Showing 15001 words to 18000 words out of 37256 words

Chapter 6 - MATAR ABBANA COMPLETE HAUSA NOVEL

03 Sep 2025

2233

miqa mata wayar hannunta iPhone me camera uku, Hafeeza ta kar6i wayar tana murmushi har dimples dinta suna lotsawa.
Hassana ta rungume Husna sannan itama tace"kuma ki tabbatar munyi kyau sosai ehe, idan bamuyi kyau ba saikin sake mana sabo"

Hafeeza ta girgiza kanta tana murmushi sannan tafara qoqarin yimusu photon da qyar kasancewar bata ta6a riqe babbar waya irin wannan ba, tarasa yanda zatayi ta dauki photon, batasan yanda ake photon ba.

Su Husna suka sauya style, Hassana tace"kin dauka?"

Hafeeza tace"A a ban dauka ba"

Husna tace"har yanzu de baki dauka ba?"(>??)

Lokaci d'aya Hafeeza duk ta rikice, tarasa yanda zatayi, yanda ta rikice din saita sake yiwa Hafeez kyau wanda yake tsaye ajikin motarsu yana kallonta,mayan kayan dake jikinsa sun sake qawata kyansa,sosai ya shagala wajan kallonta saide miskilancin sa ba zaisa ka gane cewa kallon arziqi yake mata ba.


Cikin zazzaqar muryar ta tace"narasa yanda zanyi ne, ku sake matsawa kusa"

Cikin sauri 'yanbiyu suka matsa suka sake rungume juna.

Hafeeza ta qoqarta ta dauke su, sannan cikin zazzaqar muryar ta, tasake cewa "kuyi murmushi to,kekuma Husna gyara tsayuwarki"
Duk abinda take fada musu haka sukayi, sannan ta dauka tabasu wayar domin su gani, kokadan bata lura da Hafeez dake tsaye agefe ba,shima Koda wasa baiyi gigin yimata magana ba,gaba daya ya shagala a kallonta, wani side na zuciyarsa yanajin tausayin yarinyar,dazu da safe yaganta tana suyar qosai, sannan yanzu gata awajan sauka, hakan yana nufin saida tagama yin sana'ar tasu sannan tataho wajan saukar.
Idonsa ya lumshe kad'an yana tuno shekarun baya yanda rayuwa ta kasance masa,yatuna yanda yake daukar qosai a kansa yana yawo?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? dashi waje-waje.
Cikin sauri yadawo daga tunanin daya tafi kasancewar yaji zuciyar sa tafara tafarfasa akan rayuwar daya tuno, fuskarsa babu yabo babu fallasa yakai dubansa zuwa ga 'yanbiyu anan yaga suna yin selfie tareda Hafeeza, murmushin daya gani kwance akan fuskarta shine yasa haka nan ya tsinci kansa cikin farinciki.

Maman Fadila ce tazo ta janye ta suka nufi wajansu Inna, har zuwa wannan lokacin Ta Rasulu kuka take, kawu Hamza dake tsaye a gefenta shida matarsa Maryama sai baki suke bata akan tayi haquri tadena kuka, daqyar aka samu tayi shiru sannan suka had'u waje daya gaba dayansu, Hafeeza tashiga Tsakiyar su, Maman Fadila kuma tafara yimusu photuna.


*** *** ***


Da daddare suna zaune afalo gaba d'ayansu, kayan shan'iska ne ajikin 'yanbiyu, Kaka kuwa Hijabi ne ajikinta tana jan carbi.

'yanbiyu ne suke zancen taron saukar su ta dazu.

Hafeez yana zaune agefe wando ne ajikinsa three quarter da wata riga wadda batada maraba da singlet saboda yanda dantsan hannunsa yake abude, hatta nipples dinsa kana ganin tsininsu ta cikin rigar saboda yanda rigar take ba kauri.
Jarida ce a hannunsa yana dubawa amma gaba daya idonsa ne akan takardar, tunanin sa dakuma jinsa yana wajan 'yanbiyu saboda yanaso yasake jin sunyi zancen Hafeeza ko zaiji wani abu daga cikin halayen yarinyar.

Kaka ta ajiye carbin hannunta ta shafa Addu'ah sannan tacire Hijabin jikinta ta kalli 'yanbiyu tace"Allah de kuma yakawo muku mazaje nagari, wannan yarinya data fara karatu dazu da zafe awajan sauka, haqiqa wannan kyautar data samu nasan ba saboda karatun ne kadai ba, harda masu sonta"(=??)

Hassana tace"ai Hafeeza tasamu kudi gaskiya,Kaka itace fa wannan wadda muke fada miki ta'iya karatun Alqur'ani, kuma suma malaman namu sai nan-nan suke da'ita daga gani sonta suke"

Gaban Hafeez yayi wata irin muguwar faduwa, yasaki dan qaramin tsaki sannan yasake bude wani shafin jaridar.

Kaka tace"Allah sarki ashe itace, amma daga gani tanada nutsuwa yarinyar,kuma kana kallonta zaka tabbatar ba asalin yar qasar nan bace gaskiya,kode ruwa biyu ce kokuma daga wata qasar sukazo, ni naso inji wanda yabata million biyar dinnan,ai kyautar farko ance d'an majalissa ne yabata"

Hafeez ya d'an kalli Kaka sannan ya dauke kansa.

Kafin 'yanbiyu su sake magana wayar Hafeez dake gefe tafara ringing, cikin nutsuwa da aji irin nasa yadauki wayar tareda fadin "I.B kaga saqon dana turo mane?"

Daga d'aya 6angaren I.B yace"nagani, naje nakai masa, na sameshi cikin aminci, yana lafiya babu wata matsala"

Ahankali ya lumshe idonsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya, batare dayace komai ba yakashe wayar.

Kafin wani daga cikinsu yayi magana wata Babbar mata tashigo falon, zata iya kaiwa kimanin shekara Arba'in dawani abu, Hafeez yanajin muryar ta yagane ta,ko a mafarki bazai ta6a mantawa da muryar taba, lokaci daya fuskarsa ta sauya ya runtse idonsa, kokadan bayason ganinta.
Matar taqaraso cikin falon, tana qoqarin zama akan kujera shikuma Hafeez yana qoqarin tashi,yanajin yanda 'yanbiyu suke qoqarin gaida matar, wadda ta kasance qanwar mahaifiyar su ce uwa d'aya uba d'aya,amma Hafeez ko kad'an baima nuna yasan taba, maganar fatar baki bata hadashi da itaba yabar jaridar dayake karantawa awajan yashige cikin dakinsa.

Kaka tabi bayan sa da kallo harya rufe qofar dakinsa.
Cikin sanyin jiki tadawo da dubanta zuwa wajan 'yartata cikin tsananin damuwa dakuma sanyin jiki take duban ta, ta rasa yanda zatai ta gyara baya, tarasa yanda zatai ta dedeta kan ahalinta yazama daya,kuskure an riga anyi, saide ayi haquri a fuskanci gaba,inda ace zata iya maida hannun Agogo baya, to haqiqa da zata dawo da nasu agogon qaddarar baya domin ta gyara matsalolin cikin ahalinta.




(meyake faruwa da ahalin Hafeezu ne? >??)

(Jama'ah wa zai turamin 5 million Nima in sake hijabai=?-?=?-?)





Complete document 1k


8621296018
Amina Muhammad
fcmb

Kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034





Amnah El Yaqoub
' [5/26, 1:59 PM] El Yaqoub: =ؘ?MATAR ABBANA=ؘ?
(Luv Story)



Writing By Amnah El Yaqoub

Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update=?G? https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45



7



Matar data shigo falon tayi murmushin yaqe ta kalli Kaka tace"Ummah ashe Hafeez yazo qasar"

Kaka tace"Hafeezu yazo SADIYA, su Hassana ne sukai masa magana nayi tunanin ma bazai samu zuwa ba, kuma sai gashi yazo"

Cikin Sanyin jiki Wadda aka kira da Sadiya tace" Allah sarki, nima tun safen naso zuwa kuma saboda yanayin abun hawa yayi qaranci yanzu, ba'a samun fasinjoji masu yawa atasha, shiyasa na makara, Allah ya sanya Alkhairi"

Kaka tace"Amin Sadiya, amma ai zaki zauna damu muyi kwana biyu ko?"

Cikin sauri Sadiya tace" a a Ummah,gobe zan tafi insha Allah"

Jikin kaka yasake yin sanyi kalau,tasan cewa ganin Hafeez yana gida ne shiyasa tace bazata zauna ba.
Kafin tasake wata maganar 'yanbiyu suka kawowa Aunty Sadiya abinci da abun Sha.

Aunty Sadiya ta kallesu tana murmushi tace "Husna da Hassana yanzu kuma an sauke,saura rubutawa kuma"

Kaka tayi murmushi tace"sa rubuta adakin mazajensu, aurensu zanyi, danma Husna babu mashinshini aida tuni anyi auren"

Kaka ta qarasa maganar cikin tsokana.

Husna ta harari Kaka sannan tace"ko lokacin dakike yanmatanci Kaka baki kaini samari ba,samari suna nan dayawa sai wanda nazaba"

Aunty Sadiya tayi dariya tace"Allah Husna, wato kema yanzu kinbi sahun Hassanarki bakinki yafara budewa...."

Gaba dayansu sukasa dariya kamar basuda wata matsala agabansu.



*** *** ***



Suma su Hafeeza suna zaune a tsakar gidansu akan wata babbar tabarma, kasancewar kawu Hamza yasan cewa gidan nasu zai tara jama'ah hakan yasa bai samu zuwa ba sai wajan qarfe goma na dare mutane sun tafi gida sai Inna da Hafeeza kawai.

Kawu Hamza ya kalli Inna yace"Yanzu Ta Rasulu Yaya kike ganin za'ayi da wannan kudin da Hafeeza tasamu idan ankawo mana?"

Inna tace" Haba Hamza,ai Kaine uba, Kaine zakasan abinda za'a yi dashi, nide fatana asamu adan gyara mana gidan nan, saboda da damuna munayin yoyo sosai, wani lokacin Hafeeza a zaune take kwana"

Kawu Hamza yayi murmushi yace"to dama munyi magana da shugaban makarantar tasu, yacemin nasamo account number da za'a tura mana kudin, ni ina ganin idan kudin sun shigo, kuyi tunanin wata sana'ar daban kufara, saiku ajiye wannan sana'ar qosan agefe, saikuma kayan dakinta da nakeso asiya a ajiye, kokuma abawa masu saida kayan kudin, idan aurenta yatashi kinga zuwa zamuyi mu dauka, duk da made bansani ba ko 'yartawa tanada saurayi"
Ya qarasa maganar tasa cikin salon shan ciki yana kallon wajanda Hafeeza take zaune.

Hafeeza tarufe fuskarta cikin kunya sannan tace"akwai Kawu"

Ta Rasulu ta ta6e baki tace"wannan saurayin naki Hafeeza dashi ai gara babu, saurayi kullum sai shegiyar fira yakasa tsinana miki komai, kuma shi yaqi yaturo iyayensa ayi magana, kullum de gashinan sai aukin zuwa zance, shekaran jiya yazo ta kashe kudi ta tar6eshi, ya cinye komai bai bata ko kwabo ba, yanzu yauma dazun nan yazo be tsinana Mata komai ba sai alewa daya kawo Mata itama ba tafi ta dari biyu ba, nakusa nahana ki fita zancen ma,idan zai turo iyayensa yaturo ayi maganar aure,tun shekarar dakikai candy aketa soyaiyar nan,shi idan sallah tazo ko lallen sallah uwarsa ba kawo miki take ba, Shima bazakici sisin kwabonsa ba, to gara ayi daya, kode ki sallameshi kokuma yafuto yadaukeki ku tafi can gidansa saiku qarata da mammaqonsa tunda ahaka kikeson abinki"

Kawu Hamza yayi murmushi yatashi tsaye yana yimusu sallama, dama abinda yakeson ji Kenan, kuma yasamu amsar tambayar sa.

Kawu Hamza yana fita maman Fadila tashigo gidan, Inna ta kalleta tace"Sa'adatu ina ki kabar mijin naki da wannan daren kika futo?"

Maman Fadila tayi murmushi tana zama akan tabarma tace"Inna wallahi harna kwanta Baban Fadila yashigo, kaji ne yashigo mana dasu shine na dauko muku kuma kuta6a"

Inna takai hannu ta dauki cinyar kaza takai bakinta sannan tace"haba Maman Fadila aida kinbari sai ahadu zuwa safiya"

Maman Fadila da Hafeeza sukai dariya,ganin yanda Inna tafara cin naman kaza amma tana cewa da an barshi zuwa safe.

Maman Fadila ta kalli Hafeeza tace"Hafeeza gobe akwai abinda zakiyi ne? inba abinda zakiyi kikai min Fadila asbiti mana,za'a mata allura"


Inna tace" ina zataje kuwa? ba inda zataje, saita shirya takai miki ita"

Maman Fadila tace" Nima wanki zanyi da safen,kinga idan takai min ita kafin su dawo nagama wankin na rage wani aikin"

Hafeeza tace"to Allah yakaimu"


*** *** ***


Washegari takama litinin, tunda aka idar da sallar asuba Hafeez bekoma bacci ba,sosai yayi nisa cikin tunanin ta,so yake yaje wajanda take saida qosai ko Allah zaisa yasake ganinta, yarasa meyasa yakejin idan beyi magana da'ita ba kamar zai iya Samun matsala, wannan dalilin ne yasa ya gagara komawa bacci bayan yadawo daga sallar asuba, saboda bayaso yakoma bacci daga qarshe kuma ya makara yarasa damar dazai ganta a wannan ranar.

baya cikakken minti goma beduba agogon dake hannunsa ba, qarfe bakwai da rabi tanayi yafuto daga wanka,kamar kullum yauma haka yafuto babu kaya ajikinsa, agaban madubi ya tsaya yana qarewa jikinsa kallo yanda fatar sa take shining kamar mace,cikin sauri yafara shiryawa, daga can falo yake jiyo muryar Aunty Sadiya itada Kaka suna magana da d'an qarfi hakan yasa har yake iya jiyo zancen nasu.
ahankali yasaka hannunsa ya shafo gadon bayansa lokaci daya ya lumshe idonsa cikin damuwa sakamakon tabon bulala dayake kwance abayan nasa, cikin damuwa ya shirya cikin qananun kaya riga da wando, yafeshe jikinsa da turare sannan yafuto daga dakin nasa cikin sauri.

Yana zuwa falo Hajiya Kaka kadai yagani, hakan saiya yi masa dadi saboda dama kokadan bayason ganin fuskar qanwar Mahaifiyar tasa, wato Aunty Sadiya.

Kaka ta kalleshi taga yaci uban gayu da qananun kaya, kuma tasan cewa inde yazo qasar baya ma futowa daga dakinsa sai wajan shadaya na safe, saboda yana komawa bacci bayan sallar asuba.

Cikin mamaki tace"wai Hafeezu ina kake zuwa ne kullum dasafe a cikin kwana biyun nan?"

Hafeez yadan shafa sumar kansa sannan yace" Kaka yanzun nan zan dawo"
Yafadi hakan hankalinsa yana kan agogon hannunsa saboda kada lokaci ya qure baije wajan ba, domin kuwa yayi alqawarin yau sai yayi magana da'ita.

Ajiyar zuciya tasaki batace masa komai ba,hakan yasa shima yadan kalleta yaga de idonta a kansa yake,Kaka kuwa gaban wandonsa ta kalla taga ya d'an taso kad'an, ga abu ana ganinsa taru guda kamar ansa wani abu aciki.

cikin sauri ta janye idonta, shima daga nasa 6angaren bai gane abinda take kalla ba hakan yasa cikin sauri Yajuya yafice daga falo.

Kaka ta girgiza kanta tace"uhm.... Wannan yaro Hafeezu ina tausayin matarsa"

Husna da Hassana dasuka futo daga kitchen suna qoqarin jera break fast, suka kalli Kaka, Hassana tace"Kaka magana kike?"

Kaka tace" yaron nan ne Hafeezu nake magana dashi, kullum haka yake abubuwan sa abun tausayi,ko kad'an bashida shauqi....,narasa yarinyar dazan samu na hadasu wacce zata fahimce shi, mu kanmu damuke ahalinsa mun kasa fahimtar abinda yakeso"


Husna ta zauna akusa da'ita tace"Kaka ni abinda nake gani kicire maganar auren Yaya aranki, shi aure lokaci ne Kaka"

Cikin sauri Kaka tace"haka de!, kullum haka kika iya Husna, kokadan bakyason ganin laifin Hafeezu, to idan Hafeezu beyi aure ba a shekaru irin nasa sai yaushe zaiyi? bakuda hankali ne shiyasa kuke ganin kamar ina takura masa akan batun auren, ni nasan menake hangowa, amma nariga nagama yanke hukunci zanyi magana da Alhaji Abdullahi idan beyiwa yarsa miji ba sai ahadasu ayi aurensu"

Hassana ta jinjina kanta tana murmushin jin dadi, dama kullum so take ayi aure a gidansu, shikuma Yaya Hafeez yayi biris da maganar aure.


*** *** ***


Kawu Hamza yasaki fuskar sa bayan Ma'aruf yafuto daga gida, yabashi hannu suka gaisa cikin farinciki, kawu Hamza yace"yaro Kaine Ma'aruf ko?"

Cikin mamaki Ma'aruf ya gyada kansa yace" nine Baba, meyake faruwa?"

Kawu Hamza yayi murmushi yace"wata magana ce take tafe dani mai girma, idan babu damuwa inaso mu zauna saimu tattauna akan maganar"

Ma'aruf yanuna get din gidansu da hannu yace"Bissmillah to shigo"

Cikin nutsuwa suka qarasa cikin gida, Ma'aruf yakawo masa farar kujera ta roba suka zauna can nesa da megadi, kawu Hamza ya kalli Ma'aruf yace"Magana nazo da'ita akan abokinka HAFEEZ"

Cikin sauri Ma'aruf yace"Hafeez kuma? meyafaru dashi? Yanzun nan shigowa ta kenan bana qasar naje Ghana, ko haduwa banyi dashi ba, wani abu yafaru dashi ne?"

Kawu Hamza yayi murmushi yace" ko d'aya, babu abinda yafaru dashi sai Alkhairi dayake son faruwa dashi, wato Ma'aruf, haqiqa na yaba da hankalin abokinka, na yaba da nutsuwar sa dakuma kyawun halayensa, hakan yasa natako qafa da qafa, inaso kayi masa magana kafada masa cewa idan babu damuwa zan bashi auren 'yata"

Cikin sauri Ma'aruf yadago kansa yana kallon Kawu Hamza.

Kawu Hamza yace"ko akwai alqawarin wata yarinyar a kansa?"

Ma'aruf ya girgiza kansa yace" ko kad'an,saide nasan halin Hafeez yanada wani irin ra'ayi nasa wanda bayason sauraren mace duk yanda take,amma insha Allah zan sameshi inyi masa maganar"

Kawu Hamza yasaki murmushi yace"hakane, amma nasan cewa Babu yaron da zanyi masa tayin auren yata yaqi kar6a, saboda yarinya ce me hankali da nutsuwa,amma ka sameshi kuyi maganar, ina sauraron ku duk yanda kukayi "

Ma'aruf yabashi hannu suka sake gaisawa, sannan kawu Hamza yayi masa sallama shima yatafi.


*** *** ***


Yana qarasawa wajan daga nesa ya ajiye motarsa yafuto kai tsaye yanufi inda take saida qosan, zuciyarsa banda fad'uwa babu abinda takeyi, saide yayi alqawarin yau kam saiyayi magana da'ita baki-da baki.
Abun mamakin yana qarasawa wajan yaga waje wayam!, babu ita babu dalilin kayanta, ganin wasu samari a zaune agefe yasa yaja ya tsaya daga gefensu tareda dauko wayarsa yana duba lokaci, yayi mamakin yanda akai bata futo ba,wata zuciyar tace to ko tadena futowa saboda kyautar data samu awajan sauka?

Maganar matasan dake gefe ne tadawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi, daya daga cikinsu yace"yarinyar nan saboda ita nake zuwa wajannan kullum, naso ace kudi ne dani da aurenta zanyi in huta da zuwa wannan wajan,amma babu yanda na'iya, saide kuma haqiqa duk wanda ya aure ta zai kwashi kaya wallahi"

Dayan abokin nasa yayi dariya yace"ashe kagane, ai Hafeeza ta hadu ba qarya, gashi kamewarta tayi yawa, maza dayawa suna son yimata magana amma suna shakkar ta"

Wani irin baqin ciki ne yazo ya tsaya a wuyan Hafeez, yaji kamar yaje ya shaqe su, wato masu zuwa kallon nata sunada yawa kenan?
Haka ya juyo yadawo gida jikinsa amace, ransa a6ace komai ya dagule masa saboda wannan furucin na kwasar kaya da wannan samarin sukai akan Hafeeza.

Ransa a 6ace yafuto daga motar sai sakin tsaki yake.
Tafiya yake yana shawara da zuciyarsa shi kadai, yakamata yayi magana da'ita, idan tasan zataci gaba da wannan sana'ar to karta sake futowa, tafada masa ko nawa take kashewa kullum saiya turo mata, amma bazai juri kullum tana fita samari suna kallonta suna maganar banza akanta ba.

Ko inda dining yake bai nufa ba, ransa babu dadi ya kwanta akan doguwar kujerar dake falon.
Wayarsa ce tafara qara,yanajin wayar ya qyaleta tayi tagama kukan ta, akaro nabiyu ma aka sake kira, cikin damuwa ya dauki wayar yakara a kunnansa batare dayayi magana ba.

Daga d'ayan 6angaren I.B yace"Hafeez nakira baka kusa,dama zance ma ne na kaiwa Yaya Jabir kud'in, kuma yace ayima godia, yasan idan yakira ka ma bazaka dauka ba, sannan naga kamar Baba yana cikin yanayin damuwa,idan babu damuwa ya kamata kazo kagana da MAHAIFINKA, sannan AUNTY UMMI...."

Sai kuma yayi shiru, Hafeez dake kwance cikin sauri yatashi daga kan kujera ya zauna yace" meyake faruwa da Aunty Ummi? meyake damunta I.b ka fadamin"

I.B yace" Aunty batada lafiya Hafeez, kuskure nane daban sanar dakai dawuri ba, nayi tunanin rashin lafiyar tata zata warware cikin sauri,amma yanzu jikin nata ya matsa, ya kamata kazo ka ganta"

Lokaci d'aya kansa yasara,wannan rashin lafiyar ta Aunty da'aka fada masa ta dakeshi, saboda Aunty tanada muhinmanci acikin rayuwar sa, Aunty mutum ce, kuma Aunty 'yar halak ce da bashida kamarta.

Baisan lokacin da wayar hannunsa tafadi ba, abinda yasani shine kansa ya daure, gaba daya ciwo kan nasa yake masa, yanason zuwa yaga Aunty da kuma mahaifinsa, amma bayason ganin MAMA, yarasa yanda zaiyi da wannan damuwar, baison ganin Mama koda wasa.
Ahankali yasaka hannayen sa ya tallafe kansa dasu, yanajin wani irin zazza6i yana neman rufe shi, cikin damuwa yadauki wayarsa yakira Dr. Jamil, abokinsa ne sosai, sannan idan rashin lafiya takama wani daga cikinsu ko 'yanbiyu ko Kaka, kawai waya yake masa yazo har gida ya duba su.

Dr. Jamil yana dauka Hafeez yace"Dr. Ina cikin damuwa,ina buqatar ka"

Dr. Jamil yayi murmushi yace"to Abokina, nabaka shawara kaqi, yanzu menene matsalar?"

Hafeez ya lumshe idonsa yace" I'm serious Jamil, ina buqatar ka"

Cikin sauri Dr. Jamil yace"Subhanallah, bari in qarasa duba marasa lafiya, saina zo, kabani minti biyar haka"

Ahankali Hafeez ya girgiza kansa sannan yace"no,ba buqatar hakan, kaduba su dakyau, bari inzo hospital din"

Yana fadar haka yakashe wayar, yadauki car

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login