
A zaune muke kan wasu kayatattun
-kujeru, cikin wani kayataccen hotel wanda komai na shi ya ke na karau, tamfar madubi ta inda ka juya duk kanka ka ke gani.
A takure nake kwarai a dalilin rashin sabo ban taba samun kaina ba cikin hali makamancin na yau ban taba halartar wuri irin wannan ba, ban taba shiga cikin Jama'a, haka ba don haka na takura kwarai nake ji na a tsuke nake ganin tamfar ni kadai ce a wurin ko kuma gaba daya mutanen da ke hallare a wurin hankalinsu yana wurina ne ni kadai suke kallo.
Karimatu Aliyu ta sake kallona yanayin fuskarta a dan tsuke kadan a dalilin rashin jin dadi a hankali ta ja wani dan munafukin tsaki don gudun kar na baya da ita su ji ta wurin nan fa babu ruwan wani da wani dama kin saki jikinki kinyi walwalarki duk wanda ki ka • gani a nan da harkar da ta kawo shi babu ruwansu dake
Na dan muskuta kadan na gyara zama a kokarin da nake yi na wai ta fahimci na karbi maganar tata na gyara daga takurar da take
ganin ina ciki, amma ba ta gamsu ba sai ma wani takaicin ne ya kara kama ta sai wani zazzare ido ki ke yi kina wani kalle-kalle tanfar mai tsoron kar wani ya zo ta bayan ta ya cafke ta ki dauki cokali mana ki ci abincin da ke gaban naki, na yi maza na kai hannu kan cokali na kamfaci abincin na cika bakina da nufin wai in burgeta girman lomar da nayin ya baiwa Sakinatu Adam takaici har ta ballaka min harara abinda na yi zaton shi ne ya zamo sanadin kwarewata.
Tari-tari mai tsanani na yi ta faman yi tuni idanuwana suka kara firfitowa waje suka yi ja saboda da wahala ga wata 'yar siririyar majina da ke gangarowa daga hanci na mai ruwa-ruwa na yi maza nasa dan siririn gyalen dake kafadata na fyace majinar da iyakacin karfina abinda ya yi dalilin kara jawo hankalin mutane gare mu, kallon da Sakinah ta yi wa gyalen da na yi fyatan dashi shine ya tuna min da cewar shi gyalen da nake yafe da shi din na aro ne.
Babu kuma abinda yafi komai hadari ya kuma ba ni mamaki irin wai duk uban
wahalar nan da na sha akwarewan nan da na yi irin wai mutum daya ne kawai ya samu damar buda bakinshi cikin sanyin muryar tanfar yana tsoron kar na kusa dashi su ji shi ya ce min (sorry) sabanin abinda na saba gani a gidanmu kana kwarewa za'a soma yi maka sannu ana rige-rigen kawo maka ruwa Inna ko tana fadin dan dangwali gishiri ki lasa wani lokaci ma ta hada ma har da dan dundu, amma ba mai cutarwa ba da kyar na samu na wastsake daga kwarewar da nayi sai dai har lokacin ban dawo cikin yanayi na na sosai ba da a gefe daya nake da na takarkare na fyace hancina da kyau in da hali ma in hada har da ka ki don in dan ji saukin barkonon da ya sarke min wuyana ban san me na yi ba sai na ji Karima tana fadin wai ta shiga uku nan da nan na dago kai daga sunkuyo na kalle ta don in ga abinda ya shigar da ita ukun sai na ga ashe wai ni take kallo, ga alama kuma takaicina ne ya ishe ta.
Na ci gaba da abinda nake yi abina cikin zuciyata kuwa ko a jikina in ban da ma mitar da take yi tana fadin wai mutum ya kware har
ya fyace majina ko tari a dole su wai ga 'yan gayu ni ina ruwana?
Zuwana Hotel din (The Garden) a yau shi ne na farko da kafata ta taba taka wani wuri makamancin wannan a rayuwata, ni din sabuwa ce kwarai cikin irin wadannan al'amura saboda kasancewata sabuwar daliba da sakamakon jarrabawar (J.A.M.B) ya yi dalili ko sanadi na rabuwarta da garinta da iyayenta ya kawo ta wani sabon birni, ya ajiye ta a wata babbar Makaranta ya yi dalilin haduwarta da mutane daban-daban sannan ya kulla kawance da mu'amalla tsakaninta da sabbin mutane sabbin kawaye masu dabi'u da al'adu iri daban-daban.
Samun kaina cikin sabuwar makaranta da na yi ba tare da ina ganin uwa da uba ko wasu dangi a kusa dani ba ya tilastani yarda ko yin wasu halaye da dabiu wadanda da can ba nawa ba ne, don dai kawai in tafi cikin sabbin kawayen da nake mu'amalla da su, na samu kaina ne a tsakanin sabbin kawaye guda biyu.
Karimatu Aliyu da Sakinah Adam, ko dama dai can a shekarun yarintata shekaruna na
kuruciya kafin shigowata wannan Makarantar ni din ma'abuciyar kawaye ne da kuma baiwa kawancen muhimmanci, sai dai su wadannan kawayen nawa sun banbanta kwarai da wadanda na saba yi a gida.
A gida na saba yin mu'amalla ne da kawaye da kan bini su kuma karbi umarni daga wurina saboda dalilai guda biyu, dalili na farko shine na fisu wayewa saboda kasancewata ni kadai da na samu halartar makarantar boko a cikin su na biyu kuma ina da abin bayar wa bai yiwuwa wata daga cikinsu ta tako cikin gidanmu ba tare da na samu abinda na dauka na yi mata ihsani da shi ba, to amma a yau sai na samu kaina tsakanin kawaye guda biyu gogaggu masu takama da wayewarsu wadanda kafin in ambata musu shekaruna naji su suna kira wa kansu ashirin da biyu da kuma da uku, sai bayan da suka ji na kira wa kaina shekara goma sha shida da wata biyar ne gaba daya suka yi tsalle suka dawo kan sha tara tara haka nan tazarar dake tsakanina da su tazarce ta ko'ina tazarar shekaru tazarar wayewa, tazarar iya kwalliya tazarar abin kwalliyar tazarar mu'amalla da jama'a kai a komai ma sun dame ni sun shanye, don haka sai na zamo bani da wani ra'ayi nawa na kaina bin umarni kawai nake yi.
Kamar kuma yanda tazarar shekaru da wayewa dama dukkan abubuwan da na ambata a baya suka banbanta mu hakanan yanayin wuraren da muka fito da kuma irin
tarbiyar gidajenmu.
Bari in fara kawo misali da Karimatu Aliyu, wacce nake ganin tankar samun wayaiya ko 'yar gaye irin ta yana da wahala, Karimatu wayaiya ce kwarai, ga ta da iya mu'amala tana da hikima da jan ra'ayin mutum zuwa gare ta, a farkon gamuwata dẳ ita a ranar da na iso Makarantar a lokacin da kallo daya zaka yi min ka fahimci daga ina na fito, tsayawa ta yi tana fada a kaina a dalilin wata ta kalle ni, ta ce wannan da ganinta kauye ne garinsu, ta nuna bacin rai mai yawa da jin wannan maganar har tana fadin to nuna mana wanda asalin shi ba kauye ba ne, a nan
wurin kowa ya raina Kauye kuwa ya raina fari. Wannan abu da Karimatu Aliyu ta yi a kaina, yasa na dan saki jiki da ita har ta ja ni zuwa dakinsu, ta cemin ga gado nan hau dama dakin na mutum uku ne shi kenan mun cika kenan, na ce mata to. Na ajiye 'yar jakata a gefe ina cin abincin da ta yi min sauka dashi mai kamar burabusko sai dai bai yi sak din burabuskon tsaki da Inna kan yi mana a gida ba, sai ga Sakina ta shigo Karimatu ta kalle ta ta ce mata ga yarinya nan na samu mana mai kyau da natsuwa sai kawai mu yi zamanmu maimakon a kawo mana wata da zata dame mu Sakina ta kalle ni a daidai lokacin da take tube kayan jikinta ta ce ke kam ba kya gajiya da ambaton kyau Allah ya taimaki mata da* bai yiwo ki namiji ba da anga zara, Karima ta yi murmushi ta ce ba kyan yarinyar ba ne kawai ya debe ni kina ganinta kin san ta fito ne daga gida na asali ta ce ai ban yi miki musu ba in dai ki ka damen da maganarta ne ko kuma naga za ki sa ta shiga gonata ba zan yarda ba, da sauri ta ce mata haba Sakina, wannan ma me ta sani? Ai nima shi yasa na yi sha'awar kawo ta, ban tanka musu ba har suka yi suka gama sai daga baya ne Sakina ta kallen ta ce min ke buzuwa ce ko? Na girgiza kai na ce, a'a ta ce bafullatana ce? Na sake cewa a'a to ke Shuwa ce na ce uh'uh ta zuba min ido ba ki da yare? Na ce eh, ta ce to madallah ta hau gadonta ta kwanta.
Tun daga wannan lokaci muke da kyakkyawar alaka da Karimatu a duk lokacin da ta ganni cikin yanayin damuwa zata yi abinda zata kwantar min da hankali ko a aji ne ta ganni a takure za ta matso kusa dani ta ce min saki jikinki nan da ki ke gani wuri ne - na 'yanci babu mai shiga harkar wani in ba wanin ne ya gaiyace shi ba in kuwa ta ganni ina yiwa wani abu kallon kauyanci zata ce min wuce ki yi tafiyarki wannan ba wani abu' ba ne da za ki tsaya kallon shi in dai ba so ki ke kema a tsaya a na yi miki kallon mamaki ba.
Karimatu ta fito ne daga cikin gata mai yawan gaske a wurina iyayenta duka biya gata da'yan uwa, masu yawa maza da mata zan iya cewa ma ita din 'yar auta ce a
1 Comments
Leave a Comment
Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search
Categories
-
(2)
-
(3)
-
(4)
-
(8)
-
(12)
-
(1)
-
(11)
-
(0)
Recent Article
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Read More
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
Read More
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
Read More
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
Read More
WORST FOODS FOR BELLY FAT
Read More
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
Read More
WATA FUSKAR CHAPTER 2
Read More
GWARZON SADAUKI PART 4
Read More
WATA FUSKAR CHAPTER 1
Read More
GWARZON SADAUKI PART 3
Read More
29, September 2025
Aisha Abdulazeez
Da kyau Auntynmu