Showing 69001 words to 72000 words out of 114708 words

Chapter 24 - TUBALI book 2 complete hausa novel

18 Sep 2024

19355

ni da su Mammy, amma yanzu da naji ya samu relief Alhamdulillah, ga Mammy nan zaku gaisa.”

Ya kare maganan yana mikawa Mammy dake gefensa wayan.

“Jannart”
Mammy ta kira sunan Jannart din tana kara wayar akan kunnenta.

“Na’am Mammy Ina kwana.”
Jannart ta amsa mata cikin ladabi da matukar girmamawa.

“Lapia kalau Jannart ya mai jikin?”
Mammy ta tambaya cikin dan yanayin damuwa.

“Alhamdulillah jiki da sauki sosai, yanzu ma bacci yakeyi.”

“Allah ya kara sauki yasa kaffarane, ya kuma yaye masa wannan ciwon yasa kiyi farar jinya.”

Mammy ta fad’i hakan da iyaka gaskiyar dake zuciyarta.

Jannart kuwa cikin dan jin dadi tace.

“Ameen Mammy mungode sosai da kulawa, Ina Zaytoon.”

“Ganinan Aunty Jannart am ya jikin Hammana?”

Cewar Zaytoon da ta cafe wayar da sauri.

D’an murmushi Jannart tayi, kana murya asake tace.

“Jikinsa da sauki zaytoon ya school?”

“Alhamdulillah My beloved please ki kulamin da Hamma kinji, Allah ya kara masa lafiya .”

“Ameen.”
Jannart ta amsa tana me fadada Murmushin dake kan fuskarta.

Riyyam kuwa dake gefen Zaytoon k’wace wayar yayi, tare da maidashi kunnensa, cikin dan yanayin sigar tsokana yace.

“Gaskiya Aunty Jannart jiya kin tayar mana da hankali, duk kinsa muntsorata, Koda mukayi waya da Hamma Ramadan dazu, saida yayi ta miki dariya saboda yace, jiyan kuka kikeyi harda shid’ewa, irin bakyason mijinki ya mutu nan why?”.

Yanayin yanda ya kare maganan cike da tsokana ne, kuma yasa Jannart din shagwabe fuska, Cikin yanayin tura baki tace.

“Wallahi Riyyam banaso.”

Dariya gaba d’aya suka kwashe dashi, musamman Riyyam da Zaytoon din, harma da Mammy saidai ita nata kasa-kasa takeyi.

Jin yanda suke dariya ne kuma yasa Jannart din turo baki, ashagwab’e tace.

“Mammy ina kinajin su Riyyam ko.”

Da sauri Mammy ta kwace wayan, tare da cewa.

“Rabu dasu abunki, jeki kula da mijinki gaba dayansu duk rashin aikinyi ne ke damunsu, Allah ya miki albarka Jannart, kamar kuma yanda kika kula da Rayyern, kema Allah ya kula dake.”

“Ameen Summa Ameen.”
Jannart din ta amsa tana murmushi, tare da sunkuyar da kanta k’asa.

Mammy kuwa zuciyarta cike da nutsuwa, ta kashe wayan

Tare da watsawa su Riyyam din hararan wasa.

Cikin sakin fuska tace.

“Yarinya tana kulawa da mijinta zaku dameta, idan tayi kuka ai soyayyace ta kawo hakan, da bata sonshi bazatayi kuka akanshi ba.”

Murmushi Riyyam nsra yayi, cikin matsanancin farincikin da yakejin kansa aciki yace.

“Mammy ba auren soyayya fa sukayi ba, Hamma Rayyern bayaso itama haka, amma yanzu naga kaman rayuwar tasu tana ta juyawa, game din na canjawa, I cant wait ranan da Hamma Rayyern da Aunty Jannart zasu so juna.”

Murmushi Mammy tayi, tare da gigirza kanta, batare da tace musu komai ba kuma taci gaba da sabgoginta.

Jannart kuwa ajiye wayar tasa tayi, tare da maida kanta ta jingina da jikin gadon, ahankali take sauk’e numfashi, Yayinda zuciyarta ke cike da tunani kala daban daban.

Rayyern dake kwance kuwa, duk wani hiran dasu Jannart din keyi yana jinsu, harta k’are wayan kuwa bacci bai d’aukesa ba.

Ahankali yake sauke ajiyar zuciya, Yayinda kunnuwansa kuwa ke jiye masa sautin fitan numfashinta, kasancewar ta kashe AC’n dake d’akin, ko ina kuma yayi shiru shi yasa ko wanni sautin motsinta, akan kunnuwansa suke sauka.

Yana nan ahaka har bacci b’arawo yazo ya d’aukeshi.

Jannart dake zaune akan carpet kuwa, game ta d’an soma yi awayarta, tana cikin game din kuma itama bacci ya d’auke ta, inda tayi pillow da hannunta na dama.


1:30 pm.

Ahankali ta bud’e Idanunta, wanda tashin farko suka sauk’a akan agogon dake cikin dakin.

Da sauri ta d’an tashi zaune, tare da juyawa ta Kai dubanta kan gadon.

Idanunta ta sauke akan Rayyern, da har yanzu bacci yake, Yayinda ya sake nad’e jikinsa da blanket.

Yunk’urawa tayi Ahankali ta tashi, gudun kada motsinta ya tashe sa ne kuma, yasa cikin sand’a take tafiya, harta k’arasa bakin kofar fita, ahankali ta bud’e kofar dakin ta fice.

Tana fita kuwa ya bud’e idanunsa, saboda kusan Atare suka farka, kawai dai shi yayi jinkirin tashi ne.

K’ofar d’akin nasa yabi da kallo, kana ahankali ya zuro da kafafunsa k’asa, tare da tashi daga kan gadon ya tsaya akan k’afafunsa.

Ajiyar zuciya ya dan sauke, saboda kwarin da yaji ajikinsa, ba kamar dazu ba dako tsayuwa yayi sai yaji jiri na neman kada shi.

Direct bathroom ya shiga ya d’auro alwalan sallan azahar, bayan ya fito ne kuma ya shimfud’a sallaya tare da tada Sallah.

Acan gefen Jannart kuwa Koda tabar d’akin nasa, nata d’akin ta wuce, tare dayin alwala tazo tayi sallah.

Bayan ta idar da sallan ne kuma, ta tashi ta fice daga d’akin, direct dakinsa ta nufa Dan ta dashi yayi sallah.

Anutse ta tura kofar dakin ta shiga bakinta d’auke da sallama.

Bayan ta maida kofar dakin ta rufe ne, kuma ta juyo tare da kallon kan gadon.

Ganin gadon babu kowa ne kuma yasa ta, zaro Idanunta tare da k’arasa shigowa cikin dakin.

Karab kuwa Idanunta suka sauk’a akansa, Inda yake kwance akan sallaya, ya lumshe kyawawan idanunsa.

Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e tare da k’arasowa inda yake kwancen.
Batare da tunanin komai ba ta zauna agefensa, tare da sauk’e idanunta akan lafaffen cikinsa.

“Naan.”

Takira sunansa in a silent voice din daya sashi bud’e idanunsa ahankali ya watsa mata su a narke.

Fuskarta tad’an shagwabe, cikin kuma son lallab’asa tace.

“Please Naan na kawo maka abinci?.”

Yanayin yanda ta kare maganan cikin sakalci ne, yasa Rayyern din zubawa lips dinta idanu.

Yana mejin wani abu nayi masa yawo acikin jikinsa.

“Naan. ”
Jannart din ta sake kiran sunansa, da murya mai kamada rad’a.

“Ummmmmmmmm.”

Ya amsa mata da thesame irin muryar da ta kirasa.

“Na kawo maka abinci please.”

Ta sake maimaita tambayar.

Kansa kawai ya iya gyad’a mata alaman.
“Eh.”
Saboda zuwanta kusa dashi yanzun, duk ya sashi jin mutuwar jiki da kasala.

Jannart kuwa Ganin ya bukaci abincin ne, ya sakata sakin murmushi tare da tashi ta fice daga cikin dakin.

Kaitsaye kitchine ta wuce, abincin da Dr. Sulaiman ya kawo musu d’azu, ta zuba a plate, bayan ta d’auko goran ruwa ne kuma ta dawo dakin.

Duk da cewar yana kwance amma agabansa, ta ajiye plate din, tare da kallonsa Cikin kulawa tace.

“Naan tashi kaci, please koba mai yawa ba kaci kadan kaji.”

Tayi maganan tana me zama akusa da kafafunsa.

Shikuwa Rayyern tashi yayi ya zauna.
Tare da jawo plate din abincin kasalance ya soma ci.

Ganin yafara cin abincinne kuma yasa, Jannart daukar wayarta ta soma dannawa.

Ahankali yake tauna abincin abakinsa, yana me Kallon y’an yatsun hannunta dake kan wayarta, ahaka har ya d’anji ya koshi, duk da bai ci abincin da yawa ba, amma haka yaji ya koshi, ruwa yasha tare da sake maida bayansa ya jingina da jikin drawer.

Jannart kuwa fahimtar ya koshi ne yasa ta tartare wajen, bayan takai plate din kitchine ne kuma ta dawo dakin.

Again kusa dashi ta sake dawowa ta zauna, tare da d’an mik’e k’afafunta.

Wanda hakanne kuma ya bashi daman, sauke idanunsa akan legs dinta.
Kallon legs din nata yake Ahankali har ya gangaro zuwa kan lafaffen ciki da kuma kirjinta.

Ahankali ya saki wani Murmushi ta gefen bakinsa, wanda babu wanda zaisan yayi sai shid’in.

“Uhummm wai gadina takeyi kenan?.”

Ya fad’i haka acikin zuciyarsa, tare da Kallon fuskarta.

Itakuwa Jannart hankalin ta duk ya tafi, akan game din da yakeyi.
Kwata kwata tama manta cewar a gabansa take, Ahankali take latsa waya tata, tare dasa teeth dinta tana d’an taune lips dinta.

Lips din nata yake kallo yanajin tsikar jikinsa na tashi sosai, batare kuma daya san dalilin hakan ba.

Ahankali ya lumshe idanunsa tare da hade hannayensa ya rungume su akirjinsa.

Ahaka suka kasance har tsawon awa d’aya, kafun wani dan guntun bacci ya kuma daukar Rayyern din, saboda maganin daya sha bai gama sake shi ba.

Jannart dake gefensa kuwa game take tayi, time to time amma takan d’ago Kai ta kalleshi.


5:30 pm

Fitowarta kenan daga cikin bedroom dinta, Inda ta sanja shigar dake jikinta, zuwa riga da wando na Pallazo, sai kuma wani babban jacket mai kaman suit da ta d’aura akan kayan.

Tayi kyau sosai sai faman baza kamshi takeyi.

Isowar ta cikin falon kuwa yayi dai-dai da knocking din kofar falon da aka somayi.

Da d’an sassarfa ta k’arasa ta bud’e kofar, ganin su Dr Sulaiman ne kuma yasa ta fad’ad’a fari’arta, had’e dayi musu iso suka k’araso cikin falon.

Bayan sun zauna ne kuma ta wuce dakin Rayyern din, dan sanar masa da zuwan su Dr. Sulaiman din.

Koda ta shiga akwance ta sameshi, Yayinda shima yayi wanka ya kuma sauya shigar dake jikinsa.

“Naan.”

Takira sunansa ahankali.

Juyawa yayi ya kalleta, saidai bai amsa taba, saima tsaida idanunsa da yayi akan shigar dake jikinta, wanda yayi mata kyau sosai.

“Su Dr Sulaiman sunzo.”
Ta fad’a itama tana me kallonsa.

Idanunsa ya d’an lumshe, kana ahankali ya yunkura ya tashi, cikin dan kuzarin da yake dashi ya Mike tsaye.

Da tafiyarsa wacce yakeyi ahankali, ya nufi falon, Yayinda ita kuwa Jannart ke biye dashi abaya.

Ahankali take nazartar sa, saboda ta fahimci har yanzu bashi da wani isashshen karfi ajikinsa.

Fitowarsu Cikin falonne ne kuma yasa, su Dr. Sulaiman din kallonsa, lokaci daya duk ya sanja, yar rama ta bayyana ajikinsa, saidai kuma ya kara haske.

K’arasowa cikin falon yayi ya zauna, tare da mikawa su Dr. Sulaiman din hannu suka gaisa.

“Dr. Ya jiki?”
Dr. Sadiq ya tambaya.

Kansa ya gyad’a alaman da sauki, saboda baya wani son magana sosai.

Dukansu ya jiki sukayi masa, inda yayi kokarin amsa musu, bayan sun gaisa dinne kuma, ya kalli Dr. Sulaiman tare da tambayarsa, yau me akayi awajen meeting.

Ajiyar zuciya Dr Sulaiman ya sauke, tare da Dan gyara zama yace.

“Test mukayi akan surgery, amma dai next week zamuyi original test akan dashen zuciya, then na fad’awa Sauran manyan Doctors din, duk abunda mukayi kuma sun tura ma ta email dinka, muna saran Allah ya baka lafiya before next week.”

“Ameen.”
Ya fada yana me jinjina kansa, saboda shi kansa zaizo ace baiyi missing ko daya na daga cikin abunda ya kawo sa ba, musamman dashen zuciyan.

Haka dai suka Dan tab’a hira, Ganin lokacin sallan magriba ya kusa ne kuma yasa, su Dr. Sulaiman din tashi suka tafi.

Tun kafun su tafin kuwa Jannart ta koma d’akinta.

Shikuwa bathroom ya wuce ya d’auro alwala, tare da fitowa ya tada sallah, saboda bazai tab’a iya zuwa masallaci ba, dama ace masallacin na kusa ne.

Bayan ya idar da sallan ne kuma Yana nan zaune akan sallaya, Wayarsa ta soma k’ara, Ahankali ya kalli wayar ganin sunan Barrister Kabeer na yawo akan screen din wayar ne, kuma ya sashi picking call din, bakinsa d’auke da sallama ya kara wayar akan kunnensa.

Barrister Kabir dake kan layi kuwa, Jin an d’aga wayarne yasa shi, amsa sallaman cikin sakin fuska yace.

“Rayyern barka da dare ya jikin naka?”

“Alhamdulillah Barrister jikina yayi sauki, ya fama da Jama’a.”

Rayyern din ya amsawa Abba Kabir din atausashe.

Dai-dai lokacin kuma Jannart ta bud’e kofar d’akin ta shigo, hannunta rike da wani cup, wanda ta zuba zuma aciki.

D’ago idanunsa yayi ya kalleta.

Yayinda daga can b’angaren kuwa Barrister Kabir cewa yayi.

“Masha Allah Allah ya kara sauki, ya kumasa zakkan jikine, d’azu mukayi waya da Abbanku shine yake shaidamin rashin lafiyar taka, Allah ya kara afuwa.”

“Ameen Summa Ameen Barrister nagode.”

Still ya kuma fada atausashe.

“Ba komai Rayyern ka gaishe min da Jannart.”
Barrister Kabir din ya fad’i haka da niyar katse kiran.

Kai Rayyern din ya jinjina, batare kuma daya bari Abba Kabir din ya katse kiran ba yace.

“Ga tanan ma bari na bata ku gaisa.”

Yana fad’an haka ya mik’awa Jannart, da ta zauna agefensa wayar.

Saurin d’agowa tayi ta kalleshi, Ganin irin Kallon da takeyi masa dinne kuma yasa shi, kawar da kansa gefe, cikin yin k’asa da murya yace.

“Abban ki ne.”

Da sauri ta karb’i wayan tare da karawa akunnenta, cikin jin dadi da samun nutsuwar zuciya tace.

“Abbana.”

Murmushi Barrister Kabir din yayi had’e da cewa.

“Na’am Jannart dina, ya kike ya mai jiki?”

Idanunta ta d’an lumshe cikin jin dadi tace.
“Alhamdulillah Abba jikinsa da sauki sosai, kaifa Abba ya kake yasu Aunty Dijat da Momy da Daddy na.”

Ta k’are maganan cikin raunin murya, saboda tunawa da Dadynta da tayi, wanda akullum kewarsa dana gidan nasu ke damunta.

Jin rauni acikin muryar Jannart dinne kuma, yasa Abba Kabir jajircewa, cikin son bata karfin guiwa yace.

“Duk Suna lapia Jannart, Dadynki ma yana lafiya haka su Momy da Abdull, kowa da kowa yana lafiya, kada kice zaki saka damuwa aranki kinji, ki kula kawai da mijinki saboda ayanzu, yafi kowa muhimmanci agareki, shine Garkuwanki, haka kuma shine Jagora akan komai na rayuwarki.”

Idanunta da suka cika da k’walla ta d’an lumshe, murya asanyaye tace.

“To Abba nagode.”

“Yauwa Jannart Dan Allah ki kula da kanki kinji, kada ki bari damuwar wasu tayi tasiri acikin zuciyarki, domin su ba Lallai ya zamana kamar yanda kike jinsu aranki, haka suma sukejinki ba, duniya ce Jannart akwai abubuwa da yawa wanda baki sani ba, saboda haka kada kibar damuwa tayi tasiri acikin zuciyarki ta hanaki kula da mijinki wanda al'jannarki ke karkashin digadiginsa.”

Barrister Kabir din ya fada cike dason bata confidence.

Itakam kanta kawai ta jinjina, batare da ta fahimci maganganun Barrister Kabir din ba, wanda ya fad’a mata su adunk’ule.

Wanda kuma hatta Rayyern dake gefe, saida ya fahimci wani abu acikin kalaman, kasancewar wayan an sa call volume d’inta duka shiyasa, sometimes Idan kana waya, akeji Koda kuwa baka sata a ansakuwa ba.

Ahankali ta zare wayan daga kunnenta, tare da d’an zamewa ta kwantar da kanta ajikin hannun kujera.
Idanunta ta lumshe batare kuma da ta mik’a wa Rayyern din wayar ba.

Rayyern kuwa shima d’an mirginawa yayi, ya kwanta akan sallayan.

Wanda hakanne kuma ya bashi daman facing dinta, inda ya sauke idanunsa akan kirjinta, saboda yau d’inma haka take zaune, bata saka bra ba, shiyasa yake iya hango shatin nipples dinta, da suke tsaitsaye tamkar zasu tsone masa idanu.

Ganin ta bud’e Idanunta ne kuma yasashi, saurin kawar da kansa gefe.

Itakuwa Jannart ba tare da sanin ita yake kallo ba, ta tashi tsaye, direct gaban tv plasman dake cikin bedroom din ta nufa.

Bayan ta kunna tv’n ne kuma ta dawo ta zauna.
Tare da maida hankalinta ga tv’n, saboda wata tasha da taga suna haska indian film, me suna
(Ashquie).

Anutse take Kallon film din, wanda take da yakinin cewar zai rage mata kewa.

Jin sautin film din ne kuma yasa, Rayyern ma juyawa ya kalli tv’n.

Almost 30mn suka d’auka kowannensu hankalinsa, nakan film din.

Dai-dai anfara wak’an Tumhiho ne kuma, Atare duk suka d’an lumshe idanunsu.
Saboda yanda amo da sautin wakan ya fara dukan zuk’atansu.
Musamman alokacin da stars din, suka samu keb’ancewa daga ruwan sama.
Kamar yanda suka lumshe idanun nasu atare, Atare suka kuma bud’ewa.

Ahankali Jannart ta d’an juya da niyar Kallon Rayyern din, karab kuwa idanunsu suka sauk’a acikin na juna.

Idanun nasa masu kalan bacci da suke a narke ya d’an lumshe, tare kuma da d’an turo bakinsa gaba, cikin yanayi mai kama da na shagwab’a cike da kasala yace.

“Meye kike wani kallona, ki kalli abunda kika saka mana.”

D’an juyawa tayi ta kalli tv,n saidai da sauri ta d’auke idanunta, saboda wani gani da idanun nata yayi mata, inda Arjay da Arohi suka fad’a cikin wata duniya ta daban.

sake yin kasa da Idanunta tayi, akasalance kuma cikin yanayin shagwab’a, kamar yanda yayi mata tace.

“To ni ai bansan na kalleka ba, kuma ma ai dole ne na duba lafiyarka.”

Idanun nasa dake ci gaba da sanja launi ya lumshe tare dayin wani narkekken mik’an da yasa D dinsa miƙewa sama, da wani irin yanayin dashi kansa baisan yana dashi ba yace.

“Why gadi na kikeyi ne?”

“Ummm dole ne ai, saboda haka nema nazo nan.
Tunda abinda ya kawoni k’asar ma kenan, can you imagine idan da ka suma jiya bana nan, you think me zai faru.”

Tayi maganan tana cije labb’anta, tare da karyar da wuyanta gefe.

Hakan da tayi dinne kuma ya sashi zuba mata ido, domin sai ya ganta like babies, Yayinda daga cikin jikinsa kuwa shi kad’ai yasan me yakeji, akan kowanne shagwab’arta, to mimmik’ewan jijiyoyin jikinsa ne.

D’an d’ago Kanta tayi ta kalleshi, Ganin yanda ya kura mata idone kuma yasa ta, turo baki kamar yanda yayi mata d’azun tace.

“Nima me yasa kake kallona?”

Kansa ya d’an girgiza, lokaci daya kuma ya janye idanunsa daga kallonta, tare da maidasu kan tv, yana kallon yanda taurarin film din ke romancing juna, acikin blanket d’aya hakan yasa ya karajin wani irin azabebben kasala mai narka jiki da zuciya idanunshi duk suka juye suka narke kamar d’an maye.

Murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Na kalla ɗin, ai halal na gani don na biya sadaki”.
Yayi mgnar ta yadda yasan bazata jiba.

Ita kuwa Jannart kasa sake d’agowa ta kalli tv’n ma tayi, saboda abunda akeyi din ya wuce tunaninta da saninta.

Kofin zumanta ta d’auka tare da soma lasa ahankali, bata d’ago Kanta ba kuwa, har saida taji an wuce wak’an.

After 1hour.

“Zanyi wanka.”

Rayyern din ya fada ahankali batare kuma daya bude, fitinannun idanunsa dake lumshe ba, domin film din da ya gani yanzun duk yasa, mood d’insu na safiyar yau ya dawo masa sabo jinsa yakeyi tamkar ya hayewa babu.

Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa Jannart, juyowa ta kalleshi, saidai kuma ganin ba ita yake kallo bane, yasa ta cewa.
“To.”
Ahankali ta tashi ta wuce bathroom d’insa.

Ruwan wanka mai d’an d’umi ta had’a masa, Koda ta fito kallonsa tayi tare da cewa.

“Na had’a maka ruwa a bathtub.”

Kansa ya jinjina hade da mikewa tsaye, da d’an kuzarin daya rage masa din ya wuce toilet.

Itakuwa Jannart drawer’n sa ta bud’e, hade da ciro masa wasu kayan bacci masu taushi ta ajiye masa akan gado.

Ganin har zuwa lokacin bai fito bane, kuma yasa ta wuce nata d’akin, inda itama ta sake sabon wanka.

Rayyern kuwa Koda ya fito a wankan, Ganin bata cikin dakinne yasa shi zare towel din jikinsa kamar yadda ya yakeyi a lokuta da dama, dashi ya tsane ruwan jikinsa ka ya shirya kansa anutse.

Bayan yasa kayanne kuma ya koma kan gado ya zauna.


Acan d’akin Jannart kuwa, shirya kanta tayi, cikin wani sleeping gown mai adon net, duk da yana da kauri, amma hakan bai hanashi yi mata yaro yaro ajiki ba.
Sosai rigar tayi mata k’yau, saidai ganin yanda breast dinta, ya bayyana karara ne yasa ta d’aura jacket akan rigar.

Duk tunaninta ayanzun ya tafi ne akan yanda zata kwana ad’akin Rayyern din, saboda batajin zata iya barinsa ya kwana shi kad’ai.

Kashe wutan dakin nata tayi, tare da jawo kofar dakin ta rufe, kaitsaye ta nufi d’aki nasa...!


*Albishirinku! Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login