Showing 90001 words to 91952 words out of 91952 words

Chapter 31 - KWANTAN ƁAUNA HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

4816

Asad yayi har hak'oran sa suka bayyana fuskar sa ta washe sosai annurin ta ya fito kyau da zatin da Allah yayi mata ya fito k'arara ba tare da ya shirya ba. Ganin hakan ya saka Hydar yayi murmushin shima yace, "Kayi murmushi mana nasan zaka iya sabida kana sonta."

Baice komai ba Hydar daman yasan bazai ce ba sai yace, "Deaf nifa ina ganin rashin gaskiya a tare da Aliyu cikin kwanakin nan, bana amincewa da yanayin sa gabad'aya." Tab'e baki Asad yayi kawai baice komai ba dan shima ya fahimta musamman ma halayya da shiga da ya canja ya koma sak irin nasa kafin ya d'auki wayar sa ya fara dannawa. Haka suka zauna shiru babu mai magana a cikin su sai daga baya suka tafi suka bar gidan.

*☆☆*

Mum ce a zaune a gaban wani malamin daban ba wanda suka je wajan sa da Mama ba yana ta dube-duben sa kafin ya d'ago ya kalle ta yace, "Auren nasu yana da wahalar rabuwa amma za'a raba shi." Mum ta girgiza kai tace, "haka nake so naji Malam, so nake a raba auren a saka masa tsanar yarinyar itama a saka mata tsanar sa ta har abada." Malam yace, "wannan baki da matsala Hajiya Sadiya, sai dai za'a kashe kud'i."
"Kud'i ba matsala ta bane ba Malam ayi kawai."

Malam yace, "Zaki ga aiki kuwa nan bada jimawa ba." Gyara zama tayi tace, "Aiki na biyu so nake a saka masa k'aunar Jidda a ransa fiye da yadda yake k'aunar ita gurguwar, ya manta da kowa da komai Jidda kawai yake gani. Hatta uwar sa Rabi'atu ya manta da ita gabad'aya ya zama Jidda ce zata juya shi yadda take so duk abinda tace shi zaiyi." Girgiza kai tare da yin dariya kad'an yace, "Za'ayi hakan tabbas. Amma yana da wahala kasancewar sa mai ibada da zama cikin alwala muna buk'atar lokacin da ya kasance babu tsarki a jikin sa a sannan aikin mu zai tafi yadda muke so. Dan aikin da zamuyi masa akan Jidda ba k'arami bane ba gaskiya."

Mum tace, "ta yaya zamu san bashi da tsarki?." Malam yace, "Wannan ba abin damuwa bane ba zamu gano hakan da kanmu." Mum tace, "to ma sha Allah haka nake so naji. Batun auren sa da Jiddan yana nan dai ko?." Malam yace, "yana nan kawai dai akwai sauran lokaci amma akwai maganar auren su kamar yadda nake shaida miki, kuma dole sai ita gurguwar bata tare dashi sannan zai kalli Jidda."

Mum tace, "Za'ayi maganin ta ai. Ina maganin da mukayi zaka bani?." Malam ya juya gefen sa ya d'auko wani turare a k'aramar kwalba ya mik'a mata yace, "Wannan turaren zaki shafa in zaki je wajan ta ko in zaki had'u da ita a ko wanne lokaci, ina tabbatar miki tana shak'ar sa a lokacin babu wani sirrin ta da zata b'oye miki komai sai kinji sai kuma abinda kika ce mata shi zatayi."

Mum ta karb'a ta saka a jaka ta fito da kud'i masu yawa ta ajjiye masa kafin tace, "Na gode Malam, a cigaba da aiki in komai yazo mana yadda muke so duka tare zamu ji dad'i, sauri nake mayi waya" ta fad'a tana mik'ewa ta fita da sauri.

*☆☆*

"Me kike so kice mana kenan master planer? Asad zaiyi aure?" Waziri ya fad'a a bayyane cike da mamaki da kuma al'ajabi. Daga cikin wayar Hajiya tace, "Nima dai jin abun nayi wani iri, kika ce kuma gurguwa zai aura?."

Dariyar tayi tace, "tabbas Asad zaiyi aure nan bada jimawa ba zai bar k'asar Nigeria zai tafi can wata k'asar yaje kula da matar sa, a wannan lokacin muke da damar sake nisanta shi da k'asar gabad'aya."

Waziri yace, "To ya maganar Aliyu kuma? Ya amince min amma har yanzu bai sake tuntub'a ta ba nima kuma haka."
"Ya fika wayo wannan yaron raba k'afa yayi yana nasa aikin yana kuma naku aikin, duk maganar auren nan shine assasata badan komai ba sai don cikar burin sa. Zai mana amfani a tafiyar mu sosai domin kansa yana ja fiye da tunanin ku zai kawo mana mafita lokacin da abubuwa suka yi mana yawa."

Hajiya tace, "Sai nake ganin kamar yaudara ce amma baya tare damu." Master tace, "yana cikin mu yana kuma saka idanu akan ku gabad'aya duk motsin ku ya sani, tafiya dashi zata yi mana amfani sosai amma sai nan gaba zaku fahimci inda na dosa. Tsarin da ya saka muka jawo shi cikin mu yanzu babu batun sa tunda shi Asad d'in zai bar k'asar nan da wasu kwanaki ba buk'atar mu canja shi da Aliyu."

Waziri yace, "kuma kina ganin tsarin zai tafi yadda muke so kuwa?."
"Sosai ma kuwa fiye da hakan ma ku dai ku shirya ta kusa fashewa mu samu abinda muke so, boom!" Ta fad'a tana yanke wayar compress call d'in ya rage daga shi sai Hajiya a kai. "kana ganin abinda tace haka ne kuwa? Nifa ban ji maganar aure a cikin gidan nan ba ta ya akayi ita ta san da ita?."
"Tunda tace haka tofa haka d'in ne, zan bincika yanzun nan naji gaskiyar lamarin koma meye ai bazai b'uya ba, in da gaske akwai maganar auren ai sai munfi kowa farin ciki da hakan. Ki saurare ni zan sanar dake abinda na binciko" ya fad'a yana yanke wayar shima.

*☆☆*

Rauda haka ta wuni sukuku bata son Anas amma bata jin dad'in raba su d'in da akayi lokaci d'aya ba gabad'aya sai taji tana jin zafi a zuciyar ta hakan ya haifar da sanyin jiki a gangar jikin ta. Tana zaune a d'akin da suke kwana ita da Ummulkhairi tana juya wayar da ya bata gabad'aya wani iri take jin ta kamar ba ita ba zuciyar ta a jagule kamar ta zubar da hawaye. Shigowar sak'o taji wayar ta tayi kamar bata ta duba ba sai kuma ta duba ta bud'e tana karantawa.

_Assalamu Alaikum Rauda ina fatan kin wuni lafiya ya jikin ki da jikin Umma?. Nasan kin ji labarin abinda yake faruwa wata k'ila zaki ji babu dad'i duk da ba sona kike yi ba amma nasan zaki tausaya min tunda kin san ke kad'ai ce a zuciyata ke kad'ai kuma nake k'auna. Wallahil azim ke nake so Rauda har gobe har jibi har na mutu amma iyayena sun nuna min wacce suke so na aura babu yadda zanyi na amince musu sabida matsayin su gare ni. Bazan ce ki jira ni nayi aure na dawo na aure ki ba nasan abu ne mai wahala shiyasa na saka a raina na rasa ki har abada, wallahi ina rubuta miki message d'in nan ina hawaye Rauda domin na tabbatar na rasa abinda nake so wanda bazan mayar da kamar sa ba har abada. Ina sonki Rauda, ina k'aunar ki har gobe, naso ace zan rayu dake har abada amma hakan bai yu ba duk da har yanzu ban cire rai dake ba amma ni kaina ina ganin wahalar hakan. Ki yafe min wallahi ba'a son raina ba banyi kuma dan na yaudare ki ba, kunyar ki nake ji shiyasa na kasa ko kiran ki a waya dan ban san me zance miki ba in na kira ki, ina fatan zaki yafe min za kuma ki dinga min addu'ar Allah ya bani ikon yiwa wacce za'a aura min adalci domin matuk'ar ba ke ba bana tunanin akwai wacce zan zauna da ita da zuciya d'aya. Ina miki fatan alkhairi Allah ya baki miji na gari ya baki lafiya Amin. ANAS._

Babu tsammani taji hawaye yana bin fuskar ta wanda batayi tunanin zasu zuba ba a wannan lokacin ba, ta ajjiye wayar tana kuka mara sauti tana fad'in, "Allah ya baka juriyar rashi na Anas, ni kaina zanyi rashin wanda yake sona da zuciya d'aya, ko bana son ka zan iya zama dakai Anas sabida kai me k'auna tane na tabbata bazan yi dana sanin zab'ar ka ba, Allah bai amince zan zama matar ka ba, Allah ya baka hak'urin rashi na" ta fad'a tana goge idanun ta jikin ta duk ya mutu murus.

Asad ne ya fad'o mata a rai nan take gaban ta ya fad'i ta dafe k'irjin ta tana jin yadda yake bugawa tayi shiru ta nutsu tana sauraron bugun zuciyar tata a hankali, ta rasa meyasa in ta tuna shi take jin bugun zuciya ta rasa dalilin hakan. kawar da tunanin tayi ta d'auki wayar ta ta shiga mayarwa da Anas amsa da kalamai masu sanyaya zuciya da taushi had'i da tausasawa har ta kammala ta ajjiye wayar a gefe tana tunani.

'Matuk'ar bai bayyana min yana k'auna ta ba bazan amince da auren sa ba, a soyayya ba'a nuna mulki da izza shi na lura abinda yafi mayar da hankali kenan a kai, zan nuna masa ba'a samun ko wacce mace da k'asaita ko izza.' Abinda take fad'a a zuciyar ta kenan a bayyane tace, "to ma in ya furta zan amince kenan? Anya na dace da rayuwar sa na kuma yiwa kaina adalci..? ga abinda mahaifiyar sa take fad'a ban kai kaina inda za'a kashe ni ba kuwa?. To wai duk da nake wannan tunanin sonsa nake kome..?" Ta fad'a tana jan dogom tsaki tana kallon sama abubuwa sun mata yawa a kanta duk sun cushe mata zuciya.

K'arar wayar ta taji duk a tunanin ta a Anas ne ta jawo ta ta d'auka bata duba waye ba ta d'aga wayar ta kara a kunnen ta tana jiran taji maganar Anas sai taji sab'anin hakan, nan take zuciyar ta ta sake bugawa ta cigaba da bugu kamar ana doka ganga tunanin ta ya tsaya cak lokacin da taji ance, "Ina sonki, na fara sonki lokacin da ban shirya ba........!."

*End of Book1*🤗⛹‍♀️

_Waye ya kira Rauda wannan lokacin..? Asad ne ko kuma Hydar ne ya kira a madadin sa...?. Rauda zata amince da Asad tunda babu maganar Anas a halin da ake ciki ko a'a..? In ta amince dashi tayi ya da Mama wacce take shirin kashe ta? Anya auren su zai kasance Mama tana raye...?. In ya kasance kuma ta yaya ta wacce hanya hakan zata faru...?. Ina matsayin Jidda da kuma Mum da suke son ganin bayan Mama? Asad zai amince da Jidda kuwa har ya aure ta? In ya aure ta kuma ya kenan in suka raba shi da Maman sa?. Aliyu fa? Anya shima zai bar Asad zaman lafiya duba ds yadda ya koma acting like Asad..? Anya babu abinda yake shiryawa a kan hakan tunda dukkan mu mun shaida yana son ganin bayan Asad?. Wacece master planer? A ina take da zama da take sanin sirran cikin gida tun kafin na gidan su sani?. Ina makomar su Waziri zasuyi nasara ko a'a? Shin Asad zai mulki katagum ne ko a'a? Shin Rauda zata zata aure shi ko a'a? Shin Jidda zata aure shi ko a'a?. Akwai rikici, akwai makirci, akwai tashin hankali, akwai dana sani, akwai soyayya, akwai akasin ta duk a cikin book2._

_Duka amsar wannan tambayoyi suna cikin littafin kwantan b'auna book2 da zai fara zuwa nan bada jimawa ba in sha Allah akan naira 500 kacal. domin biya tuntub'e ni akan number via whatsapp 09030398006. Kar ku sake a baku labari tabbaci nake dashi akan KWANTAN B'AUNA salon sa ba irin wanda kuka saba karantawa bane, daban yake a cikin littafan sai kayi sa'a zaka samu irin sa._

Sai na jiku mutanen amana🥰

#Vote
#Share
#like
#Comments
#gidan sarauta
#makarci
#fuska biyu
#Soyayya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login