Showing 15001 words to 18000 words out of 36837 words
mai mulkar jahar su, take wasu suka futar da hoton shi a matsayin governor mai jiran gado nan da wata biyu suka dinga bin jikin gidaje da kan titina suna manna kasuwanni da shagunan mutane suka dinga manna hotonan amjadu a matsayin governor.
Duk abunda yake faruwa mun gani labarai Ya Aminu ya kirani a waya yana fad'amin min wai nasan abunda yake faruwa kuwa nace"Gani a labarai Ya Aminu ni bana son siyasa nan fa." ! Yace." Kiyi hakuri ki taya shi addu'a kinji ko."! Ni dai shiru nayi kawai hankalina duk a tashe burina kawai ya dawo gida gashi na kira wayarsa ya kai sau ashirin bai d'aga ba..... Daki na shiga nayi kuka na mai isata na futo na tadda Granny ta jurawa TV ido inda suka nuno Amjadu lokacin da yake bayanin godiya a fadar me girima shugaban kasa. Ta kalleni idonta ya Tara k'walla tace"Zo kiyi min bayani me suke cewa ne naga sojoji sun kewaye shi, ga mutanan masu nacin tsiya sun kewaye shi da na'ura fadamin me yake ce musu jikina duk yayi sanyi.."!
Nace"Granny suna so ne ya zama governor kano babu wani damuwa sai Karin daukaka da ya samu kuma shine yake da nasara a tafiyar wannan 'yan jaridar da kika ga sun kewaye shi duk murna suke taya shi suna so su ji ta bakinsa ne."
Granny tace"Alhmdullahi Allah nagode maka dama nasan addu'a ta baza ta fad'i 'kasa ba nasan 'kato bashi da hakkin su amma ni kam bana sha'awar siyasar nan akwai zube war mutumci da dai su k'yale shi kawai."
Nace"Wallahi nima haka granny bana so amma gashi tun bai dawo garin anji ta bakinsa ba jama'a sun fara fidda hotonan sa a matsayin d'an takara governor ." Granny ta sauke ajiyar zuciya tace"To Ubangji Allah ya dawo dashi lafiya muji ta bakinsa ni dai sanin da nayi wa 'kato baya sha'awar siyasa ban sani ba ko yanzu."
Shiru nayi mata zuciya ta nacan tunanin wani Abu. Mik'ewa nayi na koma bedroom dina waya ta na d'auka ina 'kara kira shi cikin sa'a ya d'aga, ajiyar zuciya na sauke cikin damuwa nace"Abban baby sannu."! Muryar shi bata futa sosai naji yace." Yawwa ya gida babu matsala ko."? Nace"Eh nayi ta kiran wayar ka kana gani ka'ki dagawa." Ajiyar zuciya yayi yace." Sorry sai yanzu wayar tazo hannuna mybe lokacin da kika kira tana gurin Doh-doh."""" Shuru nayi yace." Shikkenan ko."!? Da sauri nace"Amma yau zaka dawo ko."? Kai tsaye Yace."A'a."! 'Kasa nayi da murya ta nace"Meyasa kasan fa ba lafiya gare ka ba." Kwanciya yayi kan bed yana lumshe ido yace." Menene damuwar ki da lafiya ta bayan idan ina nan d'in bakya kula ni. " Naji wani sanyi na shigata jin yanayin yanda yayi magana nace"Baby na kuka abbanta."
'Karya kike yi sai dai idan kece kike kuka kina so in dawo ai na gane. " ya fada yana siriryar dariya , cikin jin nauyi nace"Da gaske nake don Allah yaushe zaka dawo."? Ajiyar zuciya ya sauke yace." Idan na dawo d'in me zaki bani. " ? Shiru nayi masa, yace." Ok bari in kashe wayata." Da sauri nace"Sai dai ka dawo d'in komai kake so."
'Yar dariya yayi yace." Kinyi alk'awari ko." ? Lumshe idona nayi ina jin wani fleengs nace"Eh" yace." Ok sai jibi zan dawo zan huta anan tukkuna hayaniyar gari tayi sau'ki kinsan in na shigo gobe zasu takura min ko baki San abunda yake faruwa bane."!?
Nace"Na sani munga komai a labarai Abban baby na taya ka murna kuma ina maka fatan alkairi har 'karshen rayuwar ka."!. Sosai yaji dadin addu'ar ta yaji yarinyar ta 'kara samun wani matsayi a zuciyar sa yace." Thank you my wife I will not leave you forever."!
Naji dadin abunda yace cikin jin kunya nace "Thank u my life patner."!! 'Kit!!! Na kashe wayar cikin jin kunya gabana sai dukan uku-uku yake ina mamakin yanda na sake har nake magana dashi haka.... Nashi 'bangaran kuwa rike wayar yayi yana sakin wani irin murmushi Wanda shi kad'ai yasan ma'anar shi, ya mike da kuzari a jikinsa ya shige toilet domin gasa jikinsa saboda wani irin ciwo yake masa ni kam nace" Dole ne ko don dambe da kasa kai da Kumurci!
********
Washe garin ranar Innah Suwaiba ta dira cikin gidan ita da 'yar ta Hafsa had'e da 'kullikan kayan su wai sun dawo gidan da zama domin labarin duk abunda yake faruwa ya isa gareta don haka arzikin d'anta ne tunda d'an 'yar uwarta ne itama ta dawo kusa a ci da ita.... Mamaki kamar ya kasheni na dinga kallon matar na marasa a wane matsayi zan aje ta, gaisuwar da nayi mata ma a banzace ta amsa, Hafsa kuwa ido ne tsakanina da ita granny tace"Haba Suwaiba ai ko wani kika kawo cikin gidanan kikace yana so ya zauna zai zauna saboda darajar ki ba sai kin dinga tashin hankali ba don Allah ki dinga yin komai cikin nutsuwa da fahimtar juna." Wannan magana da granny ta fad'a sai Innah tace"ai ta fad'a mata ba'kar magana ta inda take shiga ba tanan take futa ba. K'arshe dai granny bar mata parlor tayi domin baza ta iya da jarabar Suwaiba, dakinta na bita na tadda ta a zaune nace"Granny wannan matar tana so ta d'aga mana hankali a gida." Tace"Sai hakuri Suwaiba taki sanin abunda ya dace Wallahi kiyi hakurin zama da ita ni kam 'kato na dawowa zan tattara in tafi inda nafi kauri."
Nace"Babu inda zakije granny kina gidanan domin ni dake zan zauna gaskiya. " tace"Yanda nake da matsayin a gidanan haka Suwaiba take dashi domin a matsayin uwa take ga mijin ki saboda haka ki kula da kyau." Kuka NASA nace "Wallahi kin San Allah bazan zauna da ita ba sai dake domin ina ganin idan ta cigaba da yimin wannan halin nata watarana zan rama ko in zage ta."
Ganin ina kuka yasa granny fadin "Shikkenan kiyi hakuri mu Bari tukkuna mai gidan ya dawo sai muji ta bakin sa." Hawaye na nagoge nace"Me zan girka miki na rana." ? Tace"ki bari Iyami sai tayi ke kije ki huta mana." Nace"A'a ki fad'a min dai." Tace"yi min towon alkama da miyar kuka." Nace" Tom" futa nayi daga d'akin na tadda Innah Suwaiba ita kad'ai ta d'au 'kafa daya ta d'ora kan d'aya kicin na wuce ta Bini da banzan kalo tana Jan tsaki .!!
Me zan gani Hafsa na tsaye ta kunna gas sai fasa 'kwai take yi gefe ga Uwar doya nan ta tsame ta cikin wani kwando ta d'ora mai zata fara soyawa..... 'Bata fuska ta nayi nace"Hafsa meye haka kikeyi min a kicin duba don Allah gurin a gyare duk kin bi kin zubar da 'bawon 'kwai da doya Haba don Allah."!!
Hafsa da ada take bala'in tsorona itace yanzu ya juyo tayi min wani banza kallo ta d'auke kanta daga kaina ta cigaba da abunda take..... Wani irin zagi na kurma cikin zuciyata amma a zahiri nace"Ko bakyajin abunda nace ne."!!! A wula'kance tace"Ina ce da akwai me aiki da zaki wani dame ni da surutu, idan na gama aikina sai ta zo ta gyara."
Gyad'a kaina nayi nace"Yayi kyau."! 'Karasa wa nayi kusa da ita kawai na murd'e gas d'in na kashe had'e da dauke man da take soya na aje kaskon gefe kana na kalleta fuskata babu annuri ko na kwabo nace"Futa ki bani guri in gama abunda zanyi in yaso sai ki dawo kiyi kome Nene. """
"Baki isaba."! Tafad'a kanta tsaye gashi ta tsare ni da ido har da ri'ke 'kugu gaskiya nayi mamakinta nace" OK sai inga yanda zakiyi min iko a gidana."!
Wata irin shewa ta buga tace"Masu gida manya, hahahahaha da dai bamu San komai bane sai kice wani abu, to mun San komai aure ne akayi shi dake da My love d'ina bisa 'kaddara da har zaki dinga wani famkama da hura hanci kin auri me kud'i tom bari kiji ba a sanja 'yan uwa har karshen rayuwa ke kuwa fa my love zai iya sanja ki har abada ya kawo wata saboda haka ni nan da kika ganni jinin mu d'aya da Amjadu za'a iya tsaga jikinsa a tsaga nawa a ga jinimu yazo d'aya saboda haka ki iya bakin ki Wallahi idan ba hakaba wannan gallafirin auran naki zamu iya yin sanadin sa."
Naji wani irin takaici ya rufe ni jin abunda Hafsa take cewa danne zuciyata nake yi ina kokarin hanata aikata abunda tayi niyya nace"Hafsa kin San halina ba tun yau ba bani da kyau ke kanki kin sani bana so muyi irin wannan zaman daku ki iya takunki ki bar shiga hurumin da bana ki ba, idan kin 'kiji zaki sha mamaki wallahi."!!
A hasale tace"Ke kar ki kawo min maganar banza da wofi da dai da kikayi min abunda kike so a skull lokacin ki ne yanzu baki isa ba wallahi kutumar ubanki zanci la'ada waje kuma in zauna....... Kafin ta 'karasa na tsinke ta da wani irin gigitacan mari! Ta rike kuncin ta da sauri tana kallona da ido jazur tace" ni Kik....... Kafin ta 'karasa na kifa mata wani a d'aya kuncin nata, nace"Ina fatan yanzu kin tuno wacece Asma'u Sulaman 'yan a waki."!!! Ihu! Hafsa ta kurma ta d'auki soyayyan man dake cikin kasko ta watso min da sauri na kauce saboda nasan da zafin sa zai iya 'kona ni. Kaina tayo aikuwa santsin mai da 'bawon doya ya kayar da ita cikin man dake da sauran zafi kafin kace kwabo fatar hannunta ta kwailaye! Ina tsaye ina kallonta tana kuka.
Granny da Innah Suwaiba suka shigo kicin d'in hankali a tashe! Innah Suwaiba kaina tayo tana fad'in"Shine kika 'kona min yarinya saboda kina ba'kin cikin zata zama kishiyar ki shine tun yanzu kike so ki nakasta min ita Dan ubanki! Mari ta kai min a fusace.!!!
*8/12/2019*
[12/9, 10:38 PM] .: *BABBAN YARO*
*80*
Nayi saurin dafe kuncina ina kallon matar cike da d'umbun mamaki! Ta cigaba da cewa"Shikkenan kawai saboda ta shigo tana soye-soye a gidan d'an uwanta sai ki 'kona ta da mai saboda sharri da ba'kin ciki to Bari kiji wallahi ki sanya a ranki sai kin zauna da ita a matsayin kishiyar ki, domin ita tudu biyu taci ga aure ga 'yan uwan taka."!
Ta 'karashe maganar tata cikin kumfar baki.
Hawaye masu zafi ne suke zurarowa a daga idona tace"Kina tsatsare mutane da idon ki na rashin kuny...... Kafin ta 'karasa granny ta katse ta ta hanyar fad'in"Wannan ba girman ki bane Suwaiba abunda ya kamata kiyi kafin ki yanke hukunci shine ki fara tambayar su me ya had'asu ba ki za'bi taki ba Asma'u ma 'yar ki tunda tana auran d'anki." Granny ta 'karashe maganar cikin sigar rarrashi.
Botsarewa tayi tace"Kina kallo fa ta 'kona mun yarinya wane irin ba'asi zan tsaya tambaya anan ga gaskiya a zahiri duk bakin cikinta baza ta ci arzi'kin ita kad'ai to kaji."!!
Cikin saurin na futa daga kicin d'in ina ji zuciya kamar zata fashe saboda takaici tabd'ija lallai akwai rigima mutu'kar matar nan tace zata zauna min a gida domin na lura bata 'kauna ta ko kad'an nima take naji wata irin tsanar ta ta shiga zuciya ta, zama nayi gefan bed ina tunani matakin da zan d'auka kan Hafsa babu shakka tayi ganganci tace zata had'a miji dani... Aure bazan hanashi yayi ba, kuma Hafsa 'yar Uwar shi CE bazan rabasu ba amma ko da wasa bazan d'auki raini daga gurin kowa ce shegiyar ba ciki kuwa har da ita Innah Suwaiba.
Waya ta dake kan drawor ta fara ringing Sam banyi tsammanin shine ba ina dubawa nagan my one and only da abunda nayi serving d'in numbar shi kenan.
Murya 'kasa nayi sallama inajin ya sauke ajiyar zuciya kana ya amsa sallama ta, shiru nayi domin har yanzu akwai sauran 'bacin ran su Innah Suwaiba a tare dani.... Yace." Me kike cewa d'azu kika kashe min waya."?
Shiru nayi ina tunani nace" inajin shi yace." Kat ki 'kara kashe min waya daga yau." A hankali nace "Tom."!! Ina baby."? Ya fad'a cikin wani irin voice Wanda ya sanya ni jin wani yanayi nace" sun futa cefane da Iyami. "
Yanayin yanda yayi magana ya nuna min ransa ya 'baci yace." A kan me za ki bari a futa da ita kasuwa dole ne cefe nan." ! Na sassauta murya ta tare da fad'in"Dole ne mana tunda bamu da wasu a bubuwam a kicin Rambo bayan nan, Doh-doh kuma kun tafi tar...... Kafin in 'karasa ya katse ni a hargitse yace." Kada ki kuskura ki 'kara bari a tafi min da yarinya kasuwa ko ina gari ko bana gari Wannan si shirme ne ita Iyami me yasa baza je ita d'aya ba."
Cikin zuciyata nace "Ikon Allah ."! A zahiri kuwa ha'kuri nake bashi ina fad'in " Baby ce take kuka dole sai Iyami taje da ita." Aiko saurara ta baiyi ba ya kashe wayar sa......
Wayar nake bi da kallo cike da mamakin hakinsa Sam shi idan ya d'auki zafi baya tsayawa ya saurari mutum... Na fi minti goma rike da wayar a hannuna, kana Naji motsin shigowar Iyami parlor na futo kamar babu abunda ya faru nace"Iyami kin dawo ne."?
Tace"Na dawo yanzu baby nayi ta min kuka s hanya." Nace." Sakkota mu gani." 'Kokarin sakkota take daga baya ta sanya kuka Iyami tace" barta kawai a bayan nawa." Nace"Ke da zaki shiga kicin yanzu." Tace"Hakane fa yanzu da na shiga kicin din aje kaya nace"Ba'ki mukayi a gidanan ken..... Innah Suwaiba ta katse ta ta hanyar fad'in"Mu ba ba'ki bane 'yan gidane sai dai kece ba'kuwa." Iyami tayi saurin fad'in"A'a sannu Innah Suwaiba Ashe kece." Banzan kallo tayi mata tazo ta zauna kan kujera hannunta rike da wani plate cike da doya da 'kwai ta zauna ta fara cin abunta.
Iyami kicin ta nufa ni kuma na wuce d'akina rungume da baby domin nayi alk'awarin banza 'k'ara shiga har Kar matar ba gaisuwa ma don ta zama dole ne."
Waya ta na d'auka ina kirashi tana ta ringing ya'ki dauka har ta katse na 'kara kira ta katse bai dauka ba, sai da na kira sau uku bai d'auka ba na hak'ura nace Fushi yake yi kenan take naji zuciya nima nayi min zafi nace karfa wannan guy ya samu hanyar wula'kantani don yaga na saki jiki dashi dashi har yake mun fad'a domin a rayuwata na tsani in kira mutum a waya ya kashe ko ya'ki dauka.... Wata zuciyar tace min Kin manta Irin zaman da sukayi da Mimi dama kuma granny ta fad'a miki shi mutum ne me d'aukar zafi amma bashi da rik'o, lokacin sai naji zuciyata tayi sanyi saboda nasan zuwa dare ya sakko dole zai nemi ya kira waya ko don yaji gwalantun babynsa da ya saba. Ranar haka na yini sukuku sai bayan sallahar Isha'i sannan na futo parlor. Granny Iyami Innah da Hafsa duk suna zaune suna kallo Cikin kwanciyar hankali abunsu.... Kai tsaye daining na nufa domin cin abunci granny tace"Kin futo kenan." Ina tafiya nace"E Granny sannun Ku da hutawa. " hankalinta na kan TV tace"Yawwa kinga hankalina ya d'auke gurin kallon Wannan wasa Dad'in mu ko dad'in kowa ina son kallon diramar nan. " ta k'arashe maganar tana dariya... Ina kokarin zama nace"Ba kya kad'ai ba granny shirin dadin kowa ya shiga zuciyar mutane sosai." Hira muke tsakani mu Innah Suwaiba na makamin harara ko kallonta banyi ba nagama abunda nake yi na bar gurin bayan nayi wa Granny sallama.
Ko da na shiga d'akinta wanka nayo jikina duk babu kuzari na duba wayata ya Kai sau biyar banda ko misscal d'insa ba, haka dai nayi shafe-shafe jikina sanyi 'k'alau na shirya baby cikin kayan baccin ta kwantar da ita nayi saman cikins na kwanta rigingine waya ta na d'auka na lalubo numbar Munnu wacce muka rabu da ita tun ana ya gobe d'aurin auramu.
Buga d'aya tayi ta shiga Munnu da zumud'i ta d'aga wayar tana fad'in"Sai yanzu kika tuna dani saboda kin samu duniya ko."? Nace"Munnu ke wannan ya dama Wallahi ni fargaba duk ta cika min ciki kinsan dai abunda yake faruwa ko."? Tace"Ya Aminu ya fad'a min INA muku fatan alkairi Asmy." Nagode Munnu kin San wani Abu."? Tace "Sai kin fad'a."
'Wallahi Yayar Mahaifiyar Abban baby ce ta sanya ni a gaba masifaffiyar mata Babar du Hafsa mai warin.! " munnu tace"Ikon Allah dama fa naji labarin 'yan uwan sune." Nace "Babu wai a ciki Munnu a takaice dai matar ta tattaro kayanta ta dawo gidan da ita da Hafsa."
Salati Munnu take yi cike da mamaki tace"Kaji mu da mata 'yar rainin hankali." Nace"Wallahi munnu ni ba wannan ba ma da tazo da sigar son mu zauna lafiya sai mu zauna meye duniyar amma Baki ga irin abunda take min ba, ke d'azu fa har da mari."! Munnu ta rike Baki cike da mamaki tace"Akan me ta mare ki." Nan na kwashe abunda ya faru tsakanin da Hafsa na fad'a mata
Munnu tace"Meyasa baki ci kutumar Uban Hafsa ba wato ita Dan bata da hankali tana ganin a haka Amjadu zai aure ta lallai bata da hankali wallahi.
Nace"Hafsa dole in kiyaye saboda na lura matar na da matsayi a gurin shi kuma kema kin San halin d'aukar zafin guy kin San dai irin zaman da suka yi da Mimi shiyasa nake bin komai a sannu.: Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace"Kina da gaskiya anan kiyi hakurin zama dasu kafin kiga irin matakin da zai dauka nasan ki da saurin hasala da rashin hakuri ki danne zuciyar ki ga duk abunda zasuyi.'!! Nace " Insha Allah Munnu." Na muka cigaba da hira inda take tsokanata wai sai ta rigani haihuwa tunda yayana ya takura mata kullum Abu d'aya, nace"Munnu duk dake kema kikaje kina bankar maganin aunty Hauwa Dole ya Aminu ya samu guri."
Tace" kuma Wallahi da farko na ji zafi amma da yayi na biyu na uku sai na daina ji sai dad'i. " dariya nayi nace"Munnu baki da kunya wallahi bakin ki ya iya fad'ar dad'i. " tana dariya tace"Sai kin ji yaya yake sannan zakice baki bazai iya