Showing 27001 words to 30000 words out of 114708 words

Chapter 10 - TUBALI book 2 complete hausa novel

18 Sep 2024

19380

sakawa muryarsa, kana shima cikin sanyi yace.

“Ameen summa Ameen, ai Riyyam kam babu wani rigiman da yake yi mana, harma mun saba dashi kwannan yana ta cewa kin matsa ya komo mu kuma bamu son rabuwa dashi.”

Murmushi Mammyn tayi, cikin kuma karfin hali da danne bugun zuciyar da takeji, tace.

“Shikenan to Baba Maud’o ahuta gajiya.”

“Yauwa.”
Baba Maud’on ya amsa, tare da zare wayar akan kunnensa, cikin sanyi da kuma wani irin tunani dake dukan, kwakwalwarsa ya mikawa Riyyam nsra wayan.

Karb’an wayan Riyyam-nsra yayi tare da Karawa akan kunnensa.

Jin muryar Riyyam dinne kuma yasa, Mammy sauke wani irin nannauyar Ajiyar zuciya.

Cikin sanyi tace.

“Riyyam ka had’ani video call da Rayyern, inason naga ya yanayin jikin nasa.”

“To Mammy zan hadaku amma maybe sai gobe, saboda nasan yanzu haka yana sama, kuma Idan magriba ta kusa bayason yawan magana.”
Riyyam din ya fada atausashe.

Daga can b’angaren kuwa Kai Mammy ta jinjina, tare da cewa.

“Shikenan to badamuwa Allah ya kaimu goben.”

“Ameen”
Riyyam din ya amsa kana sukayi sallama da Mamyn.

Duk abunnan da sukeyi kuwa Jannart na kallonsu, saboda gaba daya hankalinta ya tafi garesu ne ma, yasa har yanzun take nan bata tafi ba.

Shikuwa Rayyern tuni ya shanye kunun da ta zuba masa din tas.
Ganin bata da niyan kara masa ne kuma yasa shi, dagowa ya kalleta.

Akaron farko kenan daya tsaya ya k’are mata kallo, idanunsa ya dan tsayar akan fuskarta, saboda yanda yaga hankalinta ya tafi izuwa wani waje na daban.

Ajiye cup din dake hannun nasa yayi, Karan ajiye cup dinnasa ne kuma yasa hankalinta dawowa garesa.

Ahankali ta juyo da kanta zuwa garesa, karab kuwa idanunsu suka sarke acikin na juna.

Sunkuyar da kanta k’asa tayi, tare da sauke numfashi, cikin silent voice dinta tace.

“Nak’ara maka ne?”

Kansa ya d’an girgiza mata, tare da lumshe idanunsa, cikin wani irin yanayin daya saka zuciyarta harbawa yace.

“Um um nakoshi.” yayi mgnar yana jin dadi bakinsa yayi masa wasai yawunsa ya sinke alamar dandanon bakinsa zai dawo.

Kallonsa tayi, haka kuma shid’inma.

Kasa tayi da Idanunta tare da matsowa ta durk’usa, tray din ta ke kokarin dauka.

Dan kusancin da sukayi ne kuma yasa, daddad’an kamshin turarenta ratsa cikin hancinsa.

Idanunsa ya dan lumshe, Yayinda itakuwa tray din ta dauka Anutse ta juya ta tafi.


Kaitsaye kasa ta sauka, bayan takai kayan kitchine ne kuma ta wuce dakinta.

Shikuwa Rayyern kiran Sallan magriba ne ya tadashi awajen.

Washegari.

Yau dinma kunun da Jannart din tayi masa jiya ya kuma sha, sai kuma abu mai romo da Mamy tasa ta dafa masa, babu laifi kuma yaci sosai.


After 3days.

Mamy ce tsaye agefensa, Yayinda shikuwa ke zaune akan daya daga cikin kujerun falon.

Murmushi Mamyn tayi tare da dubansa cikin danjin dadi.

Tace.

“Masha Allah Babana Lallai jiki yayi sauki, tunda har ka iya fitowa falo.”

Murmushi ya d’anyi tare da Kallon Mamyn nasa, cikin sanyi yace.

“Mamy yunwa nakeji sosai, kuma nafison abu mai dan tsami, please Mamy roasted fish da ruwan lemon tsami nakeso, ko kuma miyan da akayi ranan nan pls Mamy.”

Murmushi Mamyn tayi tare da cewa.

“To Rayyern amma ni bansan yanda akeyin miyan ba, rannan ma bani nayi ba Jannart ce tayi, amma bari na turo maka ita saikayi mata bayani.”

Fuskarsa yadan kwabe cikin shagwaba yace.


“Eyyah Mamy kifada mata mana, dole sai ni?”

“Eh mana bakaine kakeso ba.”

Mamyn ta fad’a tana me nufar dakin Jannart.

Ramadan dake zaune agefe kuwa, Kallon Hamman nasa yayi, tare da mik’o masa magungunan daya b’are.

Cikin kulawa yace.

“Please Hamma Rayyern karb’a maganinka kasha.”

Fuskarsa yadan yamutsa, kamar zaice a’a sai kuma ya karba yasha.

Bayan yasha maganin ne kuma Ramadan ya Mike ya tafi, domin dama hospital zai tafi, ya tsaya bawa Hamman nasa maganine.

Already Abba kuma dama ya tafi company, Riyyam-nsra kuwa yana waje .


Jannart kuwa dake falon ta zaune take, inda tayi kyau cikin wani fitted gown na maroon lace dake jikinta, sosai rigar tabi jikinta ta zauna, saboda yanda dinkin ya fita sosai.

Bak’aramin kyau yau Jannart din tayi ba, musamman da ta watsa jelan gashinta haka bata kitseshiba, tare dasa dan siririn mayafi daga kanta zuwa kirjinta.

Shigowar Mamy ne kuma yasa ta d’agowa, fuskarta dauke da murmushi.

Itama Mamyn murmushi tayi, tare kuma da Kallon Jannart din Cikin kulawa tace.

“Jannart kije mijinki yana kiranki.”

Kai Jannart din ta d’an sunkuyar kasa, cikin sanyi kuma tace.

“To.”

Juyawa Mamyn tayi ta tafi, Ganin hakanne kuma yasa Jannart din mikewa, Cikin yanayin nutsuwarta ta nufi part din nasa.


Ahankali ta murd’a handle din kofar ta shiga, bakinta dauke da sallama.

Saidai kuma dan ja baya tayi, ganinsa da tayi yana waya, hakan yasa ta matsawa jikin kujera ta d’an zauna, wanda hakan yasa suka zama suna fuskantar juna.

Ahankali ta dan saci kallonsa, musamman yanda taga yayi kyau cikin shigar riga da wandon DG dake jikinsa.


Ahankali ya ajiye wayar tare da d’ago kansa ya kalleta.

K’asa tayi da Idanunta, cikin sanyi tace.

“Ina kwana.”

Idanunsa ya sauke akan labbanta zuwa kan kirjinta, wanda dinkin jikin nata ya masifar fitar da shape din samansu.

Kauda kansa yayi batare da ya iya amsa mata ba


Itakuwa Jannart jin bai amsa mata dinbane yasa ta cewa.

“Ya jiki.”


“Da sauki.”

Ya amsa mata da wani irin murya, wanda yasa ta dago ta kalleshi.


Ahankali kuma tace.

“Gani Mamy tace kana kira na.”


Idanunsa ya dan marairaice cikin sanyin murya mai hade da zallan shagwab’a yace.

“Yunwa nakeji sosai, kibani abinci, but mai dan tsami kawai kinji....”

Yaja maganar tasa cikin wani irin yanayi, tare dasa hannunsa ya shafa cikinsa.

Hakan kuwa shiya sanya Jannart ta d’ago Kai ta kalleshi, lokaci daya kuma taji wani irin tausayinsa ya cika mata zuciya.

Ahankali Cikin yanayin ta itama dake kama da shagwab’a tace.


“To meye kakeso? Miya ko kuma abinci?.”

Idanunsa dake lumshewa ya rufe, tare da bud’e labb’an sa ahankali yace.


“I don’t know kimin komai kawai, ko miyan da kika tab’ayi ranan mai ɗan sami.”

“To.” Tace asanyaye tare da juyawa ta nufi hanyar fita.


Koda ta fito daga dakin nasa, Anutse ta soma sauka daga kan steps din.

Dai-dai lokacin kuma Riyyam-nsra yake haurowa saman, hannunsa rike da waya.

Ganin Jannart dinne kuma yasa shi sakin murmushi, Cikin kulawa yace.

“Good morning My Aunty ya jikin Hamma Rayyern.”

Murmushi tayi tare da dubansa, cikin sakin fuska tace.

“Jikinsa da sauki Riyyam, yanzu ma na sameshi afalo.”

Murmushi Riyyam din yayi tare da cewa.

“Masha Allah, bari naje na sameshi.”

Riyyam din ya fada, Yayinda ita kuwa Jannart kaitsaye kasa ta wuce, inda ta nufi kitchine Dan fara had’a masa abunda zaici.

Riyyam kuwa direct falon ya wuce, yana zuwa zuwa kuwa ya zauna akusa da Hamman nasa.

Tare da dan rankwafar dakai cikin sanyi, yace.

“Hamma Rayyern Mammy tanason yin magana dakai, tace kuyi video call saboda taga ya jikin naka, na kirata please?”

Idanunsa ya dan lumshe, akasalance kuma ya d’an gyad’awa Riyyam din Kai alaman “Eh.”


Murmushi Riyyam din yayi cikin, Jin dadi kuma ya zaro wayartasa tare da dannawa numbern Mammy kira video call.

Ring kadan kuwa wayar tayi Mammy ta d’aga.

Tana d’agawa kuwa Riyyam yayi murmushi, tare da Kallon Mammyn nasa Cikin kulawa yace.

“Mammyna Barka da safiya, ga Hamma Rayyern dinnan ku gaisa.”

Ya k’are maganan yana me mik’awa Rayyern din wayar.

Kasancewar kuma kan Rayyern din yana dan jingine ne yasa, Riyyam cewa.

“Hamma Rayyern ga wayan.”

Ahankali ya d’an juyo tare da kai dubansa ga fuskar wayar, wani irin bugawa yaji zuciyarsa tayi da karfi, wanda hakan ya sashi zabura tare da yunkurawa ya gyara zamansa, inda ya sauke ganinsa akan fuskar.........!




Littafin TUBALI dai na kuɗine ko kin gansa a wasu group ɗin na satane

By
*GARKUWAR FULANI*
22/12/2021, 19:45 - 🥰🥰: Tare da fuskantarsu dukansu, cikin dan nisawa yace.

“Gaba d’aya matsalarmu a kullum akan Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara ne, wanda kuma ni kaina bani da iko, ko wani matsayi da zan iya dakatar dashi akan abunda ya saka agaba, saboda duk wani k’a’ida da dokokin da akebi ya bisu, Idan kuma har nace zan wargaza masa tsari.
To tabbas zai iya Kai k’arata wajen na sama dani, hakan kuma zai iya sawa na rasa aikina, yaron ya wuce duk yanda muke tunani, kowacce hanya da zamu b’ullo masa ya sani, kansa yana ja sosai, babban abunda na lura dashi kuma shine, kwata kwata baya tsoron magautansa yaron yana nan Tamkar a haifeshi ne domin daukan fansa!!!.”

Numfashi mai nauyi duk suka ja, musamman Alhaji Idi Sale Dakata wanda gaba daya abubuwa suka had’e masa.

Ga zafin b’atan Jannart ga kuma, na wannan shegen yaron Dr. Rayyern.
Barrister Kabir kuwa, kalaman Alhaji Bala Tambari na karshe yaketa nanatawa a zuciyarshi don son fahimtar wani abin.

Haka dai taron nasu ya watse gaba d’aya zuciyar Alhaji Idi, da kuma na Dr. Lukman Alhaji Abdu Tababa babu dadi, kowannensu kuma saboda Rayyern.

Dr. Lukman din, da kuma Alhaji Abdu Tababa ne suka had’a hanya wajen tafiya, haka ma Alhaji Bala Tambari shima tafiya yayi.

Hakan yasa falon ya rage daga, Daddy sai Barrister Kabir.

Juyowa Alhaji Idi Sale Dakata’n yayi? Ya fuskanci Barrister Kabir, cikin kuma nuna halin damuwa yace.

“Kabir ayanzu babu abunda yake damuna, kamar b’acewar Jannart, har yanzu babu wani labari, kwata kwata ayanzu ma ba batun companyn Rayyern Mai-nasara bane ke damuna, matsalar b’acewar Jannart itace ke damuna hukuma suna iya yinsu abin yaci tura.”

Afakaice kuma ta k’asan idanu, Barrister Kabir ya kalli Yayan nasa, tare da d’an ya mutsa fuskarsa.

Wanda kuma daga wajen Alhaji Idi Sale Dakata’n ma hakan yake, domin kuwa bayan yayi maganar shima, ta k’asan idanu, ya kalli K’anin nasa, tare da sakin wani Shu’umin murmushin, da shi kad’ai yasan ma’anar yinsa.

Barrister Kabir kuwa, mur yasha tare da saka fuskar tsare gida, irin tasu ta lawyoyi, saboda shima akwai wani abu daya gano amatsayinsa na lawyer.

Shi yanayiwa Barrister Kabir kallon biri, shi kuwa Barrister Kabir yanayiwa yayan nasa kallon Ayaba.

Koda suka fito daga d’akin taron Alhaji Idi Sale Dakata’n, main falon gidan suka dawo, inda suka samu Momy ta gama had’a abinci.

Sama sama haka Barrister Kabir yaci abincin, bayan sun kammala ne kuma yayiwa Yayan nasa sallama, kaitsaye kuma daga gidan Alhaji Idi Sale Dakata’n, gidansa ya nufa.

Koda ya isa gidan afalo ya samu Dijat.

Hira kadan suka tab’a kana kaitsaye ya wuce bedroom d’insa.
Key ya sawa kofar bedroom din, tare da komawa ya zauna, bayan ya d’auko wasu takardu.

Anutse yake wargaza takardun, tare da Ware wasu daga ciki yana duddubawa.
D’ago wata takarda da yayi ne kuma, ya sashi tsurawa rubutu, da kuma hoton passport din dake jiki idanu.

*** ***

Almost 4weeks kenan yanzu da, dawowar Rayyern daga China, Alhamdulillah kuma jikinsa ya warware.

Bisa taimakon Ramadan da kuma Jannart, way’anda suke kula da shan maganinsa.

Hakan yasa ciwon cikin nasa yayi sauki, ya kuma gama samun karfin jikinsa, duk da cewar time to time ya kanji, ciwon cikin na tashi masa, amma da yasha magani yake jin sauki.

Ahankali yake sauk’owa daga kan matattakalan falon, inda yayi kyau cikin shigar Ash colour suit dake jikinsa.

Yayinda hannunsa ke rik’e da briefcase, da alama kuma aiki zaije.
Ya dawo asalin Rayyern d’insa, big man wanda bai wani cika son wasa ba, wani Rama da yawan kasalan da yakeji ada, duk sun kama gabansu.

Mamy dake tsaye akan dining table, jin alaman takun takalmansa ne yasa, ta d’ago kanta ta kalleshi.

Ganin yanda yayi kyau ne kuma, yasa Mamyn sakin murmushi, Cikin kulawa tace.

“Babana yadai, yau na ganka cikin shiri haka fita zakayi ne?”

Kansa ya jinjina, adaidai lokacin da yake gama sauk’owa daga kan steps din yace.

“Eh Mamy yau zanje company.”

Murmushin dake kan fuskar Mamy ne ya fad’ad’a, cikin jin dadi tace.

“Ah Lallai Masha Allah Babana ya samu sauk’i, amma Ina fatan kanajin karfin jikinka sosai.”

Idanunsa ya d’an lumshe tare da jinjina mata kai alaman. “Eh.”

“To kayi breakfast tukun kafun ka tafi.”

Mamyn ta fad’a tana me nuna masa kujera, tare dayi masa alama akan ya zauna.

Fuskarsa ya d’an shagwab’e, kamar zaice a’a kuma saiya zauna.

Dai-dai lokacin kuwa Jannart ta shigo cikin falon, sanye take da riga da wando ajikinta, saidai wandon irin mai fad’in nan ne, haka ma rigar Wacce take da igiyan d’aurewa, hakan ne kuma yasa lafaffen cikinta bayyana, saboda yanda ta d’aureshi da igiyan, haka ma shape din cikin nata ya bayyana sosai.

Kasancewar kuma kayan nada kalan baki, shiyasa ta yafa siririn mayafi daga kanta zuwa wuyanta.

Sassanyan kamshi take bazawa, shigowarta cikin falonne kuma yasa shi sauk’e idanunsa akanta.

Mamy kuwa Ganin Jannart dinne yasa Cikin kulawa tace.

“Yauwa Jannart yi saving din mijinki mana, yana sauri zai tafi wajen aiki ne.”

Kai Jannart din ta d’an sunkuyar k’asa, cikin yanayin nutsuwa tace.

“To Mamy.”

Kaitsaye dining table din da yake zaune ta nufa, saidai koda wasa bata bari sun had’a idanu ba.

Koda ta k’arasa inda yake, plate ta d’auka tare da bud’e food flask, cikin sanyin muryar dake bayyana nutsuwarta tace.

“Ina kwana.”

“Lafiya.”
Ya amsa mata atak’aice, tare da zubawa kyawawan fararen yatsunta idanu.

Abincin ta zuba masa, bayan ta kammala ne kuma ta turo masa plate din gabansa.

Tare da saka masa apple juice din da ta had’a, acikin wani d’an glass cup.

Ahankali ya soma cin abincin, tare kuma da dan lullumshe idanunsa, saboda yanda yake jin kamshinta na shiga hancinsa.

Jannart kuwa Ganin ya fara cin Abincin ne, yasa ta wucewa kaitsaye ta nufi sama, Dan d’auko maganinsa.

Ahankali ta tura kofar d’akin ta shiga.
Lumshe Idanunta tayi saboda, wani irin kamshi daya bugeta.
Ga kuma sanyin ac dake busa ko ina.

Dan bud’e Idanunta tayi, tare da soma bin ko ina dake cikin dakin da kallo, komai nasa need babu alaman datti, duk da cewar ya kwana acikin dakin, amma saida ya gyara komai kafun ya fita.

Hakanan kawai ta samu kanta da sakin murmushi, kaitsaye kuma cikin nutsuwa, ta wuce ta dauko magungunan nasa.

Koda ta sauk’o k’asa harya kammala cin abincin nasa, saidai juice dinne da bai gama shaba, wanda kuma yake sipping d’insa ahankali.

K’arasowa kan dining table din tayi, Anutse ta b’are magungunan tare kuma da zuba su acikin tafin hannunta.

Kallonsa ta d’anyi, tare da mik’a masa magungunan, alaman ya karb’a.

D’ago idanunsa yayi ya kalleta, cikin yanayinsa daya saba yi mata magana yace.

“Ni yaro ne, da har sai kin b’aremin magani, ni bazan iya dakai na bane akace miki? Sai kiyi ta wani ɗuɗɗuramin magunguna babu ko tausayi”

Idanunta ta d’an janye daga kallonsa, saboda ayanzu babu wani abu nasa da bata sani ba, saikayi masa abu sau goma, amma baya tab’a gani yanzu zai gwatsaleta ta fahimci zarginta yakeyi ma shi.

K’wayoyin idanunta tad’an juya ahankali, sau d’aya kuma cikin sigar lallashi tace.

“Okay I’m sorry take it.”

Hararanta ya d’anyi ta k’asan idanunsa, sanin Mamy na cikin falonne kuma yasa shi, bud’e tafukan hannunsa, Anutse ta zuba masa maganin ahannunsa, gudun kada hannunta da nasa su had’e, tayi hakanne kuma saboda, ita kadai tasan me takeji, aduk sanda ta tuna lokacin da fatar hannunsa ya tab’a nata.

Rayyern kuwa bayan yasha Maganin ne ya mik’e tsaye, tare da d’aukan briefcase d’insa, cikin sauri yace.

“Mamy na tafi saina dawo.”

“A dawo lafiya Allah ya bada sa’a.”

Mamyn ta bashi amsa, Cikin kulawa.

Da “Ameen.”
Ya amsa kana ya sakai ya fice daga cikin falon.

Ganin hakanne kuma yasa Jannart dawowa, kusa da Mamyn ta zauna.

Shikuwa Rayyern yana fita kaitsaye company ya wuce,
Koda yaje kuwa ya samu ma’aikatan nata aiki, kowa na aikinsa kamar yanda ya dace.

Gaba d’aya ma’aikatan sun bada himmansu wajen yin aikin tsakani da Allah.

Domin har anfara har had’a cattoon's din abubuwa, wanda kowanne kwali d’auke yake da sunan tambarin.
MAI-NASARA.

Komai Yayi masa sosai, hakanne ma yasa shi jinjina kansa, kaitsaye kuma ya wuce office d’insa dake nan cikin companyn.

Wasu d’an aikace aikace yayi, bayan ya kammala ne kuma ya fito, kaitsaye hospital d’insa ya wuce.

Bashi ne ya dawo gidan ba kuwa sai k’arfe 10:00 pm dai dai.
Hakan ya faru ne kuma saboda tsayawa da yayi, yiwa wata operation, baya ga haka kuma, ya tarawa kansa aiki sosai, wannan dalilin yasa shi tsayawa, ya d’an rage ayyukan.

K’asa k’asa ya danna Horn din motar tasa, cikin abunda bai wuce mintuna 2 ba kuwa, aka wangale masa gate din gidan.

Anutse ya tura hancin motar ciki, bayan yayi parking motar ne kuma ya fito.

Tare da Kallon Baba Maud’o wanda shine ya bud’e masa gate din.

“Baba Maud’o da kanka, ai daka bari na fito na bud’e, sam banaso naga kana wahalar da kanka, saudayawa Idan naga kana wannan aikin sai naji duk babu dadi, please Baba Maud’o ka bari.”

Rayyern din ya fad’i haka ga Baba Maud’o cikin tausasa harshe.

Baba Maud’o kuwa Murmushi yayi tare da d’an gyara tsayuwarsa, kana Cikin kulawa yace.

“Haba Rayyern meye na damuwa kuma, bayan kasan hakan aikina ne, kuma gashi Ari yayi bacci shiyasa.”

Fuska Rayyern din ya d’an kwab’e, hade da karyar da wuyansa yace.

“Ni dai Baba Maud’o da gaske banason hakan, banajin dadi Idan naga kana bud’e gate inajin wani nauyi a zuciyata.”

Murmushi Baba Maud’o yayi, tare da komawa wajen zamansa ya zauna.

Ganin hakanne kuma yasa Rayyern d’in ma, matsawa ya zauna akusa da Baba Maud’on.

“D’azu Barrister Kabir yazo dubaka da jiki, amma baisame ka ba, saidai yace agaisheka.”

Baba Maud’o ya fad’a yana me Kallon Rayyern din.

Shikuwa Rayyern Ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da d’an mammatsa hannunsa.
Cikin kuma taushin murya yace.

“Ina amsawa, bari na shiga ciki Baba Maud’o, yau duk na gaji aikin office ya gajiyar dani.”

“To Rayyern Mukwana lafiya.”

Da “Ameen.”
Rayyern din ya amsa, tare da wucewa ciki kaitsaye.

Koda ya shiga main falon nasu babu kowa, hatta su Ramadan da Riyyam nsra duk suna daki.

Kaitsaye kuma shima d’akin nasa ya nufa.
Yana shiga kuwa ya soma rage kayan jikinsa.

Bayan ya shiga toilet yayi wanka ne kuma, ya shirya kansa cikin lallausun kayan bacci.

Bayan yasha Nutri milk ne kuma ya koma kan gado ya kwanta.

Kasancewar agajiye yake ne kuma, yasa yana kwanciya bacci ya d’aukesa.

Washegari.

Arewa24 tv station.

Aunty Fauziya ce ke tafe cikin d’an sauri, saidai kallo d’aya zaka yiwa Fuskarta, ka fahimci cewa tana cikin yanayin damuwa.

Fitowarta kenan kuma daga dakin yad’a labaransu, sukayi Karo da Salman.

Kallonta Salman din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login