
To kuma washe gari dai-dai lokacin da suka fito lecture suna zaune gindin inuwa suna hutawa
Fatimar ta hangosu zaune, sai ta iso wajensu ba zata, sai dai suka ji sallamarta. Idanuwan Idris tar! a kanta sai yaji faduwar gaba ya yin da Jibrin ya amsa mata da sakin fuska. Ta ce, "Sannunku da hutawa"
. Idris ya sauke kanshi yana duba wani littafin da ke hannunshi, a ganinshi babu dalilin da zaya sanya yarinyar ta rinka shige masu irin haka. Ko da yake duk laifin na Jibrin ne, shi ya sakar ma ta fuska, sai wani rawar jiki yake yi da ita, ya ga farar fata. Shi kau haka Allah ya yi shi sam lamarin mace baya gabanshi. Kai hidimar karatunshi ma ta sha mashi kai, yaushe za ya tsaya bata ma kanshi lokaci akan yan matan yanzu da basu da tabbas?
Yana jinsu suna gaisawa da Jibrin, bai sanye masu baki ba, to ita kuma sai hankalinta yafi karkata akan Idris din, ta lura yafi kamun kai, burinta ke nan ta samu wanda ta san yafi ta kokari da za ya rinka wayar ma ta da kai a kan komai. Ta tsura mashi ido a sanyaye ta ce, "Yayana bamu gaisa ba. Ina kwana?". Sai ta dora mashi nauyi, ko ba komai yaji kunya, sai ya dago kai yana murmushi ya amsa ma ta. "Kin tashi lafiya. Ya ya makaranta?". Ta amsa,
"Lafiya lau". sai ta nemi wuri ta zauna a hankali suka fara hira akan abin da ya shafi karatunsu. Ya yin da Idris ya rika nazarin kalamanta ga alama
yarinya ce sosai, sai dai tana da kamun kai, ta fadi masu sunanta Fatima Shattima, ta zo ne daga jahar Barno. Shi kuma Idris ya fadi ma ta sunanshi Idris Abdulsalam, mahaifinshi dan asalin Pataskum ne Jahar Yobe, amma suna zaune cikin garin Bauchi, ya yin da Jibrin ya ce, "Sunanshi Jibrin Musa. Anan garin Jos yake zaune".
Basu rabu ba ranar sai da suka kulla abota mai karfi. Idris ya rinka yi ma ta nasiha akan kada ta biye ma lalatattun 'yan mata ta bata rayuwarta, ta zauna tayi karatunta da zuciya, da haka ne za ta cimma burin rayuwarta. Ya daukar ma ta alkawarin cewa zaiyi tsayin daka ya ga ya taimaka ma ta akan komi, amma da sharadin idon ta kama kanta, don shi baya son sakarci'. Sai taji dadi. Da za su rabu suka
yi ma ta alkawarin za su hadu da yamma su yi lecture tsakaninsu. Hankalin Fatima ya kwanta da su. Dama abin da take so ke nan ta samu wanda za ya rinka taimakoa ma ta. Don haka da yamma da wuri ta fito suka hadu, kusan ita ce tafi karuwa da zaman da suka yi. Tayi mamakin irin kokarin da mutanen ke garesu daga ciki har ta gaza gane wanda yafi wani cikinsu.
Tun daga lokacin tayi iyayen daki, idon dai ba su da lecture to kuwa tana tare da su. Haka nan duk lokacin da suka ga za ta yi wani abu da bai dace ba za su tsawata ma ta, abin da ya kawo muguwar shakuwa tsakanin su ke nan, idon ka gansu sai kayi tsammanin yayyenta ne, ko kuma dama sun san juna. Yau da gobe lokaci na tafiya sai ya zamo Idris ya fara nuna ra'ayi a kanta sabo da yarda da yarinyar, kuma ya yaba da halayenta. Shima dai Jibrin ya so hakan, to sai dai shi ba wai so bane na tsakani da Allah, sha'awace kawai, ya nemi ya jata jikinshi amma yarinyar taki amincewa, sai ya zamto ko zaune suke tafi mai da kai wajen Idris, kuma shima Idris din ya zuba ido sosai akanta, ko hangota ya yi tana magana da wani nan da nan za ya bata rai, kuma sai ya tambayeta abin da ya hadata da shi. Ire-iren abubuwan da suka sanya dole ya zuba ma ta ido ke nan, baya so su samu matsala da Idris din.
To kuma sai gashi karara Idris din ya fito ya nuna sonta yake yi. Kafin ya farga sun kulle da wata irin asirtacciyar soyayya da sai mutum ya zauna da su sosai ne za ya iya fahimtar halin da suke ciki, ko shi sun sanya shi cikin duhu, sai da ya gaza daurewa, ya tambayi Idris din sannan yaji daga bakinshi. Tun* daga lokacin ya daina tunanin komi akan Fatimar ya sallama ma Idris, ko da wasa baiyi tsammanin soyayyarsu za ta yi karko ba, abin da ya dauka kawai ta dan lokaci ne da zarar ya gama ya tafi shi ke nan. To shi kau Idris da gaske ya ke yi da nufin aurenta yake sonta, kuma itama ta amince mashi, idon suka zauna su kadai hira suke yi sosai tare da tsara yarda abubuwa za su kasance masu.Ta bashi tarihin rayuwarta.
Mahaifinsu
hamshakin mai kudi ne dan kasuwa, kuma dan siyasa, ya yi fice sosai a Maiduguri da kewayenta.Mahaifiyarsu ce kabilar shuwa, a wajenta ne suka samu usulin kyau nasu, su uku ne 'ya'yanta, ita ce babba sai kannenta maza biyu. Aliyu da Usman, mahaifiyarsu ta rasu sakamakon cutar kansa da ta kamata, sai da ta ci karfinta sannan aka farga, kafin ayi wani abu Allah ya dauki ranta. Sun shiga rikici sosai na rashin mahaifiyarsu. Hatta Babansu ya damu kwarai, kwatsam! Rannan ya jajibo auren wata mata bayaraba Kudirat. Ai kuwa tana shigowa tayi babakere a cikin gidan ta katantance komi, rayuwarsu ta komo gata nan dai, basu da ikon komi ga gidan, haka nan basu da karfi a wajen mahaifinsu, ita ke tsara komi a gidan.A haka suka ci gaba da rayuwa har zuwa
wannan lokaci da ta samu jarrabawarta tayi kyau, kuma ba tare da shawaraba mahaifinta ya nema ma ta karatu a nan jami'ar Jos sai dai suka ganshi da takardu har ya gama ma ta komi. Abin bai yima Hajiya Kudurat dadi ba, sabo da idon tana kaunar yaran tana kaunar mutuwarta. To sai dai tana yin komi ta karfushi kasa, don haka bata fito fili ta nuna ba, sai dai bayan ya fita Fatima ta sha bala'i. Haushi
takeji za ya kashe ma ta kudi tayi karatu alhalin ita tana zaune bata haihu ba, balle ta sanya ran ko nan gaba itama za ayi ma nata. Fatima ta zuba ido kawai addu'a take yi babu adadi Allah ya taimaka mata ta samu ta taho kada ta kulla mata tuggun da za ta sanya ta rasa karatun.
Cikin yardar Allah babansu ya yi tsayin daka sai da ta taho, kuma tun daga lokacin ya bude ma ta account ya kan turo mata kudaden da take amfani da su, bata da matsalar komi, don haka da wuya taje gida, amma komi take yi zuciyarta na tunanin 'yan Kannenta da ta baro. Ta san suna can cikin wahala, duk wani haushinta akansu za a huce shi. To sai dai bata dauka da zafi ba, ta yarda komi lokaci ne, in da rai wata rana sai labari. Ba su da kowa sabo da mahaifinsu bai basu dama suka saba da dangin mahaifiyarsu ba, suma tamkar sun yada su, babu wanda ya neme su. Don haka ba karamin dadi taji ba da ta taho makaranta. A kalla dai ta samu 'yancin kanta tana walawa tayi raha da wanda take so, kuma shi kanshi mahaifinsu yanzu da ta taho yafi sakin jiki yayi ma ta abubuwan da suka kama, sai ta yarda cewa lallai shakkar Auntyn su ke hana shi kyautata musu.Idris ya tausaya ma ta, don haka ya dauki kaunarta da muhimmanci, ya yi alkawarin kyautata mata tare da rikon amanarta ba za ya yaudareta ba,
wani abin da yafi so ga yaron shi ne hazaka ga karatu, yana maida kai ga karatu sosai, don haka dukkan karatunshi mai tsada ya rika biya mashi.Wannan abun da yake yi ne ya kara haddasa wutar kiyayya a tsakanin Hajiya Khadija da Hajiya Ladi, suma ya'yan suka goyi bayan uwarsu. Idon suna kaunar Hajiya Ladidi da danta to kuwa suna kaunar mutuwarsu. Haka ake ta tafiya, rannan kwatsam! Hajiya Ladi ta na bisa hanyarta ta dawowa Bauchi daga Pataskum suka hadu da mummunan hadari da ya yi sanadiyar rasa rayuwarta. Hankalin Alhaji Abdussalam da na Idris ya tashi sosai, amma Hajiya Khadija da 'ya'yanta kamar za su taka rawa dan murna, makiyarsu ta bar dunya.
Bayan komi ya lafa Alhaji ya tattaro Idris da
kayanshi ya dawo da shi cikin 'yan uwanshi. Nan fa suka ce ina wuta su saka shi? Suka sako shi gaba da : kyara, hantara, bugu da zagi kau har ba'a magana.
Abinci sai an ga dama a bashi, haka nan dakin kwanciyarshi ma komi a lalace babu wani gyara, idon har ya samu hutu sai ya tafi makarantar kwana, amma da zaran ya dawo ya gama zama lafiya.
Lokaci kadan duk yabi ya sukurkuce ya lalace, karatunshi yaja baya. Shi kuma Alhaji sai Allah ya aza mashi masifar son yaron, duk inda yaje ya dawo sai ya nemo shi, yana jin zafin irin rikon da ake yi mashi cikin gidan. To sai dai ya yi imanin kwanciyar hankalin shi ke nan ya zuba ido, muddin ya ce za ya rika sanya baki a cikin al'amarin shi to kuwa ya gama zama lafiya.
Ya kan samu lokaci ya zauna da yaron yana lallashi. A haka suka ci gaba da tafiya. Rannan da suka sami hutu yaron da kanshi ya nemi izinin mahaifinshi yana son .yaje hutu wajen kanin mahaifiyarshi dake zaune Jos. Alhaji ya amince mashi ganin yaron baya da kwanciyar hankali, don haka ya sanya ya shirya. Hatta 'yan kayanshi duk sun lalace, sai da suka fita ya tsaya aka sai mashi har da jikka. Da kanshi ya kai ma Abbati dan hutunshi, ya ce idon hutunsu ya kare za ya zo ya dauke shi.
Abbati ya yi murna kwarai Sain da koda yaushe zuciyarshi na tunanin yaron, gashi dama su biyu ne iyayensu suka haifa daga shi sai Hajiya Ladi. Nan Jos yake zaune, yana aikin dan sanda, lokacin yana da mukamin D.P.O. kuma har zuwa lokacin Allah bai bashi haihuwa ba, don haka ya kama Idris hannu bibbiyu ya rinka nuna mashi gata, yana son yaron sosai.
Kwana kadan Idris ya warware, jikinshi ya dawo dai-dai. Lokacin ne ya rinka ba Kawun labarin irin ukubar da yake ciki a gidan mahaifinshi. Sai yaji tausayinshi don haka da hutunsu ya kusa karewa sai ya tafi har Bauchin ya tarda Alhaji ya roki alfarmar ya bar shi da Idris ya zauna hannunshi. To shi kanshi Alhajin hankalinshi yafi kwanciya da yaron ya bar gidan, zaluncin da tauye hakkin da ake yi mashi ya isa, don haka ba tare da jayayya ba ko musu ya amince mkashi ya bashi rikon Idris. Mafarin zamanshi garin Jos ke nan,
Ya ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali yana samun kyakkyawar kulawa, gashi yana ci gaba da karatunshi mai kyau, kuma yana samun kyakkyawan sakamako har ya kammala karatun sakandare. Lokacin Kawun ya matsa mashi yaje ya dubo mahaifinshi sabo da kwana biyu ya rabu da zagayo su, gashi lokacin akwai karancin hanyoyin sadarwa. Don haka ya shirya yaje sai dai bai ji dadin zuwan da ya yi ba, sabo da cikin mawuyacin hali ya tarda Alhajinsu yana fama da cutar Kansa (Cancer) a kafarshi, ciwon ya ci karfinshi sosai. Ranar ya yi kuka sosai, gashi babu wata kyakkyawar kulawa da ake yi ma shi daga Hajiya Khadija har 'ya'yanta harkar gabansu kawai suke yi suna fantamawa da dukiyarshi da motoci basu damu da halin da yake ciki ba.
Dole ta zauna tare da shi sai da ya samu wata daya yana jinyarshi, daga nan Hajiya Khadija ta ce,Fita za a yi da shi waje sun samu labarin wani asibiti a Germany za su kai shi." Sai da suka shirya komi na tafiyarsu sannan ya yi sallama da mahaifinshi suna tafiya shima ya koma Jos ya ci gaba da zama cikin halin zullumi da juyayi.
Satinsu hudu suka dawo an yi aiki an cire kafa daya, lokacin yaje dubashi Alhaji ya rinka yi mashi nasiha akan ya yi hakuri ya zauna da kowa lafiya, kuma ya bi rayuwa a sannu. Haka nan ya daure duk rintsi ya yi zumunci da 'yan uwanshi kada ya kula abubuwan da suka yi mashi. Sannan ya tsaya kan gaskiyarshi, duk rintsi ya nemi na kanshi, kanda ya dogara ga abin wani,ya sanyama zuciyarshi tsoron Allah. A karshe ya ce ya rinka yi mashi addu'a Allah ya bashi lafiya.
Idris ya yi kuka sosai, ya dauki alkawari za ya kula da dukkan abubuwan da ya fadi mashi.
Hankalinshi ya tashi sosai, ya tabbatar yanzu ba ya da kowa bai ga alamar tashi a wajen mahaifinshi ba.
Kwananshi biyu da zuwa sai ga Kawunshi ya zo duba Alhaji, shima ya tausaya mashi ya yarda rayuwar duniya ba matabbata bace.
Alhaji na kuka ya ce, "Abba ga amanar Idris nan na baka, nayi imanin za ka yi mashi dukkan abin da zaka yi ma dan cikinka, ka ci gaba da rikonshi riko na amana, ka tarbiyantar da shi da halaye masu kyau, ka tsaya mashi ya samu ilimi mai kyau, idon kayi mashi 'yar uwarka ka yi mawa, kuma nima ka taimaka mani sabo da hakkinshi a kaina yake, sai dai rayuwata ta zo karshe, gashi 'yan
Leave a Comment
Your email will be kept private. Required fields are marked *
Search
Categories
-
(2)
-
(3)
-
(4)
-
(8)
-
(12)
-
(1)
-
(11)
-
(0)
Recent Article
Stop doing these things if you don't want to damage your looks
Read More
HEALTH BENEFITS OF DRINKING GREEN TEA
Read More
SIGNS YOU’RE IN A MENTALLY ABUSIVE RELATIONSHIP
Read More
THE BEST FOODS THAT MAY HELP YOU LIVE LONGER
Read More
WORST FOODS FOR BELLY FAT
Read More
MOST ADDICTIVE DRUGS IN THE WORLD
Read More
WATA FUSKAR CHAPTER 2
Read More
GWARZON SADAUKI PART 4
Read More
WATA FUSKAR CHAPTER 1
Read More
GWARZON SADAUKI PART 3
Read More
0 Comments