Showing 3001 words to 6000 words out of 19186 words

Chapter 2 - SAUYIN LAMARI BOOK 2 HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

36

karye gaba d'aya sun zama maruru kaman kuna sai uban ruwa da kafafun ke yi. Yau tsananin azabar data tashi da ita taita ihu cikin d'akin ta kaman mahaukaciya. Kiran duniya anyiwa Asiya amma shiru ka ke ji. Tana can tare da Jojo ko ta kan Moha da auren ba bata bi. Tana ganin yanzu tayi wauta data nacewa auren Moha. Jojo ita ce wacce take so . Maganan Jojo gaskiya ce da tace. Yanzu bata da y'anci kanta sai abunda namiji yace mata tayi. Abunda bazata yarda dashi ba kenan. Babu wanda ya isa ya hanata jindaɗin rayuwa.

Hankalin Balaraba ya tashi matuƙa da ganin irin rashin ci gaba da kafafuwan nata suke gashi, Suwaiba itama kwana biyu shiru bata jinta bare ta samu labarin abunda ke wakana a waje. Ita kam sam batayi sa'ar haihuwa ba. Daga Asiya har Isma'il babu wanda ya damu daya zo ya dubata ko sau d'aya. Ganin abun babu sarki sai Allah ta kira Daddy tana kuka da magayi yasan yanda za'ayi a fita da ita waje a dubata, kafa taki kyau. Washegarin ranan da sukayi waya ya dira a AZARE. Babu jiran komai ya juya da ita India don a can ya yi mata transfer na asibitin. Duban farko manyan likitoci da suka had'u a kanta suka ce k'afa ta rube sai dai a yanke su duka. Wayyo Balaraba kad'an ne bata had'iye zuciya ta mutu ba jin wannan mummunan magana. Sai taji ina ma bata zo duniyar ba. Ranan duk wanda yaga Balaraba saiya tausaya mata ta jeme ta k'ode duk ta fita hayyacin ta .Daddy duk yanda yake jinta a ransa haka ya wuni yana bata kulawa cike da tausayi. Yanzu tasan ba komai ke bibiyar ta ba sai hakkinsa. A ranan kuwa kwana tayi tana neman gafarar sa da gaya masa dukkanin irin abubuwa da take yi masa don ganin ta mallake shi da dukiyar sa. Sosai ran Daddy ya sosu amma duk da haka ya cigaba da zama da ita har aka zo shiga da ita aiki. Tayi kuka tayi kuka kaman me tana neman yafiyar sa data Moha aka shige da ita theater.

Saboda aiki ne dake buƙatar nutsuwa da hankali ba'su fito da Balaraba ba sai dare. Lokacin Daddy ya yi kira dangin Balaraba ya sanar dasu abunda ke faruwa. Asiya da Isma'il babu wanda ya nuna wata damuwa kan abunda sukaji bare suyi tunanin zuwa duna Uwar tasu.



21/25.





Washegari Jadwah ta tashi da kiran wayarta da Moha ya yi. Bayan tayi sallan asuba ta shige bargo ta kundune saboda sanyi da ake. Bata jima da fara barci ba wayarta ta fara ringing saman drawer. A hankali ta miƙa hannu ta d'auko tana kallon sunan Moha dake yawon saman screen din wayar. Baki ta d'an cije idonta na hasko mata abunda ya faru jiya tsakanin su. Wani irin yanayi taji ta tsinci kanta a ciki ta kasa d'aga wayar harta tsinke wani kiran ya k'ara shigowa. A kasalance ta d'aga wayar tana sauke y'ar b'oyayyiyar ajiyar zuciya. Shima nashi b'angaren numfashi ya sauke a hankali yace

"Baby"

Lumshe ido tayi saboda irin sigar daya kisa sunan mai kashe ga'b'ba da sassan jiki.

"How are you?, did you miss me?"

Buɗe ido tayi tana d'an turo kaman na shagwaɓa da ita kanta bata san tayi ba tace

"Saboda me zanyi missing naka?"

Sautin murmushin sa taji ya fito ta wayar yana cewa

"Don't lie. Nasan kinyi enjoying precious time namu jiya. And I cannot wait for it to happen again. Zanyi making show na baki pleasure da zaki dinga screaming sunana"

Kitt ta kashe wayar jikinta yana rawa. A lallai ta yarda maza basu da kunya. Tsintar kanta tayi tana murmushi haka kawai take jin nishaɗi tattare da ita. Kasa komawa barcin tayi ta miƙe ta fito ta hau gyara musu gidan kafin ta shiga kitchen d'ura musu abinci.

B'angaren Moha wani irin murmushi ya saki ya rungume wayar kan k'irjinsa yana tunanin abubuwa da dama. Bai dad'e da kashe wayar ba kiran Amina ya shigo wayarsa. D'auko wayar ya yi a take yaji ransa ya b'aci. Yana d'agawa sautin kukanta ya fara ratsa dodon kunnen sa.

"Haba Yayanmu. Saboda Allah kayi min adalci kenan?. Ace a matsayina na Amarya ka a kawoni gidanka amma ango bai kwana a ciki ba. Anya yanzu kana sona kuwa?"

Numfashi ya fesar yana d'an jin bai kyauta ba, amma daya kwana gurinta harta buk'aci wani abu ya kwammace ya kwana wani gidan. Shi a yau d'innan ma zai wuce Dubai da Jadwah don haka ya bata amsa

"Sorry aikine ya gaggauta ya taso min. Anjima inshaAllahu zan wuce Dubai zanyi miki booking flight idan naje sai ki taho"

Yana gama fad'in haka bai jira amsarta ba ya kashe wayar sa ya miƙe ya shige banɗaki ya watsa ruwa. Fitowa ya yi ya shirya cikin maroon d'in riga mai dogon hannu da kwala, sai farin wando daya sa. Sosai rigar ta kwanta tsan kan faffaɗan k'irjin sa da balle botira gudu uka, hannun rigar ya tattshi zuwa gwiwar hannun sa. Tsintsiyar hannun sa sanye da dankareri daimon watch. Kai tsaye ya fito ya yi gidan Gwagwo don karyawa. A hanya suka yi waya da Lameen da zai biyota nan cikin jirgun su su wuce Dubai.

Jadwah na zaune da y'ar k'aramar riga data kama jikin saita d'aura zani kanta babu d'ankwali ta tufke gashin kanta ta saki jelar ta sauke k'asa. Kosai take soyawa hankali kwance gida gaba d'aya ya kaure da kanshin suyar. Gefe kuma tayi musi gashin kaza da roma da soyayyar agada. Sai shayi data dafa musu da yaji kayan kamshi. Babu zato Moha ya yi sallama ya kutso kai cikin gidan. Saboda karatun Qur'ani data kunna a wayarta tana bi da zazzakar Muryar ta mai dad'i bataji sallaman nashi ba ,bare taji shigowar sa. Cak ya tsaya bakin k'ofar kitchen d'in ya zuba mata manyan Blue eye's nashi. Wani irin numfashi ya sauke ya matsa jikin kitchen d'in ya jingina da bango hannuwansa zube cikin aljihun wando. Sosai yake jin wani irin dad'i karatun da take kaman tana rera wak'a. Tsawon minti biyar ya d'auka tsaye bakin k'ofar yana kare mata kallo. Tun daga kan dogon gashinta daya sauka a k'asa har zuwa kugunta da shape d'in sa ya fito sakamakon zaman da tayi. K'asa ya k'arayi da idansa zuwa hip's nata da kujerar ta kasa d'aukan su. Wani irin lashe lebe ya yi wata matsananciyar sha'awar ta na ratsa sassa sa gabban jikin. Muryar Gwagwo da yaji bayansa yasa shi o saurin juyawa yana kallon Gwagwo data fito sanye da hijabi da carbi a hannun ta. Tana yin sallan Walaha taji shigowar sa.

"A'a Taheer. Ka tsaya kuma a nan ka shiga daga ciki mana"

Y'ar kunya ta kama Moha saboda kallon data riska yanawa Jadwah. Gwagwo ba yarinya bace tasan kallo da dama. Kai ya soso ya d'an sunkuya yana gaisheta kafin ya d'an k'ara kai kallonsa kan Jadwah data sandare a zaune ta kasa motsi jin muryar Gwagwo na magana. Da taji tayi kiran sunan Taheer gabanta ya yanke ya fad'i wani ya shigo ya ganta babu hijabi. Amma jin muryar Moha na gaidata tayi suman zaune. Haba biri ya yi kama da mutum, ita tun d'azu jijinta ke bata ana kallonta amma saboda yanda hankalin ta ya yi kan suyar da take da kuma karatun ta yasa bata juyo ba. Tana ji ya wuce ya yi falo Gwagwo ta matso tana cewa

"Maza ki k'arasa ki zubo masa kije kiyi wanka"

Jikinta a mace ta gama had'a abincin ta shirya cikin flask mai kyau ta jera kan flasks ta miƙe ta shige d'aki ta saka hijabi sannan ta fito tayi falo. Hira suke sosai shifa Gwagwo sai dariya suke alamun tana musu dad'i. Gabansa ta ajiye kayan abincin ta yunƙura zata tashi taji muryar sa a hankali da wata irin siga.

"Serve me"

Da sauri ta d'ago ta kalli Gwagwo dake kallon TV kaman bataji abunda yace ba. Jiki na rawa ta zuba masa abincin saboda mayen kallon da yake binta dashi ko kunyar Gwagwo bayaji. Tana gamawa ta yunƙura zata mike ya riƙe hannun ta. Ido waje take kallonsa tana k'ok'arin kwace hannun. Bakinsa ya kai ya sumbaci da d'an k'arfi da sautin tasan babu tantama Gwagwo taji. Wani irin fisge hannun tayi ta zauna k'asa d'abar kafinta tashi sukwanne ta fice daga d'akin ya bita da kallo yana murmushi. Tana fita yaja abinci yana ci sai zuba santi yake Gwagwo nayi masa dariya. Saida yaci ya yi nak sannan ya dubi Gwagwo da d'an taushin murya yace

"Gwagwo yau nake son zuwa gida Dubai . Ummi ta matsu na kai mata Jadwah . Yau nake so zamu wuce da ita k'arfe shida na yamma"

D'an Jim Gwagwo tayi tana tunani tace "bawai naki ka tafi da ita bane Taheer. Kaga bata shirya ba. Akwai shiri da zatayi da zaka yi hak'uri zuwa sati mai zuwa saita bika daga baya"

Harshe ya taune duk da baiso hakan ba. Ya yi murmushi

"To babu komai Gwagwo Allah ya kaimu. Amma ni anjima zan wuce inshaAllahu. Ranan juma'a zan aiko mata da jirgi."

Murmushi Gwagwo tayi tana sa masa Albarka. Yanda taga yana nuna zalama kan Jadwah ai bazata bari ta tafi haka ba bata sha Zuma da zata k'ara rikita masa lissafiba. Kudi ya ciro bandar na dubu sababbi fil ya ajiye mata guda uku. Gwagwo sai godiya take da karin Albarka. Sosai yake jindaɗin Addu'ar Gwagwo ya miƙe zai tafi tace

"Ka shiga ka mata sallama ko"

Kaman kuwa tasan abunda ke ransa kenan don haka ya fice da sauri yana cewa to.

Tana zaune kan gado riƙe da waya tana kallon wani series na PHILIPPINES 'THE LEGAL WIFE' . Tunda na fara ganin film d'in baya wuceta. Kullum saita kalli episodes biyu ko uku. Film d'in kan wasu kawaye aminan juna. Star din film d'in tasha wuya a rayuwar tun tana k'arama har tasowarta. Ta had'u da star ba film din sukayi soyayya har sukayi aure. Daga bisani yaci amanan ta da aminiyarta har suka haihu da ita. Sai take ganin labarin kaman ita da Amina ne. Babu zato taji an karb'e wayar daga hannun ta da sauri ta d'ago idonta ya fad'a cikin na Moha dake tsaye a gabanta. Wani iri zabura tayi ta miƙe tsaye k'irjin ta na harbawa bakinta na rawa tace

"Me...me ka ke anan?"

Bai bata amsa ba ya k'ara matso ta taja baya da sauri ta had'e da gadon babu gurin gudu. Da wata irin murya yana matso ta yace

"What are you watching?"

Tayi saurin dafe k'irjinsa dake shirin had'u da nata.

"Don Allah ka bari. Mene haka wai?"

Tayi maganan kaman zata fashe da kuka. Da tasan halin data jefashi da batayi masa magana haka ba. Leben sa na k'asa ya d'an cije yana kallon d'an k'aramin bakin nata da take turowa.

"Mene me? ,laifi nayi?"

Da sauri tace " eh nanfa dakin Gwagwo ne, bai kamata ka shigo mata d'aki ba kai tsaye"

"Injiwa ya?"

Ya yi maganan kaman rad'a yana k'ara matso da fuskarsa kusa da tata har tana jin kamshin mint breath nashi. Lumshe ido tayi jin yanda numfashi sa ya daki fuskar ta. Hannu ya d'ago a hankali da hankad'a ta tayi baya luu ta zube kan gadon. Yanda abun yazo mata a bazata ta saki y'ar k'ara tana k'ok'arin riƙe shi suka fad'a gadon gaba d'aya ya yi mata rumfa da katon jikin sa. Numfashi ta sauke a wahalce tana kallon sa kaman yanda yake kallon ta ya saka hannu ya dafe gefen kanta ya d'an d'agata kad'an. Wani nishin ta k'ara saukewa idonta ya yi rau-rau.

"Don Allah ka d'aga ni. Wai menene haka? Idan Gwagwo ta shigo fa"

Baice komai ba ya sunkuyo da fuskarsa wajen tata tsinin hancin ya had'e , har zuwa lokacin idonsa na cikin nata. Saida ya hura mata iska kan lebe sannan yace

"To sai me inta gani? Dawa nake tare ne? Matata ko?"

Saurin maida ido tayi ta lumshe bata bashi amsa ba. Kaman jira yake kuwa ya karkata kai gefe ya hade bakin su. Saukar bakinshi cikin nata ta buɗe idonta da suke a waje kaman mujiya. Tana ji ya yi murmushi cikin bakin nata ya fara fisgar lips nata da zafi-zafi. Wani irin zazzafan French kiss yake bata yana gurnani cikin bakinta. Tuni Jadwah ta fara tsurewa ta fara dukansa da neman kwatar kanta. Sai suka ara y'ar kokawa kan gadon suna ta juyi kaman macizai. Sosai yake jindaɗin yanda suke ya k'ara shige mata yana Deeping kiss d'in harya samu damar kama harshenta ya tura cikin bakinsa yana masa wani irin tsotsa da dukkanin notin kanta ya kwance jikin ta ya yi wani irin sanyi kaman an watsa mata k'ank'ara. Wani juyin ya k'arayi ta dawo samansa. Hannu d'aya yasa ya riƙe kanta dashi d'ayan kuma yna shafa gadon bayanta zuwa hip's nata. Ganin yana neman shek'ata barzahu ta kwace bakinta da k'arfi tana sauke wata wahalarliyar ajiyar zuciya. Hakan ya bashi dama ya tura kai wuyanta yana bata zafafan kiss da yana lasan wuyan. Maida hannun ya yi kan Mazaunata ya matse yana d'an bata wani spank. Gasp ne ya fito daga bakinta ta fara k'ok'arin kai hannu ta riƙe nashi dake matsa mata hip yana d'an gugata a jikinta.

"Nashiga Uku" ta furta da d'an k'arfi saboda yanda taji ya matse kugunsa da nata yana gugata a kikinsa da k'arfin kaman wacce ke riding nashi. Nashi ya saki da k'arfi saitin wuyanta yana cigaba da lasanta ta ko ina. K'ok'arin kwacewa tayi ya k'ara matseta yana wani irin gurnani taji ya sakar mata wani d'an cijo gefen wuyanta. Tasan dole ya nuna abunda turawa ke kira da HICKEY. in dai aka ga wannan tabon to an san kin kasance da lover naki. Numfashi taji ya sauke a hankali ya juyar da ita gefen sa ya kwantar. Maida idanuwan ta tayi ta runtse su gam don bazata iya kallom kwayar idonsa ba. Murmushi taji ya yi mai sauti ya sumbaci goshinta da kuncinta ya miƙe ya ajiye mata wayarta da rafar kuɗi guda biyu ya fice daga d'akin. Tana jin fitarsa ta sauke wani gwauran numfashi ta miƙe zaune jikinta gaba d'aya a mace. Gadon ta kalla taga yanda duk ya cukurkude ta miƙe da sauri ta gyara k'irjin ta na harbawa. Yanzu me Gwagwo za tayi tuni ya shigo d'akin ta ya dad'e. Wai anya kuwa dashi da kunya sun had'a hanya?

Inbanda haka har uwar d'akin Gwagwo zaizo ya yi mata wannan abu?. Numfashi ta k'ara sauke duk ta tsargu kanta ta kasa motsawa daga inda take tsaye. Gwagwo ce ta d'aga labulen ta shigo . D'an firgita Jadwah tayi harta kusa baw Gwagwo dariya ta matse ta. Kallo d'aya Gwagwo tayi mata taga yanda duk ta firgice kaman wacce aka kama tana wani mugun abun. Batace da Jadwah komai ta matso ta kwashi kuɗin daya ajiyewa Jadwah ta fice tana kiran Lami mai kayan mata a waya. Ranan haka ta wuni a d'aki ta kasa fita Gwagwo kuwa ta nuna mata batasan me take ba.



To b'angaren Amina bak'in cikin kaman zata had'iye zuciya. Suna gama waya da Moha ta kira Saudat tana kuka ta gaya mata dukkanin abunda ya faru. Saudat taja dogon tsaki

"Kaga shege d'an iska. To wlh in kina da kuɗi yau d'innan ba gobe ki shirya na rakaki wajen Jalli tun wuri ayiwa tufkar hanci. Wannan y'ar iskar yarinyar ba haka take zaune ba na gaya miki. Ke kin tsaya kina jin tausayin ta. Muje a haukata shegiya kowa ya huta"

Wannan karan saboda yanda ran Amina ke suya bata musa ba. Wajen biyar na yamma bayan y'an zuwa ganin d'aki sun watse suka fice ita da Saudat. Saboda babu mota a hannunta tunda Moha bai bata mota ba tukun ,kuma bata so asan ta fice daga zuwanta suka fita suka nemi d'an sawu suka hau. Kai tsaye suka d'auki drop. Saida sukayi tafiya mai nisa sai ya d'auki wata hanya da daban. Daga Saudat har Amina babu wanda ya kuka saboda yanda sukayi zurfi wajen zagin Jadwah da irin tuggu da zasuyi mata. Saida suka nausa sosai cikin jeji sannan suka farga. A rude Amina tace

"Malam ina ne kuma nan ba inda mukace ka kawo mu ba"

Bai basu amsa ba sai d'an sahun daya tsayar tsakiyar dokan daji. Fito ya yi saiga wasu mutane sun fara fitowa bayan bishiyu sanye da bakaken kaya. Daga Amina har Saudat suka rungume juna suna ihu ganin wad'annan mutane dake tunkaro su.



26/30.



Ihu suke suna k'ara k'ank'ame juna. Mutanen suna zuwa suka zagaye d'an sahun gaba d'aya jikin su rufe da bakin kaya da bakin mask. Jajayen idansu kawai ka ke gani. Mai adaidaita ya fita daga motar yana kallon d'aya daga cikin su wanda da alama shine babban su yace

"Gasu nan d'anyen jini ne kaman yanda ku ke buƙata. "

Ai Amina da Saudat najin haka suka k'ara rushewa da matsanancin kuka suna roko Allah da Annani suyi hak'uri su kyale su. Muryar ogan da babu dad'inji yace da d'an sahun

"Aikin ka ya yi kyau. Makashi basu alk'awari da akayi dashi idan ya kawo harka mai kyau"

Wanda aka kira Makashi ya matso ya mik'owa d'an sahu Naira dubu hamsin cif. Jiki na rawa ya shige mota yana kallon su Amina.

"Ku saukar min a mota"

Wani irin rudewa sukayi suna wani irin ihu kaman tabbabbu. Ganin sunki sauka mutanen suka fisgo su daga cikin motar k'arfi da yaji suka saka musu bindiga a ka.

"Wani ya k'ara motsi a cikin ku kuga in ban tarwatsa muku kwakwalwa ba"

Babu wacce ta k'ara ko tari a cikin su sai wani irin kuka suke mara sauti. Sunaji suna gani mai adaidaita yaja motar yabar daji, su kuma Mutanen suka sasu a gaba suka k'ara nausawa ciki sai gasu sun fito wani d'an k'aramin gida cikin dokar dajin. Gidan suka shiga dasu suka tura cikin wani d'an k'aramin d'aki da ko windo babu suka rufe gashi d'akin mai masifar duhu. Kuka suka cigaba dayi da neman agaji. Amina ta fara dana sanin biyewa son zuciya gashi tun ba'aje ko ina ba ta fara girban abunda ta shuka. Saida suka d'auki tsawon awa uku cikin d'akin duk sun fice hayyacin su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login