Showing 60001 words to 63000 words out of 91952 words

Chapter 21 - KWANTAN ƁAUNA HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

4800

ya saka Jidda mik'ewa ta k'araso gare shi da niyar hugging d'in sa.

Baya yayi yana kallon ta ta k'asan ido, sanye take da riga da wando yan kanti kanta babu d'ankwali gashin ta ya sauka har kafad'a tayi kyau kamar baturiya, ganin kallon da yayi mata sai gaban ta ya fad'i ta kauce ya k'arasa ya zauna kana yace, "Mum ina wuni."
"Lafiya lau Aliyu, Ya Maman?."
"Lafiya lau" ya furta a tak'aice bai kuma cewa komai ba.

Jin shiru ya saka Mum ta kalle shi dan tasan Aliyu baya wannan dabi'ar in yazo gidan da tuni ya rungume Jidda sun koma gefe suna hirar su tace, "Aliyu kayi shiru yau kamar ba kai ba."
"Asad!" Ya furta a tak'aice bai kalli Mum d'in ba. Jin abinda yace ya saka Mum da Jidda suka kalli Juna Mum ta d'aga mata gira suna murmushi Mum tace, "Au daman Asad ne ka barni ina ta kiran ka da Aliyu?." Baice komai ba itama bata damu yace ba dan tasan bazai ce ba ta kalli jidda tace, "Jeki ki kawo masa abin tab'awa mana kin tsaya kina kallon sa." Da sauri ta juya ta sauka Mum tayi murmushi tana kallon sa tace, "nidai nayi mamaki nasan Aliyu baya irin wannan bakuntar a gidan nan."

In table d'in dake gaban sa ya amsa to tabbas shima ya bata amsa sai ma kawar da kansa gefe da yayi yana jin sa a takure, bata damu ba dan tasna halin sa daman a lokacin Rauda ta dawo da tray a hannun ta ta ajjiye masa ta zauna a gefen sa Mum ta mik'e ta basu waje. Suna zaune shiru babu mai magana zuciyar sa ta tafi tunanin kenan daman ta saba hugging d'in Aliyu duk wanda yazo tunda gashi da ta ganshi ta d'auka shine har ta nufo shi da niyar hugging d'in sa. Cize baki yayi Allah ya sani baya son yaga wani ya rabi abinda aka ce nasa ne indai har da gaske nasa d'in ne baya so yaga wani abun ya rabe shi, baya son hakan sam.

"My Asad" ta furta a hankali tana kallon sa. Bai kalle ta ba ya sauke ajiyar zuciya yace, "Zaki iya d'aukar wayar ki?" Ya fad'a da harshen laranci. Kallon sa tayi alamun bata gane ba tace, "Bana jin Arabic." Yamutsa fuska yayi yace, "Take your phone."
"Okay." ta furta tana d'aukar wayar ta. Sai kuma ya tsaya kallon wayar tasa tunawa da yayi bashi ma fa da number ta balle suyi chart ya fad'a mata abinda ya kawo shi.
D'an k'aramin tsaki yaja ya ajjiye wayar kamar zai magana sai kuma ya fasa.

Sun d'an jima a haka kafin ya mik'e ta mik'e itama tana kallon sa yace, "my regard to Mum" yana furtawa ya sauka daga saman gabad'aya bai kuma kallon ta ba balle ta saka ran magana ko wani abun. K'ugu ta kama tana kallon sa tana fad'in, "Lallai ma wannan gayen ya raina min wayo da hankali, shikenan har anzo zancen an tafi?, wacce irin izza da k'asaita yake ji da ita har haka?."

Mum da taga saukar sa take jin abinda take cewa tace, "D'an sarki ne fa, jikin sarki ne, shine yake niyar zama sarki. Wacce izza kike so ki gani a tare dashi in ba wannan ba?." Ta kalli Mum tace, "Amma Mum tunda fa ya zauna bai ce min komai ba haka za'a yi auren?." Dariya Mum tayi tace, "Sai aka ce miki haka zamu bar shi?, zamu sark'afo wuyan sa ta yadda ko uwar sa Rabi'atu sai dai ta sallama miki shi. Duk wannan kurmancin nasan zai shigo hannu ne sai ya zamar miki kamar rakumi da akala wallahi, barni dashi tunda har ya fara zuwa gidan nan da niyar zuwa wajan ki ai zance ya k'are duk da dai nasan itace ta turo shi."

Jidda tace, "Amma Mum ya raina min wayo wallahi." Mum ta dafa ta tace, "k'yale ni dashi Jidda barshi ya shigo hannu tukunna, da zarar ya shigo hannu to wannan kuma lokacin mu ne." Jidda ta tab'e baki ta shiga d'akin ta duk ranta a jagule.

Shi kam Asad ya kasa fassara yanayin da yake jin zuciyar sa haka ya tuk'a motar zuwa gida ransa duk ya b'aci sam baya son auren Jidda amma babu yadda zai iya Mama tace dole sai ya aure ta. Babban abinda yafi b'ata masa rai game da ita ya lura tana da kusanci da maza sosai wayewar ta tayi mata yawa shi kuma Allah ya sani irin matan nan basa cikin tsarin sa ko kusa.
Ko wajan Mama bai shiga ba ya shiga d'akin sa ya zauna ya kunna TV yana kallo.

K'aramin tsaki yaja ya kashe TV ya hard'e hannayen sa waje guda, yana son barin Nigeria ko umra ce yaje ya dawo amma zuciyar sa tak'i k'arfafa masa guiwa a kan hakan, ya rasa abinda yake damun zuciyar sa bata tuna masa komai sai yarinyar mafarkin sa da kuma yarinyar da Hydar ya buge. Tsaki ya kuma yi ya jingina da kujera zuciyar sa nayi masa zillo akan abinda bai kai ya kawo ba yake jin d'aci da suka a cikin ta. Mik'ewa tsaye yayi ya kashe hasken d'akin gabad'aya sannan ya shiga band'aki.

Washe gari.

Tunda Rauda ta tashi take jin bata san zaman gidan gabad'aya sabida gani take kamar za'a zo a d'auke ta a kaiwa Aliyu ita, ko kuma a yiwa yan gidan su wani abun. zaman gidan yak'i mata dad'i komai nata sanyaye take yin sa har magana bata iyawa sosai. Umma na lura da ita bata tanka mata ba itama kuma bata ce ga abinda yake damun ta ba.

K'arar waya taji a kusa da ita abin ka da ba'a saba ba sai ta manta an bata waya sai da ta katse aka kuma kira sannan ta kalli gefen ta taga ANAS a rubuce a kan screen d'in wayar. Numfashi ta sauke ta jawo wayar tana kallo tana tunanin ta yadda zata d'auka dan bata iya ba, garin ta d'auka ta katse kiran aka kuma kira bata san ya akayi ba taga seconds sun fara tafiya alamun ta d'auka.

A kunne ta saka wayar bata ce komai ba daga can b'angaren yace, "Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya kyakykyawar matata." Murmushi tayi kad'an wanda iyakacin sa kan fuskar ta tace, "Amin, kaima amincin Allah ya tabbata a gare ka." Y'ar dariya yayi yace, "Ni mijin ki?."
"Uhum" ta furta kawai bata ce komai ba. Jin hakan sai yace, "da fatan kin tashi lafiya."
"Lafiya lau, ya aiki?."
"Alhamdulillah, ya jikin ki?."
"Da sauk'i" ta bashi amsa a tak'aice.

"Allah ya k'ara sauk'i." Ta amsa da amin kafin yace, "Ina Umma, ina fatan lafiya take?."
"Lafiya lau kowa yake."
"To ma sha Allah, haka nake so naji."
Shiru ne ya biyo baya kafin yace, "Kiyi hak'uri Rauda wallahi aiki ne ya taso min da gaggawa wanda dole ya saka ni tafiya Abia ban shirya ba, amma in sha Allah nan kusa zan dawo zan nemi wani likitan ayi aikin nan a gama dan wanda na sani ya sanar dani baya k'asar nan."

"Babu komai, Allah ya taiamaka, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya biya buk'ata." ta bashi amsa a tare.
"Amin. Amma k'afar bata miki ciwo ko?."
"Bata yi" ta fad'a a hankali.
"Naji dad'in hakan."
Shiru ya sake ratsa tsakanin su kafin yace, "bara na barki ki huta anjima zan kira ki." Da to kawai ta amsa dan daman ta gaji ba wannan ne a gaban ta.

Umma ta shigo d'akin ta kalle ta tace, "Da Anas d'in kuke waya?." Kai ta d'aga alamun eh kafin tace, "Umma ni gidan Yaya Ummi zanje yau zaman gidan bana jin dad'in sa, ko naje gidan Yaya Shamsiyya."
"Sai kin dawo ai" Umma tana fad'a ta fita ta k'yale ta.

Sai azhar ta fito daga gidan ta nufi titi da nufin shiga mota ta tafi gidan Yaya Shamsiyya. maza ne guda biyu a bayan ta suna ganin ta d'aya daga ciki ya d'auko waya daga aljihun sa ya danna kira ya kara a kunne, ana d'auka yace, "Allah ya ja zamanin yarima mai jiran gado, yanzu muka ganta ta fito daga gidan su." Shiru yayi alamun ana bashi amsa kafin yace, "To ranka ya dad'e, a huta lafiya" yana fad'a ya yanke kiran suka cigaba da bin ta.

Rauda kuwa bata san ana binta ba tafiyar take har taje titi ta hau mota zuwa gidan Yaya Shamsiyya. Da nisa gidan sun jima suna tafiya kafin su zo unguwar babu jama'a sabuwa ce ba'a cika ba sosai. Tana sauka ta biya mai keken kud'i ta shiga layin gidan.

Da sallama ta shiga gidan Yaya Shamsiyya na aikin ta amsa tare da juyowa ganin Rauda ce ya saka ta sauri tashi ta k'araso ta rik'o ta tana fad'in, "Rauda me ya fito dake da rana ke ba lafiya ba?." Sai da suka k'arasa ta zauna akan benci ta kalli Yaya Shamsiyya tace, "Ina wuni."
"Lafiya lau, ya jikin naki?."
"Da sauk'i Yaya, ina su Amir?."
"Sun je gidan kakar su anjima zasu dawo, me ya fito dake ana rana haka Rauda?."
"Na gaji da zaman gidan ne kawai Yaya."

"Da gajiya kam gaskiya, sannu Allah ya k'ara lafiya." Ta amsa da amin suka fara hira har akayi la'asar tayi musu wainar fulawa suka ci Rauda bata fito ba sai biyar da wani abun. Har bakin titi Yaya Shamsiyya ta raka ta sai da taga ta shiga mota sannan ta juya ta koma gida.
Napep d'in da Rauda ta shiga suna cikin tafiya suka ga an sha gaban su da mota k'atuwa bak'a mai tsaho, gaban Rauda ya fad'i ganin manyan zagage sun fito daga motar sun k'araso inda suke tsaye.

"Kee fito!" D'aya daga cikin su ya fad'a yana kallon ta. Cikin k'arfin hali irin nata tace, "Akan wanne dalilin zan fito?." Mai napep din yace, "malamai lafiya muna tafiya zaku tsaya a gaban mu?."
Bulala d'aya daga cikin su ya d'auko yace, "kana kuma magana sai ta sha jinin jikin ka. Zaki fito sai mun d'auko ki?."

Ganin mai napep d'in ya tsorata yayi shiru dan ganin bulalar ma abin tsoro ce ya saka ta dogaro sandar ta k'asa ta sauko dan har lokacin bata daina jin zafin bulalar jiya ba. Sai da ta fito da sandar ta d'aya ya kalli d'aya. yace, "Zata b'ata mana lokaci fa" yana fad'a masa haka kawai ya sunkuya ya d'auki Rauda cak ya k'arasa motar ya saka ta shi kuma dayan ya kwashi sandinan ta ya k'arasa da sauri ya shiga motar suka ja a guje. Mai napep a kan idanun sa akayi komai ya koma da baya dan yaje ya sanar da wacce ta rako ta amma bai san gidan ba tunda a kan titin kawai ya gansu dole ya hak'ura ya kama gaban sa amma zuciyar sa babu dad'i ko kad'an.

Gudu suke sosai da Rauda a mota sai ihu take tana kuka amma babu mai jinta tunda gilasan a kulle suke gasu bak'ak'e na waje baya ganin ka sai dai kai ka ganshi. sun yi nisa sosai sannan suka tsaya a kan titin da babu kowa sai motoci suma sai ayi mintina goma wata bata wuce ba. Tsayawar su babu wahala suka fito daga motar aka bud'e ta suka jawo ta suka fito da ita ta fad'i a k'asa. Kallon wajan take babu kowa kamar ma daji ne domin shiru ga duhun magriba hakan ya saka hankalin ta ya sake tashi ta sake rud'ewa lokaci d'aya.

"Dan Allah kuyi hak'uri ban san laifin da nayi muku ba amma ku yafe ni dan Allah ku barni na tafi" ta fad'a cikin kuka sosai jikin ta har rawa yake sabida tsoro. Waya taji kusa da kunnen ta ana fad'in, "ke jinin talakawa, ni kika kalla kika kira da mahaukaci ko? Zan nuna miki dabi'un hauka yanzun nan, ko nan gaba aka sake cewa ki fad'awa wani irin abinda kika ce dani bazan ki kuma. Kuna jina?." Da sauri suka amsa da, "muna ji ran ka ya dad'e."
"Ku yi duk abinda kuke so da ita in kun gama ki sakar mata Bobby ku k'yale ta a wajan, in kuka yi akasin hakan taku tukunyar ce zatayi zafi" yana fad'a ya yanke wayar suka kalli juna kafin su dawo da kallon su ga Rauda da take kuka tunda taji komai.

D'aya ya kalli d'aya sannan yace, "Sako Bobby ya fara yaga naman ta kafin muyi namu." Ba musu suka k'arasa kusa da bak'ar motar su suka bud'e, Katon bak'in k'are ya fito daga boot d'in motar yana zaro harshe jikin sa har rawa yake sabida k'oshi da zallar mugunta a tare dashi. "Bobby ga nama can" d'aya daga cikin su ya fad'a yana nuna masa Rauda da yatsa yana dariya amma a zuciyar aa tausayin ta yake ji.

Karen sai da yayi wata girgiza gashin jikin sa ya mik'e sannan ya fara nufo ta a hankali yana sake zaro harshen sa, idanun sa ma da jikin sa abin tsoro ne shiyasa tunda ya tunkaro ta ta runtse idanun ta tana salati dan ta tabbatar k'arshen tane yazo babu abinda zai hana Karen bai kashe ta ba. Razananniyar k'arar da tayi shine ya saka su kallon inda take da gaggawa.
*KWANTAN ƁAUNA*

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*018.*

         Cizo ya kawo mata karen shine ya saka ta yin k'ara ta kulle idanun ta tana jiran taji sukar hakoran sa a a naman ta amma sai taji shiru, ta bud'e idanun ta a hankali taga karen baya gaban ta kamar d'azu ta juya gefen ta ta ganshi a tsaye ya juyo yana kallon ta kusa da wanda bata tantance waye ba. A hankali yake takowa yazo kusa da ita suka had'a ido sai jikin ta ya cigaba da tsuma ya had'e hannayen ta waje guda tana kuka amma ta kasa magana.

      D'auke kai yayi daga kanta ya kalli wad'anda suka sato ta sai suka zube a k'asa cikin girmamawa hannun su na jinjina d'aya yace, "Tuba muke ranka ya dad'e, zamu aikata abinda ka umarce mu yanzu, ka yafe mana zamu yi."
"Aliyu ya saka ku kawo ta nan?" Ya fad'a a tausashe cikin muryar sa mara hayaniya wacce bata fita sosai yana kallon su.

       Sai a sannan suka gane bafa Aliyu ne a gaban su ba babar giwa ce da kanta sai jikin su ya k'ara kaimi wajan tsuma d'aya yace, "Kayi mana aikin gafara ranka ya dad'e. Yarima Aliyu ne ya umarce mu da mu kawo ta nan mu sakar mata Bobby ya cize ta sannan muyi abinda muke so da ita. Mun tuba wallahi baza mu sake aikata hakan ba." Kai Asad yake girgizawa kaf yasan plan d'in nasu sune da Aliyun basu san ya sani bane amma tunda yasa a fara tracking d'inta yasan da haka.

Kallon da yayi musu ya saka jiki su rawa suka fara fad'in, "Kiyi hak'uri yarinya muma ba san ran mu bane ba wallahi saka mu akayi babu yadda zamu yi, kiyi hak'uri ki yafe mu." Kanzil Rauda bata ce ba sai kuka da take mai tsuma zuciya ya sake kallon su duk sai suka sake diriricewa dan basu fahimcin kallon na meye ba.

D'aya ne ya mik'e da sauri ya kawo mata sandinan ta guda biyu yace, "kiyi hak'uri." Da hannu yayi musu alamun da su wuce su tafi a da sauri suka hau mota suka ja da gudu. Dawo da kallon sa yayi kanta yadda jikin ta yake tsuma tana kuka hakan ya tabbatar masa da ba k'aramin tsoro take ji ba sai ta sake bashi tausayi yana so yayi mata magana amma bai san me zaice ba.

Yana tsaye tana kuka sai da ta gaji dan kanta sannan ta fara k'ok'arin tashi tsaye, bata iya tsayuwa da k'afafun ta hakan ya saka tashi yake gagarar ta ganin sai juyi take kamar wancan lokacin ya saka shi mik'ar da ita tsaye ya bata sandar ta rik'e sai kuma ta dafe kai da hannayen ta guda biyu jin yadda yake sarawa. Bata daina kuka bai kuma ce komai ya juya wajan motar sa ya shiga karen shiga mazaunin baya ya dawo da motar daidai kusa da ita amma har lokacin bai ce k'ala ba.

Wajan take kallo babu alamun abin hawa in tak'i shiga motar ta cuci kanta dan bata san a inda take ba balle tabi hanyar da zata sami mota, tana so ta shiga amma rashin yi mata magana da baiyi ba ya saka take shakka kar ta shiga ya wulaqanta ta.

      Sauke glass d'in gefen ta yayi da hannu yayi mata alama da ta shiga a sanyaye ta ja handle d'in motar ya bud'e, so take ta fara saka sanda guda d'aya sannan ta shiga sai ta shigo da d'ayar amma ta kasa ta rasa yadda zatayi. Babu tsammani taga ya fito daga motar ya dawo inda take ya karb'o guda d'aya ya saka a ciki ta saka k'afar ta mai lafiyar ta shiga cikin motar, saka mata d'aya sandar yayi kana ya kulle k'ofar ya zaga ya shiga.

Ganin ta yayi duk a tsorace tana kallon baya ya juya yaga Bobby ya san shi take jin tsoro bai ce komai ba yaja motar. kuka take cigaba da yi tana goge idanun ta har lokacin jikin ta bai daina rawa ba shi kuma bai ce mata ci kan ki ba tuk'i yi a nutse. Kukan ya dame shi har tsakiyar kansa yake jin kuka amma bai san me zaice mata ba shiyasa yayi shiru ya jure abinda yake ji ya cigaba da tafiya.

Ba tare da tayi zato ba taji sun tsaya tana d'ago kai ta gan su a k'ofar gidan su d'an hasken kwan solar da ya haske wajan gidan nasu duk da babu wani haske sosai amma dai yafi babu ya haska wajan, kallon sa tayi ta kalli gidan nasu ta tabbatar fa nan ne mamaki da tsoro suka yi mata yawa tunanin ta a ina ya san gidan su?.

"Kina da Yaya?." A sama taji maganar tasa ta juyo ta kalle shi sai taga kamar ba shine yayi maganar ba dan bama ita yake kallo ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login