Showing 6001 words to 9000 words out of 19186 words

Chapter 3 - SAUYIN LAMARI BOOK 2 HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

34

gashi daga ita har Saudat babu wanda ya fito da waya, wai don kar a kirasu aji basa gida. Babu wanda yasan inda suka tafi. Innalilllahi wa Inna'ilaihi raji'un. Wannan wace irin kaddara ce.

Buɗe d'aki a akayi wani ya shigo ya fisge Saudat suna ihu ya yi waje da ita. Amina ta k'ara takurewa tana kuka kaman ranta zai fita. Basu jima da fita da Saudat ba taji ihunta na tashi a waje kaman wadda ake yankawa. Amina batasan sanda wani irin fitsari ya kubce mata ta saki shi cikin matsanancin tsoro tana kuka sosai da kiran sunan Allah. Saudat kam wajen ogan suka kaita. Ashe y'an bindiga ne. Kullum ana kawo musu mata suyi yanda sukaga dama dasu. Wasu in an kawo su idan da rabon suna da sauran kwana suna aure su su zama matan su. Wasu kuma da sun gama abunda suke dasu zasu kashesu ,su bunne. Saudat wajen ogan aka kaita. Kaman yanda suke d'auki sabon jini ne sai yaji ba haka ba. Don Saudat a wage take ba kaman yanda ya yi zato ba. Saboda haushi ba sabon jini bace ya k'ara farke ta kafin ya wullawa yaransa ita. Aikuwa sukayi rubdugu a kanta suna ci kaman sun samu nama. Ihun da Amina ta dinga ji kenan na Saudat kafin tayi ta sume.

Basu jima da watsar da ita ba a waje don sunyi zata ta mutu suka fito da Amina da zawo ke neman kufce mata tsananin firgici da tsoro. D'akin ogan sukayi da ita taba turjewa da kokawar kwacewa. Wanda ke riƙe da ida ya zabga mata mari a take hancinta ya fashe. Duk da uban zafin marin da taji batayi k'asa a gwiba ta k'ara gartsa masa wani uban cijo da babu shiri ya sake ta yana d'ura mata ashar. Ganin ta samu wannan dama ta kwasa a guje ta fice daga gidan ta nausa cikin dokar daji dake bak'ikkirin dashi cikin wannan talatainin daren. Tana jin ihunsu a bayanta suna harbi da zaginta. Amina babu waye ta dinga sharara gudu cikin daji da ita kanta bata san ina take ba. Sosai take gudu tana faduwa har ta daina jin alamun suna binta sun gaji sun hak'ura sun kyaleta, don sunsan babu inda zataje zata mutu. Ko yunwa ta kasheta ko namun daji su cinyeta.

Bata san tsawon awanni data d'auka tana shek'a gudu cikin dokar dajin nan ba. Duk ta fita a hayyacin ta numfashi yana neman gagararta. Duk da haka bata daina sharara gudu ba saida tayi tuntu'be da wani katon dutse ta zube k'asa da mugun k'arfi kanta ya bugu da wani dutsen dake k'asan wajen. A take ta sume bata k'ara motsawa. Allah da ikonsa ashe inda ta fad'i kusa da rugar wasu Buzaye ne. Da gari ya waye JILD'E da yaran sa Habu sun fito don fitar da tirken shanun su kiwo sukaci karo da Amina yashe a k'asa har zuwa lokacin bata numfashi sai jini dake zuba goshin ta inda ta fad'a. Cikin tashin hankali suka d'auki Amina sukayi cikin rugarsu da ita don bata taimakon gaggawa.

Rayuwa kenan. Allah yasa mufi k'arfin zuciyar mu.



Da kyar Jadwah ta iya ajiye kunya ta fito tayi wanka ta koma d'aki tayi salla. Wajen la'asar saiga Lami mai kayan mata tazo har gida kaman yanda Gwagwo tace. D'aki suka kulle da Gwagwo tana mata lissafin kayan da za'a had'awa Jadwah, su gumba da romon kaza da sauran kaya dai na mata. Saida Gwagwo ta lale dubu d'ari biyu cur a take ta bata harda na gyaran jiki da a gobe zata fara zuwa tanayi mata da safe. Washegari Lami ta dawo a shirye da kayan tsumi dana gyaran jiki. Lokacin data shigo ma Jadwah ko tashi batayi ba daga barci saida ta gama kintsa komai cikin d'akin sannan Gwagwo ta tasheta. Basu bata lokacin tambaya ba Lami ta fara murje Jadwah da kayan gyaran jiki. Cikin d'an k'ank'anin lokaci fatarta ta k'ara wani laushi da sulbubi banda uban jike -jike da kullum da irin wanda za'a bata. Ita kanta tana jin yanda jikinta duk ya chanza. Komai nata kamshi yake wando kuwa a rana sai ta saka uku don nan da nan ta jik'e.

Moha kan tunda ya tafi bai kirata ba saboda aiki dayasha masa kyau na taimakon Daddy da yake na campaign. Zabe nata k'ara matsowa kuma yanda al'umman dubai ke nunawa da alamun samun nasara. Ko tunanin Amina bayayi bare ya kirata yaji wane haline take ciki. Asiya nacan UK da Jojo sam babu wata damuwa tattare da ita na ku in kula da Moha ke mata. Hankali kwance take zaune da Jojo data tare yanzu a gidan sun zama kaman miji da mata. Basa tunanin wata rana Moha zai iya zuwan bazata ya gansu cikin wani hali.

Kaman yanda ya yi wa Gwagwo magana ana i gobe zai aiko mata da Private jet ya kira Gwagwo ya gaya mata. Daren ranan bata bati Jadwah ta runtsa ba ta sata gaba da gashe-gashe da d'urin jike-jike. Da asuba ta shirya mata kayanta tsab cikin jaka k'arfe shida daidai ya kira waya ya aiko da mota tana waje tana jiranta zata kaita Airport. Har waje Gwagwo ta rako Jadwah dake k'ok'arin fashewa da kuka . Sanye take da doguwar riga pitch colour kira'ar dubai. K'afarta sanye da d'an flat shoe shima pitch sai y'ar jakatarta k'arama data saka wayarta da charger nata da sauran y'an kayanta. Da kyar Gwagwo ta lallasheta itama tana k'ok'arin hana kanta zubda hawaye ta saka Jadwah cikin had'addiyar motar Honda Sports daya aiko da ita. Gwagwo na tsaye tana d'aga mata hannu har direba ya gama saka kayanta cikin boot ya shiga motar yaja suka bar layin. Bata shiga gida ba saida taga b'acewar motar ta sauke numfashi tana goge kwallan da suka zubo mata ta koma ciki.

Itama Jadwah sosai take kuka cikin motar tana tunanin yau itace zata shiga jirgi?. Itace zata fita wata k'asa da ba tata ta haihuwa ba?. Duka-duka tafiyar minti talatin sukayi suka isa iya Airport. Yaron nasa ya yi komai tun daga kan passport nata har zuwa field d'in jirgin dake jiranta. A hankali cike da nutsuwa ta shiga jirgin tana k'ok'arin hana kanta kauyenci. Yau itace a jirgi? Ita kadai sai ma'aikatan jirgi dake bata kulawa duk bayan y'an mintina. Bata jima da shiga ba jirgi ya rufe ya daga zuwa Dubai.


DUBAI.


Asubar fari suka sauka a babban Airport dake garin dubai. Numfashi Jadwah ta sauke a hankali tana godiya da Allah daya kawata lafiya. A hankali ta juya tana kallon waje ta window inda taga wasu shegun motoci na nufo jirgin. Gaban jirgin suka faka aka buɗe ta tsakiyar Moha ya fito sanye da da k'ananan maya bak'ar riga mai kwala da botira ya d'ura da bak'in wando. Kayan kaman na suits. Ya d'ura katuwar jacket a kansu saboda sanyi da ake. Wani numfashin ta k'ara saukewa tana kallon yanda ya nufo jirgin da wata irin tafiyar izza masu tsaron sa na take masa baya. Tana kallo aka buɗe k'ofar jirgin amma ta kasa tashi har Moha ya shigo cikin jirgin. Ido suka had'a ya sakar mata wani irin kallo mai mashe sassa da gabban jiki. A hanzarce ya k'araso inda take zaune ya d'agata ya matse cikin k'irjin sa. Ajiyar zuciya suka sauke baki d'ayansu wani irin spark ya ratsa su. A hankali yace

"Oh i miss you Baby. Welcome to Dubai "

Batace komai sai take jin wara irin nutsuwa na ratsata. Tanaji ya k'ara tura kai wuyanta yana shak'ar k'amshinta. Sun jima haka a tsaye taga bashi da niyar sakinta ,ta fara k'ok'arin zamewa ya k'ara matsetaa jikin. Chak taji ya d'auke ya yi waje da ita. Da sauri ta fara k'ok'arin sauka a jikinsa ya matse suna fitowa tayi saurin kifa fuskarta cikin k'irjin sa saboda kunya. Haka ya shiga da ita cikin mota tana zaune cinyarsa yaki sakinta sai shak'ar kamshinta yake. Wani katon mansions suka shiga da duk irij kunya ta Jadwah saida ta ware ido cike da kauyenci tana kallon wannan Aljannan duniya. Wata kyakkyawar macec ta fito daga cikin wata had'addiyar glass door sanye da abaya da mayafinta. Kallo d'aya zaka mata kaga Balarabiyar asali. A hanzarce tayo wajen motar tasu fuskar ta d'auke da matsanancin farin ciki. Saida ta buɗe motar sannan Moha ya saki Jadwah da tayi zuru kaman wacce suke wani mugun abu. Cikin tsananin fari jawo Jadwah ta fito daga motar ta rungume tana cewa

"Marhaban biki ya habibty. Barkan ki da zuwa. "

Tafar d'aya Jadwah taci son matar ya ratsa don daga ganinta bata da matsala. A d'an shagwaɓe taji Moha na cewa

"Ni kuma fa?"

Harara Ammi ta watsa matsa taja Jadwah suka shiga gidan duk ta rasa inda zata sata. Moha sai murmushi yake ya rufa musu baya. Zaune had'adden falon suka ga Daddy sanye da farar jallabiya da Jarida a hannun sa. Murmushi ne kwance kan fuskarsa yana kallon Jadwah data durkusa har k'asa tana gaishe shi. Kamata ya yi ya mik'ar yana cewa

"Tashi ,tashi. Yata ce ke kaman yanda yake a matsayin d'ana. Sannunki da zuwa. Habibty a kaita d'aki ta huta ko?"

Da azama Ammi ta matso tana cewa "Na'am. Yalle ya binta "

Hannun Jadwah ta riƙe suka haura sama Moha ya miƙe da sauri zai rufa musu baya Daddy ya riƙe shi yana murmushi.

"Ka bari su gana da Ammin ka tukun. Tana nan babu inda zataje."

Kai ya d'an sosa badan yaso ba yabi bayan Jadwah da kallo da suke haurawa sama. Had'adden d'aki Ammi tayi mata masauki. Banɗaki ta fara nuna mata taje ta watsa ruwa saboda gajiya kafin a kawo mata abinci duk da tasan cewa taci a jirgi. Wanka Jadwah ta fara shiga ta jima tana kallo banɗakin kafin tayi wanka da ruwan da Ammin ta had'a mata cikin kwamin wanka. Saida da murje jikinta sosai sannan ta fito daure da alwala. Ammi ta samu riƙe da wasu kaya doguwar riga da hijabi ta bata ta saka sannan ta nuna mata gabas ta tada sallan asuba. Tana idarwa Ammi ta shigo da katon tire shak'e da kayan abinci. Da kanta Ammi ta zauna tana bawa Jadwah wanda hakan yasa taji hawaye sun cike mata ido tuna mata da tata uwar da tayi.

Saida ta tabbatar ta koshi sannan ta jata ta kwantar kan cinyarta tana yi mata tausar kai. Sannu a hankali kuwa barci mai nauyi ya yi awon gaba da Jadwah da murmushi kwance kan fuskarta. Allah ya k'ara bata wata uwar lokacin da take tunanin ta rasa soyayyar uwa a gareta.



31/35.


Ganin tayi barci Ammi ta gyara mta kwanciyar ta ,taja mata bargo yana murmushi ta miƙe tana kaon Jadwah. Tana tsananin san yara musamman ma mace, gashi kuma har yanzu Allah bai bata ba shekaru ashirin kenan da auren ta da Daddy. Tana fitowa sukaci karo da Moha dake k'ok'arin sawo kai ciki d'akin. Tsayawa tayi bakin k'ofar ta hanashi shiga tana jefansa da mugun kallo. Sosa kai y yi yana d'an tabe fuska na shagwaɓa.

"Ina zaka?"

Ta jefa masa tambaya. Baki ya k'ara turawa gaba. Shikenan kuma shida matarsa an hanashi sakewa da ita.

"Ammi ina son ganinta ne"

"Tayi barci yanzu ya ka barta ta hutu "

Hannun sa ta kama tana jansa yana d'an turjewa da kumbura fuska. Kyaleta ya yi saida suka sauka k'asa suka sami Daddy dake zaune yana kallon news. Jin hayaniyar su yasa shi ya juyo ya kallon yanda Ammin ke jan Moha yana tirjewa da zumbura baki. Dariya ya yi yana k'ara girgiza kai. Wani iri shammatan Ammi Moha ya yi ya fisge da sauri ya kwasa a guje ya haura sama yana dariya. Da ido Ammi ta bishi baki a sake kafin tayi kwafa ta juya tana kallon Daddy da shima ya tuntsure da dariya. Kai kawai ta girgiza ta wuce kitchen. Zai sakko neya sameta.

A hankali ya tura k'ofar d'akin ya shiga. Can kan gadon ya hango ta kundune sai sharar barci take hankali kwance. Murmushi ya yi ya nufi gefen gadon ya zauna kusa da kanta yana k'arewa kyakkyawar fuskar ta kallo. Gata so innocent. Hannu ya mik'a a hankali ya tattare gashin kanta daya zubo mata gefen fuska ya rufe. Murmushi ya k'arayi ya miƙe tsaye. Farar rigar dake jikin sa ya cire ya haye gadon daga shi sai dogon wando dake jikinsa. D'aukan ta ya yi chak ya d'ura kan faffaɗan k'irjinsa ya matse yana shafa dogon gashinta zuwa gadon bayanta. Sannu a hankali barci ya fara fisgar sa yana shak'ar masifaffen kamshi da kanta yake mai shegen dad'i.

Jadwah bata san meke wakana kusa da ita. Saboda gajiya da yanda take jinta kan wani abu mai tsananin laushi da kamshi yasa ta k'ara shige masa ta cigaba da barcinta hankali kwance ya k'ara matseta yana murmushi. Basu suka farka ba sai wajen azahar. Shiya fara farkawa saboda jin muryar Ammi daga can bakin k'ofa tana kwala masa kira. Murmushi ya yi yana kallon k'ofar duk da cewa a buɗe take amma bata shigo. Motsin Jadwah da yaji a jikinsa ya maida hankali kanta tana k'ok'arin buɗe ido. A hankali t buɗe su kan k'irjin Moha da take kwance. Wani irin zare ido tayi da d'ago da kanta idanta ya fad'a cikin nashi. Bata san sanda tayi wani wuntsule ba ta dire gefe tana kallon da zararrun ido k'irjin ta na matsanancin bugawa. Garin ya hakan ta kasance bata sani ba. Hannunsa yasa ya talleb'e k'eyarsa yana mata wani irin kallo tun daga sama har k'asa. A firgice ta juya k'ofa da taji Ammi na kwala masa kira tana cewa zata shigo.

Ganin yanda duk ta rude yasa saki wani d'an murmushi ya miƙe ya d'auki rigarsa yasa yana kallonta. Matsowa kusa da ita ya yi tayi saurin ja da baya. Ya k'ara wani murmushin ya wuce ya buɗe k'ofar ya fice. Aikuwa yana fitowa yaci karo da Ammi dake jiransa. Kunnensa ta kama kaman yanda larabawa suke tana masa fad'a. Shida banda dariya babu abunda yake har da cire d'an takarmi ta kwad'a masa ya fisge a guje ya yi k'asa yana mata dariya harda gwalo. Kai Ammi ta jinjina tana murmushi ta tura k'ofar d'akin ta shiga. A tsaye taga Jadwah tayi tsuru-tsuru da ita. Gadon ta kalla taga babu abuda ya yi ta mayarda kallonta kan Jadwah taga itama kayanta ne a jikin. Saida ta k'ara k'are mata kallo ta tabbatar babu abunda ya faru tsakanin su taja y'ar ajiyar zuciya ta k'arasa shigow tana wa Jadwah murmushi. Yanzuma da kanta ta had'a mata ruwa tace taje tayi wanka. Kafin ta fito ta k'ara gyara d'akin ta kunna turaren wuta. Ammi badai tsabta ba. Ita ta shirya Jadwah bayan ta idar da sallan cikin wata had'addiyar abaya ashe da aka yiwa ado da wasu had'addun dutsawa kama daimon sai sheki suke. Hoda kawai ta shafa mata da d'an lipgloss ta yi mata irin nad'in su da suke na larabawa. Zo kaga kyan da Jadwah tayi sai kallon kanta take tana murmushi, Ammi na fesheta da turaruruka kala-kala masu sanyin kamshi. Hannun ta kama suka fito falon suka iska Daddy da Moha da suka shigo yanzu daga masallacin zaune kan Dinner suna jiran Ammi. Wani irin kallo Moha yabi Jadwah dashi harda lashe baki. Matsanancin kunya yasa ta sunkuyar da kai k'asa tana k'ara mamakin rashin kunyar sa. Kaman wanda ke gaban abokansa ba iyayen sa ba. Dariya Daddy kawai ya yi baice komai sai Ammi ce tayi masa dakuwa ya d'an turo baki yana k'unk'uni. Abinci sukaci mai rai da lafiya irin nasu na larabawa. Jadwah taci abincin babu laifi duk irin matsanancin kunya da takeji. Bayan sun gama ta kira Gwagwo sun jima suna waya har Ammi ta bawa suka dinga waya da Gwagwo kaman wanda suka shekara da sanin juna. Ita dai Jadwah na zaune kan kujera tana murmushi tana jin idan Moha dake zaune kujerar dake fuskantar a kanta. Daddy zaune kusa dashi suna maganan siyaya.

Satin Jadwah biyu a Dubai. Ammi ta kasa ta tsare Moha kad'ai cewa da ita. Don sosai take yiwa Jadwah wani mahaukacin gyara irin nasu na larabawa. Moha ya cika fam kaman zaiyi bindiga. Saboda yanza Ammi ta kasa ta tsare ya daina zama sosai a gidan. Ga kuma yanayin zabe dake k'ara gabatowa. Yau asabar garin Dubai ya d'auka da murna da farin cikin samun nasarar hawa kujera da Daddy ya yi. Duk inda ka wuce za kaga ana murna da celebration. B'angaren Moha da Daddy kuwa abun ba'a cewa komai ranan mutane da sukayi cincirindo a gidan abun sai wanda ya gani. Y'an uwa da abokan Arziƙi kaf babu wanda bai hallara ba. Moha takanas yasa aka d'auko Gwagwo. Sai wayar gari Jadwah tayi da Gwagwo a gidan. Murna da farin ciki abun ba'a cewa komai. Gwagwo da Ammi suka k'ara d'inkewa. Kwanan Gwagwo biyu suka rankawaya gaba d'aya Saudi har Gwagwo do sauke farali. Addu'a sosai sukayi kan wannan Mulki da Daddy ya hau. Allah ya bashi ikon sauke hakkin daya rataya a wuyansa ya bashi ikon Adalci. Saida sukayi sati a Saudi sannan suka wuce ENGLAND wajen Baba. Kai ranan duk wani masoyin Jadwah da Gwagwo saida ya zubar musu da hawaye. Haka suka rungume Baba da suka tarar idonsa biyu suna ta kuka shima saida ya zubda hawaye. Farin ciki ya yi masa yawa ya sake ganin Jadwah da Gwagwo bayan wasu y'an lukata. Kwana biyu sukayo wajen Baba kaman zasu had'iye shi. Sosai suke bashi kulawa bayan wadda likitoci suke masa. Ranan da suka cika kwana uku Daddy ya koma Dubai su kuma sai washegari Gwagwo da Ammi suka wace Dubai d'in. Dan Ammi tace k'afarta k'afar Gwagwo. Nan suka bar Jadwah da Moha sukaci gaba da bashi kulawa. Saida sukayi sati guda Cur Moha ya shirya musu wuce UK.

Ranan kwana Jadwah tayi tana kuka ita babu inda zata. Saida Baba ya yi ta lallashinta da bata baki. Jikinsa alhamdulillah an samu cigaba sosai da sosai. Dan yanzu yana iya tashi da kansa ya d'an taka ya yi sallah. Kwana ranan Jadwah tayi k'irjin Baba, Moha ya sasu a gaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login