu da auren sa da Asiya ba tunda tuntuni tasan da wannan. Kuma a ganinta Asiya bata isa ta hana ya sota ba. Babban bak'in cikinta Jadwah. Ta san yanda take masifar son shi amma ta zagaya taci amanarta. Ashe tasan abunda take tsabar munafurci idan tayi mata zancen sa tayi ta kushewa. Kwafa tayi ta sharce hawayen dake fuskarta tace da Saudat
"Yanzu menene abun yi? ,in har number nashi ne ba abu ne mai wuya ba. Nasan Ya Junaid bazai rasa ba"
Murmushi Saudat tayi " abunda za'ayi ki shirya yanzu zan kai ki wajen Malami dake min aiki. Cikin d'an k'ank'anin lokaci kema zaki samu Moha. Taya ki ke tunanin nake juya wannan alhazawan cikin yatsun hannuna?"
Murmushi Amina tayi ta miฦe da sauri tayi b'angaren Junaid. Da sallama ta shiga shiru babu kowa. D'akin sa tayi kai tsaye nan ma bayanan sai k'arar ruwa da takeji daga banษaki. Dad'i ne ya kamata hango wayarsa da tayi kan gado . Da sauri ta d'auko wayar ta buษe tana bincika number Moha. Wajen number biyar suka bayyana ko wacce k'asar ta daban. Duka ta kwas.he numbobin don bata san da wacce yake amfani ba yanzu.
Karya sukayi wa Maman su suka fito da zummar zasuje dubi wata k'awar su da bata da lfy. Can kasan ran Amina abunda take shirin yi tana d'an shakkar sa amma inta tuna cin amanar da Jadwah tayi mata sai taji tsananin b'acin rai da tsanan ta.
Suna zuwan wajen Malami kaman yanda Saudat tace. Ya gama bincikensa ya d'ago yana kallon su yana wani lashe lebe yace.
"Mafita guda d'aya ce. Wannan yaran da ki ke so yana da burin ganin ya hayayyafa da yawa. Yana da son yara. Zan iya juya mahaifar matars da yake zaune da ita yanzu ta hanyar da bazata tab'a iya haihuwa ba. Ke kuma zaki shiga gidansa ki hayyafa ta yanda zaki kasance ke kaษai ce cikin zuciyar sa. Amma fa da sharad'i guda d'aya "
Ido Amina ta zuba masa tana jiran taji menene sharad'in. Lashe harshe ya k'arayi
"In har kina son hakan ya tabbata dole ki shiga wannan d'akin yanzu"
Ya nuna mata wani k'ofar d'aki mai duhu. Ido Amina ta zaro matsanancin tsoro ya rufeta ta shiga uku. Anya kuwa zata iya wannan abu?. Tayi alkwarin ajiyewa Moha budurcinta na har abada. Ganin damuwa dake kwance kan fuskar Amina kaman tana son janye kudurin nata Saudat tayi maza tace
"In har kina son Moha wannan ba komai bane. Ki sawa ranki kin same shi kin gama sai yanda ki ka yi dashi kuma bazai tab'a rabuwa dake ba. Abunda ki ke damuwa dashi bazai tab'a ganewa ba .akwai hanyoyi da dama da zaisa bazai gane ba. Kedai karki damu ina tare dake"
Numfashi taja mai k'arfi ta fesar. Tabbas maganan Saudat gaskiya ne. Akwai hanyoyi da yawa. In har burinta zai cika zata mallaki Moha za tayi komai a kansa. Kai ta d'aga ta kalli d'akin kafij ta miฦe tayi ciki. Murmushi Saudat tayi Malam ya miฦe da sauri yabi bayan Amina. Malam an samu y'an shila bai damu wai Amina budurwa bace ya zage yana juyata sai sumbatu yake yayinda Amina keta ihin azaba ga uban wari da hamami da Malam yake.
Saida ya gurji Amina san ranshi sannan ya fito zuciyar sa fes sai washe jajayen hak'oran sa yake. Da kyar Amina ta iya fitowa sai sharce hawaye take . A hankali ta zauna kusa da Saudat daketa jera mata sannu. Zama Malam ya yi gaban k'asar sa ya yi wani rubuce-rubuce kafin ya d'ago yana kallon Amina dake share hawaye.
"Kina da number nashi?"
Da kyar ta iya d'aga kai. "To maza a kirashi yanzun nan. Duk inda yake zaizo gareki"
Amina najin wannan batu ta wartsake jiki na rawa ta fara neman number Moha. Saida taki wajen uku a kashe ta hud'un ne number shi ta US ta shiga. Wayar na fara ringing Amina ta dafe k'irjinta dake tsananin bugawa kaman zai tarwatse. Har ta fidda rai zai d'auka sai taji wannan muryar mai tsananin taushi da gardi ta ratso speaker wayar
"Hello"
Wani iron d'auke numfashi tayi ta kasa cewa komai saida Saudat ta zungureta. Muryar a hankali tace
"Ya Moha"
Shiru ya ratso wayar na y'an mintina kafin taji yace
"Who is this?"
"Amina ce"
"Amina" Ya maimaita sunan da wata irin murya data kaaa fuskartsa. Da ido Malam yace yi mata nuni ta kashe wayar. Bata musa ba ta kashe do gaba d'aya ta rud'u bata Sam abunda zatace ba.
"Wannan kiran nashi da ki ka yi. Baza ki k'ara ba daga yau. Shi zai dinga kiran ki a ko da yaushe. Ki tsaya ki gani. Aikina yankan wuk'a ne a take yake ci"
Ya k'arasa maganan da wani irin murmushin mara kyau kam fuskarsa. Yana rufe baki kuwa wayar Amina ta fara ringing. Wayyo Allah ran Amina kaman wacce aka yiwa albishir da Aljanna.
SOME WEEK'S LATER.
US.
A gajiye ya faka mota harabar motoci. A hankali ya fito sanye yake da k'ananan kaya farar riga mai botira da bakin jeans. Kayan sunyi masa kyau sosai duk da rashin barci dake tattare dashi. Kai tsaye cikin gidan sa ya nufa tun daga k'afar bene ya fara balle botiran rigar sa ya cireta ya wurgar. Yana buษe k'ofar d'akin sa ya tsaya turus ya k'ara wara ido yana kallon Asiya dake kwance kan gadonsa da wasu y'an iskan kaya a jikinsa. Yaushe tazo nan har tasan inda yake zaune.? Wani irin mayen kallo Asiya ke masa tana bin murdadadden k'irjin sa da kallo zuwa fatar cikinsa dake shak'e da Abs. Lebe ta lashe ta taso tana wata y'ar iskar tafiya sai tana juya Mazaunai ta nufo shi. Ido kawai ya zuba mata fuskarnan babu expression harta k'araso gabansa ta tsaya. Hannu ta kawo a hankali zata d'ura kan k'irjin sa ya wani riฦe hannun kaman wanda ya riฦe kashi.
"Are you mad? What are you doing in my house?"
"Gidan ka? Gidan ka kai kad'ai? Nima ai gidana ne. Ai ba laifi bane idan mata tazo wajen mijin ta"
Taune harshe ya yi yana kallonta da wnai irin tsana. Kina matsayin mace amma kece ke nuna maitar ki kan namiji. Yana kallon yanda take wani kashe ido tana cije lebe ya wurgar da hannun nata kafin ya juya da sauri zai bar mata d'akin. Da azama tasha gaban sa
"Gaskiya abunda ka ke kana d'aukan hakkina. Yau watanmu nawa da aure? Tunda ka bar Azare baka k'ara waiwayata ba bare ka duba Mummy dake kwance gadon asibiti. Kasan ni dai ba dutse bace dole na buk'aci mijina tunda an daura shi yasa nayi tattaki nazo har inda ka ke"
Haushi takaici yasa ya zuba mata manyan ocean Blue eye's nashi ya kasa cewa komai. K'ara matsowa tayi sosai k'irjin ta kad'an ya rage bai had'u da nashi ba. Da wata y'ar iskar murya tace
"Kaima nasan kana buฦatar haka. Ba waliyi bane ba kai. Ka bari muji dad'in juna. You will enjoy this yanda baka tunani"
Wani irin shafo k'irjin sa tayi zuwa nipples nashi wani irin shock ya ratsashi .yana jin sautin numfashin ta daidai wuyansa tana k'ok'arin kai masa sumba. Kaman rad'a yaji wannan murya mai tsananin taushi da dad'i cikin kunnan sa kaman iska
"MOHA"
firgigit ya wartsake daga trans daya shiga daidai Asiya na neman had'e bakin salu . Wani irin ja ya yi da baya labbanta ya sauka kan iska. Idonta dake rufe ta buษe tana kallon Moha daya juya da sauri yana sauka daga kan benen. Bata san sanda ta saki ihu na frustration ba tana kallon sa har ya fice daga gidan gaba d'aya. Da ihu ta shige d'aki tana jifa da dukkanin abunda taci karo dashi. A mugun buk'ace take ga Jojo bata nan. Rashin sanin abunyi ya haye gadon da hoton Moha tana saukewa kanta ishin dake damunta. Ihunta da sunan sa kawai ka ke ji yana tashi cikin d'akin.
A guje ya fice daga gidan shi kansa bai san inda ya nufa ba. Abubuwa ne sai kara jagule masa suke. Gefen titi ya faka motar ya koma ya kwanta jikin sitiyarin motar yaba sauke numfashi. Can ya d'auko wayarsa yana k'ok'arin kira kiran ya shigo masa waya. Ido ya zubawa number Amina dake yawo kan screen nashi. Wai what is happening to him ne?. Sam baya jin yarinya cikin ransa but ya rasa dalilin da yasa ya kasa cireta cikin ransa haka ya kasa daina kiran wayarta a kullum. Ya kasa hana kanshi neman aurenta duk da cewa can k'asan zuciyar sa bashi da wannan burin. Numfashi yaja mai k'arfi ya k'ara wayar a kunne.
A shagwaษe ta kirasa kaman za tayi kuka
"Big Brother ko nayi maka laifi ne yau?"
Saida ya fursar da numfashi yace " No. Sorry nayi busy ne yau. "
Murmushi tayi " OK dama nace bari na sanan da kai abubuwan dana shirya na bikin da event da zamuyi"
"Hmm"
Kawai yace harta gama b'ab'atun ta baice komai ba sai OK. Suna gamawa ya kashe. Tunda ya tura mahaifin sa neman Auren ta bayan neman shawarar Gwagwo ta bashi had'in kai d'ari bisa d'ari. Shi yasa yake son matar duk da sanin matsayin sa gurin Jadwah . Sam bata da son kai. Numfashi yaja mai k'arfi ya fesar yana maimaita sunan JADWAH kan leben sa. Lokaci ya yi da ya kamata yaje ya ganta. A hankali ya d'auko wayar ya lalubo number Gwagwo ya danna mata kira.
Miฦewa nayi ina mik'a bayan na idar da sallan isha. Gwagwo dake kwance kan gado har ta fara munshari na kalla nayi y'ar dariya na gyara mata bargo. Garin yau sanyi ake sosai sabida ruwa da aka wuni anayi. Kan tawa katifar na nufa ina k'ok'arin cire hijabin dake jikina. Rigar barci nasa mara nauyi na samu guri na kwanta ina Addu'a tunanin Baba fal cikin raina. K'arar wayar Gwagwo yasa na d'ago da sauri ina kallon gefen Gwagwo da wayar ke ajiye. Da azama na tashi na d'auko wayar ina kallon suna TAHEER JIKA NA da Gwagwo tasa. Baki na tab'e na d'aga wayar da y'ar sallama
"Hello, Slma"
Wani irin shiru ne ya ratsa wayar sai numfashi da naji an sauke a hankali. Shirun nima nayi ina sauraran ko zaice wani abu.
"Gwagwo tayi barci"
Nace ina cigaba da sauraran yace wani abu. Haushi ya kamani na cire wayar daga kunnena ina d'an tsaki . Da wata irin rad'a naji ance "JADWAH " sai kuma diff wayar ta katse. Baki na hangame ina kallon wayar da tunanin waye ne kuma wannan? Ina kuwa nasan wannan muryar?.
๐ฆ๐๐จ๐ฌ๐๐ก
๐ณ๐จ๐ด๐จ๐น๐ฐ.
๐ธ๐ฮ๐ธ๐ต๐โฒจ ๐เซฆ๐
๐.โก๏ธ
๐๐ 10.
Washegari ban gayawa Gwagwo kiran da akayi mata na cigaba da sabgogin gaba. Bayan kwana biyu da faruwar hakan yau muna zaune tsakar gida ina yiwa Gwagwo kalba. Duk da cewa shekaru sunja amma gashin Gwagwo har yanzu da tsayin sa da santsin sa, da kyar yake kamuwa .gashi ne har gadon baya. Baba da Ammi na basu da gashi sosai, amma ni kuwa gashina har hip's d'ina yake nayi gado wajen Gwagwo. Gashi baki mai tsantsi. Numfashi naja mai k'arfi na fesar Gwagwo ta d'an juyo tana kallo na.
"Lafiya ki ke sauke ajiyar zuciya? "
Murmushi nayi da baikai zuci ba nace
"Wlh Gwagwo ina son cigaba da karatu na. Yanzu lokacin saukar mu ya gabato za'ayi babu ni. Bansan ya ake ciki game da saukar ba. Zaman gidan ne ya isheni. Ina son na cigaba da karatun boko ma"
Kai Gwagwo ta jinjina kaman mai tunanin wani abu tace
"Kina da gaskiya. Bari za muyi magana da TAHEER naji yanda za'ayi "
"Waini Gwagwo waye wannan Taheer d'in ne da komai zakiyi sai kin nemi shawarar sa?"
Nayi magana da jin haushi. Y'ar dariya kawai tayi batace komai. Washegari na tashi da kiran Gwagwo. Miฦa nayi na miฦe zaune ina kallon agogo dake kafe jikin bango. Numfashi naja a hankali na miฦe ina salati. Hijabi na d'ura kan rigar barcin dake jikina na fito nayi falo inda nake jin muryar Gwagwo na kira. Baki na turo da d'an shagwaษa na d'aga labulen d'akin ima cewa
"Waini Gwagwo kiran na menene haka kaman zaki fasamin dodon k..."
Maganan tawa ta mak'ale sakamakon tsarkewa da idona ya yi dana Big Brother. Wannan manyan Blue eye's nashi sun kafeni da ido. Dum k'irjina ya buga nayi saurin d'auke nawa ido na k'arasa shiga falon na samu guri kusa da Gwagwo na zauna.
"Yauwa kin taso. Maza ki gaidar da Muhammadu. "
A hankali na d'ago inda yake zaune sanye da k'ananan kaya. Farar riga mai botira da bak'in wando sai bak'ar jacket d'aya d'ura kan rigar tashi. K'asa k'asa nace
"Ina kwana?"
Bai amsa ba sai ido kawai daya zubamin ko kunyar Gwagwo dake zaune gurin baiji. Rai na k'ara b'atawa Gwagwo tace
"Maza jeki deb'o masa Kiddirmun nan da ki ka hada akwai ragowar sa da gashin naman nan"
Ban musa ba na miฦe da sauri na fice daga falon ina jin idansa na bina. D'aki na koma na fara chanza kayan dake jikiba zuwa doguwar riga bak'a da d'an hijabin ta, sannan na fito nayi kitchen. Kiddirmun da na had'a mana jiya da daddare daya sha kwakwa da inubi na d'auko na zuye cikin glass jug da cup