Showing 66001 words to 69000 words out of 91952 words
gyara zama yace,"Na shirya wani abu a raina amma ban sani ba ko zaka amince."
Da hannu yayi masa alama da yana jin sa.
Gyara zama ya sake yi yace, "Daman mafita ce na nemo amma ina jin shayin fada maka." Aliyu ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa yace, "Go ahead."
"Daman cewa nayi mai zai hana mu b'atar da Asad ya bar k'asar nan ma'ana ayi masa abinda bazai sake waiwayo mu ba, kai kuma sai ka koma acting d'in Asad a fad'awa duniya Aliyu ne ya b'ata ba Asad ba. Ni da kai mun san Aliyu ne yake nan amma duniya za'a ce mata Aliyu ne ya b'ata; kaga mai martaba zai mallaka maka mulkin katagum a matsayin Asad kaga shikenan ciki lafiya baka lafiya."
Wani irin kallo Aliyu yake masa gaban Waziri sai fad'uwa yake yi yana b'oye tsoron sa babban burin sa kar yak'i amincewa da batun sa hakan ya saka tsoro ya bayyana k'arara a tare dashi duk da yana so ya b'oye amma hakan ya gagara sai da tsoron ya kwanta a fuskar sa. Numfashi Aliyu yayi kafin ya saki dariya mai d'auke da izza da k'asaita kafin ya kalli waziri yace.......
*KWANTAN ƁAUNA*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*019.*
Irin kallon da yake yi masa jikin Waziri yayi sanyi qalau kuzarin sa ya ragu amma duk da hakan bai nuna ba ya daure ya cije baya so ya bayyanar da raunin sa kar Aliyu ya gano shi, Aliyu wani irin murmushi yake yi ya sauke k'afar daga kan d'aya ya kalle shi ta k'asan idanu yace, "kana ganin hakan zai yu kuma?."
Jin abinda yace sai ya sauke ajiyar zuciya yace, "Mai zai hana ya yu ranka ya dad'e?, indai zaka bada goyan baya abu ne mai sauk'i faruwar hakan."
Ya juya manyan idanun sa ya sauke su akan Waziri kana ya mik'e tsaye yana kallon sa yace, "Zan yi tunani a kan hakan" yana gama fad'ar hakan ya fita daga falon bai sake kallon waziri ba. Waziri ya dafe k'irji gaban sa yana fad'uwa sosai ya d'auko waya da sauri jikin sa har rawa yake, kiran yake ba'a d'auka ba ya cillar da wayar akan kujera ya mik'e yana zaga d'akin.
"Me yaron nan yake nufi dani? Yaji sirrina a banza ya tashi ya tafi ya barni....? kenan yana nufin na jira shi?, in bai amince bafa?." Naushin iska yayi ya koma ya zauna jikin sa har b'ari yake sabida tashin hankalin da yake ciki.
Kamar kuma anyi masa allura ya mik'e da sauri ya shiga d'aki dan bai ga ta zama ba.
Aliyu lokacin da ya fita mota ya shiga ya zauna yana tuno abinda Waziri ya fad'a masa sai yayi murmushi yaja tsaki yace, "Wai ni zai yiwa wayo, an fad'a masa ni d'in shashasha irin sa?, ko kuma ya d'auka zuciya ta irin ta Asad ce?." Sai kuma ya tsaya da dariyar ya d'auki waya da sauri ya kira Waziri, kamar jira yake yaji an d'auka ya gyara murya yace, "Na amince da tayin ka." Yana jin ajiyar Wazirin a waya baice komai ba ya yanke wayar ya ajjiye wayar wayar yana kallon glass d'in gaban motar.
Asad bai koma gida ba sai da ya gama yawon sa har dare yaci abinci sannan ya koma, ko wajan Mama bai shiga ba ya shiga apartment d'in su ya tarar da Aliyu a zaune ya kunna sigari yana sha, har ya wuce ya dawo yana kallon sa har ga Allah baya son warin ta ko kad'an ya masa magana sau babu adadi amma yak'i.
"Aliyu ko a lafiyar ka abinda kake yi ba daidai bane" ya furta yana kallon sa. D'ago idanun sa yayi ya kalle shi ya murmusa ya sake zukar sugarin ya fesar kana yace, "lafiya ta kace ba taka ba, a gani na ai hakan ba damuwar ka bace ba."
Asad bai kuma cewa komai ba ya d'aga kafa zai wuce yaji yace, "kabi a hankali ka kuma taka tsan-tsan akwai lokaci Asad." Baice komai ba ya wuce ya k'yale shi ya shiga d'akin sa. Can k'arshen d'akin ya wuce ya janye labule sai ga k'ofa ta bayyana a wajan wacce in ba kasan da ita ba baza ka tab'a cewa tana wajan ba ya shiga ciki ya kulle k'ofar. K'aton wajan karstu ne mai d'auke da drawer na littafai manya-manya na addini dana karatun zamani, littafai ne sama da guda dari uku a wajan ko wanne rukuni da cover sa da sunan su a k'asa ga table da kujera mai guda d'aya a wajan da k'aramar lamp a kai.
Kujerar yaja ya zauna ya dafe kansa da duka hannayen sa biyu kansa na juyawa ya rasa dalilin da ya saka yake jin hakan da zarar ya shigo d'akin sa, daurewa yayi ya tashi ya k'arasa jikin cover ya d'auki littafai guda biyu ya k'araso ya zauna a kan kujerar ya fara dubawa. Karantawa yake a nutse yana bin rubutun daki-daki yana Nazariin abinda yake yi.
Rufe na farko yayi ya bud'e na biyun yana sake bi a hankali har ya kammala karanta inda yake da buk'ata ya kulle ya kifa kansa a kan littafin kamar mai bacci.
Juma'a ce gobe kuma shine zai gabatar da hud'uba shiyasa yake ta dube-duben littafai amma zuciyar sa ta kasa bashi topic guda d'aya da zaiyi hud'ubar a kansa, d'ago kai yayi ya saka hannu biyu ya d'an daki kansa a hankali ya furzar da iska waje yana kallon d'akin gabad'ayan sa. Zuciyar sa yaji yana bugawa da sauri har yana jin sautin ta a kunnen sa ya runtse idanun fuskar Rauda ta bayyana a gare shi.
"Hasbunallahu wani'imal wakil" ya furta a hankali yana dafe da kansa har lokacin bai kuma daina jin bugun zuciyar ba.
Cize bakin sa yayi ya runtse idanu kafin ya koma ya jingina da kujerar, sautin muryar ta yake tunowa a hankali tana shiga ilarin jikin sa, tasirin muryar da dad'in ta ya saka shi kulle idon sa yana sauke numfashi gashin jikin sa na tashi. sautin muryar yarinyar mafarkin sa yaji sai ya bud'e idanun sa; ya kasa banbance shin itace yake gani a mafarki ko kuma ba ita bace?, bai tab'a ganin waccan fuskar ta completely ba amma idanun ta da goshin ta irin na Rauda ne, akwai banbanci a maganar su waccan muryar ta tafi zak'i a kan ta Rauda, ita kuma ta Rauda tafi sanyi da taushi kamar mai mura in tana magana.
Tashi yayi ya kashe hasken d'akin ya fita daga cikin da ya dawo d'akin sa ya zauna a gefen gado ya rasa tunanin ma mai zaiyi.
Kiran wayar Suhail ya gani ya jawo wayar ya d'auka ya saka a kunnen sa yayi shiru alamun ana yi masa magana kafin yace, "Alright" daga haka ya yanke wayar ya tashi ya shiga band'aki. Sai bayan ya gama komai sannan ya kwanta da burin Allah ya sa yau yayi mafarki da yarinyar da yake gani ko zai gane ta.
Washe gari da ya farka yaso yaje ofishin fasko amma sabida juma'a ce dole ya tsaya yayi hud'uba ya saka babu inda yaje har aka shiga masallacin cikin gari, kamar ko yaushe yayi hud'uba ya kuma yi sallah bayan an idar ya hau mota ya wuce office d'in. Da kansa ya karb'o faskunan nasu guda uku da hotuna yana shiga mota ya zauna yana kiran agent d'in su a waya, ana d'auka yace, "Egyptian visa nake so guda uku" Shiru ya kuma yi kafin yace, "Okay better" yana fad'a ya yanke wayar ya ja motar sa ya bar wajan.
Gida ya wuce ya ajjiye faskunan ya fito zuwa wajan Mama kamar yadda ya saba. A hakimce ya same ta tana danna waya kamar koda yaushe ya zauna a gefen ta kana yace, "Barka da juma'a."
"Barka Asad" ta furta kawai ba tare da ta kalle shi ba. Shiru ya biyo baya babu wanda ya kuma yin magana kafin yace, "Mama anyi inviting d'ina wani event a Cairo"
"Kwana nawa zakayi?."
"I think one week."
"I'm not allow u to go."
Kallon ya yayi itama ta kalle shi yace, "but Mah...." D'aga masa hannu tafi tace, "Na gama magana Asad, tafiya indai ba ta kwana biyu bace ban amince ka jeta a yanzu ba maybe kaje wani lokacin."
Numfashi ya sauke ya tashi ya fita daga falon nata zuwa falon Hajiya kamar yadda ya saba duk juma'a, tana zaune ita da hidiman ta ya shiga da sallama, "Barka da zuwa Yarima, barka da zuwa fari mai farar wutsiya, fari mai farar aniya, indaroro sai kan soro, kaga tufa mad'aukar d'aki, sikari bakayi farin banza ba, walikiya kake duk inda kabi sai ka haska......" zasu kuma magana ya d'aga hannu sama sukayi shiru cikin girmawawa.
Murmushin yake take tana kallon sa ya zauna a k'asa yana kallon yace, "Barka da Juma'a Hajiya"
"Barka dai Asad, ya jama'a ya kuma k'ok'ari?."
"Alhamdulillah, ina suke?" Ya fad'a yana kallon falon alamun yana neman kannen sa.
"Sunje gidan Yayar ku sai zuwa anjima zasu dawo." Tunda tace Yayar ku ya gano wacce take nufi dan babar yar ta wacce ta kasance babba a gida gabad'aya bata fad'ar sunan ta daman. "Na barki lafiya" ya fad'a yana mik'ewa tsaye tace, "Na gode Asad." Bai amsa ba ya fita ya tafi b'angaren Umma, kamar ita tana zaune itama a zagaye da hadimai suka gaisa kamar waccan ya tafi.
Kasancewar rana ce bai samu mai martaba ya bada kud'in da ake rabawa dan bazai samu damar yi da kansa ba ya koma apartment d'in sa.
Sai yamma sannan wanda zai karb'i faskunan yazo ya bashi ya wuce Abuja dasu domin a buga musu visa. Bayan wanda karb'a ya tashi yana zaune Suhail ya kira shi, bai d'auka ba har ta katse bayan ta katse ya d'auki wayar ya kira hidiman k'ofar ya bada umarnin a bar shi ya shigo ya ajjiye wayar.
Da sallama ya shigo ya zauna kusa dashi Asad yace, "Suna bin umarnin Mama ne."
Suhail ya murmusa yace, "Hakan yana da kyau sosai tsoron lafiyar kace, sai naga kamar ka rame." Tab'e baki yayi baice komai ba kafin Suhail ya kuma cewa, "me yake faruwa?."
Iska ya furzar a hankali yana sauke numfashi amma bai ce masa komai ba, jin hakan sai shima yayi shiru ya saka hannu a aljihun gaban rigar sa kamar mai neman wani abu, "me kake saka min?" Yaji muryar Asad a kansa yayi saurin janye hannun sa daga kusa dashi.
Had'a idanu sukayi Asad ya d'aga gira alamun ya bashi amsa, nutsuwa ya aro ya saka a fuskar sakana yace, "me kuwa zan shafa maka Asad? Kalli hannu na mana" ya fad'a yana nuna masa tafikan hannun sa. Murmushin gefen baki Asad yayi kafin ya d'auke kansa daga kallon sa yace, "lafiya ka ke nema na?."
"Normal ina so mu had'u ne kawai."
"Really?" Asad ya fad'a yana wara idanun sa waje.
"Sure, naga duk ka canja Asad kamar baka yadda dani ba, ko da Aliyu nake tare ne ban sani ba?."
Baice masa komai ba ya shafa kai kawai kafin yace, "u can go." Suhail ya kalle shi yace, "Okay bye" ya fad'a yana mik'ewa ya fita yana mamakin canjawar Asad. Waya aka kuma yi masa ya kalla yaga masu tsaron k'ofar sane ya share kiran ya katse aka kuma kira ya ja k'aramin tsaki ya d'auka baice komai ba, daga can b'angaren suka ce, "Ranka ya dad'e Allah ya wuci zuciyar ka na dame ka, wata yarinya ce take so tayi magana da kai, tana ta magiya mu barta ta ganka."
Jimm Asad yayi yana tunani kafin ya bada umarnin tazo, ba jimawa ta shigo da sallama jikin ta har rawa yake ta zube a kan carpet tace, "Barka da yamma ranka ya dad'e."
"Wacece ke?" Ya furta a hankali yana kallon ta.
"Sunana Habiba ni jikar Gwaggo Gambo ce da take gidan nan. K'awa tace ta samu matsala da Yallab'ai Aliyu to tsoro take ji kar ya mata wani hukunci shiyasa muka kawo k'ara gaban ka a taimaka a bashi hak'uri. "
Shiru yayi bai amsa ba hakan ya saka tace, "Sunan ta Rauda tana da matsalar k'afa shiyasa bamu zo tare ba, mun tab'a zuwa gidan nan da ita ta buge shi bata sani ba ya mare ta, had'uwar su ta biyu kusan hakan ce ta faru, had'uwar su ta uku shine ta mayar masa da abinda ya fad'a mata. Yayi alwashin sai ya d'auki mataki a kanta duk taji tsoro sai kuka take hankalin ta ya tashi matuk'a. A bashi hak'uri ranka ya dad'e wallahi y'ar talakawa ce kar ya cutar da ita."
Yana sauraron ta dan a hankali take maganar hakan ya saka shi nutsuwa yana jin ta, tunda ta ambaci Rauda gaban sa ya fad'i ya sake bata hankalin sa har taje k'arshe kafin, "kar ki damu."
"Na gode ranka ya dad'e, Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana, ya ja da ran Mama da mai martaba." A lab'b'an sa ya amsa da amin ya sanya hannu a aljihun sa ya d'auko kud'i ya mik'a mata ta karb'a hannu na rawa zatayi godiya ya d'aga mata hannu ta tashi ta fita.
Numfashi ya fesar kalmar ya mare ta tana yi masa amsa kuwa a kunnen sa nan take ransa yaji ya b'aci ba kad'an ba yaja tsaki baiyi niyar fita ba amma ya tashi ya fita daga gidan gabad'aya.
Habiba na barin gidan wajan Rauda taje ta bata labarin duk abinda ya faru har kud'in da ya bata ta nuna mata, Rauda tace, "Bari kawai Habiba baki san me ya faru washe garin da kika zo nan ba."
"Meya faru to?."
Kwashe duk abinda ya faru tayi ta fad'a mata sannan ta d'ora da cewa, "Jiya ya saka aka kai mu ofishin fasko za'ayi mana zai kaini waje ayi gyaran k'afa madadin k'anin sa."
Habiba tace, "ban sani ba ai da banje na same shi yanzu ba tunda komai ma ya wuce. Amma nayi murna da za'a yi miki aikin k'afar nan Allah ya sa ayi a sa'a."
"Amin."
"Kika dinga zagin wanda ya kad'e ki kina ganin kamar wasa ne babu wani rashin lafiya ashe gashi wanda muka sani ne ma."
"Wallahi kuwa, na d'auki hakki."
"Ina Anas ne wai?." Rauda tace, "Yaje Abia."
"Masoyin ki kenan, wai har yanzu baki bashi dama ba?."
"Na bashi Habiba tunda ina sauraron sa yanzu. Tunda ya siya min maganin da aka wulak'anta ni a kai ya kawo mana kayan abincin da ko rabin rabin sa bamu ci ba wallahi nake ganin k'imar sa sosai. Ta silar abincin nan Baba ya daina d'orawa Rahma tallah."
Habiba tace, "Ai yana son ki wallahi zaiyi komai sabida ke; Allah ya saka masa da alkhairi."
"Amin."
"Kin fara son sa kenan?."
"Ina fa, kedai Allah ya kyauta." Habiba tayi dariya ta amsa da amin kafin su cigaba da hira suyi sallama ta tafi.
Maganar Habiba ta dinga tunawa musamman halayen Asad sai taji ya burge ta sosai ko babu komai baya wulak'anta talakawa kamar Aliyu.
B'angaren Asad bai dawo ba sai dare direct ya wuce b'angaren mahaifin sa sai da aka bashi izinin shiga sannan ya shiga, baya babbar fada ta farko ya shiga ta biyu nan ma baya nan hakan ya bashi tabbacin yana d'aki kenan. Shi kad'ai mai martabawa yake lamuncewa ya shiga amma gudun kar ya shiga ya tarar da wata matar tasa a ciki ya saka yaja tunga tunda ba girkin Mama bane ba. Kamar kuwa ya sani yana nan tsaye Ammi ta fito ganin sa ya saka tace, "Asad daman kai yake nema kuwa, kaje ciki" ta fad'a tana wucewa shima ya shiga d'akin da ya san mallakin mahaifin sane.
A zaune ya same shi a kamalance ya k'arasa ya zauna a akan carpet yace, "Barka da dare Takawa." Murmushi yayi yace, "Barka dai Asad."
"Ya k'arfin jikin?."
"Jiki Alhamdulillah ana ta samun lafiya."
"Allah ya k'ara lafiya yasa kaffaara ce."
"Amin Asad. Allah ya yi maka albarka ka rayu cikin aminci da walwala."
A labban sa ya amsa da amin kafin mai martaba yace, "Ya batun zuwa taron malamai masu shekarun naka a Dubai?."
"Mama ta hana Abba" ya furta a sanyaye.
Kai ya girgiza yace, "Rabi'atu manya, ko kad'an bata so kayi nisa dani gudun kar ka tafi a bawa wani sarauta ba kai ba, tana mantawa da Allah ya riga ya rubuta wanda zai gaje ni."
Shiru Asad yayi bai ce komai mai martaba yace, "Ta hana ka aikin da kake mafarki tun kana yaro, ta hana ka komawa Dubai kamar yadda sarkin su ya nema, ta hana ka aiki da Saudia yanzu kuma ta hana ka zuwa taron kwana bakwai kacal; in kana so ka shirya ka tafi na baka damar hakan."
"Allah yaja zamanin mahaifina, tunda tace na bari na bari d'in."
Mai martaba yayi murmushi mai kyau yace, "Shiyasa albarka take baibaiye dakai a koda yaushe, indai nace kar ayi ko tace kar ayi baza kayi koda a bayan idanun mu. Amma tauye ka da take yi yayi yawa nan gaba indai aka kuma zuwa irin wannan gab'ar bazan bari ta tauye ka sai kayi abinda kake so." Shima murmushi Asad d'in yayi yana kallon mahaifin nasa.
"Ya batun yarinyar da take nema maka?." Take fuskar sa ta koma yadda take a d'azu yace, "bata dace dani ba Abba, na sanar da Mama tace ba haka ba ita ta zab'a min, amma na karb'a."
"Da zarar ka samo wacce kake so ko wacece a fad'in duniya ka sanar dani Asad, zan shige maka gaba wajan ganin ka mallake ta ko waye mahaifinta a garin nan ko a k'asar nan."
D'ago idanu yayi suna had'a ido da Abban nasa kwarjini ya saka ya sauke kai k'asa ba tare da ya shirya ba yaji bakin sa yace, "Ko y'ar talakawa ce?."
Mai martaba ya tashi sosai yace, "Ko y'ar wace Asad; shi talaka ba mutum bane? Ko y'ar shugaban k'asa ce indai ba y'ar gidan sarauta bace y'ar talaka ce a gidan sarauta. Indai da tarbiya da ilimin addini zance ya k'are. Inda za'a samu matsala in aka bincika aka gano wata dabi'a a tare da ita ko tare da dangin ta, kasan gida irin wannan baya d'auko irin wannan yaran."
Jin abinda mai margaba yace sai kuma ya rud'e