
Ta kalli Idris, ya yi murmushi, suka fito tare yace,Kayi hakuri, mutuniyar ce sai a hankali idon ina tare da ita mantawa na ke yi da kowa da komi". Fatima tayi dariya ta ce, "Haba Baban Abba kada ka hada ni da Jibrin ya yi tsammanin gaskiya ne ka fadi mashi.
Gaskiya wanka kayi, kuma ai gaya nan ya gani da idonshi"Jibrin ya lumshe ido, shi duka haushinsu yake ji.
Sai ya mike ya ce, "To ni bari in isa masaukina in dan huta". Idris ya ce, "Wane masauki kuma? Muna da guest house, muna da guest room a cikin gidan nan, inda kake so nan za ka zauna, ba za ni so kayi mani nisa ba cikin wannan lokaci"ba
Sai ya koma ya zauna, lokacin Fatima ta mike ta nufi kicin ta rika jero masu nau'i-nau'i na abinci da na sha har suka rasa abin da za su fara da shi. Kamar kullum Idris cike da alfahari ya umarci Jibrin su fara cin abinci baya shakku akan Fatima, idon dai akan girki ne tamkar abin da ta karanta ke nan. Ta saba ma shi da abincinta mai dadi, don haka duk inda za ya je matukar yana garin to kuwa za ya dawo gidanshi cikin iyalanshi ya ci abinci.
Haka nan baya shakkar kawo ko wane irin bako ne gare shi, jar fata ne ko balarabe ko kuma mutanen shi 'Yan Asia, duka Fatima ta iya masu, haka nan suna yaba mata, ire-iren abubuwan da suka sanya ta saye zuciyar shi ke nan har ake fadin ta mallake shi. Don haka kalubale ne ku mata, ashe iya girki na sanyawa mace ta saye zuciyar mijinta.
Ganin sun natsu da cin abincin sai ta janye ta -bar wurin, ya yin da abokan suka saki jiki aka baje a tsakiyar
falo ana kwasar gara. Jibrin ya sha mamaki soasi da jin dadin girkin, to amma sai ya dauka cewa kuku ne ya yi shi ba wai Fatima ba, a tsammaninshi matsayinta dana mijinta da yarda ya fahimci tayi karfi sosai a cikin zuciyar Idris ba za ya barta tayi aikin wahala irin haka ba, dole ne ya aje mata masu aiki da za su rinka yi mata hidimominta. Bai sani ba matan da suka san ciwon kansu suka san abin da suke yi haka nan suka dauki rayuwar aure zaman bautar Ubangiji basu gajiya idan akan aikin kyautatawa miji ne, dan haka nake ganin ba hutu bane kuma ba gata bane ga diya mace komun kudin mijinta ta sakar ma masu aiki aikin abincin miji, kuskure ne babba, kuma ta haka akan samu matsala.
Wata mai aikin idan kin muzguna mata ba za ta rama ba sai ta bari sai ta tashi abinci tayi marar dadi wanda mijinki ba za ya yi murna da shi ba, haka nan daga ke har maigidan da ya'yanku ba za ku ci irin wanda ta ci ba, idan kuma kika hadu da muguwa, sai a hada baki da ita ayi mashi wani mugun abun, ko a zuba mashi wani sihirim, idon ma tayi tsanani har guba ana zuba mashi, kin ga ke nan kuskuren ki ne kuma son jiki da lalaci ya janyo miki babu wani hutu ga diya mace idan dai akan aikin mijinta ne.
Haka nan ire-iren wadannan mazajan ne za ka ga suna gararanbar bin gidajen abinci suna cin abincin da basu san yarda aka girka shi ba, mata da basu kai matsayin matansu ba su rika hidima da su, inda wasu daga nan ake jan ra'ayinsu har su fada cikin rayuwar da ba ta dace ba.
Ba wai aje masu aiki bane illa ko kuma ba su aiki, babu wanda ya ki taimako, sai dai yana da kyau idan ana aikin ya kasance kina kusa kina ganin yanda ake tafiyar da komi, idon ma ya kama za ki iya sanya hannu inda ya kama, sai ki ga komi ya tafi dai-dai, ba wai kiyi kwance cikin falo ba sai dai a shigo ace Hajiya me za a dafa yau? Idon an gama a kawo a ce maki ga na ki, baki damu ki kula yarda aka zuba ma maigidanki ba, balle
'ya'yanki da ya dace ki ba abinci mai gina jiki. Koda yake akasarin mu mata muna da mastala akan abincin yaramu, da yawa za kiga mai dan maikon mai dadi dayar tsokar ita ake kwashewa aba miji, su kuma 'ya'ya a hada su da kashi, gaskiya bai dace ba, anan akwai bukatar gyara, sabo da yara da ke tasowa su ne jikinsu yake bukatar abinci mai gina jiki da za ya yi masu amfani su kara lafiya da kuzari, shi kuwa miji jikinshi ya riga ya gama ginuwa, ko kin bashi sai dai yaci yaji dadi, amma babu abin da za ya yi mashi, don haka yana da kyau mata su hankalta a kalla ku rinka yin adalci tsakanin 'ya'ya da maigida. Mun ji shi ne mai nemowa, dole ne a bashi mai kyau ya ci, to sai ki duba su ma
'ya'yan dole ne a abasu mai kyau din don su jikinsu yafi bukata. To sai dai ki duba kiyi yarda ba za ki kwaro kowa ba. Ke kanki kina bukatar mai kyau din, musamman lokacin da mace take goyo.To amma anan dole ne su kansu maza su fahimci cewa sune ya dace su yi hakuri da duk abin da ya samu, kada su duba abin da suka kawo, wani zaya iya cewa,
"An raina mani wayau, in sawo nama sai a bani kashi?" To sai ka duba su wa aka ba tsokar? na sani wasu matan dole take sanyawa suna juyewa ma mazan tsikar da mai maikon-maikon don a zauna lafiya, ya yin da wasu kuma neman suna ne cusa kai ke sanyawa su yi haka, to koma dai mene ne ya dace muyi adalci a tsakaninmu.
Kunnuwanshi suka rika motsi har ya gaza daurewa ya dauki wata damfararriyar tsokar kaza da aka soya bayan an cudeta da attarugu da albasa, sai aka bada filawa aka saka cikin mai aka rufe har ta hadu ta soyu.
Ya gutsura sai ya rike yana kallon Idris bakinshi cike da tsoka ya ce, "Kada ka ce na yi santi fa, don Allah ina ka samo wannan kukun naka? Ya iya girki mai gamsawar kamar na matan Hausawa ba wanda aka koya a rubuce
ba?". Idris ya tuntsure da dariyar keta ya ce, "Ka zauna dai, ba an gaya maka kayi aure ba ka tsaya kana jin tsoro, masu gidan abinci na ta yin kudi da ku, alhalin abincin nasu ma duk 'yan dabaru ne ba wai iyawa akayi ba, abin haushi ka kira mai kawo abinci sai ta zo maka kai bude ya sha kari da gashin doki don Allah baku jin kyamar
irin wadannan matan?"
Jibrin ya ce, "To ai ni baka bani amsar tambayar da na yi maka ba ka tsaya kana yi mani sharhi sai kace dan jarida". Idris ya yi mashi kyar ad ido, ya ce, "Idon na fadi maka za ka yarda?". Shima ya bishi da idon. Ya ce,"Wallahi duk duk abin da ka gani nan Fatima ce ta girkashi ba wani ba. Hasalima dai ni ban taba daukar kuku a gidana ba, ra'ayinta ke nan, tafi son ta shiga kicin da kanta ta girka, masu aikin da ke garemu daga mai gadi sai direbana sai mai wanki da guga, sai wata yarinya da ke yi ma ta share-share da goge-goge, amma banda girki.Wallahi Jibrin Fatima mace ce har mace, matar da ta san
ciwon kanta, ta san hakkin aure. Ka ga dai gashi na yi kudi, kudin da suka kai matsayin da za ta iya zama ta lankwashe kafa ta ce komi sai an yi mata, amma sam bata tsiri mun wannan ba...Wani abin ma ko na bukaci ayi shi idan ta lura cewa bai zama dole ba sai ta ,ce a
barshi. Ni kaina har mamakinta nake yi, dai-dai da rana guda ban taba zuwa da wani bako gidan nan ba ko wane irin jinsi ne ace naji kunya. Ka'idane za ta bashi abincin da ya dace da shi, kuma a yaba sosai"
Wani irin kududun bakin ciki ya tsaya ma Jibrin a wuya, sai yaji dama baiyi tambayar ba. Ya tsani yaji yana zuzuta sunan Fatima, wani irin kishi ya ke ji tamkar ya shakeshi ya mutu, sai ya yi shiru bai sake magana ba.
Da suka gama Idris ya jashi suka nufi masallaci, don haka Fatima ta fito ta kwashe kayan da kanta ta gyara falon fes irin yarda take so, sai ta canza kamshin falon da wani irin mayen turaren wuta na ruwa da ta sawo a Dubai. Kamshin shi na da kwantar da rai, duk lokacin da ta sanya shi Idris kan nacewa zaman falon, sai ya ce nishadi yake ji, yana yi mashi dadi sosai. Kafin su dawo ta maida komi fes-fes, ta zauna falon tare da Al'amin suna kallo, ko dama bacin kallon da Jibrin ya matsa mata da shi ne ya koreta kallon har ya wuce na sha'awa. Idan ya kafa ma ta ido tamkar ya hadiyeta, da zarar ta hada ido da shi sai kuma ya kashe ma ta ido, don haka sam bata ji dadin tayin da Idris ya yi mashi ba na zaman gidanshi, sam ba abokin kirki bane da za ka kusantashi da iyalinka. Kai gabaki daya ma bata yarda da takunshi ba, to sai dai ta san kaunar da ke tsakanin Idris
da Jibrin sai Allah, balle halayyar Idris daban ce, yana da saurin yarda da mutum, yana so ya ga yaja wanda ya sani a jikinshi ya karu da shi. Mutane da yawa sun yi arziki ta jikinshi, yin hakan ba illa bane, kuma ta san ya cancanta ya yi ma Jibrin ko ma mine ne, don haka ba ba abin mamaki bane don ya yi mashi haka. Sai dai tana zargin wani abu a karkashin zuciyarta game da shi, illa dai ta bar komi a cikinta, ba za ta so ta shiga tsakaninsu ba, alhalin sun jima suna neman junansu.
Sallamarsu ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula. Ta dago kai tana kallon Idris ta ce, "Ina fatan dai kin sanya an gyara dakin baki na ciki, nan Jibrin zai zauna don kwanan hira zamu yi da shi"
. Tayi dariya tace, "Komi lafiya lau yake, ya dubashi ko yanzu" Sai ya wuto ya zauna kusa dà ita har yana shakar kamshin jikinta a sanyaye ta dago kai ta kalli Jibrin, sai ta ga ya hade fuska ya dauke kai yana kallon Al'amin yace Yàya maigida zo mu gaisa mana"
. Al'amin ya mike ya nufi
wurinshi, sai ya rungumeshi cikin jikinshi, kaunar yaron ta shiga zuciyarshi tamkar ya rungume Fatimar ne, kamar su daya da ita, gashi yaron dan kidif-kidif, mul-mul da shi gwanin ban sha'awa. Yana da koshin lafiya da kuzari.
Sai ya shiga tunanin wai me yasa komi na Idris ya fita daban? Duk ta bangaren da ya duba sai yà ga ya yi mashi fintinkau, tamkar shi ya tsara ma kanshi rayuwa.
Husna ta fito daga dakinsu na yara, ta iso jikin Daddynsu tace,"Daddy sannu da dawowa. .Ka baro Abba can ko?. Ya yi dariya ya janyota cikin jikinshi ya ce, "Kada ki damu my baby, za yazo hutu karshen shekara,
kuma za ku je mashi visiting tare da
Mummynku idon yayi six month da tafiya". Sai tayi dariya. Ya nuna mata Jibrin da yatsa wanda ya yi jagale yana kallonta, sai ya ga yarinyar tafi kowa kyau a gidan gata fara gentle. Idris ya ce, "Ga wani Daddyn baki gaida shi ba". Ta tsura ma Jibrin ido, sai tayi murmushi ta zame daga jikin ubanta ta durkusa tana gaida shi.
Jibrin ya yi murmushi ya ce, "Yauwa babu na gode. Ko me sunanki?".
. ta ce, "Asma'ul Husna". Ya ce, "What, a
nice name. Ni kuma sunana Uncle Jibrin"
Idris ya yi dariya ya ce, "Kai ma da taya bera bari kake, shi ne har da fadi ma ta sunanka. In don wannan ce lokaci kadan za ta buwayeka". Jibrin ya shafi kan
Al'amin, har yanzu yana nan manne jikinshi ya ce, "Ba damuwa, ina son yara irin haka, ban gajiya • da hidimarsu". Idris ya ce, 'To ai laifin kane da kana da su a gidan ka ba za ka ji irin haka ba"
Yana dariya ya narke ma Fatima, idanuwanshi a cikin na ta, jikinta ya yi sanyi, sai tayi sunkui da kai kai gabaki daya ma zaman duk ya gundureta, ba ta ga amfanin shi ba, addinin Musulunci ya yi gaskiya, gaskiya matsala ce babba barin matarka ta zauna da abokinka ana ta hira. Ita kam yau ta ga illar hakan, duk sai ta tsargu, gashi ta lura Idris ya saki jiki da shi sosai.
A karo na biyu da ta kara kallonshi a asirce ya sakar ma ta wani tattausan murmushi na yaudara. Sai da yan cikinta suka kadu sabo da duk abin da ya ke yi ma ta sai ya fakaici idanun Idris, baya bari ya gani, don haka ta * diga alamar tambaya a cikin lamarinshi. Shi kuwa gogan ya yi dai-dai bisa kujera sai zuba mashi dumi yake yi, abin haushi har da abubuwan da basu shafeshi ba,
addu'o'i, da haka abubuwa suka rika dawo mata cikin kai tiryan-tiryan.
Ranar da mahaifinta ya kaita jami'ar Jos za ta fara karatu, ita ce rana ta farko da ta fara haduwa da Idris lokacin suna daf da kare digirinsu.
Tana tafiya zuwa hall dinsu da suke lecture ne tayi kicibus da su, sai ta tsaya tayi masu sannu da natsuwa.
Idris ya tsura ma ta ido yana mamakin kyawunta, don haka Jibrin ne ya amsa gaisuwarta. Tayi musu bayanin inda take nama. Jibrin ya ce, "Hala ke bakuwa ce ko?" Sai tayi murmushi ta ce, "Yau din nan na fara zuwa. Yayi dariya ya ce, "Babu mamaki, muna tayaki murnar shigowa cikin jami'a. Sai a dage da karatu' taji dadin
kalamanshi. Ya ce, "Mu koma a nuna ma ki, kin baro shi a baya."
Tayi godiya, amma sai ta kallo Idris tana mamakin halin ko in kula da ya nuna ma ta. Hasalima dai bai sa musu baki ba a cikin maganar su da abokinshi, Jibrin ne ya kama hannunshi, ya san halin mutumin na shi in dai akan harkar 'yan mata ne baya shiga, ko zuwa suka yi wajensu sai dai su gaji da duminsu su tashi bai kula kowa. Ra'ayinsa daban ne, don haka ake yi mashi daukar miskili.
Jibrin ya dafa kafadarshi ya ce, "Muje dan Allah a nuna ma ta hall din nan".
'. Ya dan kalli Jibrin din babu
sakin fuska akwai alamar gajiya sosai a tare da shi ya ce,Kana so ka wahalar damu ne kawai, me ye laifi idon kayi ma ta kwatance za ta fi fahimtar wajen sosai"
Ya dago ido, sai suka hada ido da ita, ga alama ba ta ji dadin kalamanshi ba, to shima sai jikinshi ya yi sanyi, har ya dan dabarbarce, bai san dalili ba, sai kuma yaji tausayinta. Ya dan lashi lebenshi yana kallon Jibrin, ya ce, "Shi ke nan muje". Muryarta ta katse shi tace
"Kada ka samu damuwa, kuyi mani kwatancen kawai zani iya ganewa na ga kamar a gajiye kuke".
Hakan da tayi ya yi ma Idris dadi, ya yin da Jibrin bai so ba, ya so ace sun tafi tare ta yarda za ya samu damar cusa kanshi gareta. Baya da zabi dole yabi umarnin Idris din, bai cika yi mashi musu ba, kusan matsayin uban dakin shi yake, shi ne cinshi, shi ne shanshi, kusan gabaki dayan hidimar karatunshi shi ne ke yi ma shi.
Leave a Comment
Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search
Categories
-
(2)
-
(3)
-
(4)
-
(8)
-
(12)
-
(1)
-
(11)
-
(0)
Recent Article
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Read More
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
Read More
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
Read More
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
Read More
WORST FOODS FOR BELLY FAT
Read More
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
Read More
WATA FUSKAR CHAPTER 2
Read More
GWARZON SADAUKI PART 4
Read More
WATA FUSKAR CHAPTER 1
Read More
GWARZON SADAUKI PART 3
Read More
0 Comments