Showing 27001 words to 30000 words out of 37256 words

Chapter 10 - MATAR ABBANA COMPLETE HAUSA NOVEL

03 Sep 2025

2238

yasa kina jin magana ba kamar takwaranki ba"

Kan Hafeeza ya daure tarasa gane waye takwaranta, sai tayi murmushi kawai ba tace komai ba.

Husna ta kawo lemuka da ruwa da meat pie ta ajiye agaban Hafeeza sannan ta bawa Kaka wayarta tana cewa "Kaka kinga dinkin da telan mu yayi mana, ankon gidan Uncle Shu'aibu,ni kwata kwata dinkin bemin ba"

Hajiya Kaka tayi zooming photon dinkin tagani sannan tabata wayar tace"ai anko ne, koma Yaya ne kunde saka,kada yan'uba suce baku saba"

Tajuya ta kalli Hafeeza cikin salon jan magana tace"koba haka ba Hafeeza?"

Hafeeza tayi murmushi tace"hakane kam"

Hajiya Kaka tasake cewa"ko kin iya dinki su dinga kawowa kinayi musu?"

Hafeeza tayi murmushi tace"A a Kaka ban'iya ba"

Hajiya Kaka tace"Au to! jinake kin iya,Nima da sai in dinga bawa HAFEEZU nawa yana kawo miki, amma gaskiya ni in dinkin Zaki min ma saide kimin irin wanda kike sakawa,koba haka ba? saboda Idan zanzo gidanki inci kwalliya ta dashi inzo ko Allah zaisa mijin ki ya yaba"(=??)

Hafeeza tayi murmushi,ta lura matar tanada barkwanci sosai dakuma iya zama da mutane,cikin murmushi tace"Kaka ai abunda zan d'inga mikin ma shine zai siyo miki da kudinsa"

Hassana ta bude lemon da Husna ta kawowa Hafeeza ta zuba Mata a cup sannan ta tura Mata gabanta tana cewa "inde Kaka ce to zata qwace miki miji kuwa"

Hajiya Kaka ta miqe zata shiga kitchen ta kalli Hafeeza tace"kici dan abun ta6awar 'yar nan,bari na baku waje ku danyi gulmar samarin ku"

Gaba dayan su dariya suka saki,Husna ta gyara zama tace"Hafeeza bakici komai ba"

Sai alokacin ta dauki meat pie din taci dan kadan, ta ajiye sauran.

Cikin nutsuwarta ta kallesu tace"bari in tafi gida,kada a nemeni"

Husna ta Harare ta tace"har wani? daga zuwan naki? gaskiya ki tsaya muyi fira tukunna"

Hassana tace"Hafeeza ya samari? nasan suna nan lodi-lodi yaushe zamusha biki?"

Hafeeza tayi murmushi tace"wa? a a wallahi nima bansani ba"

Hassana tace" mukam wallahi Gara ayi mana auren mu,mazaje suna futowa zamuyi wuf, mu shige"

Hafeeza tayi murmushi tadan saki jikinta ganin Kaka bata wajan, tace"to wanne irin mazaje kuke so? ance yawanci yanbiyu sunfi son su auri mazaje suma Yan biyu"

Husna tace"hakan ma yanada dadi,ko banza kasan cewa kana tareda yar'uwarka, amma kinga ai abun dace ne, nide gaskiya inason namiji mai irin halin Yaya HAFEEZ, bana son hayaniya"

Hafeeza tanajin sunan gabanta ya fadi, tun kafin tayi magana Hassana tace"maganar gaskiya nide duk wanda nasamu banda za6i, kefa Hafeeza?"

Tafadi maganar tana kallon Hafeeza.

Adede lokacin Hafeez yabude qofar d'akinsa zai futo fuskar nan tasa ahade kamar hadari,har yanzu taqaicin rashin haduwarsa da'ita yake, saide sako kan da zaiyi zuwa falon idonsa ya sauka a kanta, gabansa yayi wata irin faduwa, cikin sauri yajuya da baya, ganin babu wacce ta lura da budewar qofar dakin nasa acikin su,saide bai maida qofar ya rufeta duka ba, yana iya hangosu, sannan kuma yana iya jiyo abinda suke magana akai.

Hafeeza kuwa zuciyarta daya tadan juya fararen idonta sannan tatafi duniyar tunani tana hango siffar saurayin ta Gaddafi acikin idon zuciyar ta sannan tace" inason namiji hafizin Alqur'ani,ban damu da rashin kudinsa ba,saide inaso ya kasance me qirar jarumai,me murdadden dantsan hannu"

Cikin sauri Hafeez dayake Jin firar ya kalli dantsan hannun sa,mamaki yagama kashe shi dama tana magana haka? hakan yana nufin batada aure kenan.

Hafeeza taci gaba da fadin"miskili wanda baya son hayaniya,kuma kyakykywan gaske"

Wannan Karon ma cikin sauri ya kalli fuskar sa ta screen din wayar sa dake hannun sa,har wani gyara sumar Kansa yake,gaba daya hankalin sa ya tafi zuwa gareta,besan ma yana wannan dube duben ba.

Adede lokacin wayar sa ta dauki qara,cikin sauri su Hafeeza suka juya suna kallon wajan, saide dayake ala6e yake, basu ganshi ba saide qarar wayar kawai.
Cikin taqaicin shigowar kiran Hafeez ya runtse idonsa,ya daidaita Kansa fuskar nan tasa ya daure ta kamar bashi ba,kawai yayi shahada yafuto daga dakin yana d'an danna waya.

Yana dan dago Kansa daga danna wayar dayake,idonsa ya fada cikin na Hafeeza,gabanta yayi wata irin faduwa sakamakon kayan data ga yana sanye dashi,kwata kwata wandon iyakar sa gwiwa,ga wannan Riga gaba daya dantsan sa awaje suke anyi masa zanen tattoo ajikin hannayen nasa,ga dan kunne amaqale a kunnansa na hagu, bata ta6a ganin namiji haka azahiri ba, hakan yasa cikin sauri ta sunkuyar da kanta qasa,gabanta banda faduwa babu abinda yake tana Addu'ah cikin ranta Allah yasa baiji abinda ta gama fadaba.

Complete document 1k




Amnah El Yaqoub
'
[6/14, 2:25 PM] El Yaqoub:


Koda wasa bai nuna wata magana tata6a had'ashi da'ita ba,d'auke Kansa yayi fuskar sa ahad'e kamar koda yaushe.
Hassana da Husna atare suka had'a baki wajan gaidashi tunma kafin ya zauna.

Furucin YAYA da Hafeeza taji 'yanbiyun sun fada hakan yasa tagane cewa kenan shid'in Yayan sune, tsananin mamaki yagama kamata,kuma har zuwa wannan lokacin gabanta banda faduwa babu abinda yake, kanta aqasa tana tuna abubuwan da suka faru tsakanin su ita dashi, yanzu fa kamar fanko yake ganinta tunda yariga yaga qirjinta,wani irin baqin cikin abinda ta aikata na bawa Fadila nono ya kamata,mema yakai ta ne? meyasa tayi hakan? Kowa yana ganinta da daraja, amma ban dashi, shi din kallon da zai dinga yimata daban.
Tunanin tane ya tsinke,taji kamar wani abu ya fada cikin qirjinta sakamakon Zaman da Hafeez yayi dab da'ita,saide akwai 'yar tazara atsakanin Zaman nasu, amma duk da hakan, awajan Hafeeza kusancin yayi kusanci sakamakon bata sababa.

Kanta aqasa yake har lokacin,gade esi iya esi afalon amma fuskarta harta fara hada gumi,cikin rawar murya tadan kalli gefensa kadan sannan tace"Ina kwana''

Agajarce ya amsa da "Lafiya"

Yadan kalli gefenta yaga abinda yake nema Wato remote,hakan yasa yakai hannun sa ya dauki remote din sannan yafaki idon qannan nasa, yayi sauri Yadan sake matsawa kusa da Hafeeza,itade Hafeeza kanta yana qasa,gabanta sai faman faduwa yake,Sarai taga lokacin daya sake matsowa kusa da'ita.

Hafeez ya kalli Hassana yace"Ke kawo min Coffee"

Cikin sauri Hassana ta miqe tashige kitchen.

Ahankali Hafeeza ta dan dago kanta, adede lokacin Hafeez ya kalleta afakaice,idonsu yana haduwa tayi sauri tasake yin qasa da kanta.

Hajiya Kaka tashigo falon taga yanayin Zaman Hafeez da Hafeeza yayi d'an kusanci,mamaki ya kamata ganin yanda Hafeez din ba mai sakewa da mutane bane, musanman yanmata, amma gashi a zaune dab da yarinyar kuma ko a jikinsa.

Ta kalli Hafeeza taga kamar atakure take da Zaman, ta zauna tareda fadin" 'yar nan cire hijabin naki mana kisha is'ka"

Hafeeza tatuno maganar Maman Fadila da take cewa abinda yagani ne ya dawo yaqarasa gani, Wato ta cire hijabi yanzu ma yasake kallon qirjinta, ahankali ta danyi murmushi tace" a a babu damuwa Kaka"

Hajiya Kaka tace"tokici abinda qawayen naki suka kawo miki mana,ko adafa miki wani abincin?"

Cikin sauri Hafeeza ta Girgiza kanta, batare da tayi magana ba.

Hajiya Kaka tayi murmushi, gaba daya tagama karantar yarinyar a firgice take, ta kuma tabbatar saboda Zaman Hafeez Akusa da'ita ne, cikin son Jan magana tace" ni qosai Naso ci kuma sunje nemomin basu samu ba"

Hassana ta kawo wa Hafeez Coffee ta'ajiye agaban sa.

Ahankali yasaka hannu ya dauki coffee din sannan ya kalli Kaka cikin maganar sa me aji yace"Aina fada miki tadena,ba zatayi ba"

Gaban Hafeeza ya Yanke ya fadi ganin akanta ake maganar.

Hajiya Kaka tace" ko zatayi ma abaqin miskilancin ka ai zaka min baki taqiyi, kaide Matarka ta shiga ukunta da baqin miskilanci"

Hafeez yayi sipping Coffee din hannun sa sannan yajuyo yana satar kallon Hafeeza,duk da cewa ta kasance tana masa kwarjini yarinyar Gara yayi kokari ya kawar da hakan aransa kada yan maza suji kunya.


Wannan Karon ma sun sake hada ido shida ita,hakan yasa cikin ranta ta Yanke shawarar tafiya gida, kafin ta miqe Hassana tace" Hafeeza yaushe ne tafiyar ki Saudia?"

Cikin murmushi ta Kallesu tace"bazan wuce sati biyu ba"

Hafeez yajuyo Kansa tsaye ya kalleta, sannan ya ajiye Coffee din ya tashi yafice daga falon.

Yanajiyo Hajiya Kaka tana cewa "to nide Abayar da Zaki siya kiyiwa saurayin ki ado da'ita, Nima irin ta Zaki siyo min"

Hafeeza tayi murmushi ta miqe tsaye tace"Kaka duk abinda nasiyo kema naki daban zan siyo miki"

Hajiya Kaka tace" to Allah yayi muku albarka, Allah yabaku mazaje nagari"

Hafeeza tace"Amin Kaka,zan tafi gida kada anemeni"

Su Husna suka kwashe duk kayan snack din da suka kawo Mata da lemuka suka zuba Mata aleda, sannan suka rakota bakin get sunata tsokanar ta,daga bakin get din ta dakatar dasu saboda babu Nisa sosai tayi musu godia bayan sunsha Fama da'ita kafin ta karbi snack din da suka biyota dashi.

Zuciyarta daya ta futo daga gidan ta dauki hanyar gida tareda ajiyar zuciya tanajin wani irin dadi saboda cikin gidan atakure take kasancewar Hafeez yana wajan.

Ba tayi nisa sosai ba kawai taga mutum agaban ta,qiris ya rage su hadu da juna hakan yasa tayi saurin yin baya,hannunsa ya harde a faffadan qirjinsa ya zuba Mata narkakkun idanunsa, gabanta ne ya fadi ganin irin kallon dayake Mata,ahankali ta matsa zata wuce ta gefensa cikin sauri yasake shan gabanta, Hafeeza ta kalli ko'ina taga layi shiru babu mutane, gashi tana tsoro kada yayi mata wani abu,kuma dama Maman Fadila tafada mata cewa idan zatazo wajan sa kada tatafi ita kadai, to dawa zatazo bayan ita ba wasu qawaye ne da'ita ba?
Cikin dauriya ta dago kanta ta Kalle shi tace" kabani kudin Inna zan kai Mata"

Haka nan Hafeez ya tsinci Kansa dajin dadin yanda suke maganar su biyu,cikin wani irin nishadi yace"wanne kudi?"

Hafeeza ta lumshe idonta cike da damuwa sannan ta bude shi akansa,Hafeez yazubawa qwayar idonta kallo me kama data mage,cikin sauri dakuma qaguwa da tsaiwar ta awajan tace" Kabani"

Wani miskilin murmushi yasa ki,yanayin yanda tayi maganar cikin fishi sai hakan yasake birgeshi, duk da gabansa yana dan faduwa sakamakon rashin Sabo, hakan ya daure yajefo Mata tambaya, yace"Babyn wa kika kai asbiti rannan?"

Gabanta ya Yanke ya fadi,cikin taqaici ta runtse idonta sannan ta bude tace"Malam Kadena min wannan maganar,bana so!!"

Ta qarasa maganar cikin tsananin 6acin rai dakuma quluwa.

Hafeez yadan shafa sumar Kansa sannan ya kalli layin dasuke tsaye yace"gidannan akwai qaran Gen. , kina min bayanin Babyn dana ganku tare,sai naji kamar kince narabu dake"

Cikin 6acin rai Hafeeza tace"malam cewa nayi Kadena min wannan maganar, kabani kudina natafi "

Hafeez yace" waye zai baki kudi?"

Cikin sauri tace" waye zai bani idan bakai ba? "

"an rad'awa kudin cewa nine kawai mai ba dashi? nabaki kudin ki mana, kiduba nabaki"

"yaushe kabani?"
Cewar Hafeeza.

Hafeez yasaki ajiyar zuciya yace"kiduba rigar ki yana ciki,kokuma nina duba"

Ran Hafeeza yasake 6aci ganin irin rainin hankalin da Hafeez din yazo Mata dashi,yaushe yabata kudi? yaushe yasaka mata kudi arigar ta?

Cikin 6acin rai tace"Malam bazan duba ba kawai kabani natafi"

Cikin dakiya dakuma aji yasake matsowa dab da'ita, gabanta yasake tsananta faduwa har tana iya juyo numfashinsa akan fuskarta,cikin wata irin muryar rad'a yace"tsaya na dauko miki"

Bai saurari amsar ta ba yakai hannun sa cikin aljihun doguwar rigar da take jikinta,Hafeeza tanajin haka ta zaro idonta,cikin hanzari tafara kiciniyar qwacewa, nan da nan kokawa ta 6arke a tsakanin su, shi yana kokarin dauko Mata kudin daya Riga yasan cewa yasaka Mata kudin a jikinta, ita kuma tana kokarin qwace kanta tana so taraba kanta dashi,cikin azama tayi kokarin ruqo hannun sa mai cike da gashi,tayi Sama da hannun nasa zata bige hannun,Shikuma Hafeez a maimakon dawo da hannun sa cikin aljihun rigarta by mistek hannun sa yadan bige boob's dinta, laushin da yaji ne yasa yakai idonsa kan hannun sa,adede lokacin itama takai idonta kan abinda ko a mafarki bata ta6a tunanin kafin tayi aure wani namiji zai iya kai hannunsa wajan ba, atare suka zaro idonsu, cikin sauri Hafeez ya janye hannunsa, wata irin kunya ta kamashi,yakasa hada ido da'ita,hakan yasa Kansa aqasa yace mata" I'm sorry,pls I'm sorry"

Cikin sauri yabar wajan yajuya zuwa gida,ko takan motarsa da take ajiye agefe baibi ba.

Cikin tsananin baqin ciki Hafeeza ta tsugunna awajan ta fashe da wani irin kuka.

Lokaci daya,maganar Maman Fadila ta fad'o Mata, cewa idan zatazo wajan sa karta kuskura tazo ita kadai, sosai take kuka kamar anyi mata mutuwa, saida ta gama shan kukan ta kafin tamiqe cikin baqin ciki tanufi gida,kana ganin yanayin tafiyar ta dakuma fuskarta zaka tabbatar da cewa ranta a6ace yake.

Tana zuwa gida kai tsaye tanufi daki ko kallon Inna da take zaune cikin rumfa ba tayi ba.
Ta Rasulu ta kalleta tace"kin kar6o kudin ne?"

Ataqaice Hafeeza tace"A a"

Ajiyar zuciya Ta Rasulu tayi, sannan tace"dama bakida niyya"

Hafeeza tayi shiru batace uffan ba.
Ta Rasulu tasake kallon ta tace"kin zauna kinyi shiru sai zun6urawa mutane baki kike, kinyi waya da saurayin naki yau kuwa?"

Yanzunma a taqaice Hafeeza tace"A a"

Inna ta jinjina kanta tace"zan baki shawara Hafeeza,wannan saurayin naki dakika dora ranki akansa batake yakeba, duk lokacin da kikaje Saudia kawai kiyi Addu'ah Allah yabaki wani"(=??)

Cikin sauri Hafeeza ta kalleta,ta rasa me Gaddafi yayi mata bata sonsa,bawani saurayi da zata roqa face tayi Addu'ah Allah ya tabbatar Mata da Alkhairi ita da Gaddafi.


Tana gama yanke wannan tunanin ta tashi tashige cikin daki tafara qoqarin cire kayanta domin shiga wanka, tana cire rigar jikinta taga wata takarda ta fad'o daga aljihun rigarta,cikin tsananin mamaki ta tsugunna ta dauka, tana budewa taga dala dari, gabanta yayi mugun faduwa, idan bata manta ba kwana ki anta6a fada musu cewa duk dala d'aya ta haura dubu da dari biyar, wannan mutumin Kansa daya kuwa? Meyake damunsa? mezatai da wannan kudin? Idan Inna tasani aita shiga ukunta, yaushe ma yasaka Mata kudin? tunani tatafi, ta tuna yanda yasake matsowa jikinta afalon gidan su, babu makawa a wannan Zaman yasaka Mata, shiyasa bayan tafuto yace yariga ya bata taduba jikinta, lokaci daya hannun ta ya dauki rawa, ta tashi ta saka dalar acikin kayanta, sannan tashige wanka.



*** *** ***


Acikin satin Hafeeza tatafi Saudia, gida ya rage daga Inna sai masu dan leqo mata suna dan tayata fira, sai kuma Maman Fadila tadake yawan shigowa tana kawo Mata Fadila duk da suna fafatawa kafin Inna ta kar6eta.

Duk wani motsin Hafeeza dayake Saudia Hafeez yana sani, satinta daya da tafiya da daddare yana kwance adakinsa bayan yagama shirin bacci yadokawa Ma'aruf waya.

Daga can 6angaren Ma'aruf ya kalli wayar sa cikin tsananin mamaki ganin shabiyu saura, cikin sauri ya dauki wayar, Yace"Hafeez lafiya kake kuwa?"

Murmushi Hafeez yayi yace" lafiya ta kalau Ma'aruf ,inaso muyi sallama ne gobe zan tafi Saudia"

"zakaje Umarah ne?"

Cikin aji yace"zanje Umarah da neman iri,akwai yarinyar da take hargitsa min lissafi Ma'aruf,inajin abubuwa dayawa akanta"

Ma'aruf dayake kwance agadonsa ya tashi zaune tareda dora fillo akan cinyarsa cikin tsananin murna yace"wow,wacce me sa'ar ce wannan?"

Hafeez yasake juyi akan gadonsa cikin jin dadi,wannan firar dasuke ta Hafeeza tafi masa komai dadi, cikin wani irin Nishadi yace" ina yawan Jin faduwar gaba duk lokacin dana tun kare ta, tanada kwarjini sosai,ina yawan Jin feeling akanta, Ma'aruf rana daidai ne banayin mafarki da'ita wallahi"(=?H?=?J?)

Ma'aruf ya kwashe da wata irin dariya yace"Abokina kakamu wallahi, please kayi Mata magana mana,meyasa zaka tafi Saudia? ka tsaya ku fuskanci juna tukunna,but Wai Kaka ma tasani kuwa?"

Hafeez yayi ajiyar zuciya yace" idan Kaka tasani ai tun kafin na fadawa yarinyar zataje ta nema min auren ta,gaskiya bata sani ba, inaso ne nafara tunkarar yarinyar dakaina, naga ita din ustaziya ce, kullum tana cikin hijabi, yanzu taje Saudia,inaso nasameta acan muyi magana,daga nan zanyi Addu'ah saina dawo."

Ma'aruf yasa ki ajiyar zuciya yace"harna matsu ayi abunnan wallahi Hafeez,kuma kayi sa'ah mutumina, kasan ustazan yaran nan komai kaine zaka koya musu,babu damuwa saika dawo,Allah yasa muji alkhairi,amma ka kawar da wannan kwarjinin dakace tana ma kuyi magana"

Hafeez yace"ok"

Daga nan sukai sallama fuskar Ma'aruf cike da farinciki.


Bayan kwana hudu acan Saudia Hafeeza tabar harami tana zaune awani wajan shan shayi tana jiran akawo mata,sanye take cikin baqar abaya me adon stone baqi da kuma fari,saide baqin stone din yafi farin yawa, tasake yin fari tayi Shar abun ta bazaka taba cewa bahaushiya ceba musanman yanda tayi rolling da mayafin abayar akanta, daga Saman goshinta kana iya hango yanda gashinta ya kwanta luf.

Waya ce a hannun ta babba tana dannawa hankalin ta kacokam yana kan wayar, tana so tasan abubuwan dayake kan wayar kasancewar ba iya wayar tayi ba, har yanzu tana so tasan waye yake aiko Mata abubuwa na more rayuwa tunda tazo qasar, hakan yasa tayi wa Kawunta Hamza magana ganin yanda data bar harami idan takoma masauqin ta zata ga an ajiye Mata abubuwa naci da Sha masu kyau, kuma kawun nata ya tabbatar Mata cewa dan majalissa ne, Wato wanda yabiyamata kujerar zuwa Saudia, bata kawo komai aranta ba, hankalin ta kwance take ibadarta, tana yiwa kanta Addu'ah da qasa da kuma Sauran musulmi, saide rabi Addu'ar tata tafi yawa ne ga iyayen ta dasukabar duniya.

Wannan hutu da sauyin Cima data samu shine yasa tasake yin wani fresh,tayi fari sosai hatta nashanunta sun sake cika sosai.

Wani irin daddan qamshin daya daki hancin ta, shine yasa ta dago kanta da sauri, dede lokacin shima ya zauna hakan yasa idonta ya fada cikin na Hafeez, yayi masifar kyau cikin qananun Kaya,farar rika sai kuma baqin wando, yasaka glass Jan duhu wanda yasake qawata fuskar sa.

Cikin sauri ta janye idonta daga Kansa,duk da gabanta yana faduwa haka ta maze taci gaba da danna wayarta.

Adede lokacin aka kawo Mata shayin, wanda yakawo Mata yayi magana da larabci taba shi amsa, sannan yajuya, hakan ba qaramin dadi yayiwa Hafeez ba, sosai ta birgeshi.

Cikin dakewa yadan motsa lips dinsa sannan yace Mata "Sunana HAFEEZ"

Ataqaice tace"HAFEEZA"

Murmushi yasa ki yace"nasani"

Kallonsa tayi ta dauke kanta, sannan ta dauki cup din shayin tafara Sha, Adede lokacin shima aka ajiye masa wani, ya dauka yafara Sha idonsa akanta, sosai yake kallon dan mitsitsin bakinta yanda take shan shayin kamar yakai bakinsa ya lashe lips din nata.

Hafeeza tafara tsarguwa da kallon dayake Mata, ahankali itama ta dago kanta ta Kalleshi ko zai janye idonsa daga kanta,tana kallon sa idonta ya sauka akan faffadan qirjinsa har tana hango gashi a kwance akan qirjin nasa kasancewar bai gama rufe botir din gaban rigar ba, saide kuma abun mamaki data kalleshin ma ko alamun janye idonsa baiyi ba, sai ma wani murmushi dayake binta dashi wanda yasake qawata kyakykywar fuskar sa.

Adede lokacin Kira yashigo wayar sa, kasancewar wayar tasa a ajiye take agaban su akan table din dake gabansu hakan yasa Hafeeza taga sunan MAMA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login