Showing 9001 words to 12000 words out of 37256 words

Chapter 4 - MATAR ABBANA COMPLETE HAUSA NOVEL

03 Sep 2025

2234

can ki dauka kije kisiyo wake ki gyara"

Hafeeza taturo d'an qanqanin siririn bakinta gaba tace"Inna wake kuma?"

Inna tace" gashi kuwa kinbawa kanki amsa?"

"Inna jibi fa Saukarmu kuma yanzu goben ma sai munyi qosai?"


"idan bamuyi sana'ah ba dame zamu rufawa kanmu asiri? kitashi kije kisiyo nace"

Cikin fishi ta dauki kud'in tafice daga gidan, bata zame ko'ina ba sai gidan Maqociyar su Maman Fadila.
Maman Fadila tana ganinta tace"Alhamdulillah dama gidanku zanje yanzu,Baban Fadila ne ya siyo miki takalmi, Nima ga material na dinka miki,kinga material din yayi Kala da hijabin da'aka raba muku a islamiya wanda zaku saka awajan sauka,kinga saiki saka material d'in naki"

Lokaci d'aya farinciki ya mamayeta, ta daka tsalle ta rungume Maman Fadila tana zuba mata godia, Maman Fadila tayi murmushi tace"ni ki daina yimin godia Hafeeza kamar qanwata haka nake jinki,yanzu de meyafaru kika shigo da 6acin rai?"

Hafeeza ta Yatsina fuskarta tace" Wai Inna ce tace naje nasiyo wake gobe zamuyi qosai, shine nazo in fada miki ko zaki mata magana,jibi fa saukar mu, kuma dan Allah kamar mu mukafi kowa neman kudi kwana biyun ma ba zamuyi haquri ba?"

Maman Fadila tayi murmushi tace"Haba Hafeeza,yanzu idan badan kuna wannan sana'ar ba tayaya zaki kai kud'in saukar ki makaranta? Nan jiya Baban Fadila ya zauna yana yabonki yana cewa bakida girman kai kina kokarin nema muku abinda zaku rufawa kanku asiri to yanzu kuma karki bani kunya mana,Inna kamar mahaifiyar ki ce,duk abinda tafada miki me dadi da marar dadi kiyi haquri wataran sai labari,idan Gaddafi ya shirya ma rana daya zamu dauke ki mu kaiki can gidansa saide kizowa Inna ziyara"

Hafeeza tanajin wannan maganar kunya ta kamata,ta kalli Maman Fadila tace" Maman Fadila nawane Sauran kudin dakika ragemin wanda zan sai kayan kwalliya dashi?"

Maman Fadila tace" Dubu uku da dari takwas ne, kona dauko miki Zaki biya ta shagon ki siyo?"
Hafeeza ta Girgiza kanta tace"a a, kawai ni abar kayan kwalliyar, kibawa yaro ya siyo nama kiyi wa Gaddafi Farfesu anjima zaizo da daddare, kinga saina hada da kayan rabon nabashi nasa tun yau ko?"

Maman Fadila tace"haba Hafeeza,kayan kwalliyar ma idan kin siya ai shi zakiyi wa kwalliyar,ki bar kudinki kisai kayan kwalliya irin na yanmata, Shikuma idan yazo saiki zo ki dauki qullin kayan rabon ki bashi"

Lokaci daya Hafeeza ta sauya,cikin damuwa tace"Maman Fadila idan na kashewa Gaddafi kudi ban fadi ba, Dan Allah ki barni ayi masa Farfesun tunda ni kwalliya ba damuna tayi ba"

Maman Fadila ta saki Ajiyar zuciya tace"eto hakane, shima kuma tunda saukar taku tazo ai nasan zai bada contribution dinsa kinga sai mu sai lemon talakawa dashi"

Cikin murna Hafeeza tace"niko be bani komai bama babu komai"

Maman Fadila tace"um su Hafeeza masoya, irin wannan soyaiya haka"

kunya ta kama Hafeeza, cikin sauri tafice daga gidan tatafi wajan siyo wake tana dariya.



*** *** ***


Da yamma suna zaune afalo duka su ukun,Kaka ta zubawa tv ido tana kallo, Husna ta ajiye wayar hannunta wadda tagama karanta azkar din yamma, ta kalli Hassana tace"Sister kitashi muje mu gyara wa Yaya dakinsa,kinga baya raina datti ko Ya yake,karyazo gobe yace bamu gyara masa dakin sa da kyau ba, kekuma kin zauna sai faman karatu kike, jibi de zamuyi saukar nan kowa ya huta"

Kaka ta kallesu tace"gyaran dakin me? har wani gyaran daki zaku masa? meya hana yayi aure matarsa ta masa? babu wanda zai gyara masa daki"(=?2?)

Husna ta kalleta tace"Kaka an dade ba'a gyara masa dakin bafa"

Kaka tace"wanne irin dadewa? Naga ga dakin nasa nan ko giftawa kazo yi ta wajan qamshi ne yake tashi"

Hassana ta ajiye Alqur'anin hannunta tace"muje driver yakaimu supermarket muyi cefane nasan yanason farfesun kaza sai muyi masa mai dad'i dan yasan cewa muma yanzu mun qware a girki"

Kaka ta kalli Hassana tace"wacce irin kaza kuma ana zaune lafiya? ku kuwa kuhuta mana, kullum kuna cikin girki ku rabu dashi goben kafin jirgin su ya sauka sai muyi order ko Fizza ce"

Hassana da Husna suka kalli Kaka,zasu gyara masa daki tahana su tace idan yanaso yayi aure matarsa ta gyara masa, yanzu suna qoqarin siyo abun cefane suyi masa girki shima ta hana, basusan me Kaka tataka ba.
Husna tasaki murmushi takoma cikin kujera tayi kwanciyar ta,cikin zuciyarta kuwa Allah-Allah take gobe tayi domin taga yanda Kaka zata qare tsakanin ta da Yaya Hafeez.



*** *** ***


Kamar yanda tasaba sassafe tafita wajan suyar qosanta, kamar kullum yauma Hijabi ne ajikinta dogo har qasa,hijabin yayi wa farar fatar ta kyau sosai mai launin ruwan toka me duhu,kyakykywar doguwar fuskar ta tayi kyau sosai acikin hijabin,mutane ne zagaye da'ita tana zuba musu qosai akan takarda sannan tasaka acikin Leda tabasu, yayinda wasu samari agefe suke tsaye suna jiranta wasu a mashin wasu kuma zaune suke daga gefe suna jira tasaka musu suci abunsu anan.

Wani dayake zaune akan machine yana jira asaka masa yazuba mata ido yana kallon kyakykywar fuskarta, dad'i yakeji idan yana ganin yanda take komai cikin nutsuwa da kamewa, bayaso yabar wajan yadena kallonta hakan yasa dazaran layi yazo kansa saiyace kada ta damu ta sallami wasu tukunna shiba sauri yake ba(>?-?)

Adede lokacin motocinsa guda uku da sukaje dauko shi daga Airport sukazo wucewa ta wajan,hankalinsa yanakan jaridar dake hannunsa yana dubawa,daga tinted glass din motar tasa kamar wasa yaga uban mutane sun taru awajan, hakan ne yadauki hankalinsa har ya ajiye jaridar hannunsa akan cinyarsa yamaida hankalinsa wajan yanaso yaga me akeyi awajan da mutane suka taru har haka, adede lokacin yaron da Hafeeza ta zubawa qosai ya matsa daga wajan har fuskarta tayi nasarar bayyana.
Cikin sauri Hafeez yasake gyara zamansa yana kallonta, qosan daya gani agabanta tana soyawa shine yasa lokaci daya yaji wata irin fad'uwar gaba wadda ya dade rabon da yaji irinta,wannan qosan datake soyawa shine yatuno masa da wasu shekaru dasuka shud'e acan baya tun kafin a haifi 'yanbiyu.

Fuskarsa babu walwala ya kalli Danladi driver yace"juya baya Danladi"

Cikin bin umarnin sa Danladi yace"to Yalla6ai"

Yayi kwana, suma sauran motocin dasuke bayansu sukai kwana,suka sake dawowa cikin layin akaro na biyu,suna zuwa daidai wajanda Hafeeza take soya qosai ya tattara nutsuwar sa ya maida wajan,adede lokacin ta dago kyakykywar fuskar ta tana magana da wata mata dazata kai Yara makaranta da alama yaran nata ta tsaya zata siyasa qosan.

Fad'uwar gabansa bata sauyaba, saima sake jin wata fad'uwar gaban dayayi sanadin kallon fuskar yarinyar,ahankali yasaki wani irin murmushi, ya kalli driver akaro na biyu yace" Danladi asake juyawa" (=?F?)

Danladi yayi murmushi yasake juyowa akaro na biyu, suna sake juyowa wajan yace"dakata"

Danladi yacika umarni ya tsaida mota, sauran motocin ma suka tsaya suna mamakin yanda suke maimaita hanya daya, sun wuce ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?akaron farko,sannan sun sake dawowa akaro na biyu, sau uku kenan suna zagaya wajan.
Kafin su gama mamaki sukaga Danladi yafuto da sauri yabudewa Yalla6ai mota, cikin sauri suka futo daga tasu motar suna qoqarin tambayar sa ko akwai abinda yakeso,da hannunsa ya dakatar dasu hakan yasa dole suka tsaya,.

Ahankali yasaka hannunsa yacire jacket din jikinsa,hakan yasa nan take kallo daya zaka masa ka hango yanda jikinsa ya mummurde tacikin suit din musanman dantsan hannunsa,ta gefensa wuyansa kuwa ga zanen tattoo nan yafuto sosai kamar ba dan Musulmai ba, yayinda kunnansa na dama yake saqale da dankunne, hannunsa d'aya yazura cikin aljihun wandon sa sannan yanufi wajanda Hafeeza take suya gadan-gadan.

mamaki yagama kashe dandazon mutanan dasuka rakoshi suna tunanin me Oga Hafeez zaiyi awajan yarinyar,?
shi Kansa Hafeez tafiya kawai yake,banda fad'uwa babu abinda gabansa yakeyi, wanda shi akaran kansa yarasa dalilin fad'uwar gaban.





Complete document 1k


8621296018
Amina Muhammad
fcmb

kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034






Amnah El Yaqoub
' [5/24, 10:40 AM] El Yaqoub: =ؘ?MATAR ABBANA=ؘ?
(Luv Story)



Writing By Amnah El Yaqoub

Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update=?G? https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45



5




Shi Kansa Danladi driver mamaki yake me yalla6ai zaiyi da qosai? kode shima yana so ne kamar yanda Hajiya Kaka take yawan aikoshi wajan yarinyar siyan qosai?
kasancewar babu wanda zai bashi amsar tambayar sa yaja bakinsa ya tsuke.

Hafeez kuwa, bai daina jin fad'uwar gaba ba har saida yaje wajan,daga gefenta ya tsaya shima kamar yanda yaga sauran mutane sun tsatstsaya, mutane da yawa kuwa sai kallonsa suke, daga cikinsu wasu tunani suke da alama ba musulmi bane irin kiristan nan ne masu zama acikin hausawa saboda sunga dankunne guda daya a maqale a kunnansa na hagu, ga kuma zanen tattoo a hannun sa kasancewar ya d'an tattare hannun rigar tasa kadan.
Tunda ya tsaya awajan idonsa akanta yake,ba komai ne yafi daukar hankalinsa da'ita ba sai idonta, idanuwan nata sunyi masa kyau kamar idon jarumar fina-finan India wato Ashwariya, ba normal idone kamar na kowa ba.
Ganin tana qoqarin tsame na cikin man da alama yagama soyuwa hakan yasa ya laluba cikin aljihun wandon sa yaji wayam babu kud'i sai wata takarda dayaji guda daya,sai yanzu ne yake tunanin mema yakawo shi ne?.

Ahankali yasake shafa dayan aljihunsa, ya dauko wallet dinsa yabude, saide itama babu kudi sai dubu daya aciki, yayi mamakin ma yanda akai yasamu dubu dayan aciki saboda yariga yasan cewa shiba ta'ammali yake da kud'i a hannu ba saide transfer kawai kokuma yabada Atm dinsa,inde ya zauna da kudi kuma takarda to saide dollars.

Bai saurari mutanan dasuke jiranta ba,yasake matsawa kusa da'ita yamiqa mata dubu dayan, cikin muryar sa me aji yace"Abani"

Duk da kud'i yake bata, Koda wasa bata dago kanta ta kalli wanda yake bata kud'in ba,kanta yana sunkuye, saide wani daddadan qamshin Turare daya cika mata hanci wanda tunda take a tarihin rayuwarta zata iya cewa bata ta6a jin qamshin Turare me dadi kamar wannan ba, amma hakan baisa ta dago ta kalli mamallakin qamshin ba.
Ahankali ta meqo siraran yatsun ta ta kar6i dubu d'ayan daya bata, sannan tafara zuba masa qosan,yanda ta sunkuyar da kanta tana zuba masa qosan hakan yasa hular hijabin jikinta ta danyi baya kadan, har sumar kanta me laushi tafara bayyana.

Harta gama zuba masa qosan tabashi idonsa yana kan lallausar sumar gashinta daya hango.
Ahankali Yajuya yabar wajan, yana qarasawa wajan motocin da suka dauko shi aka bude masa yashiga motar, sannan suka dauki hanyar gida, Danladi driver mamaki yake kode duka jikokin Kaka suma sunyi gadon cin qosai ne kamar ita? yasan cewa rana daidai ne baya zuwa wajan yarinyar nan yana siyawa Hajiya Kaka qosai, to kuma yau abun mamaki yaga shima Oga kwata-kwatan da kansa ya yatsa yasiya, to Kaka yasiyawa Qosan kokuma shine zaici?.
Bama wannan ne abun tambaya ba,duk saboda siyan qosai yasa suka sake zagaye layin har sau uku kokuma saboda yarinyar datake qosan ne?(>??)

Bai gama tunanin sa ba yaji Hafeez yace"dakata Danladi"

Cikin bin umarninsa ya dakata, Hafeez yamiqa masa ledar qosan dake hannunsa sannan yayi masa nuni dawani almajiri yace" kabashi wannan"

Babu musu Danladi ya kar6i qosan yabawa almajiri, sannan yadawo motar sukaci gaba da tafiya, tunani yaci gaba dayi to idan Yalla6ai yabayar da sadakar qosan daya siya hakan yana nufin ba qosan ne ya birgeshi ba, yarinyar datake saida qosan ce ta birgeshi,idan hakane kuwa wannan aiba qaramin abun farinciki bane,duba da yanda Yalla6ai din hatta su mutanan gida sun san cewa ba ma'abocin shiga sabgar mata bane,da alama itade Malama mai qosai kakarta ta yanke saqa.(=??)

Suna qarasowa gida yadauki jacket din suit dinsa a hannunsa, yayinda hannunsa d'aya yake cikin aljihun wandon sa, cikin takunsa na qaqqarfan namiji yanufi falon nasu Danladi yana biye dashi da qaramar jakarsa.

Yana shiga falon 'yanbiyu suka taho da gudu suna masa oyoyo, saide suna zuwa kusa dashi suka tsaya turus suka kasa rungume shi, sai shine cikin aji ya d'an jasu zuwa jikinsa kad'an ya rungume su, lokaci daya kuma ya sakesu, fuskarsa babu walwala yace"ya kuke"

Atare suka had'a baki sukace "Alhamdulillah Yaya"

Daga haka bai qaraba,yawuce kan kujera ya zauna, adede lokacin kaka ta futo daga dakinta tana dariya, cikin farinciki ta nufeshi ta zauna akusa dashi sannan ta jashi jikinta ta rungume shi,babu musu ya kwantar da kansa akan qirjinta tareda lumshe idonsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya,ya dade rabon da yaji nutsuwa irinta yanzu daya ji shi ajikin kakar tasu, wadda ta maye musu gurbin uwa da uba, sun dauki lokaci ahaka sannan yatashi daga jikinta yace"Nasameku lafiya Kaka?"

Cikin farinciki Hajiya Kaka tace" ras!,kalau muke Hafeezu,Yaya wajan aikin naku?"

Fuskarsa a kame kamar Koda yaushe yace"Alhamdulillah"

Kaka ta kalleshi tace"Hafeezu kullum fuskar ka a cunkushe yau daya de kayi fara'ah mana gaka ga yan'uwanka,menene yafi gida da yan'uwa dad'i?"

Ataqaice yace mata"to Kaka"

Kaka ta girgiza kanta sannan ta dora hannunta akan murdaddan dantsan hannunsa tace"Kaga yanda kasake zama gardi? mutane dayawa cewa zasuyi kafi shekara talatin"

Dan qaramin murmushi yayi kawai yace"uhm...."

Sannan yafara qoqarin cire agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa.

Husna ta kawo masa ruwan gora ta zuba masa a cup, sannan ta zauna tad'aga dinkin su da suka karbo daga wajan tela cikin shagwa6a tace"Kaka Allah wannan dinkin kamar na koma na maida masa nakeji"

Kafin Kaka tayi magana itama Hassana tace"eh wallahi, yatashi yamana kaya da uban fadi kamar buhu,kiga fa yanda yabar wajan hips dinnan da fad'i to tayaya zamu cika wannan wajan,? Kuma fa saida ya gwada mu, amma yamana wannan wajan hips din me girma,ina mu ina wannan abun, wannan ai saide Hips din HAFEEZA 'yar ajinmu, tana sakawa zata cika shi, dan Allah Kaka ki barmu muje mu maida masa ya rage mana"

Ta qarasa maganar cikin shagwa6a.

Hafeez ya kallesu sai yanzu yasake ganin yanda yaran suka sake zama cikakkun yanmata,sai wata ta6ara suke suna shagwa6a, haushi ya kamashi da alama Kaka tagama sangarta yaran,ji yanda suke shagwa6a saikace qananun Yara,ji yake kamar ya lakad'a musu d'an iskan duka, yatsani sakarci a rayuwar sa.(=?#?)

Baqin ciki ne ya hanashi magana,Yara ko kunyar sa basaji agabansa suke maganar Qugu harda kawo zancen Qugun wata sakarya.(=?2?=?F?)
Ahankali yatashi yawuce dakinsa yana 6alle botiran gaban suit dinsa,Kaka ta bishi da kallo harya shige dakinsa, sannan tadawo da kallonta wajan 'yanbiyu tace"rashin aure yana damun Hafeezu, gaba d'aya a firgice yake"(>?-?)

Ko minti biyu beyi da shiga dakin nasaba yafuto yana kallon 'yanbiyu fuskarsa a daure yace"Meyasa baku gyara dakin nanba?"

Cikin sauri Husna tace" Yaya zamu gyara Kaka tace mu barshi karmu gyara wai....wai..."

Takasa qarasa maganar kamar yanda Kaka tace idan yayi aure matarsa saita gyara masa, shakkar sa yasa ta qare maganar tata da wai... wai...

Kaka ta kalli Husna tace" wa? ni?, to yaushe akai hakan bansaniba?, gaskiya bansan anyi ba"(>?-?)
tafadi hakan tana kawar da kanta gefe.

Hafeez yadawo cikin falon ya zauna ya d'ora qafa d'aya kan d'aya fuskarsa a d'inke,yanda ya 6alle botiran gaban rigarsa hakan ne yabawa lallausan gashin dake kwance a qirjinsa damar bayyana.

Yanda sukaga fuskarsa a daure to tsaf zai iya kai musu duka, hakan yasa sum-sum suka wuce dakin nasa suka fara gyara wa.

Kaka kuwa kallonsa tayi taga ran nan nasa yayi baqiqqirin, tasaki ajiyar zuciya tana kawar dakai.

juyawa yayi ya kalleta suna hada ido tasake kawar dakai, ya dauki fillon kujera yanufota dashi kamar zai jefa Mata yace"keko"

Hajiya Kaka tasake daure fuska tace"Toni nasan yaushe akai hakanne?"

Kansa ya Girgiza kawai,domin kuwa yasan aikin ta ne.

Kasancewar dakin nasa ba datti yayi sosai ba, hakan yasa cikin qanqanin lokaci suka gama gyara masa, babu musu yatashi yashige, saida ya sakawa qofar d'an qaramin falon nasa key,sannan yashiga can cikin dakin shima yasaka key, yasaki ajiyar zuciya yafara zare kayan jikinsa saida yacire komai yadawo naked,sannan yashiga wankan sa.


Yadade yana lailaye jikinsa da mayuka da turaruka masu shegen dad'in qamshi,kafin ya kalli qirar jikinsa a cikin babban madubin dayake dakin nasa,shi kansa yasan cewa Allah yamasa halitta ta Ingarman namiji me jini ajika,yanada cikakkiyar lafiya hakan yasa Koda yaushe yakejin sa akan network, yasan cewa abunda Hajiya Ramla tagani Kenan shiyasa ta liqe masa,har yanzu yanajin baqin ciki idan yatuna yanda tasa qazamin hannunta ta ta6a masa abunsa,Allah ma ya kiyaye ba hannun nata ta zira cikin wandon sa ta ta6a abun skin to skin ba, ya tabbatar da haka tayi da shikkenan tagama cutarsa duniya da lahira, qarin baqin cikin ma yanda yakasa yimata musu alokacin.

Dan qaramin tsaki yasaki sannan ya dauki pant irin na maza yasaka, yadauki gajeren wando yasake sakawa, sannan ya shirya tsaf cikin qananun kaya yafuto daga dakin nasa yanata zuba uban qamshi.

Zama yayi akusa da Kaka sannan ya kalli Hassana yace"ke bani abinci"

Hassana ta kalli Kaka, sannan ta dawo da duban ta gareshi tace"Yaya wallahi Kaka ce ta hanamu, saida na cewa Husna muje muyi shopping saboda girkin da za'a ma, shine Kaka tace kar muyi, saika kawo matar aure tukunna"

Hassana tana gama fadar haka falon nasu yayi tsit...., Hafeez ya juya ya kalli Kaka,cikin sauri Kaka ta dauke kanta tana ta6e baki. (9&?)

Zamansa ya gyara sosai yana kallonta sannan yace"saboda naqi yin aure horon yunwa za'a fara min a gidan nan?, zanzo daga wata qasa amma kinamin horon yunwa Kaka?"

Kaka tace" ikon Allah, wai duk yaushe akai hakanne? ban ta6a jiba"

Husna tace"lalle ma Kaka,yazaki zame ki barmu aciki? kece fa kikace karmuyi,za'a yi order fizza"

Kaka tace" mecece wata Fizza kuma ni Rabi'atu? inani ina wata Fizza saboda Allah?"(>?-?)

Kafin 'yanbiyu subata amsa tajuya ta kalli Hafeez tace" kaikuma nadawo gareka, dakake cewa saboda kaqi yin aure nakema horon yunwa ai zancen bana kaqi yin aure bane, baka dai samu wacce zata amince tayi haquri ta aureka bane saboda baqin miskilancin ka"

Hafeez yasaki ajiyar zuciya ya lumshe idonsa batare daya tanka ba, yana jinsu su ukun suka shiga kitchen suka shirya masa abincin da yafi so, bayan sun ajiye masa abincin ko kallonsu baiyi ba,saida Kaka tayi da gaske, ta lallasheshi kamar Baby, sannan yatashi yafara cin abincin kamar bayaso, ganin haka yasa Kaka ta kar6i spoon din tafara bashi abincin da kanta.

Da yamma yasake wanka yashirya cikin manyan kaya,farar shadda ce a jikinsa harda babbar Riga, yayi kyau sosai kamar ranar daurin aurensa, sosai turare yake ambaliyar qamshi a jikinsa yafuto zai tafi masallaci wayarsa tana kan kunnansa yana magana da Babban abokinsa Ma'aruf.
Kaka tace"dakata Hafeezu"

Juyowa yayi ya kalleta bayan ya kashe wayar.

Kaka tace"ina zakaje haka kayi wannan kwalliya?"

Ataqaice yace" zanje masallaci"

Cikin hikima irinta tsofaffi Kaka tace"to Hafeezu acire wannan d'an kunnan mana,ai zakafi kyau idan ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login