Showing 21001 words to 24000 words out of 36837 words
a kanki yana Abu d'aya duba don Allah jini kamar an yanka kaza ai komai a sannu ake binsa."
Ya tsinci kadan daga cikin surutan da take yi don haka ko da ya shigo 'bata fuskar sa yayo don ma kar ta kawo wargi. Ya bude firji hade da dauko goran ruwa Mara sanyi ya nufi gurin Asma'u. Granny ta kalleshi cike da takaici tace"Ka dawo cikin dare kamar wani munafiki ka haikewa yarinyar mutane don rashin imani ba dole tayi zazzab'i Haba! Sai ka yi mu'amula da ita a hankali cikin laluma tunda bata saba ba ni wallahi wannan jinin ya bani tsoro ! Yo ko mu da muke mutan da ai bamu zubar da Wannan jinin ba daran farkon mu."!!
Bai kulata ba, ya d'ago Asma'u da kunya ta kusa kashe ta a gurin yana kokarin bata magani Granny ta kwa'be hannunsa maganin ya zube kasa.!
Hararasa tayi tace"Baza ta sha d'aci ba da safiyar nan ka gama wajigata zaka dauko kayan d'aci ka bata to da sake."!!!
Dariya ya 'kunshe wa yace." Wai ke granny meye ruwan ki ne ? Wannan fa sa'ido ne tsakanin mata da miji ki daina shiga ki k'yale mu, kome ma nayi aike ce kika bani maganin 'karfi."
A hasale! Tace"Dana baka maganin 'karfi sai nace kayi wulakanci son ranka tou Shikkenan tunda ka samu lafiya bazan kuma baka ba balle ka cutar musu da yarinya."
Dariya yasa sosai yana mamakin granny da 'k'arfin halinta... Ganin ya mai da ita shashasha yasa ta futa daga dakin hannunta rike da bedshirt din tana ta faman fad'a kamar ta ari baki.!
Kallonshi nayi a fakaice naga sai dariya yake yi da annushuwa ni ya barni da wahala da cizon leb'e a hankali nace"Kaje ka 'karbo bedshirt din can don Allah."
Ido ya tsira min hade da d'age gidansa guda Yace." Saboda me."? Kauda kaina nayi nace"Bamu kad'ai bane a gidan nasan halin granny zata nunawa mutane."
"Mu da suwaye a gidan."? Yafad'a yana me tsurawa k'irjinta ido kamar wani tsohon maye sai cizar lips d'insa yake. Lokacin shi kadai yasan halin da yake ciki.
A hankali nace" 'Baki muka yi jiya da yamma, Innah da yarinyar ta." Shiru yayi yana tunanin wace Innah take nufi." Yace." Wai Innah Suwaiba ce." ? D'aga masa kai nayi kurrum.
Shiru na minti biyu yana kallona yace." Yanzu wane irin yanayi kike ji a jikin ki."?
"Zazzab'i" na fada ina lumshe idona.... Koka rin shigowa bargon yake yi yana fad'in"Bari kiga abunda zanyi miki yanzu zaki daina jin sanyi.... Rigar ta yake kokarin cirewa na buge hannusa da sauri nace" Don Allah k'yaleni ni kam ka k'yaleni da rigata.!!! Tsaf na fahimci wayon sa tunda naga ya tsira min idona yana cije lips nasan abunda zaiyi..... Da siriryar murya yace." Ni kika bugewa hannu." ? Baki na zumb'ura nace"Yi hakuri ba da gayya nayi ba."
A sake yace." Ok bari in miki fiffita nasan kina jin zafi har yanzu. " kafata guda ya d'aga sama! Na rintse idona cikin jin a zaba nace"Please Abban baby don girmar Allah ka k'yaleni wallahi ni kadai nasan abunda nake ji.""" Amjad da ya fara hawa network yace." Ki bari min ki fiffita a gurin zaki ji sauki ko kuma ki bari in 'kara wani shikkenan kin wuce komai kin dawo babbar mace, yanzu ma don farko ne."
Cikin zuciya ta nace"Wallahi komai nacin ka dole ka rabu dani a zahiri kuwa kuka nasa masa ina bashi hakuri domin na lura da gaske yake...... Da kyar na samu ya bar d'akin.. Yana futa ya tadda granny Innah Suwaiba A tsaye a parlor granny hannunta rike da bedshirt tana wassafawa Innah Suwaiba abunda ya faru kamar wacce aka yi a gabanta take fad'in"Ni yarinyar ta burge ni wallahi na Dade banga budurwar da ta kawo 'yan cinta gidan miji ba.
Fad'ar wannan magana da Granny tayi sai Innah Suwaiba ta tsargu tace." Insha Allah zaki ga budurcin wacce tafi Asma'u daraja a gidanan." Karaf a kunnan sa, sai ya fara mamakin wace macece ce wacce zata fi Asma'u shi daraja a gidansa
*10/12/2019*
[12/11, 1:09 PM] .: *BABBAN YARO*
*83*
Cikin tafiyar sa ta jarumin namiji ya 'karaso tsakiyar parlor inda su granny suke tsaye suna mai da magana. Ina Suwaiba tace." Ka futo yaron kirki."? Zama yayi cikin kujera yana fad'in"E Innah yaushe kika zo gidan." ? Washe Baki tayi tace." Jiya muka zo da yamma ai bani Kad'ai bace tare muke da 'k'anwar ka Hafsa." Yace." Duk ya mutan gida da sauran 'yan uwa."? Tace"Kowa lafiya Lou kuma suna taya ka murna da farin ciki Ubangiji Allah ya taya ka rik'o ." yace." Ameen Innah nagode k'warai. " mik'ewa yayi zai wuce ta dakatar dashi ta hanyar fad'in"Nace dama ai mun dawo kusa dakai da zama duk inda zaka shiga muna 'kungun ka ko da ko gidan gwamnatin ne, arzikin mu ne."
Dariya Ta bashi don haka sai da ya dara tukkuna sannan yace." K'warai kuwa innah amma fa ni wannan mulkin ba son shi nake ba, don dai jama'ar gari sun matsa ne." Tace" A'a mu kam muna so zamu yi ta taya ka da addu'a. " yace." Nagode Innah.''
Yana 'kokarin shiga d'akinsa tace" baka tambayi 'yar Uwar taka ba." Ajiyar zuciya ya sauke al'amarin Innah ya soma bashi haushi yace." Tana ina."?
Tsaki ta buga tace"Tana cikin d'aki kwance jiya daga zuwan mu matar ka ta 'kona ta da soyayya man 'kuli.''
Juyowa yayi cike da mamaki yana kallon Innahr tasa. Granny tace"Haba Suwaiba a dinga Sara ana duban bakin gatari mana, ki bar shi yaje ya kwanta ya huta tukkuna kome sai a ayi ki duba da kyau ki gani yana tare da gajiya ga bacci jiya ya kwana yana ibadar aure."!
Ya'ke Innah tayi tace"K'warai zance ki haka yake ka shiga ka kwanta ka huta Idan yaso in ka tashi sai muyi maganar dole ka jawa matar kunne ta ga mutumcin mu domin mune kai baza ka tab'a janza mu ba."
Amjad ya 'bude dakinsa ya shiga yana mamakin maganganun Innah Suwaiba idan ya fahimci maganar ta tana nufin sun dawo gidan shi da zama kuma tana so ta cusa masa 'yar ta bayan haka kuma yanda ya fahimta tana so ta tayar masa da hankali a cikin gida, sai babban abunda ya d'aga masa hankali shine wai Asma'u ta 'kona Hafsa da mai a gaban granny Tayi maganar yaga bata musa ba tabbas zancan haka yake yi, dole ya sanya ido kuma ya tsawatar matsayin matar shi daban matsayin dangin sa daban amma Sam bazai lamunci zaman Innah Suwaiba cikin gidan shi ba yasan halin matar muguwar 'yar rigima ce.
[12/11, 10:30 AM] BintuUm@rAbb@le: Wayoyin shi dake kan drwoar ciki ya d'auki guda ya kunna tun jiya suke a kashe saboda yasan mutukar ya barshu a kunne babu shakka jama'a zasu dame shi shiyasa ya kashe su, yana kunnawa messages suka dinga shigowa ya aje ta kan bed d'in bathroom ya shiga ya had'a ruwa sosai yayi wanka ya futo daure da towel a kungun shi, ya zauna yana duba sa'konni mutane wasu ma Sam bai San su ba, suna yi masa fatan alkairi, sa'ko har daga Garin mahaifin sa Chadi ya duba iya Wanda zai iya ya aje wayar kwanciya yayi rigingine yana tunanin ta yaya za'ayi ya sallami Innah domin gaskiyar magana sun ta kura masa da sa ido mussaman granny yanzu da babu kowa cikin gidan yasan suna tare da matar shi amma parlor d'aya duk abunda zai yi idonsu na kai. Tsaki kawai yake ja..... Kira ne ya shigo wayar sa, yana dubawa ya numbar Ali 'Dan jaridar nan Ali ya wuce komai a gurin sa ya d'auki wayar had'e da sallama.
Suka gaisa cikin girmama juna Ali yace." Yallab'ai muna Neman alfarma a gurin ka idan zamu samu." Yace." Ali fad'i kome ye."! Ali yace." Muna so zamu yi hira dakai a gidan redion mu yau da misalin 'karfe takwas na dare."
Jim! Yayi yana tunani yace." Babu damuwa insha Allahu zan amsa gayyatar Ku. " Ali yayi mamakin saurin amincewar sa, murna ya yi sosai yayi masa godiya kana suka yi sallama. Aje wayar yayi gefan sa yana lumshe ido, minti biyu tsakani kira ya 'kara shigowa ya bude idonsa had'e da kallon fuskar wayar.....Hibbah sunan da ya gani yana yawo kan screen din wayar, tsaki yaja kawai ya share wayar har ta katse. Wani kiran ya 'kara shigo ..... Dauka yayi ya k'ara a kunnesa ba tare da yace." Kome ba, ita kuma jin ya d'auka yasa ta ma'ke Muryar ta tana fad'in"Zumana ka ya dani ko."? Yana sane yace." Wacece ke."? Hibbah takaici ya ishe ta tace." Nice Hibbah mayar ka, duk wulakancin da zaka mun bazan yi zuciya ba ina sonka ina 'kaunar ka." Idonsa ya 'bude sosai yace." Ke baki da hankali ko bakin San abunda ubanki yayi min ba ne." ? Take tace" Nasan kome zumana, kuma mahaifina a halin yanzu yana cikin tsananin tashin hankali da nadama shine dalilin ma da yasa na kira ka a waya ina me baka hakuri ko don darajar son da nake maka ka YAFE masa domin yana cikin halin damuwa. Amjad yaji zuciyar sa nayi masa zafi da maganganun da take yi masa na shirme yo shi ina ruwan sa da Alhaji Hashimu mai citta can gasu gada kuma Allah ya raka taki gona, don haka a kaurare yace." Hibbah kike ko meye? Ki kula ki kama kanki daga yau sai yau kar ki kara yimin magana makamanciyar wannan duk wata ukuba da mahaifin ki ya shiga shine ya jawa kanshi, ki dauka a rayuwar ki kamar baki ta'ba sanin Amjadu ba a rayuwar ki kuma ki fad'awa ubanki cewa ko da wasa kar ka kuskura ya shiga hurumi na idan bai wasa ba wallahi sai na d'aure shi."!
Hibbah ta fashe da kuka tace"Ni kaka fadawa wad'annan kausasan maganganun naka don kayi sabon aure kuma zaka zama governor shine kake min wulakanci kar ka manta da cewar Kaine ka fara keta min rigar mutumci na wallahi Idan bakayi wasa ba sai na tona maka asiri domin duk abunda ya faru a tsakanin mu dakai INA da pictures d'insa a waya ta."
Yace."Hibbah Idan baki fasa tona min asiri ba bakya 'kaunar Allah da manzon sa kije duk inda zakije ki fad'a cewa ni fasi'ki ne kuma nine na fara sanin ki 'ya mace wannan ba damuwa ta bace taki ce duk abunda zaka yi kije kiyi kanki zaki 'batawa suna a duniya."!! Yana gama fad'in maganar shi ya kashe wayar zuciyar sa na yi masa mugun zafi haka kurrum yana cikin farin ciki da annushuwa Hibbah ta 'bata masa rai da Safiyar Allah.
******
Aunt Hauwa ce tayi sallama cikin gidan su. Umma na zaune a rumfa tana lissafin 'kudi tace." Kece da yamman nan." Aunt Hauwa ta zauna kusa da mahaifiyar ta suna gaisawa tace"Wallahi daga kasuwa nake sai da na fara zuwa gida na aje kaya san nayo nan."
Umma tace"Hakan yayi kyau ai.... Aunt Hauwa tace"Jiya Aminu yaje min da wata magana wacce ta d'aga mun hankali mutuka." Umma tace" Humm al'amarin mutane na da ban mamaki wallahi mutuwa she kara goma sha biyar amma saboda rashin imani da tada zaune tsaye suka 'bullo mana da wannan maganar."
Aunt Hauwa tace"Ni wallahi abun yayi mugun daure min kai ayi abun nan tare da sanin shaidu da sanya hannun kowa amma daga baya a sanja magana."
Umma tace"Duk Ku kwantar da hankalin Ku insha Allahu kamar yanda suka buk'ata din zamu tashi mu bar musu gidan su ko hayane mu kama ai Shikkenan. "
Aunt tace"Insha Allah ba zamuyi haya ba Umma zanje gurin Kawu Yunusa tunda akwai gurare cikin gidan shi ko d'aki guda ne ya baki ki zauna a ciki kafin mu San abun yi."
Umma tace"A'a ni bazan je gidan Yunusa ba kun San halinsa nayi sa dashi ma ban tsira ba balle INA kusa dashi ai har dukana ma sai yayi, Aminu yace." Inje gidan shi in zauna dakin nam na tsakar gida ni kam bana sha'awar zama da suruka gwara inje in biya 'kudina in San na biya babu me yi min wulakanci." Umma ta 'k'arashe maganar ta tana goge hawaye
Aunt taji zuciyar ta nayi mata zafi sosai tace"Umma me za'ayi da rashi talauci baiyi ba a rayuwa amma dole ne in Sanar da Asma'u halin da ake ciki a halin yanzu itace take da dama a hannu kuma mijinta yana da rufin asiri ko sa wani taimako da zata yi mana."
Umma tace"Kul! Kar ki fara domin yin hakan zai zama kamar ro'ko me Asma'u take dashi da zata taimaka Idan ba so kike yi ki koya mata ro'ko ba zamu tashi daga gidanan ba tare da ta sani ba, Shikkenan daga baya sai taji kome ye."
Aunt Hauwa tace"Umma nifa bana sha'awar ki zauna gidan haya wallahi ki bari ayi wa Asma'u magana nasan insha Allahu a siri zai rufo." Umma ta futtuke bata so Dole aunt Hauwa ta hak'ura amma ji take kamar taje ta ciwo bashi ta siyawa Ummsn su gida su huta da ganin wannan bakin cikin.
To 'bangaran Ya Aminu ma tun da ya futa da safe take fafutukar gurin ganin ya samu gurin da Ummansu zata zauna abun ya fassakara da kyar wani abokinsa ya samo masa gida a kurna shima daki daya ne gidan mutum uku ne Umma ce ta hudu tace"Taji ta gani haka zata zauna.
Aunt Hauwa kamar ta mutu don bakin ciki haka ta tattara yana ta yana ta ta bar gidan zuciyar ta nayi mata suya.
****
*Assalamu alaikum jama'a kamar yanda muka shaida muku tun da safe cewa yau zamu yi hira da shararran kuma sanannen mutumin nan da kuka sani a jahar kano wato Amjadu AbulAbbas mainasara Wanda kuka fi sani da Young millionaire gamu tare dashi a yau zai fad'e mana biri har bindinsa zamu ji komai daga bakinsa."* d'an jaridar ya 'kare maganar sa yana gyara wa Amjadu Abun magana dake ma'kale a jikin rigar shi.
Amjad yayi sallama cikin dakakkiyar muryar shi ya gaida jama'ar jahar kano sosai kana d'an jaridar ya d'ora da fad'in" Yallab'ai jama'ar jahar kano suna 'bukatar ka zama shugaban su kamar yanda maigirma shugaban kasa ya basu damar za'bar governor su saboda abunda ya faru, d'umbin masoyan ka suna so suji ta bakin ka suna so suni ra'ayin ka kan hakan."
Amjad yayi gyaran murya a nutse yace." Alhmdullahi Allah ne abun godiya hak'ika babu abunda zance da masoya da jama'ar jahar kano babu shakka sun nuna mun 'kauna ta hak'ika ta inda nake ganin bazan ta'ba bujerewa bukatar su ba, babu shakka na karba kuma zan tsaya ra'ayin daka kan jahar kano domin in kawo cigaba mutukar na zama shugaba a cikinta duk wani 'k'aramin ma'aikici zai samu promotion zan dauki sabbin ma'aikata da suka dace masu bukatar tallafi da kowa ne b'angare gwamnati na zata tallafa musu , zamu yiwa matasa aure zamu basu sana'ar yi kana zamu ya'ki da 'yan daba gami da 'yan Sara suka zamu sanya ido sosai a jahar kano zamu sanya jami'an tsaro ta ko wane fanni zamu kula da marasa lafiya gami da nakassasu zamu yi yak'i da cin hanci da rashawa mutukar Allah ya bamu mulki zamu tsaya mu kula da hakkin Al'umma da izinin Ubangiji. "
Cikin nutsuwa ya 'k'arashe maganar sa.
Jama'ar hajar kano suna ma'kale da redio mussaman matasa sai ihu suke yi jin cewar za'ayi musu aure ayi musu lefe kuma a basu abunyi babu shakka baza su taba mancewa da guy nan ba, ma'aikata kuwa babu Wanda ya kaisu murna jin abunda amjad din yace, wadanda suka aje takkadun su tuni suka fara murna zasu samu aiki da basu samu ba Kai yara da manya dattaija har da mata na cikin gida murna suke yi jin cewar Amjad din yace." Suma zai basu tallafi na sana'oi iri-iri..... Tambayar 'karshe da ta bawa kowa mamaki har shi Amjadu din inda d'an jarida yake tambayar sa da cewar"Yallab'ai munji wani labari daga majiya me tushe shine muke so muji daga bakin ka shin hakane ko ba haka bane ko kuma sharrin magauta ne wai da gaske ne Matar da kake aure a yanzu cikin gidan haya ta 'kare rayuwar ta har ka aure sannan a halin da ake ciki yanzu Wanda suke hayar a cikin gidan ya basu notis domin su tashi su bar gidan hak'ika wannan labari da muka samu ya bamu d'umbun mamaki ta inda muka k'aryar ta hakan saboda sanin da makayu maka cewar kai mutum ne mai taimako da tallafawa Wanda yake dashi hakikanin gaskiya baza ka bar iyayen matar ka cikin gidan yaya ba, yallab'ai muna so muji komai daga bakin ka, sannan muna Neman afuwa a gurina saboda mun San dole ranka ya 'baci dalilin wannan tambayar."
Amjad yayi shiru na tsawon mintina biyar kana ya sauke ajiyar zuciya yace." Wannan maganar da kayi ba gaskiya bace, babu shakka akwai abunda yake rufe Wanda ni dakai da su da kuma ita wife dina bamu sani ba, So nasan dai gidan da suke ciki cikin unguwar Gigiginyu na company ne Wanda ya mallakawa mahaifin ta tun yana raye had'e da shaidu da sa hannu yau shekara goma sha hudu kenan da rasuwar sa wannan shine abunda na sani, amma dole zan bukince kan maganar taka."
'Dan jaridar yace." To babu komai Yallab'ai mungode mutuka da samun damar hallatar mu da kayi muna maka fatan alkairi a rayuwan ka Allah yayi maka jagora ya taya ka rik'o." Amjad yace." Amin suma amin."
Nan D'an jaridar yayi sallama kana ya rufe kayan aikinsa........ Amjadu tun a mota zuciyarsa take masa wani irin ciwo ranshi ya gama 'abaci da abunda Asma'u tayi masa domin shi yana ganin duk laifin ta ne har akazo wannan jalli tabbas ya Dade da sanin mecece siyasa a rayuwa babu sauki a al'amarin duk inda zaka wa mutum baza ka futa ba dole sai ya San yanda yayi ya bata maka rai! Yana mamakin Gidan haya Asma'u suke zaune amma bata ta'ba fada masa ba dole ya nuna mata 'bacin ransa..
*12/12/2019*
[12/11, 10:37 PM] .: *BABBAN YARO*
*84*
Sai wajan 'karfe goma ya