Showing 3001 words to 6000 words out of 37256 words

Chapter 2 - MATAR ABBANA COMPLETE HAUSA NOVEL

03 Sep 2025

2228

cikakken saurayi yanda yake fama da matsala ta tsananin sha'awa.

Husna ta kalleta tace"Kaka bakici abinci ba"

Cikin damuwa Hajiya Kaka tasaki ajiyar zuciya,fuskarta cikeda tsantsar damuwa tace"qyaleni Husna bata abinci nake ba, ta rashin auren yayanku nake"

Hassana dake zaune agefe ta kalleta tace"Kaka da kinyi haquri da batun auren nan, shi Yaya miskiline, ko yanmatan layin nan baya kulawa, bare su sasanta da wata ayi maganar aure"

Kaka ta kalli Hassana tace"ke rabu dashi da Allah, miskilancin banza, to ai irinsu sune 'yan'iskan"(=??)

Husna dake kusa da Kaka tasaki murmushi.
Hajiya Kaka tabawa Hassana wayarta tace"ungo kiramin shi awaya"

Hassana taduba number Yayansu ta doka masa kira, saida ya dauka sannan tabawa Kaka wayar.
Hajiya Kaka ta kara waya a kunnanta tace"Hafeezu ya aiki?"

Cikin damuwa ya runtse idonsa,bayason wannan Hafeezun datake fada,gaba daya lalata masa suna take,saida ya saita kansa kafin Ataqaice yace"Alhamdulillah"

Hajiya Kaka tace"Hafeezu ita Rayuwa dakake gani,bahaka ake tafiyar da'ita ba,tsakani da Allah shekara da shekaru Hafeezu kana zaune babu aure,ka girma harka riqa kana zaune a tuzuru,shine nace Hassana ta kiramin kai nace konaje nayi magana ne a had'a ka da yarinyar nan Hafsa 'yar wajan Alhaji Qani nakan layin mu?"

Ajiya zuciya yasaki daga cikin wayar,tsawon lokaci ya dauka batare dayayi magana ba harta cire rai zaiyi magana sannan yabude baki cikin tsantsar aji da tsananin miskilanci yafara magana a rarrabe kamar bayaso "Koda yaushe Kaka...,bakida aiki sai zancen had'a aure....,kina daga zaune,kin zama me dalilin aure" (=??)

Cikin sauri Hajiya Kaka tace"yaushe nata6a had'a aure Hafeezu? yaushe akai haka? banta6a jiba"
Tana fada masa haka ta dauke wayar daga kan kunnanta ta miqawa Hassana tace"ungo kashemin wayata"

Hassana ta kalli wayar sannan ta kalli Hajiya Kaka tace"Kaka yana magana fa"

Cikin 6acin rai Hajiya Kaka tace"Kashemin waya nace!!"

Babu yanda ta'iya dan dole ta kashe wayar.
Kaka ta saki tsaki tace" abinda yasa kukaga na damu da aurensa bafa komai bane, sonake muma mu dinga ganin qananun yara acikin gidanmu, bamuda kowa, 'yar'uwa ta qwalli d'aya data ragemin ta mutu,Zaman lafiya suke itada kishiyarta na innaa-naha, da kishiyar tata ta mutu damuwa tasa ta susuce daga baya itama ta mutu, zamansu lafiya kalau duk inda zasuje suna tare, ko girki daya zatayi to tare sukeyi kokuma d'aya tayiwa d'aya,komai nasu tare sukeyi, to yanzu shi ban'isa nayi masa maganar aure ba saiya fututtuke fuska dama shi fuska kullum a d'aure, kuma tausayi yake bani wallahi, wannan rashin auren nasa yasa duk ya sauya, gaba d'aya a firgice yake"(=??)



*** *** ***


Kamar kullum yauma sassafe tatashi takama aikin da tariga tasan cewa nata ne,kasancewar bata kwanta da wuri ba sakamakon hadda datayi daren jiya, hakan yasa idonta yake cikeda bacci, aikin take amma tanayi tana Hamma tana murza idonta dake cikeda jin bacci,yau Inna Ta Rasulu idonta biyu, tana ganin duk yanda Hafeeza take ayyukan ta cikin sanyin jiki saboda rashin samun isasshan bacci yasa gaba daya kasala ta lullu6eta, ganin gari yana sake wayewa ko niqan wake bata kai musu ba hakan yasa Inna ta miqe da azama ta nufi Hafeeza tana fad'in "ke da Allah bani wankin waken nan na qarasa, kina abu kamar sauna"

Tafadi hakan tana qoqarin meqa hannu zata kar6i robar da waken yake ciki, tana sako qafarta santsin ruwan da Hafeeza ta zubar awajan ya kwashe ta saiji kake timm....,Inna Ta Rasulu tazame tafadi. (=?F? @&?)
Sai akai sa'ah fad'uwar tahadu da raki,lokaci d'aya Inna tasaka wani uban ihu tana fad'in "Wayyo Allah ni Tarasulu na mutu na lalace!!!"

Cikin sauri Hafeeza tayi kanta tana dora hannunta akan qafar tana fad'in "Inna kinji ciwo aqafar ne?"

Cikin azaba Inna tace"qaniyar ciwo naji Hafeeza,cire hannunki daga wajan kiyi sauri ki kiramin Bala mad'ori "

Cikin sauri Hafeeza tazari hijabin ta tafice daga gidan, kasancewar safiya ce sosai hakan yasa babu mutane awaje, uwa uba unguwar tasu ta manyan mutane ce kowa yana gida, shiyasa kanta tsaye ta kwasa da gudu tayi gidan Bala Mad'ori, bata juyo tadawo gida ba sai tare dashi, daqyar da kururuwa da rakin kuka aka samu aka gyara wa Inna Ta Rasulu targaden da taji qafarta, Hafeeza ta taimaka mata tadawo cikin Rumfa, sannan ta dauki niqan tafice daga gidan.
A wannan rana de Hafeeza bata samu tafita suyar qosai dawuri ba,amma dayake ita kasuwa ta Allah ce babu abinda tarage saida ta saida qosan tas sannan tadawo gida.
Bata dawo gida ba saida ta siyowa Inna Robb, tana shigowa gidan kuwa ta shafa mata awajan, sannan taci abinci tasha shayi ruwan bunu me cikeda ganyen na'a na'a, sannan tayi sauri tafice makaranta dayake yau sunada bada haddar tulawar da'aka basu, bata dawo dawuri ba kasancewar itace qarshen biyawa, hakan yasa tabiya wajan wani me saida tsire ta siyo wa Inna, daga nan tataho gida,tabude mata tsiren tanaci ita kuma tawuce wajan wanke-wanke tafara wanke kwanukan data dawo dasu daga wajan suyar qosai.

Wata mata ce tayi sallama tashigo gidan tana yiwa Inna jaje, Inna ta dauki tsokar tsire ta danna a bakinta sannan ta kalli matar tace"wallahi Lami kingani de yanda tsautsayi ya sameni, yarinyar nan tana aikinta ka'in da na'in, da shegen iyayi na nace tabani aikin zanyi, kuma fa dama can bani nake aikin ba, ko tsinke bana daukewa agidan nan komai itace takeyi, to yau d'in tsautsayi ya debeni,qasar wajan ta jiqe, zuciya ta d'aya ina meqa qafa, naji an sureni anyi sama dani, to kinga de naji targade a qafar,Allah yaso aikin na kar6a ba suyar qosan na kar6a ba, yo inda ace suyar qosan takeyi na kar6a nace zanyi kinga aida tuni akan tanadar mai zan fada,saide ayi kama-kama akawo ni gida"(>?#?)

Lami ta girgiza kanta cikin alhini tace" Allah mungode maka,Allah yaso agida abun yafaru"

Ta Rasulu tasake kai tsire cikin bakinta tareda yatsina fuska sannan tace"kede bari Lami"

Lami ta kalli yanda Inna take cin nama tana yatsina fuska,hakan yasa tace"Ta Rasulu kode naman baya miki dad'i ne naga kina yatsina fuska?"

Cikin sauri Inna tace" a a nama da dadinsa,jikin ne de babu dad'i"(=??)

Lami ta juya ta kalli tsakar gidan nasu sannan ta maido da kallonta wajan Inna tace"Ta Rasulu ashe kunada zogale agidan naku, aida nasani da nazo nacira nayi dambu"

Inna tace"Um muna dashi zoki tsigeshi gaba daya munbaki, dama a wannan yanayin ma waye yakeda kud'in dazai sai kayan had'in zogalen?"

Kafin Lami tace wani abu, Inna ta kalli Hafeeza datake wanke-wanke tace"Hafeeza zoki dauko min wannan sauran garin kwakin namu ki jiqamin Nasha"

Hafeeza ta wanke dogoyen yatsun hannunta sirara,sannan ta taso tawuce daki ta dauko mata ledar gaarin tace"gashi Inna"

Inna tace"bude ki zuba a Kofi saiki jiqo"

Hafeeza tace"A a Inna debi da kanki"

Inna tace"ki zuba nace"

Hafeeza ta bude ledar tafara zuba mata gaarin a Kofi, Inna taga Hafeeza tana zuba gaari kamar bata so, tasa hannu ta qwace ledar tace"bani ni"

Tasake bude kan Leda tana zubawa dayawa, Hafeeza ta kalleta tace"ya kike qoqarin juyeshi duka muda muke lalla6ashi Inna?"

Inna tace" naki ko nawa? bataki d'aya tame garin jamaga, zubo min ruwa aciki kigani"

Hafeeza ta jiqo mata gaarin takawo mata, Inna tana gani tace"qara masa ruwa ki barshi ya juqu karnaje yajuqu aciki na, tayaya zansa wannan abu aciki na? ai juquwa zaiyi acikina, kar6o min aron cokali awajan Maman Fadila,duk Cokulan nawa babu kin kwashe kin zubar, lokacin da muke zuwa legas, haka nake kar6ar Cokula bashi, dozin d'aya nera dari"

Lami tayi murmushi bayan tagama bin bayan Hafeeza da kallo, sannan tadawo da kallonta wajan Inna tace"Ta Rasulu Hafeezan taki tagama zama budurwa sai had'a uban qugu take kamar babbar mace,gata kyakykywa kamar bafulatana"

Inna tayi dariya tace" tabdi toko zo in kasheki da fullanci bata sani ba"(=??)

Lami tayi murmushi tace"ikon Allah amma tana kama dasu sosai"

Adede lokacin Hafeeza tadawo gidan,da goyon Fadila abayan ta,yarinya yar sati biyar da haihuwa, tabawa Inna cokali sannan taje tana share wajan datayi wanke-wanke.

Inna tasaka cokali acikin kofin garin kwakinta tafara Sha, ta d'ago kanta ta kalli Lami tace" mahaifiyar Hafeeza ba bafulatana bace,ita tasan yaren mecece, yaqi akayi a qasar su suka dawo Nigeria itada iyayenta, iyayen nata suka rasu, sai mijina ya auro ta,lokacin da'aka kawo ta gidan nan karkiga yanda nacika nayi fam ina Kishi da'ita kamar zan fashe, saboda kyau ne da'ita kamar aljana,ga uban gashi kamar 'yar ruwa,yanda kikaga sadaka yalla yan Niger, haka uwarta take, mijina yaje ya auro min ita saboda bana haihuwa,tana zuwa Allah da ikonsa ko shekara ba'a rufa ba ta haifi Hafeeza,ashe ni aka haifa wa, uwar ta mutu, Shima mijin Namu ba'a dade ba yarasu"

Lami tace" Allah sarki,ashe Zaman bane dorewa bane"

Inna tace"to ya za'ai, kwana yaqare, yanzu duk babu kowa dagani sai Hafeeza sai Qanin Babanta dayake qoqarin yimana hidima lokaci zuwa lokaci"

Hafeeza ta qaraso cikin Rumfar ta Shimfida Sallaya ta kwantar da Fadila,yarinyar kyakykywa da'ita fara.

Lami tayi musu sallama tatafi.

Inna ta kalli Hafeeza tace"Hafeeza banji kinyi waya da saurayin kiba yau, ko kunyi wayar nice bansaniba?"

Hafeeza tace" A a bamuyi waya ba Inna"

Ta Rasulu tace"to saboda me? ki kirashi mana Kiji Yaya yake,sai kice masa dama kira nayi mu gaisa,ina laifi mai sonka ai yafi me qinka"

"Inna idan nakira ba lalle ya dauka ba,jiya da mukai waya dashi ya fadamin yanada uzururruka dayawa,baya zama agida suna asbiti an yiwa qanwar sa aiki a qirjinta,wannan shine karo na uku ana yi mata aikin"

Ta Rasulu tace"Subhanallah,Allah yabata lafiya,inajin qari ne da'ita, a qirji yace anyi mata aikin ko a Nono?"(=?J?)

Cikin sauri Hafeeza ta zaro idonta tana kallonta sannan tace"nashiga uku na, a a Inna bankai nan ba, ban tambayeshi nan ba"(=??)





littafin kudi ne, Complete document 1k


8621296018
Amina Muhammad
fcmb

tareda shedar biya ta wannan number 08033300034








Amnah El Yaqoub
' [5/22, 9:20 AM] El Yaqoub: =ؘ?MATAR ABBANA=ؘ?
(Luv Story)



Writing By Amnah El Yaqoub

Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update=?G? https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45



3


Washegari sassafe suka tashi sukai aikin komai suka gyara gidan sannan suka zauna suna break fast saboda yau sunada gyaran tulawa da safe, Husna de fruit takesha, yayinda Hassana take shan tea mai kauri idonta yana kan d'an qaramin Alqur'anin dake hannunta tana dubawa.
Hajiya Kaka tafuto daga dakinta taga har sun gyara gida, hadaddan falon nasu sai qamshi yake,ta zauna akan kujera tana fadin" Allah de yamuku albarka yaran nan,Allah yakawo muku mazaje nagari,ni bansan meyasa nasa goro a bakina ba, yau Alhamis da yanzu nawuce da azumi na kuma wai sainasa goro,kunga kuwa ai babu Azumi"

Husna ta ajiye Bananar dake hannunta ta kalli kaka tace"Dama fa Kaka ba niyya,inaji lokacin da Hassana ta tasheki Sahur tace ko zakiyi Azumi kikace Anya kuwa?"

Kaka tace" Au haba?, yaushe akai hakan? to bansan anyi ba"(=??)

Husna tace"dama ai bazaki sani ba"

'Dan ladi direba ne yayi sallama falon yakawo wa Kaka qosai kamar yanda yasaba siyo mata duk lokacin datake so,bayan yafita Kaka taja hadaddiyar food flask din tasu ta zamani, tafara qoqarin budewa da qarfinta amma taqi buduwa,ahankali tasaki d'an qaramin tsaki tace" wataran zan 6alla kwano kuwa, haba gaba daya kwanukan mu na arziqi tunna da can kunsa anbayar ankawo mana na zamani gashinan kanaso ka bude kwano amma kayi-kayi abu yaqi budewa me ake da irin wannan rayuwar?"

Hassana tace"qarfi kika Sawa flask din,ana bude abu ahankali amma Kaka ke kullum kin kasa zama 'yar gayu saiki sawa flask qarfi"

Husna tace"kuma fa ba qarfin ne da'ita ba, ko ina abun yake oho"

Kaka ta kallesu kawai ta girgiza kai sannan tabude ahankali, aikuwa flask ya budu,qamshin Qosai da zafinsa ya bugi hancinta, ta dauki guda daya ta saka abakinta tace"dan masifa qosai yakoma uku nera hamsin,kayi magana ace wake yatashi"

Daga Hassana har Husna suna jin qamshin qosan suka matso suma suka saka hannu,qosan yanada dad'i sosai ga wani yaji aqefe me shegen dad'i.
Husna tace"wai Kaka a'ina ake siyo miki wannan qosan ne me dad'in tsiya?"

Kaka tasake jefa qosai a bakinta tace"can ne layin can na baya d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ede gidan Alhaji Munzali"

Husna tatafi tunani tana fadin"Alhaji Munzali,Alhaji Munzali...."
Sannan tadawo da duban ta wajan Hassana tace"bangane shiba, ke kin ganeshi?"

Hassana ta girgiza kanta alamun itama bata gane ba,Kaka ta kallesu tace"bakusan Alhaji Munzali ba? Alhaji Munzalin? saina d'ura muku zagi"(=??=?J?)

Husna ta hada ido da Hassana sukai murmushi, sannan suka juya suna kallon Kaka.

Hajiya Kaka tace"Alhaji Munzali fa,wanda matarsa tayi hatsarin mota ta rasu,har mukaje daku gaisuwa 'yan'uwan matar sai faduwa suke suna aljannu"

Cikin sauri Hassana tad'an bugi kafadar Husna tace"ke natuna,kusa da gidan wannan 'yar ajin namu HAFEEZA KHALEED"

Husna tace"ok dama adede nan gidansu Hafeeza yake? kai wannan ai aitaci Sunanta Hafeeza din,akwai karatun Alqur'ani kamar ruwa,ga muryar ta dad'i idan tana karatu,but in hakane meyasa tana kusa da islamiya amma kusan kullum saita makara inde haddar safe zamu bayar?"

Hassan ta dangwali yajin qosai, takai bakinta tacinye, sannan tace"gaskiya de inde haddar safe zamu bayar zakiga amakare take zuwa,amma idan da yamma ne kinga bata makara,gata kyakykywa kamar aljana,suma malaman namu naga sai nan-nan suke da'ita kamar ma sonta suke"

Husna tace"su sukasan me suka gani,ai rannan kafin kidawo daga toilet tashigo late, tana sauri zata shigo ajin ashe qusa ta riqe mata gefen hijabinta ita kuma dayake sauri take bata sani ba, aikuwa Hijabin nata yad'age sama, karkiga uban qugun wannan yarinyar, shi kansa malam Sabo bakiga idonsa ba kamar zai fado, ya qwarawa guqun baiwar Allah ido,kuma ahakan kullum tana cikin Hijabi, gashi batada qawaye kullum ita kadai zaki ganta, to dan Allah tanasa Hijabi ma malamai suna mata haka idan wataran tasa mayafi tafita gari ai baza'a rasa samari masu kawo mata Hari ba"

Kaka dake sauraron firar su tace"ikon Allah, aikuwa taji dad'in ta,Hijabi ai shine cikamakon mace mai hankali da tarbiya"


*** *** ***

Da yamma tana zaune tana wanke musu kayan su itada Inna sai Yatsina fuska take tana runtse idonta saboda yanda marar ta take murd'awa, tun safe take jin ciwon marar har zuwa yanzu,kuma maganin ta ya qare gashi aiki yahanata fita ta siyo wani maganin.

Inna dake zaune daga cikin Rumfa tana jin Radio a wayar Hafeeza, wayar ma har tayi ja babu caji, tana qoqarin kashe Radion aka sako wa'azin wani malami,bata fasa ba ta kashe tana fadin''aikuwa bawan Allah saide kayi haquri baqin wa'azin naka nayi ba,caji saura yanka d'aya"(=??)

Maqociyar suce tayi sallama ta shigo gidan, Wato Maman Fadila, mace me kimanin shekaru 35, tana dauke da Fadila a kafadarta, adede lokacin Hafeeza tadena wanki ta sunkuyar da kanta qasa tana tauna siraran lips dinta.
Maman Fadila tace"Subhanallah,Auntyn Fadila meyake damunki naga kina runtse ido?"

Inna Ta Rasulu tace" wankin ne bataso,tun dazu taketa faman yatsina fuska ina kallonta"

Maman Fadila tayi murmushi tace"haba Inna ita ta'isa tace haka?"

Tajuya wajan Hafeeza tace" ko cikin ki ne yake ciwo?"

Cikin sauri ta girgiza mata kai tace" marata ce take ciwo tun safe,kuma yaune ranar dazan gama hutun sallah ta,bansan meyasa takemin ciwo ba,qila wannan aikin ne wallahi,kullum mutum bashida aiki daga wannan sai wannan"

Inna tanajin haka tace"Hafeeza ki kiyaye ni, karki sani abakin duniya,yanzu inda wasu baqi ne agidan Namu kika fadi haka ai sai azata naman jikinki nake yanka saboda azaba,wani ma cewa zaiyi azaba na ganawa uwarki harta mutu, nan kuwa ciwon naqudarki ne ya kashe ta,Shima Babanki majanunin Laila bata dade da mutuwa ba shima yabita,idan baki mana wanki ba wanne kaya zamu sa?, Ya zakiyi? haka zaki daure ki qarasa wankin, ni wallahi badan wannan ciwon qafar tawa ba ni Ta Rasulu har a fadamin aiki?"(=?2?)

Maman Fadila tayi murmushi tace"Inna da Hafeeza drama, kinga riqe min Fadila inje gida in kawo miki magani,nida nakawo raino Uwar raino ba lafiya ai banga ta zama ba"

Daqyar Hafeeza ta kar6i yarinyar ganin idon yarinyar akanta ko qyaftawa batayi, sai taji tausayin yarinyar, ta kar6eta ta goya ta, sannan ta dauraye kayan tafara shanya wa.

Bayan tagama shanya kayan tadawo cikin Rumfar ta zauna akan kujera.
Daga qofar gida Inna tajiyo wani dan gwangwan yana cewa"tsohon kwano mataccen kaya akawo mu siya..."

Daga inda suke zaune Ta Rasulu tace" me za'a kawo ku siya? asato kusiya de, nan almajiri yashigo da sassafe muna baccin asara, ya sace min sabon bokiti na yakawo muku kuka siya, kwana ki dana fita Unguwa wata tukunya dana gani awajansa sabuwa dal nace a'ina kasamu wannan tukunyar yace siya nayi, nace a a, aka sato kuka siya dai, kudena siyan kaya awajan yara yawanci duk na sata ne, nayi masa nasiha de yace yadauka, shine dan tsaurin ido yanzu ma kinji ya dawo"

Dataji Hafeeza shiru bata tanka mata ba, saita kalleta tace"Hafeeza kinyi waya da saurayin ki yau kuwa?"(>??)

Hafeeza ta dago kanta da qyar tace" Inna ba kincinye cajin wayar kinajin radio ba?"

Inna tace"Af....haka akayi fa, na manta, sannu Hafeeza, Allah de yabaki lafiya"
Kafin Hafeeza tayi magana Maman Fadila tashigo takawo mata magani tasha, sannan ta shinfida mata tabarma ta kwanta, ta dauki Fadila zasu tafi, Hafeeza ta meqa mata hannu daga kwancen tace "Bani ita"

Babu musu Maman Fadila ta miqa mata yarinyar tanajin dadin yanda Hafeeza take dawainiya da Fadila,duk maqota kowa yasan yanda Hafeeza take son Fadila,hatta shima Baban Fadila kasancewar yasan Hafeezan tanada hankali da nutsuwa uwa uba duk unguwar kowa yasan cewa Hafeeza ta amsa Sunanta, mahaddaciyar Alqur'ani ce, hakan yasa shida kansa Baban Fadilan wani lokacin yake cewa akai Fadila raino wajan Hafeeza.

Hafeeza ta kar6i Fadila ta d'orata akan ruwan cikinta, tadora mata kanta akan tudun tsayaiyun nashanunta, yarinyar kuwa tayi luf kamar ta tada kai da nonon uwarta.(=?H?)

Cikin sati biyu su Hafeeza suka gama bitar tilawar su gaba daya,har makaranta ta saka musu ranar da za'a yayesu tareda bikin saukar su,acikin sati biyun nan bata zama, kullum tana cikin neman kudi ta hanyar qosai, da daddare bata baccin kirki saboda yanda take raba dare tana tulawar Alqur'ani kasancewar an riga an tantance su itace daliba ta farko dazata fara karatun Alqur'ani aranar saukar tasu, hakan yasa takowanne 6angare take shirye-shirye cikin farinciki.

Yau bayan tadawo daga wajan suyar qosai tabawa Inna kudin kamar yanda tasaba, zata wuce tashiga wanka Inna tace"zo muyi lissafi Hafeeza"

Cikin nutsuwa ta dawo ta zauna,Inna ta janyo asusun dasuke tara ribar su ta fasashi, tahada da kud'in cinikin ranar suka qirgasu,Inna tace"to Islamiyar taku nawa sukace zaku bayar kudin saukar?"

Hafeeza tace"Dubu hamsin ne Inna,kuma tun ranar da suka fada mana nabiya gidan Kawu Hamza nafada masa"

Inna tace"toga ribar mu kinga munsamu kusan dubu saba'in da shida,kidauki dubu hamsin din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login