GWARZON SADAUKI PART 2

Mr Novel

  

25 Apr 2025

231

GWARZON SADAUKI PART 2

guntun murmushi ya dubi bakon fursunan ya ce."Sunana Gadaraz, ni ne shugaba a wannan kurkuku.Ya kai bawa Insan in yi maka barka da zuwa gidan mutúwa. Labari ya riske ni cewa sau biyu kana samun nasarar guduwa daga can kurkukun cikin gari ana kamoka da kyar to ka sani nan ba a iya guduwa. Duk fursunan da aka shigo da shi nan sai dai a fitar da gawarsa amma bai isa ya fita a raye ba. Yau tsawon shekaru goma sha hudu kenan da kafa wannan kurkuku ni da jama'ata muna gadinsa babu wani fursuna da ya taba karya wannan tarihi. Ka sani muna da dokoki, guda tara a gidan nan.

Dokoki biyar daga ciki idan ka aikata su za a yi maka hukuncin dukan kawo wuka gami da horo mai tsanani. Ragowar dokoki guda hudu kuwa hukuncin kisa ne a kan su. Ina mai yi maka gargadi da ka kiyaye wadannan dokoki wadanda za a sanar da kai su yanzu take idan kana son ka tsira da lafiyarka da rayuwarka."

Koda gama fadin hakan sai shugaban dakaru Gadaraz ya dubi wani Badakare ya ba shi umami.Badakaren ya bude baki ya ce.

"Doka ta farko a gidan nan itace...".

Caraf sai bawa Insam ya tari numfashin Badakaren ya ce, "Dakata ba na bukatar jin dokokinku. Ina son na karya kowacce doka daya bayan daya har guda taran in ya so naga yadda za a iya hukunta ni. Daga yau ina mai tabbatar muku da cewa babu

  • wata doka da za ta yi aiki a kaina sai dai a kan sauran fursunoni."
    Ko da jin wannan batu sai
  • dakarun dake kewaye da Gadaraz suka daga kulakensu suka yunkura za su afkawa Bawa Insam. amma sai Gadaraz ya daka musu tawa ya ce,
    "Ku dakata ka da ku taba shi."
    '*Da jin haka sai dakarun suka ja da baya suka tsaitsaya. Gadaraz ya dubi Insam ya bushe da dariyar mugunta. Lokaci guda kuma ya murtuke fuskarsa ya ce "Da kyau
  • haka nako so na ga jarumi mai dakakkiyar zuciya da karfin hali irin ka. Ai ka rage mana wahala tun da ka zabi hanyar da ta fi sauki a garemu. Mu dama amfaninmu a. gidan nan horo, tsaro da hukunci.
  • Burinmu kawai a aikata laifi. Ga fili ga mai doki, kai ku kwance masa duk sarkokin dake jikinsa kuma a nuna masa dakinsa na kwana amma da zarar ya karya doka daya a zartar - da hukunci a kansa."
  • Ko da jin wannan batu sai mataimakin Gadaraz cikin alamun fargaba ya ce "Á'a ya shugabana Sarki ya gaya min cewa wannan yaron yana da matukar hadari don

haka bai kamata a kwance masa sarkokin nan ba."Gadaraz ya daka wa Bartus tsawa ya ce "Ai so nake na ga iyakar hadarin nasa. Maza ku kwance masa sarkokin na ce."

Da jin haka sai wasu dakaru biyu suka

zaro mukullai suka

kwankwance sarkokin dake jikin

- hannayensa da kafafuwansa. Saboda dadewar daurin duk shatar karfe ta fito a kan hannayen da kafafun. Ko da Insam ya ga an kwance shi sai ya yi mika gami da murmushin murna domin ji ya yi kamar ya samu 'yanci

ne daga matsayin bawa, shi kuwa Gadaraz sai ya juya da baya ya nufi kofar da ya fito dakarun dake tare da

shi suka bi ski a baya. Wani Badakare daban ya dubi Insam ya ce ka biyo ni

Ba tare da wata gardama ba kuwa sai Insam ya bi Badakaren a baya suka nausa wani bangaren dabam na gidan. Duk wannan abu dake faruwa sauran fursunonin gidan suna ta kallon bakon bawa insam.

Ko da aka nufi cikin gidan da shi sai ya ga gabadayan fursunonin gidan sun biyo su a baya. Hakan ne ya sa Insam ya fahimci cewar lallai akwai wani abin da ke shirin faruwa don haka sai ya yi shirin tarar ko mene ne a ransa.

Lokacin da aka iso wajen da rukunin dakunan barcin fursunonin

haka bai kamata a kwance masa sarkokin nan ba."

yake sai insam ya hango wani babban daki guda daya wanda ya bambanta da sauran dakunan. Zaune a kofar dakin bisa wata kujera wani narkeken kato ne bakar fata, kansa ya sha asikin kwallin molo, ga katon yari guda biyu a kunnuwansa. Yana da saje gami da murtukaken gashin baki. Wannan bakin mutum ya kasance mummuna kuma dogo ne sosai domin a gabadaya gidan babu mai tsawonsa da kira ta sadaukai face sadauki Gadaraz.

Fursunoni ashirin ne a zagaye da kujerar da wannan bakin mutum ke zaune suna fadanci. Kai da gani ka san shine shugaban fursunonin wannan gida. Duk fursunan da ya zo

wucewa ta gabansa sai ya zube kasa bisa guiwoyinsa biyu ya yi gaisuwa sannan zai wuce. A cikin fursunonin dake kewaye da shi akwai masu yi masa fifita, akwai mai yi masa tausa sannan akwai masu dauke da faratan ya yan itatuwa da abinci da ababen sha kala-kala.

Shi dai wannan bakin bawa ana kiransa da suna Barsad. A iya rayuwar Barsad bisa binciken da akayi ba a taba ganin ya yi murmushi ba sai dai dariyar mugunta. Kullum da koyaushe fuskarsa a murtuke take babu annuri. Zuciyarsa cike take da zunzurutun rashin tausayi da zalunci.

Shi kansa bai san iyakar adadin mutanen da ya kashe ba a rayuwarsa.

0 Comments

Leave a Comment

Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search


Recent Article
FOODS THAT CAUSE ACNE AND PIMPLE
FOODS THAT CAUSE ACNE AND PIMPLE
Read MoreFOODS THAT CAUSE ACNE AND PIMPLE
REASONS WHY YOU SHOULD CUT DOWN ON SUGAR
REASONS WHY YOU SHOULD CUT DOWN ON SUGAR
Read MoreREASONS WHY YOU SHOULD CUT DOWN ON SUGAR
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Read MoreStop doing these things if you don't want to damage your looks
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
Read MoreHEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
Read MoreSIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
Read MoreTHE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
WORST FOODS FOR BELLY FAT
WORST FOODS FOR BELLY FAT
Read MoreWORST FOODS FOR BELLY FAT
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
Read MoreMOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
WATA FUSKAR CHAPTER 2
WATA FUSKAR CHAPTER 2
Read MoreWATA FUSKAR CHAPTER 2
GWARZON SADAUKI PART 4
GWARZON SADAUKI PART 4
Read MoreGWARZON SADAUKI PART 4