GWARZON SADAUKI PART 1

Mr Novel

  

20 Apr 2025

387

GWARZON SADAUKI PART 1

Kurkuku ne wanda aka gine dakunsa da katangarsa da zallan duwatsun wuta. Kofofin gidan gabadaya da tagoginsu an yi su ne da bakin mummulallen karfe mai

• kaurin kamuy guda. Tsayin katangar wannan kurkuku kamu sittin ne don haka duk wani fursuna da ke cikinsa bai taba tunanin haurewa ba. Akalla akwai zaratan dakaru guda dubu daya da dari biyu masu gadin wannan kurkuku wadanda su kansu ababen tsoro ne saboda kwarjininsu gami da surarsu ta manyan sadaukai domin ido ba mudu ba ne amma ya san kima.

A daidai wannan lokacin

fursunoni na tsaitsaye a tsakiyar wannan kurkuku suna 'yar hada-hadarsu kamar yadda suka saba.Wasu suna wasan motsa jini, wasu hira suke yi, wasu kuma suna kai kawo. Dama kullum an ware musu irin wannan lokaci domin samun nutsuwa. Kwatsam! Sai suka ji motsin bude katuwar kofar gidan wacce tsawonta da fadinta kamu . sittin-sittin ne. Karar bude kofar ta cika dajin gabadaya da amsa kuwwa kai ka ce wani katon dutse ne ya mirgino da gudu. Ita dai wannan kofa ana budeta ne da wata irin na'ura mai dauke da kaca da kuma hakoran mawanin karfe mai juyawa.Dakaru ashirin ne ke iya juya mawanin sannan kofar ta bude a tsawon dakika dari uku da sittin.

Kofar na gama budewa sai fursunoni suka ga dakaru kimanin guda arba'in sun tuso keyar wani mai laifi wanda aka daure hannayensa da kafafunsa da manyan sasari kai ka ce giwa a ka janyo.

Shi dai wannan mai laifi ya kasance matashin saurayi wanda shekarunsa ba za su haura ashirin da shida ba. Ya kasance kyakkyawa ne mai kirar sadaukai. Fuskarsa cike take da murmushi kawai sai kalle-kalle yake yi yana duban tsawon katangar gidan da kuma tsarin kofofi da tagogi. Bayan an shigo da wannan saurayi tsakiyar kurkukun a lokacin da aka rufe kofar shigowa sai aka tsayar da shi cak aka fara kallon kallo tsakaninsa da sauran

Bursunonin gidan. Kowa sai ya tsaya , ya daina abin da yake yi. Su dai fursunonin gidan mamaki suke yi

  •   kuma suna tambayar junansu suna
  •   cewa wannan kuma wane takadari ne haka har da za a daure shi cikin
  •   manyan sarkoki. A saninsu duk wani gawurtaccen mai laifi a duniya idan aka kawo shi wannan kurkuku na birnin Kisira risina yake ya kama kuka da nadama to amma shi wannan gashi da murmushinsa ya shigo ko küwa bai san irin masifar dake ciki ba ne.
  • Wata irin muguwar rayuwa ake yi a cikin wannan kurkuku wacce mai karfi ne kadai yake tsira. Ba a raba abinci a cikin nutsuwa sai masu Karfi sun fara dibar nasu sannan in ya yi ragowa marasa karfi su diba.
  • Idan mutum bai samu ba sai dai ya kwana da yunwarsa. A kullum akan dauki gawa guda biyu ko uku a cikin* wannan kurkuku saboda bakin zaluncin da ke faruwa a tsakanin fursunonin.
  • Idan fursunoni za su kwana suna yaki a tsakaninsu ko kallonsu dakaru ba za su yi ba, amma fa da zarar fursuna ya karya doka guda daya take dakaru za su rufe shi da luguden duka sai sun ga ya suma sannan za su kyale shi kuma a dauke shi a kai shi wani kuntataccen daki wanda ko kwanciya zai yi ba zai iya mike kafafunsa ba kuma daki ne cike da shara, tsutsa ga doyi, sauro da kudaje ma sun ishi mutum masifa.
  • Ana cikin wannan kallon kallo tsakanin bakon fursuna da sauran fursunonin gidan kenan sai wata kofa daga can wani bangare ta bude, shugaban dakarun gidan ya fito tare da wasu tsirarrun dakarunsa masu take masa baya suka durfafo inda bakon fursuna yake.
  • Shi dai shugaban dakarun wannan kurkuku ya kasance wani garjejen kato mai sura irin ta mutanen farko. Kallo daya za ka yi masa ka san cewa sadauki ne kuma jarumin gaske mai fasa taro.
  • Shigarsa ta fita dabam da ta sauran dakarun gidan domin rigarsa, takalmansa da doguwar safar hannu duk na karfe ne. Takubba biyu ne rataye a bayansa.
  • Duk jikinsa a murde yake cike da kwanji ga jijiyoyi burdin-burdin. Sai da suka iso daf da bakon fursunan yadda tazararsu ba ta wuce taku bitu ba, sannan suka tsaya cak shugaban dakaru da bakon fursuna aka yi kallon kallo na tsawon dakiku biyar sannan shugaban dakarun ya yi dan

0 Comments

Leave a Comment

Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search


Recent Article
FOODS THAT CAUSE ACNE AND PIMPLE
FOODS THAT CAUSE ACNE AND PIMPLE
Read MoreFOODS THAT CAUSE ACNE AND PIMPLE
REASONS WHY YOU SHOULD CUT DOWN ON SUGAR
REASONS WHY YOU SHOULD CUT DOWN ON SUGAR
Read MoreREASONS WHY YOU SHOULD CUT DOWN ON SUGAR
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Read MoreStop doing these things if you don't want to damage your looks
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
Read MoreHEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
Read MoreSIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
Read MoreTHE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
WORST FOODS FOR BELLY FAT
WORST FOODS FOR BELLY FAT
Read MoreWORST FOODS FOR BELLY FAT
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
Read MoreMOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
WATA FUSKAR CHAPTER 2
WATA FUSKAR CHAPTER 2
Read MoreWATA FUSKAR CHAPTER 2
GWARZON SADAUKI PART 4
GWARZON SADAUKI PART 4
Read MoreGWARZON SADAUKI PART 4