Showing 9001 words to 12000 words out of 27897 words

Chapter 4 - SAUYIN LAMARI Book 1 HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

44

Sai a lokacin ya d'auke idon sa daga kan Jadwah ya mayar kan Junaid dake tunkaro sa. Ganin haka Jadwah ta rab'a da sauri ta gefen sa ta shige gida ta ya bita da kallo ta gefen ido.

Kan benci ta samu Baba riƙe da radio yana ji. Har k'asa ta durkusa ta gaishe shi kafin ta shige d'aki ta chanza kayan makarantar ta zuwa doguwar riga d'an k'aramin hijabi mai hannu daya tsaya mata gwiwa. Kai tsaye ta fito don d'ura musu abincin rana. Shinkafa ta fara d'ura ta koma kan kayan miya ta gyara su ta wanke sannan ta samu guri ta zauna kusa da Baba tana jajjaga kayan miya. Babu zato Moha ya shigo ta k'aramin gate nasu. Kallo d'aya tayi masa ta d'auke kai ta cigaba da jajjagenta tana jin Baba na gaishe shi cikin girmamawa. Wani irin tukukin bak'in ciki ya d'arsu a ranta. Kaman mahaifin ta zai zubda girma yana gaisa da yaron daya haifa.?
Bai amsa ba ya wuce fuskar nan tashi babu emotions bare ka gane abunda ke cikin ransa. Baki Jadwah ta ciji har wasu hawayen bak'in ciki suka taron mata a ido ganin Baba Sam bai damu da abunda Moha ya yi masa ba, saima murmushi dake kwance kan fuskarsa . Haka ta gama abincin ranta na matuƙar suya. Wajen la'asar Suwaiba ta shigo gidan yauma dai maimakon ta wuce ciki bayan Jadwah da buɗe mata gate, sai ta faka motar ta fito har inda Baba suka gaisa da d'an girmamawa. Mamaki sosai ya kama Jadwah dake kallon yanda ta saki fuska sosai suna magana da Baba, kafin ta kalli Jadwah da wani abu kan fuskar ta ta miƙo mata leda mai kyau.

Harshe Jadwah ta taune tana kallon ledar. Sam ranta bai kwanta ba amma saboda idan Baba dake kanta ta matso cikin girmawawa ta karb'i ledan tana mata godiya. Kaman ance ta d'aga kai idan ta ya sarke dana Moha dake tsaya jikin window na saman d'akin sa fuskarnan da wani irin expression. Da sauri ta d'auke kai ta wuce d'aki da ledar a hannu. Cikin bakko ta tura ledar bata ma buɗe taga meke ciki ba. Maimakon ta fito saita samu guri ta zauna har saida taji Suwaiba tayi sallama da Baba ta wuce ciki. Ajiyar zuciya ta sauke mai k'arfi tana tunanin. Wai menene yasa kwana biyu mutanen nan suke neman shiga rayuwar ta ne?.


Washegari suka tashi da hayaniya ta motoci dake sunturi a gidan. Manya mata ne suka dinga turuwa zuwa da y'an mata. Kafin la'asar an fara k'awata farfajiyar gidan da kujeru. Daga Jadwah har Baba suna zaune gefe suna kallon shige da fice da ake. Wajen La'asar saiga Amina ta shigo idon nan ya yi jazur alamun taci kuka ta koshi. Da mamaki sosai Jadwah ke tambayar ta meke damunta. Amina na kuka sosai take ce mata taron da ake na d'auren Asiya ne da Moha. Wannan taron na yau wai pre-wedding d'insu ne . Nan da sati biyu masu zuwa za'a d'aura aure.
Baki Jadwah ta tab'e tana kallon Amina dake rusa kuka kaman wadda aka cewa uwarta ta mutu. Mtsww taja tsaki. Ita ta rasa menene da Moha haka da Amina take masa irin wannan so haka.


Wani irin jifa ya yi da remote d'in TV dake hannun sa ya juyawa Balaraba baya dake zaune ta d'ura k'afa daya kan d'aya tana kallonsa calmly. Da k'araji ya k'ara damke wayar dake hannun sa yace

"How could you Dad. Did you even aske me?, what age nake yanzu da ake neman yimin auren dole?"

Numfashi Balarabe yaja ta cikin wayar murya a matuƙar sanyaye yace

"Son, please. Kabi umarnin Mahaifiyar ka. Da kai da Asiya duk d'aya ne. I'm sure you will be happy da wannan choice d'in. Relax "

"Relax " Moha ya maimaita da wani irin mocking voice ya cigaba.
"Your telling me to relax ?. Are you even for real dear father ?. I refuse to be her puppet just like you. And she's not my mother "

Da k'araji Alhaji Balarabe yace da b'aci rai. " what did you just call me?"

Bai bashi amsa ba ya kashe wayar ya yi wani jifa da ita. Azafafe ya juyo kan Balaraba dake zaune har zuwa lokacin da murmushi kwance kan fuskarta. Abun mamaki yanda ya juyo da fushi da tsananin kiyayya. Kalaman dake kan harshen sa ya kasa furtawa kaman wanda aka d'aure harshe da mukulli. Matsanancin mamakin abunda ke faruwa dashi yasa ya zuba mata ido yana kallon ta. Murmushi ta k'arayi ta tako da wata tafiyar izza har inda yake tsaye tana kallonsa da k'ananan idonta . Hannu ta d'an had'a guri d'aya tace

"Good. Ina muka tsaya?. Yauwa. Yau ne pre-wedding naka kai da Asiya. I expect you ka shirya ka fito kuyi hutona. Kar kayi wani abu da zai b'atamin rai. Kaman yanda mahaifin ka ke gudun b'acin raina. I hope xaka bani had'in kai kar ran kowa ya b'aci. "

'I hate you ,you witch' abunda zuciyar sa ke furtawa kenan amma harshen sa ya kasa furta shi. Wani murmushin Balaraba tayi ta juya tana kallin agogon dake hannun ta tace

"Ka shirya nan da minti talatin. Nasa Isma'il ya gayyato dukkanin wasu abokan ka na nan zasu zo nan da minti ashirin. So get ready"

Har takai bakin k'ofa ta juyo " au na manta. Saboda abune na manya zamuyi kyauta na mota da gidaje guda ashirin. Iya na yau kawai saboda duniya tasan za'ayi biki na y'an gata. So ina son yanzu kasa hannu kan takardun da zamu bayar zan aiko Isma'il ya karb'a. "

Tana gama fad'a ta fice ta barshi a tsaye kaman wanda aka d'aure. Saida ta fice ya iya motsi yaja wani irin dogon numfashi. What just happen.? Tambayar da yake wa kansa kenan. And worst abun tsintar kansa ya yi ya deb'o takardu na gidaje da motoci yana saka hannu kaman wani robot. Is like kaman zuciyarsa da gangar jikinsa sun d'auki different part. Zuciyarsa nace masa A'a. Jikin sa kuma na aikatawa dan dole. What is happening to him?.

Kaman yanda Balaraba tace kafin la'asar gidan ya cika da abokan Moha . An k'awata harabar ko a turai sai haka. Kudin da aka kashe wajen kawata gurin saika riƙe baki. Balaraba da Suwaiba sunsha ado kaman bazasu mutu ba. Ana yin Salla Asiya ta fiti cikin wani arnen gown red mai shegen kyau. Sosai tayi kyau sosai anci mutunci kayan. Gefenta wata baturiya ce dake mak'ale da ita duk inda tayi. Ba'a dade da fito da Asiya ba Moha ya fito cikin wata arniyar Maroon three pieces suit data kama jikin nan. Ya yi masifar kyau duk da yanda fuskarnan take a mugun turb'une kaman wanda ke jira a bashi bindiga ya harbe mutane.

Amina na hango shi cikin abokan sa ta k'ara rushewa da matsanancin kuka ta tashi a guje ta fice daga gidan. Ikon Allah, Jadwah da Baba suka bita da kallo. Da damuwa sosai kan fuskar Baba yace da Jadwah

"Jadwah lfy ko kinyiwa Amina wani abune?"

Haushi da takaici yasa ta kasa cewa Baba komai sai hateful gaze nata data mayar kan Moha. Yanda ta juya do wannan kallon tsanan sai karaf idonta ya fad'a cikin nashi da tun fitowar sa yake kallon ta. Kafe juna sukayi da ido haushi da takaicin sa na k'ara nunkuwa cikin ranta. For the first time tun zuwan Moha Nigeria ya saki wani d'an k'aramin crack smile da kad'an leben nasa suka motsa. Idan ba ka zuba masa ido ba baza ka tab'a kula da wannan SAUYIN yanayin tare da Shiba. In second murmushi ya b'ace daga kan fuskar sa ta koma expressionless. Blinking Jadwah tayi ta d'an buɗe baki da mamaki. Abunda ta gani hakane ko kuwa idonta ke gane mata ba daidai ba?.

Hutona akayi ta yi ango babu annuri kan fuskarsa. Asiya duk tabi ta kanannade shi babu ko kunyan mutane. In banda tsaki da girgiza kai babu abunda Jadwah ke yi gashi duk lokacin da hakan zai faru sai sun had'a ido da Moha. Idonsa baya hanata jan tsaki da disdain dake kan fuskarta. Anyi taro abun ba'a cewa komai. Kaman yanda Balaraba tace haka akayi kyauta ta gidaje da Motoci. Jadwah sai tsinewa almubazzaranci take. Idan kyautar ce suyiwa wanda suke da buƙatar ta mana, amma sai kansu suke k'ara ginawa.


Har wajen shad'aya mutane nata shige da fice. Asiya na mak'ale da Moha ta kanannade k'afad'ar sa kaman zata koma ciki. Irin matsanancin b'acin rai da yake ciki abun sai wanda ya gani. A karo na ba adadi ya k'ara kwace hannun sa data sarke da nata. Wani irin kallon tsana ya watsa mata amma ya kasa furta kalaman dake kan harshen sa. Da frustrating ya miƙe a zafafe ya yi cikin d'akin sa Asiya ta biyo shi da sauri. Da azama ya shige d'akin tana k'ok'arin sawo kai ya bugu k'ofar da mugin k'arfi sai goshin Asiya. Ihu tasa saboda azaba ta koma baya riƙe da goshi tana kuka. Tayi tunanin zai buɗe ya dubata amma harta gama kukan ta babu alamun zai buɗe k'ofar. Kwafa tayi ta juya rai b'ace tai sahen su. Can uwar d'akin ta ta samu Jojo daga ita sai pant da bra. Kallo d'aya Asiya tayi mata ta fara had'iyar yawu.

Jiki na rawa ta maida k'ofar d'akin ta rufe tayi kan Jojo data taso suka had'e tsakiyar d'akin. Wani irin rungume juna sukayi suna sumbatar juna kaman zasu cinyae kansu. Tuni suka raba Asiya da kayan jikinta suka haye gado. Kafin kace mene gurnanin Asiya da Jojo ya fara tashi cikin d'akin. Salo-salo suka dinga yiwa juna tuni Asiya ta ajiye Moha a gefe ta gigice tana sumbutu kan abubuwan da Jojo ke mata.

B'angaren Moha cikin wani irin fushi ya nufi k'aramin fridge nashi dake cikin daki ya d'auko kwalba ta whiskey ya fara diddika babu ji babu gani. Duk girman ta saida ya zuge ta tas. Cikin d'an k'ank'anin lokaci kuwa ta fara aiki kansa ya juye. Fushi da b'acin ransa komai ya dawo masa sabo. Fitowa ya yi yana tangadi yana neman inda zai huce fushin sa. Daidai Baba na mayar da gate ya rufe bayan fitar Suwaiba da wasu mata. Kai tsaye ya yi wajen Baba da muryar irin ta y'an Shaye-shaye yace

"Kaaasaniii auren ta doleee baaa?, too sai kayi....dana.. sani. Your Evil Dad"

Da mamako sosai Baba ke kallon Moha dake layi gabansa sai sumbatu yake babu kan gado kafij ya chakumi kwalar Baba yana cewa

"I hate you Dad"

"Alhaji. Alhaji Moha baka da lfy ne?. Ni ne Baba Maigadi. Ko a kira Hajiya?"

"K'arya ne. Dad. Kayi tunanin ban gane ka ba?"

K'ara shak'e wuyan rigar Baba ya yi da numfashi ya fara masa wahalar fita. Jadwah dake kwance barci ya fara d'aukan ta taji y'ar hayaniyar ta miƙe da sauri ta fito. Ido ta ware ganin yanda Moha ya shak'e mata uba sai kakari yake yana k'ok'arin kwatar kansa da ce masa bashi bane. Wai wani irin red ta gani bata san sanda tayo inda suke ba da wani irin gudu ta saki ihu da iya k'arfin ta ta d'aga hannu ta zubawa Moha kyawawan maruka lafiyayyu har guda biyu. Zafin marin babu shiri ya saki Baba ya dafe kunci yana kallon Jadwah cikin matsanancin mamaki.

Wani irin kuka Jadwah ta fashe dashi tayi kan Baba dake zaune d'abar a kasa riƙe da wuya yana tari. D'agowa tayi ta watsawa Moha kallo, matsanancin tsana da kiyayyar sa kwance kan idonta. Tuni marin da tayi masa yasa shi wartsakewa daga duniyar buguwa daya tafi ya zuba musu ido cikin matsanancin mamaki. Shi Moha aka mara? Marin ma yarinyar k'arama y'ar maigadi?




𝗦𝗔𝗨𝗬𝗜𝗡
𝑳𝑨𝑴𝑨𝑹𝑰.




𝔸𝘚Η𝔸𝑵𝚃Ⲩ 𐐛૦𝚅𝞔.♡︎




𝐏𝐆 7.



Matsanancin mamaki yasa shi k"amewa a tsaya kaman wadda aka dasa dafe da kunci. Yana kallon Jadwah ta kama Baba suka shige d'aki. Saida suka b'ace masa ya yi blinking idon sa ya k'ara blinking. Da muguj b'acin rai ya juya sashen sa zuciyarsa na dukansa kan dalilin da yasa ya kasa aikata komai kan yarinyar data mareshi. Yana shiga ya zube kan doguwar sufa daka falon bai jima ba kuwa barci ya yi gaba dashi ranshi a mugun b'ace.

Har suka shiga d'aki Jadwah kuka take. Baba dske zaune yana kallonta ya yi murmushi ya kama hannun ta ya zaunan kusa dashi baice komai ba. Sun jima a zaune a har Baba ya samu barci tana zaune tana kissima abubuwa cikin ranta. Fita tayi ta d'aura alwala tayi nafika raka'a hud'u kafin ta zauna tana tilawa ko ranta zaiyi sanyi. Cikin ikon Allah kuwa barci ya fara d'aukan ta ta rufe Qur'anin ta kwanta tana Addu'a. Wannan zafi da b'acin rai dake cinta ya kau sai ajiyar zuciya da take.

Washegari wajen k'arfe bakwai Moha ya farka daga barcin da yake mai nauyi. A hankali ya miƙe zaune dafe da kanshi da yake masa wani irin ciwo. Yunƙurawa ya yi ya miƙe ya shige d'akin sa. Wanka ya yi sannan ya fito d'aure da alwala . Saida ya fara saka doguwar riga fara sannan ya kalli gabas ya yi sallan asuba. Har ya idar da sallan kansa na sarawa ya kai hannu ya dafe. Bai tab'a samun hangover irin na yau ba. Yana nan zaunen abunda ya faru jiya ya fara masa rushing kwanyar kansa. Ware manyan idonsa ya yi ya riƙe hab'ar sa. Innalilllahi mene ya aikata haka?. Tunda yake a rayuwar sa bai tab'a cin zarafin wani ba. Babba ko yaro. Meke damunsa haka? Bazai manta kallon tsana, kyama da kiyayya da yarinyar nan tayi masa ba. For the first time a lifa nashi yaji ,yaji kunyar ganinsa da wani ya yi cikin halin maye. Wani irin numfashi yaja mai shaking ya miƙe ya zauna gefen gadon sa dafe da kai. Taya zai fara gyara wannan abu da ya yi?. Ya jima a zaune yana ta sak'awa da warwarewa kafin yaja dogon numfashi ya miƙe ya fito. K'ofar falonsa ya tsaya yana jin shakkar buɗewa. Numfashi yaja mai k'arfi ya kama murfin motar ya buɗe. Da Baba dake zaune can barandar su ya fara cin karo zaune kan benci da carbi a hannun sa. Baida Jadwah ba don haka ya fito da sauri k'irjinsa na harbawa. Da ido Baba ke kallon Moha daya tunkaro shi kanshi a k'asa.

Har ta k'araso gaban Baba bai iya d'aga kai ya kalleshi ba saida ya tsugunna sannan ya d'ago. Da d'an mamaki kan fuskar Baba ke kallonsa. A hankali ya d'an d'ago a mugun kunyace ya fara gaisar da Baba daya amsa fuska d'auke da mamaki. Numfashi Moha ya k'ara ja kafin ya cigaba da cewa

"Don Allah kayi hak'uri Baba da abunda nayi maka jiya. Ba halina bane, bansan meke kaina ba?"

D'an murmushi Baba ya yi yana girgiza kai yace

"Kar ka damu Alhaji, ni ai tuni na yafe maka"

Wani irin numfashi Moha yaja ya d'ago yana kallon Baba dake masa murmushi . Yana k'ok'arin k'ara cewa wani abu Jadwah ta shigo riƙe da d'an bokiti k'arami a hannun ta.


JADWAH POV.


Turus na tsaya ina kallon Big Brother dake durkushe kusa da Baba. Tuni raina ya b'aci tuna irin nakastamin mahaifi daya so yi daran jiya. Da sauri na k'araso ina jifansa da mugun kallona na tsana da k'iyayya. Kusa da Baba na tsaya don yasan shirye nake na k'ara zuba masa wasu marukan idan har ya yi niyar k'ara cutarmin da mahaifi. Daga shi har Baba murmushi naga sunyi kafin yana kallona da wani abu cikin kwayar idonsa dana kasa gane shi. A hankali naga ya miƙe tsaye still idonsa na kaina cikin zuciyata sai d'ura masa zagi nake . Ido muka k'ara had'awa dashi ya had'e leben sa guri d'aya kafin ya juya a hankali bayan ya yiwa Baba sallama ya wuce na bisa da muguwar harara. Muryar Baba ta katsemin tunani nayi saurin d'auke ido daga kan Moha dake nufar sashen sa

"Har anyi markad'en ne"

"Eh Baba bari na fara soya mana rana nayi"

Ina maganan ina k'ok'arin juyawa kan barandar mu. Wajen juyawar ne idona ya kai k'ofar d'akin Moha. Yana tsaye jikin k'ofar hannun sa kan murfinta amma idonsa na kaina. Baki na cije irin na ban haushin nan na watsa masa harara lebene na motsawa a hankali 'mashayin Banza da wofi' . D'an murmushi naga ya yi ya buɗe k'ofar sa ya shige naja d'an k'aramin tsaki. D'aki na shiga na ajiye hijabi na saka k'arami kafin na fito na d'ura mana kosai da kunun gyad'a.

Kwana biyu tunda nazo na same shi tare da Baba yanzu yana yawan fitowa wajen barandar sa ya zauna. Wani lokacin haka zan kamashi ya kafeni da ido kaman bak'in maye. Duk irin harara da k'ananan manganu da nake jefe masa masa baisa ya daina kallon nawa saima murmushi da zakaga ya yi, hakan kuwa ba k'aramin konamin rai yake ba. Muguwar tsanan sa na k'ara ruruwa cikin raina. Ga Amina tun ranan data tafi take kwance wai babu lfy ta d'urawa kanta wahala zata hallaka kanta a banza a wofi. Ita kanta matar tashi da zai aura kar kuga irin sintiri da rawar kai da take sashen sa, haka zata fito wani lokacin tana kuka. Jaraba kenan.

Ance rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya. Satin bikin Moha da Asiya ya gabato. A gobe juma'a za'a d'aura aure. Yau tun safe nake safa da Marwah bak'in gate. K'afafuwa sunyi kugin gajiya. Amma duk da haka na hana Baba tayani. Har fad'a saida ya yi mun nayi mirsisi dashi. A daren yau na alhamis na farka k'arfe d'aya saboda nishin Baba da nake juyowa daga d'aki da gudu na fad'a d'akin nasa na sameshi akwance cikin wani irin mawuyacin hali. A guje nayi kansa na rungume ina kira. Saboda hannuna kawai ya iya riƙewa cikin mawuyanci hali numfashi na masa wahalar fita. Wani irin kuka na saki na miƙe a guje na fito nayi sashen Hajiya Balaraba dake dake cike da bak'i . Duk da cewa dare ne hayaniyar su ta cika gidan ta ko ina. Jiki na rawa na hau buga k'ofar ina kira cikin matsanancin kuka. Saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login