
Fatima! Fatima!!"
Tana jiyo muryarshi ta saki murmushi, sai taji zuciyarta tayi santi. Sati biyu da ya yi
tafiya ya barsu da kewa sosai. Muryar Mai gida Idris ke nan.
Ta mike daga gaban madubi ta kara kallon tsarin kwalliyarta ta yarda da kanta, kuma ta san tayi kyau irin yadda yake son ganinta, sai ta dauki turare ta karama jikinta.
A karo na biyu ta jiyo muryarshi daf da dakinta.Sai tayi saurin dangwarar da kwalbar turaren da saurinta ta nufo kofar.
Dai-dai lokacin da ta murda kyauren, shi kuma ya kawo jiki, dan haka suka yi kicibis a bakin kofa. Har ta so ta dan razana.
Murna fal da cikinshi ya ce, "Fati kina jina shi ne sai an ja mani aji?"
Tayi dariya hakoranta jeras a waje ta ce, "Wane jan aji zani yi maka kuma Baban Abba?"Ya yafito ta yana kyalkyala dariya yace, "Nima abin da na gani ke nan. Amma kafin kice komai rufe idonki mu je ki ga tsintuwar da nayi yau"
Tayi dariya, ta saba da zolayar shi, dan haka ta biye mishi, idanuwanta a rufe har suka shigo cikin falon su, sai ta bude ido. Idanuwanta suka gano mata mutumin da suka jima suna jajen rashin ganinshi.
Lokaci guda murna da mamaki suka baiyana a fuskarta. Ta juya tana kallon Idris ta ce, "Baban Abbas ina ka gano Jibrin?". Ya watsa hannu ya zauna kan kujera ya ce, "Kin gan shi nan ba zato yau Allah ya hadani da shi a filin jirgin Lagos bayan mun safka kafin mu wuto Abuja.
Kuma abin mamaki shima nan ya nufo, na yi mamaki kwarai yarda tsawon wannan lokaci Allah bai hadamu ba sai yau". Fatima ta ce, "Lallai nufin Allah kam"
A hankali ta sauke kwayar idonta akan Jibrin. Yana zaune ya hakimce cikin kujera, murmushi kawai yake yi.
Ta ce, "Amma baka da kirki Jibrin, tsawon wannan lokacin ka kasa neman Idris alhali shi yana nan babu ranar da ba za ya yi maganar ka ba".
Ya yi ma ta kyar da ido na yan duniya da suka gogu da duniya. Ko kuwa shi ne dai haka, wani irin mamaki ya ke yi da sha'awar Family din abokin shi Idris.
Sai ya yi dariya ya ce, "Kada ki fadi haka Fatima, Allah ne bai kaddara haduwarmu ba sai wannan lukaci, ni kaina na jima ina neman shi amma ko duriyarshi ban ji ba. Kwanaki can har gidansu naje nemanshi na taras ashe Kawun ya tashi, sai wani da na samu gidan ya ce "Suma ba su da labarin ku"
. Tun daga lokacin ban kara jin
duriyarshi ba sai yau din nan kamar daga sama muka hadu a Air Port, kuma abin mamaki wai ashe kuna nan Abuja ni kuma na maida Abuja kamar fita kofar gida daga cikin gida, duk da cewa ba nan nake zaune ba, amma kusan koda yaushe sai nazo. Wani lokacin ma ban kwana ranar na ke komawa."
Idris ya ce, "Wanann wani abu ne daga Allah
kawai, sai mu gode mashi da ya sake hada mu"'. Jibrin yace, "Haka ne. Kuma ai ka zama babban mutum Idris, ganin irin ku wuya yake yi sai an cika form". Suka kece da dariya
Fatima ta mike ta nufi kicin idanuwan Jibrin tas a kanta, sai yaji wani abu ya taba zuciyar shi. Kishi ne ko me? Haka nan sai ya samu kanshi da jin zafin Idris a karkashin zuciyarshi, sabo da duk ta bangaren da ya duba sai ya ga ya yi mashi fintinkau a yarda ya lura da shi ya kama kasa sosai, ya yi karfi fiye da zaton shi. Dan zaman da suka yi a filin jirgi kafin su taso ba za ya iya kirga adadin mutane da yaji yana magana da su a waya ba, kusan duk manyan mutane ne, kuma dai duk harkar Business ce.
Yanzu kuma da suka iso gidanshi komai ya daure mashi kai, yana mamkin yarda za a ce kamar Idris ya mallaki kayataccen gida a Abuja irin wannan, kuma ya ce mallakinshi ne halak malak! To yanzu kuma da ya kalli matarshi sai kishinta ya tsaya mashi a zuciya. A ganinshi sam ba ta dace da Idris ba bagidaje sai shi rikakken dan duniya.
Fatima mace ce har mace, macen da kowanne da namiji za ya so ya mallake ta, shuwa ce jajir da ita, gashi har tsakiyar baya. Ban da wannan, tana da kyau, kira da tsarin halitta, ta yarda duk inda ta shiga dole a kalleta. A sanin da ya yi ma ta lokacin da sukai karatu a jami'ar Jos sam ba ta kai haka ba, amma yanzu sai ya nada mata sarauniyar mata, gani yake yi a duk fadin duniya babu macen da ta kama kafarta
"Lallai Idris ya yi nisan da bai taba zata ba, da can duk gani yake yi da wuya mace kamar Fatima ta auri Idris. Don haka ya zuba musu ido suka rika kwarara soyayyarsu har zuwa lokacin da suka gama, suka fita suka barta tana karasa na ta karatun. Tun da suka rabu basu sake haduwa ba, dan haka bai san abin da abokin na shi yake ciki ba, balle ma ya yi imanin cewa soyayyar tasu iyakarta cikin makaranta sai yau din nan a cikin jirgi da Idris ke yi mashi bayanin cewa Fatima Shattima ce yake aure. Ya yi mamaki kwarai don haka yanzu da ya ga takun rayuwarsu sai abin ya tsaya mishi a cikin zuciya har ya rinka jin bai ji dadin ganin Idris din ba.
Dawowar Fatima ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya luka, inda ta dire faranti akan tebur dauke da lemuna iri-iri da ruwa ta tsura mashi ido tana dariya.
Ta ce, "Ko tunanin Madam kake yi ne ana ta magana na ga ka shagalta". Sai ya yi dariya. Idris ya riko hannunta ta zauna kusa da shi ya ce, "Rabu da wannan sai mun yi mashi zaman kanshi, wai har yanzu bai yi aure ba, komi yake jira?" Fatima ta bude baki tana dariya ta ce, "Duk kana mi Jibrin?"
Ya hadiye wani abu da ke kokarin taso mashi ya yin da kishin Idris ke cinshi. Yanzu da ya ga Fatima zaune kusa da shi sai yaji kamar ya tashi ya shakeshi dan azabar kishi. Idanuwanshi suka kankance, sai ya dauki gwangwnain Rani ya balle ya juye cikin kofi ya zuba kankara yana kurba.
Idris ya kalli Fatima suka yi dariya.
"Kin ganshi ko? Baya so ayi mashi maganar aure, tun da na ke maganar nan a cikin jirgi bai ce mani komai ba" Ya rike kofin yana dariya ya ce, "Dadina da kai ke nan sababi. Har yanzu ba ka canja ba in ban da abin ka aure ai lokaci gareshi ko?". Idris ya ce, "Kai dai naka lokacin ya yi har ya wuce. Na gaya maka tafiyar nan da nayi fa yanzu China naje na kai first born din mu Abba za ya yi Second can. Ga Husna nan aji hudu take a primary sai Al'amin yana Nurseru, idan bacin matsalar da Fatima ta samu da yanzu mun kara wani. To kai kana zaune haka nan empty. Rayuwa yanzu gudu take yi, idon kayi wasa sai ka koma haka nan baka bar masu yi maka addu'a ba"
Suka bushe da dariya baki daya. Ya tsura ma ta Fatima ido da wani asirtaccen kallo, da ya sanya kanta cikin duhu ya ce, "Kin ji fa Madam". Sai ta rausayar da kanta tana dariya ta ce,To ai kun fi kusa"
Haka nan sai taji ta tsargu da mutumin. Karo na biyu ke nan da tayi katarin hada ido da shi, ba za ta iya fassara abin da take gani a cikin kwayar idonshi ba, sam bai dace ba, don haka jikinta ya yi sanyi, sai tayi dubara kamar zata dauko wani abu cikin daki tayi shigewarta.
Ko minti biyu ba ta yi ba taji Idris ya biyota tana tsaye jikin taga ya kwanto ta bayanta, ta saki ajiiyar zuciya ta mika hannu a saman kanshi. Idris ya lumshe ido yana shakar kamshinta, komi ya rikice mashi ya kara manne mata dam. Ya ce, "Honey i miss you"
Tayi dariya ta ce, "Babban Abba ke nan, ya ya hanya? Ya ka baro Abba?'. Ya shafi fuskarta yana dariya ya ce, "Abin da ke ranki ke nan, na san kina nan kin damu da tunanin danki ko?".
. tayi dariya ta ce, "Ba dole
ba, Chaina fa?". Ya ce, "Come on, kada ki samu damuwa komi lokaci ne idan da rai wata rana sai ki ga har ya gama. Kuma ai ci gabanmu ne nan gaba sune za su tallabe mu, kin ga kau ya zama dole mu gina rayuwarsu yarda za ta yi karko can gaba"
. Ta ce, "To ni dai idan ka
dauki mazan ka fidda su ba zani bada Husna ba nan za ta yi karatunta gabana"
. ya ce, "Nima bani da ra'ayin hakan.
Ai diya mace ce, ba wai burgewabane don mutum ya dauki diyarshi mace ya kaita karatu kasar waje, musamman ma sabo da 'ya'ya mata rauni ne da su, da an kuskuro sai ki ga rayuwa ta lalace, amma shi namiji dama shi aka sani da gwagwarmaya ko ina ya samu kanshi dai-dai ne. Sai ki ci gaba da yi mana addu'ar da kika saba yi, Allah ya tsare mana su"Fatima ta kwanta shiru a cikin jikinshi, dan haka ta ke son mijinta, yana da tunani sosai. Ta lumshe ido tana jin shi yana tsokanota, sai ta kyalkyace da dariya ta janye mashi ta ce, "Ka manta kana da bako a gidan ne?'. Ya shafi kanshi ya ce, "Ya na iya da raina? kinyi kyau ne fiye da kullum".
'. Tayi dariya ta ce, "Haka dai ka ke fada
koda yaushe. Gobe kuma idan na fito sai ka ce na fi kullum".
. Yace To ai lamarin naki ne Fatima daga Allah ne tamkar kina rikida kusan kullum kamar ana canja miki halitta, shi yasa na ke ganin wautar ki idan kina fadin wai nan gaba zani kara aure, in auri wa Fatima? Ai duk abin da diya mace ke takama da shi kin gama mallakarshi. Ke ni gani ma nake yi kin fi sauran matan duniya.."
Dariya ta rinka yi ma shi. Ta saba da kalamanshi bai kiba koda yaushe yana biye da ita yana yi ma ta kirari sai ka ce maroki, dan haka take tunanin anya akwai matar da mijinta yake sonta irin yarda Idris ke sonta?
Wani lokacin sai ta ba kanta amsa da cewa "Babu" sabo da ta sha jin ma'aurata na son junansu amma lokaci-lokaci sukan samu sabanin ra'ayi har ta kaisu ga rigima, amma su lamarinsu tamkar hadin baki ko wane cikinsu na kokarin kyautata ma dan uwanshi ba dai kaji ko musayar baki sun yi ba. Koda yaushe za ta iya shaidar mijinta ba azzalumin miji bane, dai-dai da rana guda ba ta taba samun shi da wani laifi ba da ya danganci cin amana ko tauye ma ta hakki, dukkan abin da za ya yi sai ya sanar da ita, shawararsu daya, bakinsu daya, kuma su duka ba su da kowa har kara ita tana da kanne biyu, amma shi tamkar baya da kowane, shi kadai mahaifiyarshi ta haifa ta rásu ta barshi, ya tashi cikin 'yan uba, basu son shi ko kadan, don haka ba wata shakuwace tsakaninsu ba, tun kafin mahaifinsu ya rasu sauran tausan
• rayuwarshi ta koma hannun kanin mahaifiyarshi a Jos.
Bai zauna da su ba, dai-dai da gadon dan abin da mahaifinsu ya mutu ya bar musu hana kanshi suka yi, suka yi babakere ba a bashi ko hakin tsintsiya ba.
Yanzu akuma da ya yi arziki hassada da jin zafi ta hana kowa ya rabe shi, tsakaninshi da su sai zagi da tsana, don haka ya tashi baya da kowa sai dangin mahaifiyarshi.
To itama dai iyayenta sun rasun ba ta da kowa sai yan kannenta duka maza. Aliyu na dubai yana karatu shi kuma Usman yana Maleysia. Su duka Idris ne ke daukar nauyin karatunsu. A rayuwa babu abin da ldris bai yi ma ta ba, ya kare ma ta mutunci, ya kare mutuncin kanshi, baya da wani mugun hali, abin ki da akasarn matasan da ke takama da kudi ke yi. Shaye-shaye ko neman mata, neman maza. Da sauransu. Sam Idris baya da wannan halayen, haka nan dukkan abin da za ya yi zaya fadi ma ta babu munafunci, dan haka bata zargin shi da komi.Haka shima ya yarda da ita, yana son Family din shi, yana yaba ma ta akan tsayin daka da take yi dan shirya mashi kan gida da tsara komi na rayuwa bisa tsarin addinin islama.. Sam ba ta da son zuciya ko makamancin haka.Uwa, uba, Fatima Zahra ce a cikin mata, ya kan yi alfahari da samun gimbiyar mata irinta, ya yi imanin cikar Nigeria da batsewarta masu mata irin Fatima kalilan ne, don haka baya wasa da igiyoyin auren shi, duk wani abu da ya san za ya bata ma ta rai yana kiyayewa, sam baya son damuwarta, sai kuma ya yi dace yarda yake tattalinta itama haka take tattalinshi ta san kanshi fiye da komi, don haka suke gina kansu da rayuwarsu ta zamo abin sha'awa ga kowa, babu inda za su shiga ba a yi sha'awarsu ba.
***
Ta dago kai a sanyaye tana kallonshi, ya fito wanka, sai ta matsa ta karbi tawul tana tsane mashi ruwan jikin shi, ya tsura mata ido yana kallon kwayar idonta ya ce, "Me kike tunani ne?". Tayi murmushi ta ce,
"Babu komi". Ya rausayar da kai, ya ce, "Haka dai kike fada. To bani labari ya ya gida, ban ga Al'amin ba da Baby na".
. Sai ta wuce shi ta aje tawul din ta ce, "Abin da ya kama ka tambaya ke nan. Komi normal as usually.
Husna kuma sun tafi Islamiyya, Kabir ya tafi daukosu, na san suna kan hanya".
'. Ta bude dirowa ta fiddo mashi
kaya marasa nauyi ya canza, dai-dai lokacin Jibrin ya kwankwasa kyauren dakin ya ce, "Wai kun manta da bako ne a gidan?"
Leave a Comment
Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search
Categories
-
(2)
-
(3)
-
(4)
-
(8)
-
(12)
-
(1)
-
(11)
-
(0)
Recent Article
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Read More
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
Read More
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
Read More
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
Read More
WORST FOODS FOR BELLY FAT
Read More
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
Read More
WATA FUSKAR CHAPTER 2
Read More
GWARZON SADAUKI PART 4
Read More
WATA FUSKAR CHAPTER 1
Read More
GWARZON SADAUKI PART 3
Read More
0 Comments