Showing 30001 words to 33000 words out of 37256 words

Chapter 11 - MATAR ABBANA COMPLETE HAUSA NOVEL

03 Sep 2025

2235

6aro-6aro akan fuskar wayar, wata irin ajiyar zuciya ta saki tana hamdala aranta, ko banza dole ya dauki wayar, hakan zaisa ya dauke idonsa daga kanta.

Amma abun mamaki saitaga kallo daya yayiwa wayar yanayin fuskar sa ya sauya, kuma be dauki wayar ba harta gama ringing,kiran yana yankewa wani yasake shigowa saide wannan Karon cikin sauri ya kashe wayar gaba daya.

Kan Hafeeza ya daure, Mama tagani a fuskar wayar, meyasa hakan? mahaifiyar sa na Kira meyasa bazai daukaba?

Maganar sa ce ta dawo da'ita daga tunanin data Lula,duk da shima daga nasa 6angaren gabansa faduwa yake haka ya daure ya dauki tissue ya goge kyakykywan sajen daya sake qawata fuskar sa, sannan ya fuskanceta cikin wata irin murya mai aji yace"nasha wahala awasu shekaru can baya arayuwata,hakan yanada nasaba da quncin danake ciki a koda yaushe har zuwa yanzu, tunda nahadu dake nakejin sauyi acikin zuciyata,inajin nishadi dakuma walwala aduk lokacin dana ke6e dake azahiri dakuma cikin mafarkina,inason inci gaba jin wannan farincikin,but nasan cewa hakan bazai samu ba dole saikin zama tawa,kafin nasamu hakan dole saikin fara bani dama nashiga cikin jerin manema auren ki..."

Hafeeza ta zuba masa ido tanajin yanda yake zuba Mata zance, bazaka taba tunanin shine yake zancen ba.
Hafeez yasaki ajiyar zuciya sannan yaci gaba da fadin"na fuskanci qalubalen rayuwa kafin na kawo matsayin da nake a yanzu,ki bani dama inaso na qarar da Rayuwata tare dake,zan baki lokaci kiyi shawara da mahaifiyar ki"

Kafin Hafeeza tayi magana ruwa yafara saukowa,kasancewar Abaya ce a jikinta shiyasa nan take ruwan yajiqata jalaf,shima anasa 6angaren rigar jikinsa tafara jiqewa,ya kalleta zaiyi magana idonsa ya sauka a qirjinta ga shatin bra duk ya futo, cikin sauri ya nuna Mata wani waje da hannun sa, cikin sauri suka qarasa wajan suka tsaya saide gaba daya ya daburce itama daga nata bangaren haka, duka su biyun kowa yakasa kallon kowa, hannun sa yazuba cikin aljihun wandonsa, ya dauko katinsa yabata yace"gashi"

Kanta aqasa batare data dago ba tasa hannu ta karbi katin, saide jikinta yayi sanyi sosai dajin kalaman sa,duk yanda akai ya fuskanci abubuwa dayawa acikin rayuwar sa, amma abunda yafi daure mata kai meyasa be dauki wayar Mamansa ba? meyasa dataje gidansu iya shida qannansa da Kakarsa ne kawai agidan? Ina mahaifiyar sa?, ina mahaifinsa? meyasa Basa tare gida daya?

Sun dade awajan har saida ruwa ya tsaya, babu mai magana acikin su face satar kallon juna dasuke.
Bayan ruwan ya tsaya ya nuna Mata hanya yace"muje ko?"

Kanta ta gyada masa,suka fara takawa ahankali, ita kanta ba tasan ina zasuje ba,babu wanda zai kallesu baiji sun birgeshi ba, sosai suka dace da juna.

Kai tsaye wani super market suka shiga,qa'idar super market din sai ma'aurata ne kawai suke shiga, amma ganinsu tare yasa babu wanda yamusu magana kai tsaye zakace su din ma'aurata ne, bayan sun shiga saida yayi mata siyaiyar Kaya kamar hauka, Hafeeza kawai Kallonsa take, saida yajido Mata Kaya masu shegen kyau da tsada sannan suka futo,bayan sun futo ma saida Yakoma wani shagon yasiyo Mata sabuwar waya dalleliya babbar ta hannun ta, sannan ya dauki kayan suka wuce masauqinta, har zuwa lokacin babu wanda ya cewa dan'uwansa uffan.

Saida ya ajiye mata kayan sannan yazuba hannun sa cikin aljihun wandonsa ya kalleta yace"zan tafi"

Ba tayi kuskuren Kallonsa ba tace"nagode"

"saina jiki"

Abinda yace kenan yajuya ya tafi, harya 6acewa ganinta batabar wajanba, ahankali ta sunkuya ta dauki kayan, taji nauyi sosai, hakan yasa takai wani, tasake dawowa ta dauki Sauran, bayan ta shiga dakin ta tabude kayan gaba dayan su, ta rafka uban tagumi tana tunanin yanda zatai da wannan bawan Allah, kokadan baza tace ga abinda takeji akansa ba.

Ga kuma Gaddafi agefe, ajiyar zuciya ta saki,ta dauki wayarta ta dokawa abokiyar shawarar ta kira, Wato Maman Fadila.

Ta dade tana kiran wayar amma kwata-kwata wayar taqi shiga.
Tagumi tayi tareda zubawa kayan ido,har yanzu ba zata ce ga abinda takeji akansa ba,abinda tasani kawai shine Gaddafi shine acikin zuciyar ta,harga Allah tana son mutum mahaddacin Alqur'ani,Shikuma wannan babu alamar ma yasan addinin bare ayi maganar karatun Alqur'ani.
Ajiyar zuciya ta saki tamiqe ta cire Abayar jikinta ta shiga toilet domin watsa ruwa.

Ko kwana uku Hafeeza bata qara a Saudia ba ta kammala duk wata ibadar ta,tayi shirin dawowa Nigeria, har zuwa wannan lokacin bata sake ganin Hafeez ba, haka katin daya bata me dauke da numbers dinsa ajiki shima ba tayi kuskuren saka number ta kirashi ba.

Suna sauka a Airport taga kawu Hamza da wasu daga cikin malaman makarantar su, acikin wata hadaddiyar Mota suka tafi gida, itade Hafeeza tunda suka fara tafiya zuciyarta cike da mamakin motar,tarin tambayoyi fal ranta saide babu me bata amsa,kawu Hamza kuwa sai janta yake da zance ahaka har suka qarasa gida.

Anan taci Karo da gyare-gyaren da'ake yi musu agidan, sosai gidan ya sauya yayi kyau sai son barka.
Tundaga qofar gida Inna da Maman Fadila da Sauran maqota suka tarota kowa yana murna har suna neman kada ta aqasa, daga nan suka dunguma zuwa gida aka baje kolin fira, gida yacika da Jama'ah kowa yana yi Mata sannu da zuwa.

Da daddare bayan ta nutsu suna zaune da Maman Fadila afalo, Inna kuma tana daga can gefe tana kakkarya bagaruwa wadda zata rabawa maqota, Hafeeza ta janyo???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? kayan da Hafeez ya siya Mata a Saudia taturashi gaban Maman Fadila, sannan ta kwashe labarin komai tafada mata.

Maman Fadila tayi shiru na tsawon mintuna kusan biyar, sannan tasaki ajiyar zuciya tace"to yanzu ke Hafeeza me kikeji game dashi? kinsan de kina tareda Gaddafi ko?"

Ajiyar zuciya Hafeeza tasaki tace"gaskiya ni bazan ce ga abinda nakeji araina game dashi ba,saboda dabi'una da nasa sunada banbanci, kinga shi niga ne, hatta kunnan sa harda dan kunne irin wanda Yan film suke sakawa, sannan lokacin da naje kar6ar kudi gidansu bakiga shigar datake jikinsa ba, gaba daya jikinsa anyi masa Zane irin na Yan dambe,kai nide gaba daya ma wannan dabi'un nasa basu min ba"

Maman Fadila takama hannayenta, sannan ta kalli gefen Inna taga Inna redio ma takeji qasa qasa a wayarta, hankalin ta baya kansu, sannan ta dawo da hankalin ta wajan Hafeeza tace"Hafeeza, ki nutsu,kiyi tunani, sannan kiyi istikhara,wani lokacin abinda muke so ba shine yake zama alkhairi agaremu ba, wanda bama so din shine yake zame mana alkhairi, duk acikin dabi'unsa banji inda kikace baya sallah ba, asali ma a Saudia kuka hadu harya fada miki abinda yake ransa, Hafeeza ba'a shedar littafi ta bangonsa, kamar yanda baki zauna dashi ba, ba kiyi bincike akansa ba, bazai iyu ki Yanke masa hukunci ba,atawa shawarar ki bashi dama kamar yanda ya nema, sannan kiyi Addu'ah akan Allah ya tabbatar muku da alkhairi, kuma ya miki za6in wanda yafi alkhairi tsakanin shi da Gaddafi"

Cikin rashin wayo Hafeeza tace"to yanzu me zan masa?"

Maman Fadila tace" ki kirashi awaya kice Hafeeza ce,dama Kira nayi mu gaisa,shikkenan daga haka karki sake kiransa awaya,kuma koya kiraki karki yi zuruf ki dauka,kidan ja aji, idan kinga kiransa karki daga,sannan karkibi kiran nasa saide ki tura masa saqo kice kina aiki ya kiraki,idan kin gama Zaki Kira,to karki kirashi koda an dan dauki wasu awanni,ki barshi shida Kansa ya kiraki, wannan hanyar kadai ma zata tabbatar mana da irin son dayake miki"

Hafeeza ta kalleta tace"to amma Maman Fadila menene hikimar hakan?"

Maman Fadila tace" haba Hafeeza,ya za'ai daga haduwar ku kawai babu dan Jan aji saiki bada kai dawuri? aiki nuna masa kinada masu sonki sosai,farinjini gareki, saboda kada yaga kamar bakida samari yayi tunanin shi kadai ne,idan harda gaske yana sonki to zai bada himma wajan ganin yasameki,daga nan mukuma saimu Yanke shawarar data dace akansa"

Hafeeza ta gyada kanta cikeda gamsuwa sannan tace"kuma dama ai kinga inada Gaddafi na ban rasa masoyi ba"

Maman Fadila tace"hakane kam tagidana, oh, ikon Allah kenan, abu kamar wasa shide wannan Hafeez yadage yana so yasake kallon abinda Fadila ta tsotsa"

Cikin tsananin kunya Hafeeza ta rufe idonta da tafin hannunta, cikin salon kawar da maganar tace"to yanzu ni Yaya zanyi da wannan kayan daya bani?"
Maman Fadila tace" waya de ki bawa Inna ta hannun ki sai Adinga turo Mata film tana gani,ke kuma saiki dauki wadda ya siya miki tunda tafi girma,kayan kuma kiyi amfani dashi,haba Hafeeza komai sai an koya miki?"

Hafeeza tayi dariya tace"to kema ki dauki abinda kikeso"

Maman Fadila tayi murmushi ta dauki turare,daga nan Hafeeza ta bude wayar tafara kokarin sakata a caji.

Maman Fadila ta kalleta bayan ta dawo ta zauna tace"nifa Hafeeza duk ba wannan abubuwan ne suke damuna ba, damuwa ta shine insan waye yabaki kyautar million biyar dinnan awajan saukar ku, na tabbatar bahaka kawai ya dauki wannan zunzurutun kudin yabaki ba, wallahi da wata aqasa"

Hafeeza tayi shiru tatafi tunani,sannan ta dago tace"to Maman Fadila kode wannan dan majalissar ne?"

Maman Fadila ta Girgiza kai tace" bana tunanin haka,shi kinga yace a6oye sunansa, sannan shi Alhaji Isa Yunusa ai a bayyane yake kowa yaji million biyu yabaki, su Yan siyasa anfada miki sunada sirri ne? komai nasu a bayyane yake kodan asan cewa sunyi"

Hafeeza ta daga kafadunta alamun rashin damuwa tace"shiya sani Maman Fadila"


*** *** ***


Zaune suke afalo gaba dayan su, Hajiya Kaka tana shan tea tana satar kallon Hafeez daya nutsu waje daya, tana lura dashi tunda ya dawo daga Saudia baya fita, kuma haka zai zauna ya ajiye wayar sa agefe ko nan da can baya tafiya yabar wayar sa.

Husna ce ta kawo masa bread slide hudu da wainar qwai agefe dakuma tea mai kauri,cikin nutsuwa tace"gashi yaya"

Kafin yayi magana wayar sa tayi qara, cikin sauri ya kaiwa wayar wata irin wawura har saida ya bige cup din tea dake gabansa.

Hajiya Kaka tace"subhanallah,Hafeezu lafiyarka kalau kuwa?"

Ko kallon Hajiya Kaka baiyi ba, ya dauki wayar cikin sauri yana Addu'ah Allah yasa Hafeeza ce saboda yaga new number,daga can 6angaren Hafeeza tayi shiru gabanta yana faduwa, har saida shi da Kansa yayi sallama cikakkiya, cikin ransa yana fatan ace itace, Jin yanda yayi sallamar cikakkiya hakan yasa Hafeeza ta bude baki cikin zazzaqar muryarta tace"ina kwana,Hafeeza ce"

Wani irin murmushi ya qwacewa Hafeez,cikin farinciki ya shafa sumar Kansa cikeda Jin dadi sannan yawuce cikin dakinsa.

Kaka da yan'biyu suka saki baki da hanci suna kallonsa har ya shige dakin tareda rufowa.

Kaka tayi sauri tafara ta6a jikin Hassana tana cewa"yi sauri,yi sauri kije kijiyo mana dawa yake waya"(=??)

Hassana tace"wa? lalle Kaka, salon ya kamani ya karya ni a banza, lokacin da mutane zasu zomin jaje cewa zakiyi bakisan anyi ba''(=??)

Hajiya kaka ta juya wajan Husna,tun kafin tayi magana Husna tace"karma ki fara, ba inda zanje"

"Kar Allah yasa kuje,Shikuma nasan yanda yake wannan rawar jikin yana mazari nasan mace ce ta kirashi, bari yafuto Kar wanda yasake zubo masa shayi, yanda ya Zubar da wannan din haka zai Sha Sauran"


Daga cikin dakin Hafeez kuwa zama yayi agefen gadonsa, fuskar sa fal murmushi yace"ina kwana?"

Mamaki ya kama Hafeeza,ina kwana kuma? ita akewa ina kwana?
Cikin mamaki tace"Alhamdulillah''

"inata tsammanin kiranki,maganar gaskiya kinada nutsuwa,kuma kinada hankali,yaushe Zaki bani dama nazo gidanku naganki?"

Mamaki yasake kama Hafeeza ganin yanda yake magana kamar arikice yake, daga cewa yana tsammanin Kira, kuma sai zancen hankali da nutsuwa,daga ji kawai shima yin zancen yake,bai sababa.

Hafeeza tace"idan ka shirya zuwa saika Kira wayata"

"nagode,saikin jini"

Yana fadar haka ya kashe wayar, yasaki wata irin nauyaiyar ajiyar zuciya sannan yafuto falon fuskar sa dauke da walwala.

Saida yaga Husna tana gyara wajan daya Zubar da tea sannan hankalin sa ya dawo jikinsa ya tuna abinda yayi.

Kallon Hassana yayi yace"ke zoki kawo min tea"

Hassana tace"wallahi Yaya har zamu kawo ma wani Kaka tace karmu kawo"

Kallon Kaka yayi, cikin sauri ta kawar da kanta sannan tace"to kai ka yarda nizan iya hanasu su kawo ma Shayi? ina nasan anyi hakanma,?oho bansani ba"

Hafeez ya Girgiza Kansa kawai yana sakin ajiyar zuciya,wannan wayar da yayi da Hafeeza jiyake kamar an sauke masa wani nauyi daga kan qirjinsa.


*** *** ***


Da yamma kawu Hamza yazo gidan,bayan sun gaisa ya kalli Inna yace" Ta Rasulu maganar Hafeeza ce ta kawo ni"

Inna ta karyi goro tace"to ya akayi? Inji dai lafiya?"

Kawu Hamza yayi murmushi yace"lafiya kalau saide alkhairi,ina Sanatan daya biyawa Hafeeza Saudia ranar sauka?"

Inna ta gyada kanta da sauri sannan tace" naji de,Alhaji waye da sunan sa? Alhaji Ali ko?"

Kawu Hamza yasake yin murmushi sannan yace" Alhaji Isa Yunusa de, to yaturo min mutane jiya akan yana neman auren Hafeeza"

Gaban Hafeeza yayi wata irin faduwa,cikin sauri ta dago kanta ta Kalle shi.

Kawu Hamza yaci gaba da fadin" To Alhamdulillah gaskiya mutanan daya turomin mutane ne masu dattako,na tabbatar idan ta aure shi zasu riqeta da daraja,to amma banyi gaggawar amince waba, nace yarinyar nan Amana ce agareni, marainiya ce, zan tuntu6e ta inji ta bakinta, saboda haka Yaya kike gani keta Rasulu tunda yanzu kam kece mahaifiyar ta"

Inna tace"Ahhh Hamza ni kuwa me zance? ai data auri wannan tsohon saurayin nata baqin maqaryaci Gaddafi,gara taje gidan wannan din, ko banza zata sauya,zata samu Cima me kyau, kana gani daga zuwa Saudia yanda ta koma kamar balarabiya,ai bazan so Hafeeza tayi aure agidan wahala ba, ai tana ganin yanda muke fadi tashin rayuwa"

Kawu Hamza yace"to nima de abinda nagani kenan, kina ganin yanda yake rawar jiki akan ta,yace Idan har ta amince zai tafi da'ita Abuja,bazai hadata da Matan sa ba,Matan sa uku, itace zataje ata hudu,kuma kinga yace bazai hadasu ba, Abuja zasu wuce anayin auren"

Inna ta washe bakinta tare fadin" Abuja de danakeji? a a, a a, to ai shikkenan,Allah ya basu Zaman lafiya, Allah yasa ayi damu"

Hafeeza ta kalli Inna ganin ita harta amince da wannan maganar, yanzu Yaya zatayi da wannan tsohon, kenan tanaji tana gani haka zata aure shi? Tasan cewa tabbas Gaddafi yanzu baida halin yin aure, shima ta Kansa yake,kawai qarya ce tasa yake nuna cewa shi yanada kudi,yanzu Yaya zatayi?.

Kafin tagama tunanin da take taji Kawu Hamza ya juyo gareta yace"Hafeeza Yaya kika gani?, kina son sa?"

Hafeeza taji kamar andoka Mata Sanda akanta, batada wani za6i a yanzu, dade ace ta auri wannan Sanatan Gara ta auri Gaddafi sau dubu, cikin da kewa ta dago kanta ta kalli kawu Hamza sannan tace" Kawu ni GADDAFI nakeso"

Kafin Kawu Hamza yayi magana Ta Rasulu tace"Gaddafi dai Hafeeza? Nina rasa me kika gani ajikin wannan yaron"

Kawu Hamza yayi murmushi ya juya ya kalli Inna yace"Gaddafi de wannan dan gidan Malam Usman?"

Ta Rasulu tace" shifa, yana nan bashida aiki sai qarya"

Kawu Hamza yayi murmushi tareda kallon Hafeeza yace"tashi kije, zan nemi mahaifinsa muyi magana dashi"

batare da damuwa ba Hafeeza ta wuce daki.
Ta Rasulu tabita da kallo tana Girgiza kai.


*** *** ***

Cikin farinciki yashigo dakin Hajiya Kaka, ya zauna daga gefen qafafunta kasancewar tana kwance ne akan gadon.
Qafafun nata ya dauka yad'ora akan cinyoyinsa yafara matsawa,sannan yadago Kansa ya kalleta yace"Kaka na tambayi yaran nan sunce min kina kwance adaki, nace me kika tara har Zaki shige daki ki kwanta?"

Hajiya Kaka ta Kalleshi tace" Bar batun na ajiye ko ban ajiyeba,tunda na ajiye wadda ta haifeka ai kasan nayi ajiya"(=??=?F?)

dan yamutsa fuskarsa yayi sannan yace"naji... naji,ni wasa nake miki Kaka"

Hajiya Kaka tace"inma da gaske kake kar nake kallonka Hafeezu,daidai nake daku agidan nan,fadamin meya kawoka? dan nasan wannan zuwan naka akwai dalili"

farincikin sane yasake qaruwa yace"yawwa Kaka dama... am dama zan fada miki ne nasamu wata yarinya"

Cikin sauri Hajiya Kaka ta Kalle shi, sannan ta saka tafukan hannunta ta murtsika idonta ta tabbatar ba bacci take ba, ahankali ta yunqura tatashi zaune, sannan ta Kalle shi tace"Hafeezu mafarki nake koda gaske ne?"

hannayenta yakamo ya mintsineta, cikin sauri takai masa duka abayansa yakauce yana sakin dariya.
Hajiya Kaka ta daga hannayenta sama tace"Ya ubangiji nagode ma, Allah Abun godia ashe zanga wannan ranar ni Rabi'atu, Allah na gode ma"
Ta shafa Addu'ah sannan ta fuskanceshi da kyau tace"ka tabbata da gaske kake Hafeezu?"

Kansa ya gyada Mata, sannan yace" da gaske nake Kaka, ina sonta sosai"

"gaskiya na yarda kana sonta tunda harka iya bude baki da kanka ka fadamin, yau wacce rana, Alhamdulillah, amma 'yar waye? inane gidansu?"
Cikin kunya yadan shafa sumar Kansa yace"Kaka aikin santa ma, qawar yarannan ce, yarinyar da tazo wajan su kwana ki, Hafeeza"

Cikin tsananin mamaki Hajiya Kaka ta rufe bakinta da hannayenta sannan ta bude tace"Almiri,ni nasan awajan saukar nan Kaine katura Mata wannan kudin ko?"
Cikin salon shagwa6a yace" Kakaaa"

Kaka tayi murmushi sannan tace" to shikkenan naji, aiba laifi bane hakan Hafeezu,ladanka yana wajan Allah"

Ajiyar zuciya ya sauke, sannan yasake matsa hannayenta dasuke cikin nasa yace"tun ranar da nazo na ganta, ina yawan bibibyar ta,itace take saida qosan da'ake siyo miki, tana cikin halin rashi Kaka, sannan sana'ar datakeyi itace tasake jefa min tausayin ta araina, da wannan hannayen nawa nayi irin wannan sana'ar datakeyi, waje-waje nake yawo da qosai akaina... "

ya qarasa maganar yanayin sa yana sauyawa, yayinda ya zubawa tafukan hannunsa ido yana kallonsu.

jikin Hajiya Kaka yayi sanyi,tasaki Ajiyar zuciya sannan tace"kadena tuna baya, ka fuskanci gaba, nasan cewa idan mukaje nema maka auren ta akwai qalubalen da zamu fuskanta,nariga nasan rade-radin da'ake agari a kanmu"

maimakon yabata amsa saiya sauya akalar maganar tasa zuwa wani abun daban, ya kalleta yace"amma Kaka ai kin yaba da hankalinta ko?"

Cikin gamsuwa Hajiya Kaka tace"sosai, ai naga tanada nutsuwa babu laifi,amma de abunda yake damuna daya ne, naji yaran nan su Hassana suna cewa tanada kwankwaso yarinyar, inji de ba abinda yakaika kenan ba ko?" (>??)

Wani irin kallo yayi mata ya Girgiza kansa,sannan yace"saida safe"

Hajiya Kaka tasaki dariya ita kadai,tana sake daga hannu tana godewa Allah.

Kawu Hamza ya kalli Malam Usman bayan sun gama gaisawa dashi yace"Maganar yarinyar nan marainiya yar wajan Yayanah haladu marigayi ce ta kawo ni, to kasan yaron wajanka Gaddafi yana zuwa wajanta zance, to abinda yake faruwa shine, akwai manemi da yarinyar tasamu, na zauna da'ita nayi Mata maganar sa, amma ta nunamin batason shi wanda yafuto din, yaron wajanka Gaddafi takeso, to shine nazo dakaina, kasancewar yanzu ita amana ce awajena, koda mahaifinta yana raye, ni zai wakilta wajan wannan al'amarin, banaso manemin nata yazo ya da maganar turo wa gida kuma mu ce munyi Mata miji alhalin kuma babu wata tsaiyayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login