Showing 63001 words to 66000 words out of 114708 words
tare kuma da juyowa ta fuskancesa, saidai bata yarda ta sake ajiye Idanunta akansa ba.
Cikin sanyin muryarta da akullum, take fitar da wani irin daddad’an sauti tace.
“Dama wayarka ake kira shine na kawo ma.”
Ta k’are maganar tana me d’an matsowa jikin gadon, a hankali saboda mik’a masa wayar.
“Gashi.”
Ta fad’a adai-dai lokacin da ta iso kusa dashi.
Hannunsa ya mik’a mata, still yana daga kwancen batare daya tashi ba, cikin wata irin murya yace.
“Give me.”
Mik’a masa wayar tayi, kasancewar ta sunkuyar da kanta k’asa ne kuma, yasa ta sauke Idanunta akan, wasu kwantattun gashin dake kwance akan kirjinsa, wanda kuma sudinne suka taho har zuwa, saman cibiyansa, gashi ne masu kyau da laushi, duk da cewar basu da yawa amma sun k’awata, farar fatar jikinsa sosai.
Tsaida idanunta tayi akan saman mararsa, wanda tananne gargasan sukafi yawa, kuma sun kwanta lub lub gwanin ban sha’awa, Kallon gashin jikin nasa ne kuma yasa, ta kasa sakar masa wayar da take mik’a masa.
Tana son gashin jiki sosai domin abun yana yi mata kyau, musamman awajen Namiji, duk da cewar ta saba kanin na legs din, Ya Junaid kasancewar ya saba zama da gajerun wanduna, amma bata tab’a ganin kyawawan gashi kamar na Rayyern din ba, saboda shi nasa har wasu shining sukeyi.
Rayyern kuwa dake mik’a mata hannu, Idanunta ya kalla saboda yaga ta kasa sakar masa wayar.
Ganin yanda take Kallon jikinsa ne kuma, ya sa shima ya kalli jikin nasa, saboda atunaninsa ko wani abun ta gani.
Fahimtar da yayi cewar hairs d’insa take kallone, kuma ya sashi dawo da kallonsa gareta, Cikin yanayin gajiyawa da Kallon nata yace.
“Wai duk wannan Kallon kam na menene Malama? ko cinyeni kikeson yi ne, Dan nasan zaki iya ko dai naci miki bashin wani abune kike kallonsa a jikina?.”
Maganan nasa daya fad’a ne yasa tayi saurin yin k’asa, da kanta tare da sakar masa wayar, lokaci daya kuma taji wani irin kunya ya lullub’e ta, saboda Sam bataso hakan ya kasance ba.
Jin ya karbi wayarne kuma yasa ta juyawa, da sauri ta fice daga cikin dakin.
Rayyern kuwa bakinsa ya tab’e, tare da bin bayanta da idanu, kasancewar tana tafiyar nata cikin sauri ne kuma yasa, duk wani gab’a dake jikinta motsawa, musamman big hips dinta way’anda suke da shape na burgewa, duk da cewar rigar bacci ne ajikinta, amma hakan bai hana hips din nata bayyana ba, saboda rigar jikin nata yana da santsi, ga kuma dogon gashin kanta daya sauko har bayanta.
Saurin kawar da idanunsa daga kan hips din nata, yayi tare da maida kansa ya ajiye akan pillow, akaron farko na rayuwarsa da yaji zuciyarsa na tsananta, bugawa akan wani abu na daban.
Idanunsa ya d’an lumshe tare da sauk’e Ajiyar zuciya.
Wayartasa ya kunna tare da duba mai kiran nasa, Ganin new number ne kuma ya sashi share kiran, saidai ko minti 1 ba’a rufa ba, wani kiran ya sake shigowa, Ganin kiranne kuma ya sashi d’agawa tare da kara wayar akan kunnensa.
Daga can b’angaren Riyyam yace.
“Hello Hamma Rayyern Riyyam-nsra ne.”
Ajiyar zuciya Rayyern din ya sauk’e, saboda Jin muryar Riyyam din, cikin muryarsa dake nuna d’an yanayin kasalan dake tattare dashi yace.
“Riyyam yakake yasu Mammy.”
“Lafiyanmu k’alau Hamma Rayyern, saidai nayi kewarka sosai, Mammy da Zaytoon sunce na gaisheka, kuma Hamma Rayyern mafa tuntuni nake cewa, Hamma Ramadan ya bani numbern ka, amma sai jiya ya turomin.”
Riyyam nsra din ya fad’I haka cikin tura baki.
Rayyern kuwa sanin halin surutun Riyyam dinne, yasa shi gyara kwanciyarsa tare da cewa.
“Ina Mammy?”
“Ga tanan.”
Riyyam din ya fada yana bawa Mammyn wayan, saboda dama tana gefensa.
“Assalamu Alaikum Rayyern.”
Rayyern dake kwance jin muryar Mammy, ya sashi tashi ya zauna, cikin sakin fuska ya amsa mata sallaman tare kuma da gaisheta.
Mummy kuwa cikin jin dadin jin muryar Rayyern din tace.
“Ya Mascow da kuma Surukata.”
“Lafiya lau Mammy, itama kuma tana lafiya, Zaytoon fa?”
Rayyern din ya tambaya.
Murmushi Mammy tayi kana cikin jin dadin kulawarsa agaresu tace.
“Zaytoon tana lafiya, saidai kasanta kasa ce sarkin bacci, har tayi bacci da na had’aku kun gaisa, yasu Mamynku da Ramadan, fatan duk suma Suna lafiya.”
“Lafiya lau Mammy, d’azu munyi waya dasu, Ramadan kuma yana can yanata zumudi, saboda an bashi mata, kuma naji anacewa aurensa kafun Azumi.”
Rayyern din ya fad’a yana me gyara zamansa, saboda hakanan Idan yana waya da Mammyn yakejin sakewa.
Mammy kuwa jin abunda ya fad’ane yasa cikin farinciki tace.
“Masha Allah gaskiya na tayasa murna, Allah Ya sanya alkhairi yasa ayi damu.”
“Ameen Mammy zaku zo biki ko?”
Yayi maganar kamar Wacce tazo masa afuzge, wanda kuma abunda ke cikin zuciyarsa ne ya fito fili, saboda haka kawai yakejin yana son Ganin matar ido da ido.
Daga can b’angaren Mammy kuwa murmushi tayi, cikin kuma danne damuwar dake ranta tace.
“Insha Allah zanzo mana Maud’ona Idan angayyace ni.”
Murmushi Rayyern din yayi tare da lumshe idanunsa, saboda yana jin dadi aduk lokacin da matar takirasa da suna Maud’o.
Cikin sakin rai yace.
“Mammy zaki zo mana, ai basai an gayyaceki ba saboda kema mai iya gayyatan wasu bakinne daban.”
“Hakane Maud’o Allah ya kaimu lokacin, ya kuma bamu Aron rai da lafiya, bari na barka saboda naga dare yayi, nasan awajenka ma nitsawan daren yafi haka.”
Mammyn ta fad’a cikin sakin rai.
Rayyern kuwa kansa ya jinjina, kamar Mammyn tana gabansa kuwa yace.
“Ameen Mammy saida safe, ki gaishemin da Zaytoon.”
“Zataji Insha Allah.”
Mammyn ta amsa masa, tare da zare wayar akunnenta ta kashe.
Shidinma Rayyern ajiye wayar tasa yayi, tare da komawa ya kwanta, kana ahankali ya lumshe idanunsa.
Acan b’angaren Jannart kuwa tana komawa, d’akinta kwanciya tayi tare dajan babban blanket ta rufe jikinta.
Lub tayi akan gadon tana mejin kunyan, ka mata da Rayyern din yayi tana Kallon jikinsa.
Hannayenta tasa ta rufe fuskarta.
Dan sai taji tamkar har yanzun tana gabansa ne.
Tana ahaka bacci b’arawo ya d’auketa.
*Washegari*
Yau d’in ba kamar kowacce rana ba, domin tunda ya tashi yayi sallan asuba bai sake komawa bacci ba.
6:30 am dai-dai ya gama shirya kansa cikin wasu, tsadaddun suit masu kalan light orange, suit ne masu masifar kyau da tsada, wanda suka bayyana kyawu da kwarjininsa.
Black shoe na sau ciki ya saka ak’afafunsa, tare da d’aura agogon WW a hannunsa.
Yayi kyau matuk’a musamman da ya zamana, sajen dake kwance akan fusuka kawo breakfast din da yayi order.
Amsar breakfast din yayi ya ajiye, saboda bashi da enough time ne kuma, yasa ko tsayawa ci baiyi ba, haka yasa kai ya fice sai baza kamshi yake.
Direct Babban JSC MEDICINA CLINIC MASCOW Hospital din ya nufa, domin acanne yau za suyi meeting din nasu, kasancewar kuma abunda zasuyi din nada yawa, shiyasa duk suka fito da wuri.
10:00 am dai-dai Jannart ta bud’e k’ofar d’akin nata ta fito zuwa falon.
Sanye take cikin wani straight gown mai kauri, Wacce ta kama jikinta ta zauna d’amas, sai kuma hulan sanyi da ta saka ta rufe gashinta dashi, ak’afarta kuwa wani safa ne, wanda da ‘alama yana tare mata sanyi sosai.
K’arasowa tsakiyar falon da tayi ne kuma, ya sanyata lumshe Idanunta.
Badon komai ba kuwa saidan k’amshin turarensa, da ya mamaye cikin falon, domin duk da cewar ya jima da fita amma kamshinsa na nan.
Lumsassun Idanunta ta d’an bud’e ahankali, tare da neman waje ta zauna akan d’aya daga cikin kujerun falon.
Ledan abincin daya ajiye mata din ta d’auka, tare da bud’ewa , ga mamakinta kuma yau din, chips and ketchup ne sai kuma hadin Salad da lemon tsami.
Taji dadin hakan sosai saboda dama ta gaji, da ire iren abincin kasar, wannan dalilin yasa sosai taci abincin bayan ta kammala ne, kuma ta Kai sauran ragowan kitchine, tare da dawowa falon, tv ta kunna cikin sa’a kuwa ta samu wani, tasha suna haska film mai kyau.
Komawa kan tree seater tayi, har za ta kwanta ne kuma sai idanunta, suka sauk’a akan sachet din maganin Rayyern din, dake ajiye akan kujeran.
D’aukan sachet din maganin Tayi, tare da d’an jujjuyasa saboda Ganin da tayi, saura guda biyar ne kawai ya rage maganin ya k’are.
Bayan ta duba sunan maganin ne kuma ta maidashi ta ajiye, Ahankali ta kwanta akan kujeran tare da mik’e k’afafunta, kana ta maida hankalinta duka akan tv’n.
Tana nan kwance kuwa bacci ya d’auketa, batare da ta shiryawa hakan ba.
*Nigeria.*
Abdull ne ya turo k’ofar babban falon nasu, ya shigo hannunsa rike da jakan makarantarsa.
D’an tsayawa yayi daga bakin kofar yana me Kallon, Momynsa wacce take zaune jigum acikin falon, ta d’aura hannayenta bisa kan k’uncinta.
Kansa ya d’an sunkuyar k’asa, lokaci d’aya kuma yaji hawaye sun cika idanunsa, badon komai ba kuwa saidan sanin damuwar dake, zuciyar kowannensu daga Cikin gidan.
Maida kofar falon yayi ya rufe, tare da karasowa ya zauna ad’an nesa da mahaifiyar tasa.
“Momy.”
Ya kira sunanta murya asanyaye.
Saurin d’agowa Momyn tayi saboda sam bata ji shigowar nasa ba.
“Na’am Abdull ka dawo.” Momyn ta amsa asanyaye.
Idanu Abdull din ya zubawa Momyn nasu kana cikin sanyi yace.
“Nasan akan me kike damuwa Momy, nasani akan b’atan Aunty Jannart ce, nima kuma akwai wannan damuwar acikin zuciyata, kullum dashi nake kwana nake tashi, har yau nakanji wani iri, Idan na tuna cewar wai Aunty Jannart ta b’ata, b’atan da har yau ankasa samota, tayaya hakan zata kasance Momy? Nikam nasani wasu ne kawai suka sace Aunty Jannart, Dan kawai su cutar da ita.”
Idanu Momyn ta tsura masa, saboda itama kullum irin tunanin da takeyi kenan, saidai kuma abubuwa da yawa ayanzu kan kulle mata Kai, Lallai akwai Sark’ak’iya mai nauyi, da kuma k’ulli mai wuyar kuncewa, wanda yake cikin gidan da basu sani ba, sau dayawa zuciyarta kan gaya mata, cewa Lallai akwai wani b’oyayyen abu, da ake b’oyewa.
Wanda kuma ita kanta batasan sai yaushe ne, sirrin b’oyen zai fito fili ba.
Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e tare da gyara zamanta, cikin sanyin murya mai d’auke da damuwa tace.
“Abubuwa da yawa suna damuna Abdull, bayan b’atan Jannart da kuma rashin lafiyar Dadynku, har da son sanin wani abu da aka bunne, ay’an kwanakin nan bana iya bacci Abdull, bansan mai yasa ba kwata-kwata bani da nutsuwa, saidai koma meye Ina rok’on Allah da ya kawoshi da sauki.”
“Ameen.”
Abdull din ya amsa, tare da mik’ewa kaitsaye ya wuce d’akinsa, saboda agajiye yake sosai.
Itama Momyn mik’ewa tayi ta koma d’akinta, saboda tun daren shekaran jiya da kunnuwanta suka jiye, mata wani abu gaba d’aya ta kasa sukuni, duk da ta kasa fahimtar inda kalaman da taji Mijin nata na fad’a awaya suka dosa, saidai Tabbas tasan abune mai d’auke da Sark’ak’iya, wanda acikinsa babu komai sai zallan tashin hankali, rud’ani da kuma bayyanar b’oyayyar gaskiya.
Barrister Kabir.
Ahankali yake har had’a wasu takardu dake gabansa, zuciyarsa cike take da kwarin guiwa, na samun duka shaidun da yake buk’ata.
Har had’a takardun yayi awaje d’aya, har dai yazo kan wani file na k’arshe, wanda asaman file din, aka rubuta suna kamar haka, *Barrister ABDULKARIM SALEH DAKATA.*
Ajiyar zuciya Barrister Kabir din ya sauke, tare kuma da d’an jujjuya file din, lokaci d’aya kuma yaji idanunsa, sun cika da k’walla.
Cikin jajircewa da kuma tabbatarwa da kansa yace.
“Insha Allah Koda baka raye gaskiya zatayi halinta, abunda aka b’oye zai fito fili, Ranka bazai tafi a banza ba, Lallai dole kowa zai sani, nan babu jimawa zan tone duk wani abunda suka bunne da izinin ubangiji.”
Ya k’are maganan with full confidence, tare da tashi ya taka kan wata kujera, takardun dake hannun nasa ya maida, can sama wajen ajiyarsa ta sirri, da duk duniya babu wanda ya sani daga shi sai Allah.
Bayan ya b’oye takardun ne kuma, ya bud’e k’ofar d’akin nasa, ya fita zuwa wajen iyalansa dake falo.
*Mascow*
Sai 11:30 pm Dai-dai na k’asar yake shigowa cikin gidan.
Bayan ya gama dai-dai-ta parking ne kuma, Ahankali ya bud’e murfin motar ya fito.
Kallo d’aya zakayi masa kafahimci cewa agajiye yake sosai, saboda tunda suka zo kasar, wannan ne karo na farko daya fara lattin dawowa gida, haka zalika kuma yaune karo na farko da sukayi aiki sosai.
Agajiye yake takunsa, Yayinda yasa hannayensa duka biyu, ya zare suit din dake jikinsa.
Ahankali ya tura k’ofar falon ya shiga.
Babu kowa acikin falon, wanda dama kuma bai tsammaci hakan ba, shiyasa ma kaitsaye ya wuce d’akinsa.
Briefcase da kuma car key d’insa ya ajiye akan bed, Ahankali kuma Cikin nutsuwa ya soma, rage kayan dake jikinsa, takalmi da kuma safar k’afarsa ya cire, kana ya zare duk wani kaya dake jikinsa.
D’aya daga cikin sabin towel d’insa ya d’aura akan kugunsa, duk sanyin da akeyi kuwa hakan bai damesa ba, kaitsaye ya wuce toilet yayi wanka.
Koda ya fito daga wankan kuwa, mai kawai ya shafawa jikinsa, sai wani 3quater daya saka.
Tabbas ya gaji sosai domin har wani rufewa idanunsa keyi, bud’e d’an madaidaicin fridge’n dake cikin d’akin yayi, wani babban packet na chocolate d’insa ya d’auko, tare da dawowa ya kwanta akan gado.
Idanunsa ya lumshe ahankali tare dasa, hannunsa ya d’an shafa saman mararsa, saboda kasala yakeji sosai ajikinsa.
Ahankali kuma yana daga kwancen, ya saka hannunsa ya d’auko chocolate d’aya yakai cikin bakinsa.
Jin zakin chocolate din abakinsa ra d’aune kuma, yasa shi sake lumshe idanunsa, tare kuma da gyara kwanciyarsa, bayan ya sake zuba wasu chocolates din abakinsa.
Yana taunawa ahaka har bacci ya d’aukesa, da ledan chocolate din ahannunsa tamkar wani k’aramin yaro.
Jannart kuwa tuntuni dama ta riga da tayi bacci, Dan koda tayi sallan isha, da tazo falon bata samu abinci ba, komawa tayi ta kwanta, kasancewar dama bawai wani yunwa takeji sosai ba.
Washegari kuwa kamar yanda ya saba, tun kafun ya fita yasa aka kawo masa breakfast, bayan yaci nasa yabar mata nata, kaitsaye ya sake wucewa wajen aiki.
*** ***
After 9days.
Tabbas Rayuwa tafiya take, haka ma kwanaki k’arewa suke, akullum kuma lokaci baya jira.
Koda yaushe haka sukeyin rayuwarsu shida ita, zasu kwana agida d’aya amma sai su share, sama da sati babu wanda yaga d’an uwansa, musamman Rayyern da ayanzu, yake cikin tsananin busy, Dan Koda ishashshen lokacin kansa ma bashi dashi.
Domin tun awancan ranan da takai masa wayarsa, bata sake sakashi a Idanunta ba, takan fito ta zauna afalo Idan bayanan.
Sannan aduk sanda ya ajiye mata abinci, takanci kad’an tabar sauran.
Kasancewar kuma ranar yau ta kama Wednesday ne, ya sata fitowa falon dan akwai wani series film din da takeson kallo.
Ahankali take tafiya harta k’araso tsakiyar falon, inda ta sauk’e idanunta akan ledodin halal restaurant dake ajiye akan table.
Sam bata wani jin yunwa sosai shiyasa, ko kula abincin ma batayi ba.
Zama tayi akan kujera tare da kunna tv, saidai taga ba’a fara series dinba, hannunta ta mik’a saman kujeran, dan d’aukan remote, karab kuwa idanunta suka sauk’a akan, sachet din maganin Rayyern din, wanda babu komai aciki, da alama ya shanye ragowan.
D’aukan empty sachet din tayi, tare da d’an jujjuyawa aranta tana me mamakin, Kodai ya k’arar da wannan din, har ya fara shan wani ne?
Sanin halinsa nak’in magani da tayi ne, kuma yasa ta watsar da tunanin gefe, ledan abincin daya ajiye tun na safe ta d’auka takai kitchine.
Ganin yanda kitchine din ya d’an hargitse ne, kuma yasa ta tsaya gyarawa.
Tana cikin gyaran ne kuma Idanunta, suka sauk’a akan wani babban roba mai murfi, k’arasawa tayi ta bud’e robar, ga mamakinta kuma sai taga pure honey ne, mai kyau aciki.
Wani irin dadi taji saboda dama tanason honey, kasancewar ta kammala duk wani abu da zatayi ne kuma, yasa ta d’auki wani d’an plate na glass ta zuba honey din aciki.
Anutse ta dawo cikin falon, hannunta rik’e da plate din tana lasar zuman da yatsanta na dama.
Zama tayi akan kujera tare da nannad’e k’afafunta, ta ci gaba da lasan zuman, rabin hankalinta kuwa naga tv saboda ansoma haska series film din.
Acan b’angaren Rayyern kuwa, yau din tun 1:00pm
suka shiga heart surgery, basu suka fito ba kuma sai 3:00 pm.
Tunda suka fito yakejin kansa duk wani iri, kasancewar tun safe yakejin cikinsa na d’anyi masa ciwo, dan ko abinci bai iya samu ya sakawa cikin nasa ba, drinks kawai yasha.
Ahankali ya saka tissue ya goge fuskarsa, saboda wani irin gumi dayaji na fesowa akan goshinsa, duk da sanyin da garin ke dashi.
Still jin cikin nasa nad’an ci gaba da ciwo ne, yasa shi tuna rabonsa da magani yau kwana 3 kenan wunin na hud‘u, gashi kuma magungunan nasa sun k’are bai samu ya sayo wani ba.
Sulaiman dake gefensa ne ya d’an kalleshi, cikin kuma d’anyi k’asa da murya yace.
“Rayyern are you okay?”
D’agowa Rayyern d’in yayi, batare daya kalli Sulaiman dinba yace.
“Yea I’m okay.”
D’an Jim Sulaiman din yayi, saboda tun daga cikin hospital din ya fahimci, kamar Rayyern din baya jin dadi.
Saboda ya sake tabbatar da abunda yake zargi ne kuma, ya sashi cewa.
“Rayyern ka tabbata you’re okay.”
Idanu Rayyern din ya d’an lumshe, kana cikin kosawa yace.
“I’m okay mana Sulaiman, if I’m feeling bad mood, I will tell you, so please leave me alone, cause I’m tired..”
Ya k’are maganan cikin cije l’abbansa, saboda baya son yawan tambayoyi.
Sulaiman kuwa Ganin yanda Rayyern din keyi ne, ya sake yardarwa kansa cewar he’s not okay.
D’an gyara zamansa yayi tare da fuskantar Rayyern din, cikin tausasawa yace.
“No Rayyern k’arya ba d’abi’arka bace, wallahi zan iya rantsewa baka da lafiya, gashi kana zufa a inda ban tab’ayin zufa ba, Rayyern a Mascow fa muke, garin da ko ina dinsa sanyi ne, kayi tunani Idan mutum yana lafiya zaiyi zufa awannan garin ne a irin wannan lokacin? Rayyern baka da lafiya, saboda haka tell me what’s wrong with you?”
Idanu Rayyern din ya lumshe, saboda yasan halin Sulaiman da takura, Idan bai fad’a masa gaskiya ba bazai k’yaleshi ba.
“My stomach has paining.”
Ya fad’a atak’aice.
Idanu Sulaiman din ya zaro, cike da fargaba hadi da tsoro yace.
“Subahanallah Rayyern, kana shan maganinka kuwa?”
“Eh but two days ban Shaba, saboda sun kare ban samu time na saya ba.”
Rayyern din ya basa amsa kaitsaye.
Sulaiman kuwa ido ya tsura masa, kana