Showing 57001 words to 60000 words out of 91952 words

Chapter 20 - KWANTAN ƁAUNA HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

4812

Aliyu ya shafe shi."

Tab'e bakin da Aliyu yayi ya skaa ta kalle shi tace, "Kaine Asad kenan" sai ta kalli Asad taga bama ita yake kallo ba nan ta sake rud'ewa dan gabad'aya ko wanen su acting d'in Asad yake yi. Ganin ranta ya fara b'aci ya saka Asad yace, "Allahbya wuci zuciyar Mama, ya jikin Hydar?." Yana fad'ar hakan sai ta gano waye dan Asad yafi damuwa da jikin Hydar akan Aliyu daman kuma tun farko tasu tafi zuwa d'aya, ta kalli Aliyu tace, "baku tab'a rud'a ni kamar yau ba, kamar ku ta fito a zahiri sosai har ta bani tsoro tabbas Aliyu ka koma min Asad a yau."

Aliyu yace, "ina neman izinin magana." Mama tayi masa alama da hannu yace, "Mama wata yarinya ce ta kira ni da mahaukaci a wajan ta'aziya amma Asad ya hana ayi mata hukunci. Ina rok'on Mamana da ta shiga tsakani na da Asad tun kafin raina ya b'aci hukuncina ya shafe shi, babu ruwan sa da duk abinda zan saka ayiwa wani a k'asana yake tunda talakan garin nan ne." Mama ta bud'e baki tace, "What? Mahaukaci! kaine mahaukacin?." Basu amsa mata ba tace, "y'ar gidan uban waye?."
"Ba y'ar gidan kowa bace ba Mama, beside y'ar talakawa ce gurguwa mai yawo da sanda, sau uku kenan tana k'okarin raina min hankali amma na yau yafi na ko yaushe har ta kira ni da mahaukaci amma wannan ya hana a sake b'alla mata k'afafun ta" duk da fad'a yake amma bai fito fili ba sabida a gaban Mama yake dole ya tausasa harshe.

A fusace Mama ta kalli Asad tace, "For what reason?. Mecece d'in ka da zaka hana a hukunta ta?." Shiru Asad yayi bai amsa ba ta kuma fusata tace, "meyasa kai baka san Allah ya banbanta ku da talakawa bane ba?, meyasa ka kasa gane kai da talaka sai dai taimako in kaga dama?, meyasa baka gane tazarar ku kamar tazarar sama da k'asa ce?. Ni y'ar sarki ce babana sarki ne, kakana ma sarki ne, miji na sarki. Baban ku sarki ne kakan ku sarki ne haka zalika a cikin ku akwai sarki. Ko a jinin sarautar naku daban yake, ko a y'ay'an sarautar ku daban kuke, ko a izza da k'asaitar taku daban take, meyasa kake mantawa da wannan Asad?!."

"Allah ya wuci zuciyar ki, amma dukkan mu bayin Allah ne babu wanda yafi wani ko a wajan Allah. Tunda har ita yarinyar tace masa haka maybe akwai abinds ya fad'a mata ta rama."

"K'arya kake Asad ko a wajan Allah akwai banbanci tsakanin talaka da mai kud'i nasan kasan da wannan. Kuma ko zane ta yayi ai matsayin da yake dashi a garin nan godiya ya kamata tayi masa ko babu komai ta samu k'imar da har ya tsaya ya dake ta." Yadda take magana da fad'a ya hana shi sake cewa komai yayi mata shiru.

"Aliyu ko y'ar gidan uban wacece ina so ka saka ayi mata hukunci, ina so ka saka a nuna mata ruwa ba sa'an kwanbo bane sabida gaba, in ka k'yale ta wasu ma zasu gwada tunda sunga wata tayi tasha. Ka tauna tsakuwa ko dan aya taji tsoro" ta fad'a tana kallon sa. Cikin gamsuwa ya girgiza kai domin bayanin da tayi ya saka ya sake jin izza na mamaye masa jikin sa yace, "tabbas zata gane nida ita kamar wuta da ruwa ne baza mu tab'a zama waje d'aya ba, Mama zata san ni ba d'an sarkin Bauchi bane ni d'an sarkin katagum ne."
"Good boy!" Ta fad'a tana masa jinjina.

Asad yace, "Mama yarinyar nan fa ta silar....." Sai kuma ya fasa fad'a yayi shiru da bakin sa yana kallon gefe guda. Tsaki taja tace, "baka gado ni ba sam Asad, bakayi kama da jinin sarauta ba. Har wata yarinya zata kira d'an uwan ka mahaukaci a gaban ka ka hana ayi mata hukunci, ita d'in banza da wofi, ko baban tane ba sai a hukunta shi ba balle ita." Aliyu ya tashi ya fita zuciyar sa cike da tunanin hukuncin da ya dace da Rauda.

Shima Asad d'in tashi yayi ya fita dan ya lashi takobin babu wanda ya isa yayi mata wani abun indai yana raye domin kuwa ta dalilin Hydar ta nakasa, ko babu wannan dalilin a yadda ya samu labarin ta tana da hankali baza ta saurari Aliyu ba sai dai in shine ya fara zagin ta shine ta rama bai ga dalilin da zai saka a dake ta a kuma hana ta kuka ba.

*☆☆☆*

Yadda suka nutsu suka bada dukkan hankalin su ga wayar hannun waziri zai tabbatar maka da abu nai mahimmaci ake sanar dasu a cikin wayar, motsin kirki basa yi hankalin su gabad'aya yana kan wayar sunyi shiru suna sauraron abinda ake fad'a daga cikin wayar.
"Kamar yadda na fad'a muku mai martaba ya dawo da batun bawa Asad sarauta jiya sun tattauna dashi akan maganar, wanne tunani kuka yi game da hakan?."

Suka kalli juna a tare kafin waziri yace, "bamu san hakan ta kasance ba dukkan mu mun saki jiki akan maganar ta jinkirta ne."
"To bata jinkirta ba ku fad'a min shirin ku naji."
Hajiya tace, "bamu da wani shiri sai abinda kika shirya mana."

Master planer tayi murmushi tace, "Ina da shawara sai dai shawarar tawa tana da wahalar faruwa amma zata faru in kuka jajirce." Waziri yace, "muna sauraron ki."

"Ku jawo Aliyu ya dawo cikin ku." A tare suka wara idanu Hajiya tace, "Wanne Aliyun kike nufi?."
"Aliyu nawa ne daku a gidan?."
Waziri yace, "to maganar ce na jita wani iri master kamar da kamar wuya, Aliyu fa jinin Asad ne ta yaya zai had'a kai damu."

Y'ar dariya tayi tace, "Aliyu ya fi ku son ganin babu Asad a cikin gidan nan, domin Asad shine kawai wanda yake ganin zai hana shi mulkar garin nan. In kuka samu ya dawo cikin ku ya fiku yarinta yana da matuk'ar wayo idanun sa kuma a bud'e yake tafiya zata yu yadda ake so."
Hajiya tace, "Amma in muka nemi Aliyu kamar tonuwar asirin mu ne, zai iya bijire mana yak'i amincewa bayan ya riga yaji sirrin mu."

Waziri yace, "abinda na gani kenan, inda dama a bar maganar Aliyun nan."
Master planer tace, "shigowar Aliyu shine nasarar mu."
"Ta yaya zai zama nasarar mu bayan in ya shigo cikin mu mun kashe maciji ne basu sare masa kai ba?. Kar ki manta in ya shigo cikin mu kenan mun zubar da makanan yak'in mu na neman sarauta mun barwa jinin Rabi'atu."

"Hhhh! wani lokacin bakwa saurin fahimtar inda na dosa. wato shi kan sa Aliyun amfani zamuyi dashi in mun gama burin mu ya cika mu ajjiye shi a gefe. Abinda nake nufi a nan zamu saka a b'atar da Asad amma za'a bayyanawa mutane cewa Aliyu aka batar ba Asad ba. Aliyu zai koma acting d'in Asad gabad'aya kamar yadda yake yi yanzu, zai dakatar da duk wani abu da yake yi ya dawo Asad a cikin gidan nan. Ko mahaifiyar sa bazata san bada Asad take zaune ba zai koma Asad sak babu wanda zai ce Aliyu ne. Da zarar hakan ta kasance kunga mai martaba zai bawa Aliyu mulki ba tare da yasan shi bane, mu kuma indai aka bawa Aliyun mulkin nan kwace goriba a hannun kuturu abu ne mai sauk'i a wajan mu. Wannan shine amfanin da Aliyu zai mana shiyasa nace ku jawo shi cikin ku."

Waziri ya numfasa yace, "ta yaya Aliyu zai shigo cikin mu? Shine babban tashin hankali shigowar sa cikin mu, sannan in ya shigo an gama komai an bashi mulki ta yaya Aliyu zai amince ya bar mulkin cikin sauk'i bayan kema kin shaida wayon sa?."
"Waziri kana da dawo da bara bana, nice nace zanyi ku gwada abinda nace muku ku gani in ban yi nawa ba."

Hajiya tace, "Abun ne kamar da wahala master, Aliyu fa." Ta ja k'aramin tsaki tace, "nice nace kuyi in kuka tabbatar ya shigo tsagin mu an b'atar da Asad komai zai zo mana da sauk'i, in kuna ganin baza ku iya ba a nemo wata mafitar." Waziri yace, "A'a basai an kai ga haka ba zan san yadda zanyi."
"Better" abinda tace kenan ta yanke wayar.

Hajiya ta kalle shi tace, "da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, tabbas shawarar tayi amma in ka duba ta yaya zamu shigo da Aliyu cikin mu sai kaga gabad'aya maganar bata da ma'ana." Kai yake girgizawa yana nemo mafita a kwakwalwar sa kafin yace, "tunani ya kamata muyi game da lamarin, a ganin ki mu gwada neman Aliyu ko mu bar zancen?."

Hab'a ta rik'e cikin tunani kafin ta kalle shi tace, "a rashin tayi ake barin arwa, haka zakila a yawan tayin ake shan duka. Wanne daga ciki zamu d'auka?."
"Mu taya!" Waziri ya bata amsa yana kallon.
"Allah ya bamu sa'a" ta furta tana kallon sa shima yana kallon ta.


_ya kuke gani anya Aliyu zai karb'i tayin su?. Ina batun Rauda wanne hukunci zai mata?._🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️🤸‍♀️

*KWANTAN ƁAUNA*

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*017.*

           Rauda ta jima tana bacci sanin ba sallah zatayi ba ya saka Umma bata tashe ta ba sai bayan azahar ta farka ta firgice, ganin ta a d'akin Umma ya saka ta raba idanu tana sauke ajiyar zuciya ganin mafarkin da tayi ba gaske bane ba. Mafarki tayi sun had'u da Aliyu ya kai ta wani waje tana ta bashi hak'uri yak'i ya hak'ura bai kai ga yi mata komai ba ta farka shiyasa hankalin ta gabad'aya yake a tashe.
Duk ta jike da gumi tana shafe fuskar ta Khairi ta shigo d'akin tana fad'in, "Umma ta tashi."

Kallon Khairi tayi kafin tace, "k'arfe nawa?." Khairi tace, "K'arfe biyu." K'aramin tsaki ta ja Umma ta lek'o d'akin tace, "To Rauda zan fita su Khairi zasu je makaranta ki kula da gidan."
"Ina zaki je Umma?."
"Zan koma yiwa matar nan gaisuwa, daga nan kuma zanje gidan Baba Malam mu gaisa."
"A dawo lafiya." Sakin labulen Umma tayi ta fita daga gida.

Rauda ta kalli Khairi da take shiryawa tace, "Khairi in zaki tafi makaranta ki biya gidan su Habiba kice dan Allah nace tazo ina neman ta Umma bata nan." Khairi ta amsa da to ta gama shiryawa ta fita. Gidan shiru hakan ya bata tabbacin d'akin su Rahma ma basa nan kenan ta fito daga d'akin ta zauna a kan kujerar ta a tsakar gida inda babu rana.

Yunwa take ji sosai amma baza ta iya cin abinci ba sai tayi maganin matsalar da ta d'aukowa kanta sannan zata samu abinci ya iya zama a cikinta, tana nan zaune taji sallamar Habiba ita da Walida sun shigo a tare. Amsawa tayi suka k'araso suka zauna a kan tabarma Habiba tace, "Naga fuskar ki a kumbure."
"Bacci nayi" ta bata amsa tana yatsine fuska.

Habiba tace, "y'ar hutu. Lafiya kike nema na?." Rauda tace, "Yan uwa ina cikin matsala ne." A tare suka had'a baki wajan fad'in, "Wacce irin matsala kuma?."
Shiru Rauda tayi tana kallon su kafin ta kwashe duk abinda ya faru tayi ta fad'a musu kafin ta d'ora da fad'in, "tunda kika ce min har fyad'e ya yiwa y'ar sarkin Zamfara na tsorata ku taimaka min dan Allah."

Girgiza kai suke yi cikin mamaki da tsoro Habiba tace, "Mahaukaci kika ce masa Rauda? Tabd'ijam na rantse da Allah bai k'yale ki ba kina nan a zuciyar sa sai ya d'auki mataki a kan ki, ya yiwa yar masu kud'i da mulki balle irin mu?." Sai ta fashe da kuka tana fad'in, "Dan girman Allah ku taimaka min ku nema min mafita wallahi tsoron sa nake ji, ni ko zuwa ne zanyi na bashi hak'uri indai zai yafe min."

Habiba tayi shiru tana tunanin m a fita kafintace, "mafita d'aya ce kawai abinda za'ayi zuwa zamuyi mu samu Asad ki fad'a masa duk abinda ya faru tunda a gaban sa akayi, ki sanar dashi tsoro kike ji kuma kinyi dana sanin yi masa rashin kunya dan Allah ya bashi hak'uri kar yayi maki komai, in anyi sa'a zai iya k'yalewa in Asad d'in ya saka baki."

Walida tace, "To kince sai ya kwana uku bai fito ba a ina zamu gan shi?." Habiba tace, "yana sadaka ai da kansa ranar juma'a bayan masallaci indai yana k'asar nan, ranar zamu je masa in ba ranar ba wallahi bamu da ikon ganin sa."
"Juma'a yayi nisa Habiba, kafin juma'ar zai iya sakawa ayi min wani abun, dan Allah a canja shawara. Ni tsoron abinda zai min nake yi bawai tsoron sa ba, ga Ummana bana so ta shiga wani yanayi mara dad'i a kaina shiyasa hankalina ya tashi sosai" Rauda ta fad'a cikin tashin hankali tana hawaye tana kallon su.

Cikin kwantar da murya Habiba tace, "Na rantse da Allah Rauda da ina da damar ganin Asad a yau zamu je wajan sa amma ban isa ba, Fulani ta saka an k'arawa b'angaren su tsaro sabida abinda ya faru dashi kwanaki kusa da wajan ma baki isa kaje ba sai da dalili. ki bari sai ranar jama'ar in Allah ya nuna mana sai muje ki same shi na tabbatar bazai bari a cutar dake ba, Kafin ranar ki ta addu'a Allah zai kawo miki sauk'i."

"Habiba in ya yi min wani abun na shiga uku dan Allah ku taimake ni. Ba kaina nake ji ba Ummana nake ji, abinda Baba zai yiwa Umma shi nake jin tsoro" ta fad'a cikin kuka sosai. Tausayi ta basu suka dinga rarrashin ta Habiba tace, "Allah yana tare dake wallahi bai isa ya cutar dake ba. Amma zan je yanzu in naga yana nan zan roƙe shi zance masa zan kawo ki ki masa bayanin komai in yaso sai naje na dawo muje wajan sa dake."

Rauda tace, "tashi kije Habiba." Habiba ta mik'e tsaye tace, "Walida zo muje, duk yadda ake ciki zan dawo" ta fad'a tana fita daga gidan suka barta tana sharb'ar kuka.

Haka ta zauna zaman jiran su har la'asar basu dawo ba Umma ma bata dawo ba sai biyar sannan Khairi ta shigo ita da Khalil da Sammani, bayan shigowar su ba jima Habiba ta shigo tunda taga fuskar ta tana ba'a yi nasara ba. Kusa da ita ta zauna ta kalle ta tace, "Wallahi duk yadda naso ganin Asad abin ya gagara, amma kiyi hak'uri gobe zan same shi in Allah ya yarda." Idanun Rauda yayi rau-rau zatayi kuka Habiba tace, "kiyi hak'uri dan Allah, haba komai zai tafi daidai in Allah ya amince ki yadda dani wallahi zan masa magana. Kamar ba ke ba kinbi kin rud'e keda na sanki da dakakkiyar zuciya wacce babu tsoro a cikin ta."

Kai ta girgiza tace, "Habiba wannan fad'an yafi k'arfina, bawai ina jin tsoron saba bane ina jin tsoron abinda zaiyi min ne Habiba."
"In sha Allah babu abinda zai miki."
"Na gode Habiba." Habiba ta mik'e tace, "Kar ki damu zan neme shi gobe in Allah ya amince."
"Na gode" ta furta a hankali daga haka sukayi sallama ta tafi.

Fitar ta ba jimawa Umma ta dawo su ma su Rahma suka dawo, bayan anyi sallar magriba Baba ya dawo bayan yaci abinci ya shigo tsakar gidan ya zauna ya kalli Rauda yace, "Rauda." Tace, "Na'am Baba."
"D'azu Anas ya kira ni ya sanar dani tafiya ta taso masa ta gaggawa bai samu yayi magana da likitan naki ba, amma ba jimawa zaiyi ba da zarar ya dawo za'ayi komai a gama. Ya aiko da waya yace dan Allah a baki yana so ku dinga magana na kuma karb'a, gata" ya fad'a yana mik'a mata ledar Khairi da take kusa dashi ta karb'a ta mik'a mata.

Umma ta kalli Baba ta kasa jure abinda take ranta tace, "Malam wai ka bawa yaron nan auren Rauda ne?." Ya kama k'ugu yace, "Me yasa kika tambaya?."
"Sabida naga kana karb'ar hannun sa da yawa, tsakani da Allah bai kamata ba a dinga karb'ar kud'in yaron nan ko abin hannun sa ba tunda ba'a yi auren su ba, ko maganar aure fa bata shiga tsakanin su ba."

Baba yace, "to fad'a min ke kika haife ta, dad'in ta nima dani aka haife ta ba ke kad'ai kika kawo ta duniya ba. Na riga na bashi auren ta koda bana raye shi zata aura ba wani ba, ko ban isa bane ba?" Ya fad'a yana kallon Umma. Umma bata kuma cewa komai ba ta kawar da kai yaja tsaki ya fita.

Rauda tunda aka bata wayar ta rik'e a hannun ta ko bud'ewa ta kasa yi sabida ba wannan ne a zuciyar ta ba abinda yake zuciyar ta daban wannan daban, sai da suka shiga d'aki zasu kwanta sannan Khairi ta bud'e wayar a kwalin ta ta ciro ta kunna har da sim card a kai, Khairi ta kalle ta taga ba ita take kallo ba tace, "Anty Rauda keda kike da burin rik'e waya yau Allah ya cika miki burin ki amma ban ga kina farin ciki ba."

Umma tace, "ta yaya zatayi farin ciki ana zubar mata k'ima wajan saurayi ana karb'ar komai daga hannun sa?, ai farin ciki ba nata ba." Rauda ta kalli wayar hannun Khairi ta ganta mai kyau babba ga bayan ta nan da logo d'in Samsung. D'auke kai tayi ta kwanta kawai bata ce komai ba domin ita ba wannan ne yake damun ta ba.

*☆☆☆*

Asad kuwa da ya bar gida gidan su Jidda ya tafi ya riga ya cewa Mama zashi baya son sab'a alqawari a rayuwar sa musmman ma maganar Mama. Kasancewar gidan sa ba bak'on sa bane Mama tana aiko shi wani lokacin har cikin gidan ya ajjiye motar.
Fita yayi daga motar ya shiga cikin gidan da sallama ya samu falon babu koma sai k'anwar Jidda mai suna Eman.

Ganin sa ta saka tayi murmushi tace, "Yaya Aliyu ina wuni."
"Lafiya, Ina Mum?."
"Tana sama bara na fad'a mata" ta fad'a tana hawa sama. Bai zauna ba ya tsaya a tsaye kafin ta lek'o tace, "Tace ka hayo." Ba musu ya k'arasa stairs d'in ya hau saman a nutse ba tare da wata fargaba ba. A babban falo ya tarar dasu ita da Jidda a zaune ganin sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login