GWARZON SADAUKI PART 3

Mr Novel

  

03 May 2025

300

GWARZON SADAUKI PART 3


 

Yanzu ne dubunsa ta cika aka kamo shi da kyar aka kawo shi wannan kurkuku sakamakon laifin haura gidan Sarkin Kisira da nufin yin sata shi da yaransa mutum arba'in aka yanke musu hukuncin daurin rai da rai.

.Lokacin da Bawa Insam ya zo .zai wuce ta gaban Barsad sai ya kau da kai ya yi kamar bai ganshi ba, ya wuce gaba yana biye da Badakaren dake masa jagora. Kawai sai ya ga Badakaren ya ratse gefe guda ya tsaya cak ya juyo baya, wasu fursunoni kimanin su ashirin suka taho da gudu suka yi wa Insam kawanya. Daya daga cikin su ya dube shi a fusace ya ce.

"Kai wannan bakon fursuna kayi ganganci da ka ki sauraron dokokin gidan nan guda tara dazu. To ka sani wancan na zaune shi ne Sarki a gidan nan, hatta dakaru ma shakkarsa suke bare kai fursuna. Dole ne ka rinka gaishe shi sau uku kullum kana durkuso bisa guiwoyinka a gabansa, wannan yana daga cikin dokokin gidan nan guda tara."

Sa'adda Insamn ya ji wannan batu sai ya kyalkyale da dariya sannan ya dubi fursunan da ya yi maganar ya ce.Yau an sami Sarki na biyu a gidan nan, ni ma sai dai a rinka gaishe ni kamar yadda ake gaishe shi

Kafin Insam ya gama rufe bakinsa tuni fursunonin da suka kewaye shi sun lullube shi da duka, sun durkusar da shi kasa. Kawai sai aka ga ya yunkuro sama ya watsar da su

duka, wasunsu suka yi sama tamkar da majajjawa aka janye su suka gwaru a jikin gini suka zubo kasa. Fursunonin suka sake tasowa da sauri suka rugo kansa aka ruguntsume da fada.Duk fursunan da Insam ya nausa sai a ga ya baje a kasa, ya kasa mikewa idan kuwa kafarsa ya doka ko hannunsa sai dai a ji ya kurma ihu sakamakon karyewar kashinsa.

Kafin cikar dakika dari da ashirin ya bazar da fursunonin ashirin a kasa an rasa dayansu da ya iya mikewa tsaye.

Ko da ganin haka sai sauran fursunonin da ke wajen gabadayansu suka yunkuro za su afkawa insam amma sai Barsad ya daka musu tawa suka tsaya cak.

Barsad ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune ya tako da kafafunsa tamkar wani toron giwa ya zo daf da Insam ya tsaya kai kace zaki ne a gaban kyanwa sabuda bambancin girmansu. Barsad ya sunkuyo da fuskarsa daidai kan ta Insam ya ce.

"Kai yaro ai ba a sarki biyu a birni guda. Shekarata bakwai a gidan nan ba a taba samun tsageran da ya yi mini rashin kunya ba sai kai.

Tabbas kwarin zuciyarka ya burgeni sai dai ka yi a banza domin yanzu zan kare maka ruhin numfashinka.

Sa'adda Insam ya ji wannan batu sai ya yi murmushi kuma ya juyawa Barsad baya cikin jin izza gami da yarda da kai ya ce "Ba za ka iya kashe ni ba face kwanakina sun kare, ka ja mutuncinka da kimarka in ba haka ba kuwa za ka ji kunyar da ba ka taba ji ba." Kafin Insam ya gama rufe bakinsa, Barsad ya kawo masa wawan mangari a wuya. Cikin zafin nama Insam ya sunkuya hannun Barsad ya doki iska. Nanfa sukad kacame da

masifaffon fada, ya zamana cewa Barsad na kai wa Insam naushi da bugu hannu da kafa yana karewa da hannu da kafa. Duk sa'ad da suka hada jiki sai ka ji kamar duwatsu ne suka hadu. Nan fa mamaki ya kama gabadayan fursunoni da dakarun dake wajen. Sai da Insam da Barsad suka shafe kusan dakika dari uku da arbain suna gwamarzuwa. wamma dayansu bai sami nasarar nausar wani ba, a inda zai jigata ba.

Ko da suka ga wannan naushi da bugun da suke wa juna babu nasara sai suka ja da baya suka yi cirko-cirko suna kallon juna kamar zakaru.Kowannensu tunani da mamaki yake a

cikin ransa bisa ganin yadda karfinsu ke neman zuwa daya.Nan fa suka fara tunanin dabarar da ya kamata su yi don samun nasara. Kawai sai Barsad ya daga hannun sa guda take wani daga cikin yaransa ya jefo masa takobi ya cafe.

Ko da ganin haka sai Insam ya daka tsalle sama daga inda yake tamkar daga cikin baka aka harba kibiya, ya yi wata irin alkafira a sama ya fizgo kulaken wadansu dakaru guda biyu daga hannayensu sannan ya diro kasa bisa kafafuwansa yana mai gyara tsayuwa.

Gabadaya dakaru da fursunonin dake wajen ba su san sa'adda suka

kama yi wa Insam tafi ba saboda ganin irin wannan gagarumar bajinta da ya yi. Dole ne Insam ye burge duk wanda ya ga yadda ya iya wurkala jikinsa a sama tamkar mazari.

Cikin fushi Barsad ya dubi dakarun da fursunonin yana mai daka musu harara. Nan take kowa ya yi sauri ya sunkuyar da kansa kasa.Faruwar hakan ke da wuya sai Barsad ya rugo izuwa kan Insam yana mai kwarara uban ihu mai matukar firgitarwa. Karar' takun sawun kafafunsa suka cika dodor. kunne, ihun nasa kuwa ya firgità kowa dake wajen amma shi Insam ko gezau bai yi ba,gyara tsayuwarsa

yana jiran isowarsa.

Barsad na riskar Insam sai suka ruguntsume da sabon azababben yaki mai matukar hadari da ban tsoro.

Barsad ya rinka kai wa Insam sara da suka da takobi cikin tsananin zafin nama shi kuwa Insam ya rinka karewa. Duk sa'adda takobin Barsad ta hadu da kulaken sai dai ka ji karar haduwar karafa kuma tsartsatsin wuta na tashi sakamakon cewa kulaken da karfe aka yi su.Nan fa Barsad ya dage iya karfinsa yana kokarin tafkawa Insam munanan sara domin ya tsarge shi amma sai abu ya gagara.

Haka dai suka ci gaba da bakin gumurzu wanda ya dagunzuma hankalin kawo

a wajen saboda

kuskure daya zai iya janyo hallakar dayansu.

Shi ma Insam yana ta kokarin ya gabzawa Barsad kulaken a fuskarsa kò a kansa amma bai sami damaba.

Ko da suka shafe kusan dakika dari bakwai a cikin wannan bali sai suka sauya salon fadan suka hada da kai wa juna naushi da bugu hannu da. kafa, sai ga shi kowannensu yana amfani da damarsa da hagunsa. Nan

fa suka fara hadawa junansu jini da

majina amma kuma kowannensu na iya jure naushi dabugun takar jikinsu ba na jini da taoka ba. Da zárar dayansu ya fadi kasa sai a ga ya yi zumbur ya mike an ci gaba da fafatawa.Ana cikin haka ne gumu ya kai gumu makaman kowannunsu suka zube suka cakume da kokawa, su fadi nan su tashi can, suka rinka fadawa kan tarkace da gine-gine. Idan kan teburi suka fada ko kan kujera sai dai ka ga sun ragargaje babu abin das ya daurewa kowa kai face ganin yadda duk girman Barsad a kan Insam sai ga shi karfinsu na neman zuwa daya domin a wannan gumurzu kare jini biri jini ake yi.

Kwatsam sai aka ga kowa ya danki wuyan kowa •suka shake junansu sai ga shi idanuwansu sun zazzaro har numfarfashinsu ya fara daukewa.' Tsulum sai akaga

shugaban dakarun Gadaraz ya bayyana a gabansu tamkar aljani

Kawai sai ya sa hannayensa biyu ya doki wuyan kowannensu akan wata. Take duk su biyun suka sulale kasa sumammu.

Faruwar hakan ke da wuya sai Gadaraz ya dubi wadansu dakaru guda hudu dake tsaye a wajen sannan ya bace bat daga wajen. Nan take dakarun hudu suka yi wa Insam da Barsad kama-kama suka daukesu daga wajen.Lokacin da Barsad da Insam suka farfado daga dogon suman da suka yi suka tsinci kansu a inda aka


 

 

0 Comments

Leave a Comment

Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search


Recent Article
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Read MoreStop doing these things if you don't want to damage your looks
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
Read MoreHEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
Read MoreSIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
Read MoreTHE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
WORST FOODS FOR BELLY FAT
WORST FOODS FOR BELLY FAT
Read MoreWORST FOODS FOR BELLY FAT
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
Read MoreMOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
WATA FUSKAR CHAPTER 2
WATA FUSKAR CHAPTER 2
Read MoreWATA FUSKAR CHAPTER 2
GWARZON SADAUKI PART 4
GWARZON SADAUKI PART 4
Read MoreGWARZON SADAUKI PART 4
WATA FUSKAR CHAPTER 1
WATA FUSKAR CHAPTER 1
Read MoreWATA FUSKAR CHAPTER 1
GWARZON SADAUKI PART 3
GWARZON SADAUKI PART 3
Read MoreGWARZON SADAUKI PART 3