GWARZON SADAUKI PART 4

Mr Novel

  

05 May 2025

378

GWARZON SADAUKI PART 4


 

kawosu sai  hankulansu suka dugunzuma, ba don komai ba sai saboda cikin wannan kuntataccen daki aka kawosu aka kulle.

Tsananin doyin dake tashi a dakin ya sa Insam ya kama toshe hancinsa. Kuda ganin haka sai Barsad ya bushe da dariyar mugunta ya ce.

Yaro kai ne ba ka saba da wannan dakin ba, sau bakwai ina kwana anan. Yau ba kai ba barci-kuma gobe da matsanancin zazzabi za ka fita daga nan."

Shi dai Insam ko kallon Barsad bai yi ba, kawai yana kallon ginin dakin ne, yana nazarin ta inda zai fita. Da ya kalli ginin dakin da

rufinsa ya ga ginin dutse ne ba zai fasu ba sai hankalinsa ya tashi, amma da ya dubi tagar dakin karama daga sama ya ga an zuba mata wadansu sandunan rodina guda tara sai ya yi murmushi. Sai dai kuma babu yadda zai iya kai wa inda tagar take dole sai da taimakon Barsad

Insam ya mike tsaye ya kama kai kawo yana takun da bai wuce uku ba saboda kankantar dakin. Daga can sai ya koma ya zauna ya fuskanci Barsad ya ce da shi.Idan za ka ba ni hadin kai ba zamu kwana a nan dakin ba." Sa'ad da Barsad ya ji wannan batu sai ya kyalkyale da dariyar mugunta ya ce.

Amma dai ka taba samun tabin hankali ko? Ta ya ya za mu iya fita daga cikin wannan dakin, ina mai tabbatar maka da cewa ko giwaye biyu aka kulle a cikin dakin nan ba su isa su balle kofa ko tagarsa ba bare mu."

Insam ya gyada kai ya ce "Ni dai kawai ka yi abin da na ce ka yi, za ka sha mamaki."

Har Barsad ya yi nufin ya ki sai wata zuciyar tace da shi "To ka kure karyarsa mana ka gani. Ai ko tsafi yake yi bai isa ya iya yin komai ba tun da babu mai iya tagaza tsafi agidan nan muddin Gadaraz na nan.Gama ayyana hakan ke da wuya sai

Barsad ya dubi insam yace "Me kake so na yi maka?"Insam ya ce, "So nake na hau kan wuyanka ka daga ni sama hannuna ya kai kan waccan tagar, in dai hannayena suka kai kanta zan iya zarè rodukan jikinta mu fice.

KO da jin wannan batu sai

Barsad ya ce, "Idan har ka iya zare wadancan rodukan guda tara, daga yau zan sauka daga kan matsayin shugaban fursunonin gidan nan na baka."Insam ya yi murmushi yace Ai

kuwa kujerarka ta zama tawa."Gama fadin hakan ke da wuya sai Barsad ya tsuguna bisá guiwoyinsa shi kuma Insam saiya hau kan kafadunsa ya zauna. Barsad ya mike tsaye da shi tamkar wani karamin yaro ya dauka.

Insam ya sa hannayensa ya kama rodin guda biyu wadanda kowane guda daya kaurin sa ya kai na tsintsiyar hannun Insam. Kawai sai Insam ya fara kokarin jijjigo rodunan biyu, nan take kwanjinsa ya kumbura, jijiyoyin jikinsa suka kumbura, fuskarsa ta rinka tabewa yana ciza leba:

Ba zato ba tsammani sai Barsad ya ga gini ya fara tsagewa, a hankali sai ga shi rodunan guda biyu sun fara zarowa daga cikin ginin dutsen.

Karar tsagewar ginin ne ya kai ga kunnen wasu dakaru dake can nesa kadan su biyu sai suka durfafo inda kofar dakin take domin su ga abin da ya yi motsi.

Ihun wani fursuna a can baya ne ya dake hankalinsu suka nufi can din, inda suka jiyo ihun.Damar da Insam ya samu nan ya zare rodunan guda biyu, kawai sai ya sake kama wadansu rodunan biyu ya ci gaba da zarosu. Nan da nan ya hada zufa sosai. Cikin dakiku kadan ya gama zaresu su ma kawai sai ya yunkura zai zura kansa cikin tagar ya fice daga dakin amma sai Barsad ya yi caraf ya riko kafafunsa ya ce da shi. "Kai ka hau kan wuyana ka sami damar fita ni kuma kan wuyan wa zan hau?"Insam ya ce "Ai dole na na miko maka hannuna ka kama na janyoka ka fita ko don saboda ka cika alkawarin da ka daukar mini na ba ni shugabanci."

Barsad ya ce "Haka ne kuma ni ba na karya alkawari amma ka sani cewa dokar da muka karya yanzu hukuncin kisa ne a kanmu ya za mu lya ceton kanmu?"

Fita daga cikin wannan daki ya fi tsirarmu wuya daga kurkukun gabadaya, kawai ka nuna mini hanyar da za mu bi ta kai mu inda rariyar gidan nan take mai fitar da ruwa waje."Gama fadin hakan ke da wuya sai Insam ya zura kafafunsa cikin tagar sannan ya mikowa Barsad hannunsa ya kama kawai sai ya dago Barsad sama tamkar karamin yaro ya janyo.Barsad ya cafo saman tagar da hannayensa biyu a lokacin da tuni Insam ya fita wjae ya duro kasa bisa kafafuwansa. Cikin hanzari shi ma Barsad ya fice ta cikin tagar ya dira waje.Yana dira ya wuce gaban Insam da gudu ya nufi wani bangare dabam na gidan, ai kuwa sai shi ma Insam ya rufa masa baya suka rinka falfala wani irin masifaffen gudu wanda inda mutum na tsaye a wajen idan suka zo suka gifta shi hucin iskar gudun nasu ne zai yar da shi kasa.

Koda dakaru suka hango Barsad da Insam a guje sun nufi wannan bangare na gidan sai suka biyo su aka kasa tsere.

Dakarun da ke can gabansu kuwa suna hangosu suka zare takubba suka rugo kansu, ya zamana cewa ana nema a sa su Barsad a tsakiya a yi musu rubdugu. Ko da su Insam suka fahimci abin da ke shirin faruwa sai suka fara banke dakarun ta gaba ta baya. Wata irin tafiyar yaji suka rinka yi da dakarun tamkar ana sassabe a gona. Duk da cewa dakarun na rike da makamai a hannunsu sai ya zama na banza domin bazar da su suka yi ta yi tamkar ana karkado busassun ganyayyaki kasa daga kan bishiya.

A daidai wannan lokacin ne suka ji anfara busa wani kaho mai karar tsiya, shi dai wannan kaho in dai ka ji an busa shi a wannan kurkuku to tabbas babu zaman lafiya, kuma alama ce ta cewar akwai fursunan dake kokarin guduwa.

Shugaban dakarun Gadaraz na kwance a cikin dakinsa na barci tare da matarsa laila sai kawai ya ji karar wannan kaho. Nan take ya mike zaune zumbur yana mai ture laila daga kan kirjinsa. Hakan ne ya sa•

0 Comments

Leave a Comment

Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search


Recent Article
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Read MoreStop doing these things if you don't want to damage your looks
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
Read MoreHEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
Read MoreSIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
Read MoreTHE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
WORST FOODS FOR BELLY FAT
WORST FOODS FOR BELLY FAT
Read MoreWORST FOODS FOR BELLY FAT
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
Read MoreMOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
WATA FUSKAR CHAPTER 2
WATA FUSKAR CHAPTER 2
Read MoreWATA FUSKAR CHAPTER 2
GWARZON SADAUKI PART 4
GWARZON SADAUKI PART 4
Read MoreGWARZON SADAUKI PART 4
WATA FUSKAR CHAPTER 1
WATA FUSKAR CHAPTER 1
Read MoreWATA FUSKAR CHAPTER 1
GWARZON SADAUKI PART 3
GWARZON SADAUKI PART 3
Read MoreGWARZON SADAUKI PART 3