Showing 18001 words to 19186 words out of 19186 words

Chapter 7 - SAUYIN LAMARI BOOK 2 HAUSA NOVEL

05 Oct 2025

40

nan. Wannan aikina ne. Ki je ki huta don Allah ki barshi zan cigaba"

Juyowa Ain tayi zace wani abu suka ji muryar Baba yana kira kaman danshi aka rad'a mata sunan. A hankali suka juyo gaba d'ayan su suna kallkn Baba dake tsaye bakin k'ofar cikin manyan kaya. Ya yi kyau abun har ba'a cewa komai. Kallon da yake jefan Ain dashi saida Jadwah taji wata matsanancin kunya ta rufeta. Jadwah ya kalla dake gaidashi fuskarta cike da murmushi. Shigowa ya yi cikin kitchen d'in ya kama Jadwah ya rungume yana sauke ajiyar zuciya idonsa kan Ain dake kallon k'asa. Murmushi ya yi ya janye Jadwah cike da son y'ar tasa yace

"Kin kwana lfy Habibty. Ya kwanan jika na?"

Bata bashi amsa ba sai kai data k'ara sunkuyarwa. Janyeta ya yi daga jikin sa ya kama Ain yana cewa

"Muje Ain. Y'ar ki zata k'arasa"

Badan a Ain taso ba tabi Baba suka fice daga kitchen d'in. Murmushi Jadwah tayi ta juya ta cigaba da girkin. Bata yi cikakken minti biyu ba cikin kitchen d'in taji an rungume ta ta baya. Numfashi ta sauke a hankali tana shak'ar daddad'an kamshin turaren sa mai kashe mata jiki. Gashin kansa dake jike da ruwa ya d'an saukar mata gefen k'afad'a. Hannu ta kai a hankali ta shafi gefen fuskarsa. A haka ta gama girkin yana mak'ale a jikinta kaman zai maida ita ciki.


9MNT Ltr.


Yau gaba d'ayan su suka dunguma zuwa Azare sakamakon mutuwar Balaraba data riske su. Sosai sukaji mutuwar ta ta. Jadwah dake fama da tsohon ciki babu yanda baiyi da ita ba ta yi hakuta zauna tak'i ga Ain itama dake d'auke da nata cikin d'an wata biyar. Sun tausayawa Asiya data rame ta jela ta fita hayyacin ta. Isma'il dai abun ya yi tsanani sai asibitin mahaukata aka kaishi. Yanda taga Moha na nan da nan da Jadwah sai nadama da dana sani suka rufeta. Da ace itama tayi hak'uri bata bi san zuciys ba da wata k'ila itama tana cikin wannan soyayyar. Har suka bar gidan Asiya kuka take sosai. Bayan anyi kwana uku dangin Balaraba dake zaune a kano suka zo suka tafi da Asiya.

Kaman Asiya, haka itama Amina karfi da yaji ta zama y'ar kauye. Tayi sanyi da laushi ga uban baki da tayi. Tun tana kuka harta saduda. Saida taci bak'ar wuya a can sannan mahafinta ya dawo da ita gida. Sosai kuwa tayi hankali. Burinta a yanzu bai wuce taga Moha da Jadwah ba ta nemi gafarar su.

Ina cikin mota za suyi Airport don wucewa Dubai. Nakuda ta tasowa Jadwah dagan dagan. Hankali a tashe suka juya da ita asibiti. Allah da ikonsa suna zuwa ta haufi sankaceciyar Baby Girl nata mai tsananin kyau. Kai murna wajen Moha dasu Gwagwo abun ba'a cewa komai. Ranan asibitin saida aka san Jadwah ta haihu. Don Daddy da Moha haka suka dinga kyautar gidaje da kujerar Hajji. Garin azare kuwa ya d'auka labarin ya riske Amina. Ya Huzaifa tasa a gaba ya taimaka ya kawota taga Jadwah ta nemi gafarar ta kafin subar k'asar. Bai musa ba ya kawota a motar sa. Lokacin kuwa suna ta shirin barin asibitin. Sosai Moha ya b'ata rai ganin Amina. Duk da mutanen dake gurin haka ta durkusa har k'asa tana kuka da neman gafarar sa. Yace shi tuni ya yafe mata. Sanda taga Jadwah ta da irin kyau da girma data kara ta k'ara rushewa da kuka. Sosai take dana sani ina ma dai bata bari shed'an da Saudat sunci galaba a kanta ba. Tayi tunanin zataga wani abu kan fuskar Jadwah sai taga akasin haka. Sosai Jadwah tayi murna da ganin Amina sainan da nan take da ita kace babu wani abu daya tab'a had'asu. Hakan ya k'ara sa jikin Amina sanyi. Yanzu kam yasan cewa ita da Jadwah tafi k'arfinta. Amma ita Jadwah Sam bata nuna mata komai ba. Saida tabi ta nunaw Ummi da Gwagwo ita har Ain . Kowa ya amsheta fuska da walwala. Kaiconta ita Amina tayiwa kanta.

To a daren suka bar Azare zuwa Dubai. Acan akayi walima da kayi wajen sati ana celebrate na zuwan Aishwarya duniya. Sunan Mama taci. Baba sosai ya yi kuka na tunawa da moyiyarsa har saida Ain ta nuna kishinta a fili. Murmushi Baba kawai ya yi yana rungume Aishwarya yanajin so da kaunar ta cikin dukkanin wasu sassan jikinsa. Yawancib walimar da akayi sadakace da kuma saukar Qur'ani. Jadwah taga gata da kulawa. Banda uban kyauta da Moha da Daddy sukayi mata harma da Ummi. Gidaje, motoci kai harma da jirgi duk sun bata. Sannan Moha yasa ake gina gidan Marayu da makarantu da sunan ta.


Alhamdulillah rayuwa babu abunda zasu cewa Allah sai godiya. Watan Aishwarya biyar Ain ta sankota nata Baby boy d'in kyakkyawan gaske dayaci sunan Khalilullah. Kai murna wajen Jadwah kace itace ta haihu. Finally zata zamu kani itama da zasu dinga shawara.


Some years later.


A guje Khaleel ya shigo Aishwarya biye dashi tana kuka. Aishwarya a yanzu dake da shekara biyar Khaleel kuma hud'u da. Falon suke zagayawa yana mata gwala sai rusa kuka take. Baba dake zaune yana karaton jaridar daily trust ya ajiyeta gefe ya juyi yana kallonsu yana kira. A guje Khaleel ya d'ane Baba yana dariya.

"Me kayi mata Khaleel? Baka ga yaya bace"

Baki ya zumbura yana cewa to "Daddy ba ita bace nace ta bani Baby Adeel tak'i. Wai ita kaninta ne. Shi ne nima na d'auke mata Teddy ta"

Kama Aishwarya Baba ya yi ya rungume yana lallashi yace

"Shikenan ya isa. Jeka d'auko mata Teddy nata yanzu ko muje na siyo miki wata ko "

Ai kuwa ta ware ta fara tsalle Khaleel ya b'ata fuska yana kumburi. Ain ta fito daga d'akin riƙe da Simran dake d'an shekara d'aya. Da azama Baba ya karbi yaron yan sumbace ta suka fito sai sukaci karo da Jadwah da Moha da dake k'ok'arin shigowwa sashen nasu.

"A'a Baba fita zakuyi ne"

Eh "yace yana wuce k'ok'arin wuce su. Da sauri Moha yace
"Dama zamu wuce ne muka zo yi maka sallama"

Tsayawa ya yi yana kallon su doj har yanzu yana jin nauyi ace shi yana haihuwa y'ar sa na haihuwa.
"Amma dai a nan zaku barmin Ashwa ko"

Murmushi sukayi gaba d'aya ita dashi Jadwah tace " eh Baba. Sunyi hutu ne. Kasan kuma yanayin hutun su ba irin namu na Nigeria ba. Tana nan har a koma makaranta "

Ai kuwa yaran suka daka tsalle suna murna. Aguje suka wuce wajen mota Baba ya bisu yana kira. Da kallo suna bisu Moha ya k'ara matse Jadwah cikin k'irjin sa da Adeel dake hannun sa sai wangale baki yake. Sunbatar goshinsu ya yi cikin kunne yace mata

"I love you".

Murmushi tayi ta juyo suka had'a ido. Wani kallo suke jefen juna dashi kafin su shige cike don yiwa Ain sallama.


END.



ALHAMDULILLAH. MUN GODE ALLAH DAYA BAMU ARON LOKACI HAR MUKA GA KARSHEN WANNAN LITTAFI. INA GODIYA GAREKU MASOYANA NA FILI DAN B'OYE. ALLAH YA BARMUN KU. KURA KUREN DAKE CIKIN WANNAN LITTAFI ALLAH YA YAFEMU YASA MU AMFANA DA ABUNDA KE CIKI.

SAI MUN SAKE HAD'UWA SABON WANI LITTAFIN NAWA INSHAALLAHU. INA GODIYA❤


ASHANTY LOVE .

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login