Showing 54001 words to 57000 words out of 91952 words

Chapter 19 - KWANTAN ƁAUNA HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

4801

anjima.

"Gaskiya komawa zanyi bazan iya wuce mazan nan ni kad'ai ba" ta fad'a tana gyara zaman sandinan ta zata bar wajan.
"Takawar ka lafiya d'an sarki jikan sarki, takawar ka lafiya yarima mai jiran gado, taka a sannu sikari bakai farin banza ba, inuwar kowa kake, dawisu sarkin ado, wallahi in kana wajan ba'a kowa sai kai kad'ai, d'aya kake tamkar da dubu." kirarin da ta jiyo kenan daga bayan ta kafin ta farga har an zo inda take duk sai ta rud'e ganin wanda take jin tsoro masu bulalai a hannun su. Tsawa d'aya daga cikin dogaran da suke take masa baya yayi mata yace, "gafara y'ar talakawa!" Ya fad'a da k'arfin gaske.

Duk sai ta kuma gigicewa tama rasa wacce hanya zata bi zuciyar ta na rawa dan bata k'aunar ganin su ko kad'an gashi bata son tsawa.

"Baza ki matsa bane?!" Aka sake fad'a mata kafin ta dawo hankalin ta. Aliyu face d'in ta yake k'arewa kallo ganin yadda ta rud'e ya kuma tabbatar itace fa ba k'arya idanun sa sukayi masa ba. "You!" Ya furta cike da mamaki yana k'are mata kallo tun daga sama har k'asa kafin ya cize bakin sa yana kallon motar sa wacce yafi so duk duniya tana jikin ta a tsaye har da dafawa.

Sai a sannan ta dawo nutsuwar ta ta danne tsoron da take ciki tayi niyar barin wajan yace, "ke mahaukaciyar banza, ki kiyayi idanu na su sake tozali da k'aramar mummnar fuskar ki. Duk sanda na sake tozali da bak'ar fuskar ki wallahi sai na canja miki kamannin" ya fad'a a kausasahe yana nuna ta da yatsa.
A fusace ta juyo ta zuba masa banzar harara tace, "indai har ni mahaukaciya ce tabbas kai kakana ne a hauka domin a wajan ka na gani na koya, kaine mahaukaci bani ba a zahirance ana ganin yanayin ka an san na mahaukata ne. Baka isa kayi min komai ba kuma wallahi nafi k'arfi wanda ya fika ma balle kai iskar titi" ta fad'a cikin salon rashin kunya tana hararar sa cikin tsana da b'acin rai.

Kafin kace kwabo dogarin bayan ta ya zuba mata bulala a baya ta runtse idanu domin bulalar ta shige ta sosai ta hana idanun ta kuka amma tana jin zugin ta a gadon bayan ta, kallon ta kawai yake da mamaki ya rasa abinda zai mata ya wuce daga b'acin ran da ta jefa zuciyar sa a ciki hakan ya saka shi yin cak yana kallon ta. D'aga hannu yayi zai d'auke ta da mari ganin hakan ya saka ta runtse idanu yaji an rik'e hannun nasa daga baya bayyanar wanda ya rik'e hannun nasa ya sake b'ata masa rai yana kallon sa yace, "Aliyu why?."

Jin shiru ba'a mare ta ba ya saka ta bud'e idanu tana kallon su, gaban ta yayi mummnar fad'uwa ganin sun zamar mata guda biyu hatta kayan jikin su iri d'aya komai nasu sak kwabo da kwabo baka banbance su. Murza idanun ta tayi ta sake kallon su a lokacin da Aliyu ya fizge hannun sa yana fad'in, "look Asad babu abinda ya shafe ka babu wanda ya isa ya hanani ganin waye uban yarinyar nan a kaf duniyar nan, babu wanda ya isa ya hana ni sakawa a sake b'alla mata k'afa."

Asad ya kalle ta itama shi take kallo idanun ta a bud'e yace, "Jeki." Kasa motsawa tayi jin sanyin muryar sa har cikin kwanyar ta ta kasa koda motsi sai kifta idanu da take yi. "Kee y'ar talakawa baki ji abinda yarima yace ba ne!" Aka sake mata tsawar da ta firgita ta har sandar ta guda d'aya ta fad'i.

"Kar ka sake!" Ya fad'a yana d'agawa wanda yayi tsawar tsayan sa tare da had'e fuskar sa. "Tuba nake ranka ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ka" ya fad'a yana zubewa a k'asa dan bai tab'a jin Asad yayi tsawa haka ba tunda suke. Asad ya sake kallon ta baice komai na kamar ta san me yake nufi ta duk'a zata d'auki sandar ta ya kalli dogarin sai ya zabura ya d'auka mik'a mata yana fad'in, "Wuce ki tafi baiwar Allah, Allah ya baki lafiya" ya fad'a a sanyaye yana bata hanya. Da yake babu mutane a wajan da suke masu zaman makokin suna can nesa ba hango su ake ba hakan ya saka babu wanda ya lura da abinda yake faruwa a wajan.

A sanyaye take takawa jikin ta kamar an mata dukan tsiya tana tafiya tana waiwayon su taga d'aya daga cikin su yana ta masifa d'ayan kuma yama bar wajan da alama wanda yake k'okarin dukan nata ne yake fad'a, kallon gaban ta tayi ta cigaba da tafiya gaban ta na fad'uwa matuk'a zata iya rantsewa da Allah bata tab'a ganin y'an biyu masu kama da juna kamar su ba.

K'arar mota taji a baya ta Aliyu ne ya wuce a guje ta sauke numfashi tana bin motar da kallo gaban ta na cigaba da fad'uwa tsoro duk ya mamaye mata zuciya. Tunani take son yi amma ta fi to ta samu waje tukunna ta zauna sai tafi yin tunanin dakyau.
Tafiya take a kan hanyar babu kowa kamar yadda ta biyo tana tafe a hankali tana tunani, zafi bayan ta yake yi mata inda suka dake ta da bulala ta runtse idanun ta sosai har lokacin tana ji zafi sosai.

Asad yana hangon ta yana tawowa a bayan ta a mota a hankali ya rasa me yake d'aukar sa akan yarinyar ya san tabbas tana bashi tausayi amma bayan tausayi yana jin wani abu amma ya kasa fassara meye. Yana ganin ta kamar yarinyar cikin mafarkin sa abinda ya saka bai tabbatar ba sabida har lokacin fuskar ta gabad'aya bata tab'a bayyanar masa a mafarkin nasa ba.
Yana so ya k'arasa ya taimake ta ya kai ta gida amma kuma yana jin zai iya hakan gwara kawai ya k'yale ta.

Waje yaga ta samu ta zauna a kan wani dutse dake kan hanyar tana sauke numfashi alamun ta gaji, tsayawa yayi a motar yana kallon ta zuciyar sa na angiza shi akan yaje ya taimaka mata abar a taimakawa ce. Taka motar yayi yazo kusa da ita ya sauke glass ya kalle ta itama ta kalle shi suka had'a idanu duk sai ta dabarbarce kamar mara gaskiya ta fara kallon gefen ta kamar wacce take neman wani abun da ta ajjiye a wajan. Wani abu take ji mai sanyi yana shiga duk ilahirin jikinta wanda ya kasance bak'o a gare ta shiyasa duk ta dabarbarce jin bak'on yanayi a tare da ita har tana sauke ajiyar zuciya ga bugun da k'irjin ta yake yi.


*Akwai k'ura fan's.*⛹‍♀️⛹‍♀️🤸‍♀️🤣

*KWANTAN ƁAUNA*

©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*016*

Yarda take jin gaban ta yana fad'uwa shima haka yake ji bai mata magana ba kuma bai d'aga glass d'in motar sama ba balle ya bar wajan yana tsaye har lokacin ko motsi bayayi. kanta ta sunkuyar k'irjin ta na bugawa duf, duf, duf, kamar wacce tayi gudu mai nisan zango tana raba idanu a k'asa tana ji kamar ta tashi ta gudu daga wajan. Ya bud'e baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya d'aga glass d'in motar ya ja motar ya bar wajan a guje.

Nannauyar ajiyar zuciya tayi har da dafe k'irji jin ya tafi ta bi motar da kallo har lokacin k'irjin ta bugawa yake yi tace, "Ni Rauda na shiga uku, na d'auko abinda yafi k'arfi na" ta fad'a tana haki har lokacin tana kallon inda motar ta bi.
"Ke kuma zaman me kike a nan?" Aka fad'a daga gefen ta ta kalli inda taji maganart aga Habiba da Walida sai taji dad'i a ranta tana k'okarin mik'ewa suka zo suka kama ta ta mik'e tsaye.

"Bari kawai gidan gaiswar can zan je fa har na shiga layin naga maza shine zan koma gida an jima Khairi ta rako ni." Habiba tace, "Mu ma can zamu je ai yanzu, muje to." Ba musu suka jera suna tafiya a hankali sabida yanayin tafiyar ta. Waiwaye suka ga tana yi suka juya suma suka babu abinda take kallo Walida tace, "Wai me kike nema ne?."
Bata amsa ba suka cigaba da tafiya har suka shiga cikin gidan rasuwar.

Ba jima suka fito bayan sun yi mata gaisuwa sunyi nisa da gidan Walida tace, "Oh yanzu in kin ga an cika a rasuwa to gidan mai kud'i ne an san za'a ci a sha, in iyayen mu suka rasu ko wani namu babu wanda zaki gani amma nan da yake akwai kud'i kalli motoci da maza dan Allah."
Habiba tace, "Ai yanzu daman in kin ga gidan rasuwa ya cika to tabbas akwai wani babban mai kud'i a gidan, ki duba irin abincin dake fitowa dashi fa kamar gidan biki ga kaji ga naman rago ga kuma ruwa da lemo kamar bikin gidan gwamna. Har da gwamna fa akayi jana'iza d'azu."

Walida tace, "An ce sarkin garin nan ma dashi akayi." Habiba tace, "A'a yanzu fa daga gidan sarkin nake bai zo ba baya jin dad'in amma ya turo wakilan sa Asad da Aliyu. Kuma shi ai yana da k'okari wallahi ko ba masu kud'i ba yana zuwa jana'iza, ki tuna ta gidan su Salima da baban su ya rasu shine ma ya ja sallar gawar, yanzu ne ance baya jin dad'i shiyasa ya turo wakilan sa kuma na jiki."

Jin hakan sai gaban Rauda yayi mugun fad'uwa ta kalli Habiba tace, "Waye Asad a y'ay'an nasa waye kuma Aliyu?." Habiba ta kalle ta tace, "ke dai kina son labarin gidan sarkin nan. Aliyu shine babba shine baya ji bashi da mutunci ko kad'an bai d'auki talaka a bakin komai ba, shine ya mare ki ranar nan badan nayi masa wannan kirari ba wallahi sai yace a kai ki ki share turken dokunan da kike jin tsoro kuma wallahi sai kin yi in ba haka ba a zane ki" ta fad'a tana kallon Rauda ta cigaba da fad'in,

"Bashi da mutunci ko kad'an ya raina talaka ganin talaka yake kamar ba mutum ba, in fa ya tawo bayi ko dogarai suka tawo wallahi sai kin koma can baya duk nisan wajan ya wuce sannan zaki wuce, ga shi kowa ya shaida a gidan shaye-shaye yake da neman mata shiyasa basa shiri da mai martaba. Naji ance a da yafi son Aliyun amma rashin jin sa ya saka ya fita a ransa tunda yayi yayi Aliyu ya shiryu yak'i kullum sake wastewa yake yi, gashi baya yafiya ko kad'an. akwai wani labari da naji y'ar sarkin Zamfara tayi masa rashin kunya ya saka aka d'auko masa ita yayi mata fyad'e na wulak'anci ya azabtar da k'arshe yarinyar rasa ranta tayi, amma da yake babar sa ba kanwar lasa bace wallahi tuni an manta da maganar."

Habiba bata kula da halin da Rauda ta shiga ba tace, "Asad kuma shine Kamili mai kirki duk da baya fara'a amma kowa ya shaida a gidan nan shine ya fita zakka kamar ba jinin sarauta ba in yayi miki wani abun, bazai ga ana wulak'anta d'an adam a gaban sa ya k'yale ba, bazai ga ana cin zarafin wani a kyale ba, shiyasa ko hukunci Aliyu ya saka a yiwa wani da sun ga Asad zasu daina domin tasu tukunyar ce zatayi zafi a wajan sa. Ga taimako ko a hanya yaga tsoho zai tsallaka titi Asad yana iya parking mota ya fito ya tsallakar dashi ya bashi kud'i sannan ya koma mota yaje inda za shi, labari in yaji na gidan ku baku dashi ko kuna neman wani taimako sai ya taimaka muku wallahi, wani lokacin baza ma kusan shine yayi ba. Kuma kaf gidan nan babu mai kud'in sa hatta mai martaba bashi da kud'in da Asad yake dashI, sai dai mai martaba ya nunawa Asad kadarori amma zunzurutun kud'i Asad ne yake dashi tunda shi bada Nigeria yake aiki ba. Kullum fa sai ya bawa su Gwaggona dubu d'aya sadaka, sama da mata d'ari a gidan nan kowa sai ya samu yara da manya, in kana da buk'ata ma in Allah ya had'a ku ka nemi taimakon sa an gama shiyasa kullum yake gaba baya b'ata yin baya a rayuwar sa."

"Shi bar shi da baya magana dan ya kwana uku ma bai fito daga d'aki ba abu ne mai sauk'i a gare shi tunda ba zaman k'asar yake so ba, duk inda kike tunanin miskili mara son magana da hayaniya ya wuce nan, shiyasa y'an gidan da dama kurma suke ce masa domin ance sai su zauna meeting na cikin gidan su a tashi bai ce kanzil ba, sam baya k'aunar magana shi yafi son shiru shiyasa ko gaishe ki kayi a hanya sai dai ya d'aga hannu in yaga dama yayi murmushi. Amma fa naji ance duk tsiyar Aliyu in Asad yayi fushi bai kama k'afar tasa tsiyar ba, ance duk ya fisu zafi ta Aliyu ce ta bayyana."

Walida tace, "shi na ukun fa?." Habiba tace, "Hydar kenan gidan fara'a, shine kuma basa kama da y'an uwan in kika ganshi ma baza kice y'an ukun su bane, wad'ancan sune masu kama kwabo da kwabo kika ga Asad kika ga Aliyu baza ki banbance ba. A da adon gemu ne yake banbanta su na Asad bak'i ne sosai na Aliyu kuma ya shirka da ja, cikin kwanakin nan shima ya mayar da nasa bak'in kafin ki gane su zaki sha wahala. Hydar halin su d'aya da Asad kawai shi yana da wata cuta ce da in ta tashi sai ya shafe wata a kwance kamar yadda na fad'a muku ranar nan, yanzu haka ma ciwo ya tashi yana kwance ya jima ance ko motsi baya yi."
"Allah sarki Allah ya bashi lafiya."
"Amin. Ke Rauda lafiya kike kuwa?" Habiba ta fad'a ganin kamar ta fita a hayyacin ta.

Rauda ta firgita ta kalle su hawaye ya wanke mata fuska tace, "fyad'e kika ce ya yiwa wata dan tayi masa rashin kunya fa, kuma y'ar uwar sa mai kud'i da mulki; Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Habiba na shiga uku ni yanka ni zai saka yi, bakina ya jawo min abinda yafi k'arfin dangin mu gabad'aya." Walida da mamaki tace, "Me kike nufi?."
Sai kuma Raudan ta saita nutsuwar ta tace, "Wai da ranar da ya mare ni na tanka masa."

Habiba tayi dariya tace, "ke me zai had'a ki da wannan? Yadda ya raina talakawa wallahi Allah kad'ai yasan mai zai miki. Banza matsoraciya shine har da kuka?" Ta fad'a tana kallon ta sukayi dariya ita da Walida. Habiba ta kuma cewa, "kuma baku san wani abu ba, a kaf gidan babu mai taka masa burki kamar Asad d'in, basa shiri fa amma kamar ba y'an uku ba sam Aliyu da Asad basa jituwa amma kuma in ya tsawatar akan abu ance Aliyun yana shayin aikatawa, dan Asad akwai slicent treatment."

Walida tace, "Ke wai a ina kike jin wannan labaran?."
"Ina fa kwana a gidan, kuma kin san labarin gidan sarauta baya tab'a b'uya ko me aka aikata sai ya bayyana."

Basu lura da yanayin ta ba suka cigaba da tafiya har aka zo gida Rauda ta shiga gida suma suka wuce nasu gidan. Umma na zaune taga shigowar Rauda a gigice ta bita da kallo tace, "ke kuma lafiya?." Jikin ta har rawa yake tace, "babu komai Umma" tana fad'a ta shiga d'aki ta zauna gefen gadon Umma ta ajjiye sandinan ta a gefe kawai ta fashe da kuka.

"Na shiga uku ni Rauda na jawowa kaina bala'i" ta fad'a a hankali gudun kar Umma taji. Bugawa k'irjin ta yake cikin tsoro da fargabar abinda zai je ya dawo hankalin ta ya mai k'arshe wajan tashi k'irjin ta har d'agawa yake sabida tashin hankali.
Umma da ta d'aga labule ta shigo ta kalle ta tace, "Ki sanar dani abinda yake damun ki."

Kuka take sosai bata ce komai ba Umma na tsaye tana kallon ta ganin yadda take kuka sosai sai tayi mata shiru tana kallon, sai da ta gaji da kukan sannan ta kalli Umma tace, "Tausayin kaina nake Umma lokaci guda na nakasa." Umma ta girgiza kai tace, "Wani lokacin kamar bake ba, kina mantawa da Allah yana canjawa bawa halittar sa komai tsufan sa, indai ba mutuwa kika yi ba'a gama canja miki halitta ba. Indai baza kiyi imani da k'addara ba kuka yanzu kika fara" ta fad'a tana komawa da baya ta barta.

Kwanciya Rauda tayi cikin tashin hankalin da ya hana zuciyar ta sukuni, hangowa take ya saka an kamo ta itama anyi mata fyad'e kuma an kashe ta lokaci d'aya sai taji hankali ta ya kuma tashi. Tana kuka bacci ya d'auke ta bata sani ba.

*☆☆☆*

Tunda ya shiga falon Mama ya zauna bai ce kala ba ganin hakan sai Mama ma ta share shi ta cigaba da danna wayar ta dan duk a tunanin ta Asad ne ba Aliyu ba, shigowar Asad ya saka ta kalle shi taga fuskar sa tayi kama da ta Asad ta dawo da kallon ta ga Aliyu taga sak iri d'aya dai ta Asad d'in ce a d'aure ko wanne da alamun b'acin rai a tare dashi.
Sanda Asad ya zauna lokacin ta kalle su ta ajjiye wayar a gefe tace, "Ikon Allah." Nan ma babu wanda ya tanka mata a cikin su sai suka sake rud'a ta.

"Lafiyar ku kuka shigo min ko wanne fuska a d'aure? taz'aziyar da mahaifin ku ya tura ku kenan?."
Nan ma shiru babu amsa ko wanne na kallon wani wajan daban sai suka fusata ta tace, "Malamai bakwa ji ina muku magana ne? Wanne irin iskanci ne wannan ina magana kunyi banza dani kamar sa'ar ku?. Ku banbance min kan ku tunda kun d'auko sabon iyayin saka kaya iri guda, banbancin ma da yake fuskar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login