Showing 33001 words to 36000 words out of 36837 words

Chapter 12 - BABBAN YARO Book 3

30 Jun 2024

18389

taya shi ri'ko yayi rik'o da hannayen sa Allah ya bashi ikon d'aukar nauyin jama'a."


Granny taji dadin addu'ar Iyami shiyasa take sonta Iyami macace mai karamci da mutumci sun fi shekara goma a tare duk masu aikin da tayi tafi sha'kuwa da Granny kuma tafi sonta saboda tana kyautata mata, itama kuma tana kyauta ta mata gwargwadon iko idan Iyami zata je 'K'auyan su Shatara ta arzi'ki granny take had'a mata Iyami tayi buhu-buhu da kayan masarufi ta kaiwa 'yan uwanta na can da suke ganinta da daraja saboda tana mutukar taimaka musu.

Iyami kicin ta nufa domin had'a sanwar dare ita kuma granny tayi zaune a parlor tana jiran futowar masu gidan, Baby ce ta rarrafo tazo ta kama granny ta mike tsaye tana mata gwaranci Granny ta dauke ta tana fadin "Nasan Iyayen ki kike nema Yo idan suka ji kukan ki ai sa futo Dan dol... Kafin ta rufe bakinta baby ta tsandare da ihu! Tana nuna d'adin Asma'u da hannunta.


Rarrashin ta granny take yi fafur yarinyar ta'ki yin shiru sai ya zamana ma kamar 'kara ingiza ta take yi. Iyami ta futo daga kicin da sauri tana fad'in" Baby rigima ai tunda ta fara wannan kukan nata komai zai tsaya." Granny tace"Tayi min dai-dai Wallahi ke dai je ki cigaba da aikin ki."


Iyami tace"Granny bari dai in tsaya in dama mata madarar ta kin san Abban ta baya son kukan ta abu komai a sannu dama Kuma yau ba abunci mai wahala zanyi ba."


Granny ta mi'ke tsaye da baby a hannun ta kai tsaye bedroom d'in Asma'u tq nufa tana fad'in"Iyami baza kiyi mana girkin dare ba mutukar kika tsaya rarrashin Wannan 'yar rigimar sai magariba tayi bakiyi komai ba, dole su futo haka." Iyami tabi Granny da kallo cike da mamaki.!


Granny kuwa dukan 'kofar d'akin take yi da hannunta tana fad'in"Kai d'an anace ka futo haka Haba! Wannan jaraba dame tayi kama! Ni kam na tsani wannan d'abiar taka, ku futo Ku d'auki 'yar ku ta cika wa mutane kunne da kuka." ! Baby ta 'kara tsandara Ihu! Tana zillo dole sai ta sakko.

Asma'u da Tayi mutukar galabaita ta kalli Amjad din da yake ta kyarma jiki yana 'kokarin sanja mata kaya bayan yayi mata wanka da ruwan d'umi tace"Abban baby don Allah ka bud'e 'kofar nan haka wai baka jin kukan da baby take yi ne tun d'azu."


Shiru yayi mata kawai ya cigaba da sanya mata riga kamar yanda ya niyyata sai da ya shirya ta tsaf! Sannan ya nufi kofar futa, yana jin haushin abunda granny take masa a gidan duk ta saka masa ido, shi da gidan sa da komai bai isa ya shiga daki da matar sa zata hau 'korafi fa surutai! Cikin zuciyarsa yace ." Da ya sani ma lokacin da tace zata tafi ya barta tayi tafiyar ta ya huta da saka ido."



Yana bud'e kofar ya sha kunnu domin kar taga fuska ta kawo masa wata maganar.... Harara ta maka masa tace"Oho! dai ka futo kana muzurai da 'bata fuska bayan kagama turmshe 'yar mutane kagama iface-ifacen ka na rashin imani! Irin naka baka gani yarinyar nan ciki ne da ita sai ka dinga hawanta kamar wani doki Haba! Ina dalilin wannan abu." Ta 'karashe maganar tana mi'ka masa baby da take mik'a masa hannu.

Hannu yasa ya 'karbi baby yana fad'in"Wai ke don Allah granny ina ruwan ki ne? Kin fiye sa'i do duk kin bi kin dame mu tun safe sai mita kike yi kin hanamu bacci sai kace an fad'a miki abunda kike tunani muka yi to ki shiga ki duba ki gani mana." Ya fada babu wasa


Granny taje "Oho! Kai ka sani ni babu wani shiga da zanyi in duba domin ni ba yarinya bace, wai mutumin da zai dauki ragamar mutane sama da dubu d'ari shine yake ma'kale mace a jiki babu dare babu rana, itama Asma'u duk da laifin ta da take biye maka sai kaje ka baro ta tana fama da 'karamin ciki."


Dariya maganar ta ta bashi amma baiyi ba sai ma 'kara had'e fuska da yayi yace." Shikkenan kuma saboda zan ja ragamar jama'a sai in fasa more rayuwata kawai don in cutar da kaina bazai yiwu in takurawa kaina ba." Granny tace" Oh-oh! Kaje kayi tayi 'kato Allah ya bada sa'a kadai kiyaye da 'karamin cikin ta." Tana 'kokarin barin gurun take maganar...... Yace." Kinji ki kuma da wani magana granny ciki dai nawa ne kuma nasan takan komai. " Fad'ar haka da yayi sai ta fashe da kuka tana fad'in" Yanzu 'Kato ni kake wa wannan maganar? Ni zaka yi wa gori akan d'an cikin ka." Amjad ya saki dariyar da yake 'b'oye wa yaja hannun granny d'in da take ta faman kuka tana fyace majina sai surutai take yi wai yayi mata gori.


Yace." Nifa ba haka nake nufi ba Kuma ba abunda kike nufi nake yi ba to idan ma hakane ai ba haramun bane tunda ke da kanki kike cawa dani kar in bi matan banza kin ga idan sha'awa ta kamani dole in zo ga iyalina kiyi hakuri kinji Uwar gidana." Granny ta share hawayen ta tana fad'in"Yanzu ina Asma'u take."?


Yace." Tana ciki bata jin dad'i amai ma ta gama yi yanzu." Tace"Ai kaji abunda nake fad'a maka ka 'karya tani Hummm! Mik'ewa tayi ta nufi dakin Asma'u tana surutai kamar yanda ta saba. Shi kuwa Amjadu kallo ya bita dashi har ta bud'e dakin ta shiga sai a lokacin ya saki dariyar da yake 'boyewa yana mamakin 'karfin halin tsohuwar.




******
Alhmdullahi dukanin abunda aka ce Allah a rayuwa to an gama komai kuma zakaran da Allah ya nufa da chara ko na muzuru ana shawo sai yayi, hausawa suka ce hassada ga me rabo taki ce, Amjadu ya sha gwagwar maya a rayuwar shi kafin Allah ya tabbatar da mulkin jahar kano a hannun shi, hak'ika yaga dumbin masoya kuma yaga dumbin ma'kiya dasuke ta caccakarsa gami da zaginsa a gidajan redio dukanin su maganar guda ce cewar shi d'in ba d'an gari bane babu yadda za'ayi yazo ya mulki 'kasa saboda gudun kada ya gama cin albarka cin "kasa ya gudu k'asarshi ta gado *Chadi* to dukanin wannan surutun da suke yi babu mai sauraran su domin jama'ar jahar kano sun gama yin nisa da 'kaunar Amjadu ta inda suke ganin zasu iya za'ben sa ya zama shugaban 'kasa mutukar yana nuna yana da ra'ayin haka su zasu Goya masa baya.
[12/14, 9:50 AM] .: Rayuwa kenan Asma'u a gidan gomnati lallai arzikin mutum a jikinsa yake Umma ko da wasa bata ta'ba tunanin zata haifi 'yar da zata auri kansila ba ma amma dake Allah Allah ne 'yarta Asma'u wacce take da 'karacin kyau a cikin 'yayanta itace take auran governor dole ta godewa Allah da wannan karamcin da yayi mata, Amjadu ya d'ora Aminu kan harkokinsa da yake yi a da kuma a halin yanzu ana shirye-shiryen farfad'o da company da ya ruguje shekaru biyu da suka wuce. Umma kullum cikin sanya wa Amjadu albarka take yi saboda ya tsaya mata sosai su aunt Hauwa an samu abunda ake so kasuwanci ya k'ara bunkasa kudi ko ta ina suna shigo mata tunda yanzu Alhmdullahi jari ya fara k'arfi kuma Ya Aminu ya kama 'kasa duk ta dalilin Amjadu, Umma sai yanzu ta yarda da maganar hausawa da suke cewa sai kana dashi ake yi dakai ada idan ta shiga cikin dangin mijinta kallon arziki basa yi mata saboda bata da kudi bata da sutturar kirki yanzu kuwa har rububin gayyatar ta sabga suke yi shi kanshi Kawu Yunusa kamar yayi mata sujjada Saboda tsabar ladabi da yake mata kawai kallonsa take yi, saboda tsabar tsaurin ido irin nasa kuwa cewa yayi yana so ta auri Idiris Wanda ya kasance 'kani ga Baban su Asma'u Umma tayi mamakin jin Wannan maganar daga bakinsa kawai sai barshi da halinsa tasan da cewar duk kwadayi ne ya jawo haka, duk da cewar suma Amjadu din yana tsaye a Kansu yana bukata musu sosai amma sun dauki ido sun 'Dora mata.


'Bangaran granny kuwa bayan za'be da wata biyu tuburewa Amjadu din tayi kan dole sai taje taga 'yan uwa suma da hankalin su na kanta tunda suka ji Amjadu din ya zama governor a jahar kano suke murna da yi masa fatan alkairi.... Amjad da yaga rigimar granny ta'ki karewa sai yace ta shirya insha Allah zasu je ranar Monday gabad'ayan su har Asma'u da cikinta yayi nauyi ga wata Uwar 'kiba tayi ciki wata biyar amma da kyar take cire 'kafa duk yabi nonowan ta da kwankwason ta shiyasa ta bude sosai bayan haka kuma da samun Hutu da cima mai kyau ga Ac ko ta ina ga kulawar ogo domin cikin NATA baya hanasu su more rayuwar su 'ka'ida ne sai sunyi sex dare da asuba abun ya zame musu jiki.


Duk da tarin ayyukan da suke gaban shi haka ya tsalle ke ya bar komai a hannun mataimakin shi Injiniya Jabir Hamid yasan mutumin jajurtacce ne akan komai yayi masa fatan dawowa lafiya ya tattara iyalinsa suka nufi 'k'asar shi domin gaishe da 'yan uwa.



Satin sa d'aya yayi nufin komawa najeria saboda aikin da ya bari granny ta 'kekasa 'kasa tace ita ba yanzu zata koma ba tilas ya k'yaleta yace. " da Asma'u ta shirya su wuce Asma'u dama a takure take a garin saboda bata samun yanda take so gurin mijinta Granny ta sanya mata ido ita da sauran dangi sai kafkaf suke da ita da cikinta ko da wasa basa Bari ta sake da mijinta shima haka zai gaji da mota ya kyalesu Dan dai ma aiki nayi masa yawa hade da dubba abubuwan da yake faruwa cikin system dinshi abunda yake dauke masa hankali kenan amma dai duk da haka daurewa kawai yake yi.
[12/14, 10:10 AM] .: Aikuwa granny tace"Asma'u baza ta bishi ba sai da ya bari sa dawo tare, tsakaninsa da granny aka dinga dauki babu dad'i da kyar wani yayan ta Wanda suke kira Malam Halilu yayi mata magana ta kyaleshi ya dauki matarsa ya tafi abunda take yi bai dace ba.

Sai da ta bari Malam Halilu ya bar gurin ta dinga musu masifa mussaman Asma'u tace"Kije idan ya jawo miki najudar dole kanki kika jiyo ita dai Asma'u bata ce komai sai sinne kai take yi cike da kunya cikin zuciyarta tace"Granny kenan tsoguwa me rigima, ko da zasu tafi granny shigewa tayi daki tayi kwanciyar ta har suka bar gidan Asma'u ta yana da karamcin mutanan sosai suka sad'o ta da kayansu na can irin nasawa da abubuwan gurginsu kayansu na gargajiya duk da dai sun San tafi k'arfin abun Sam basu damu ba tunda Annabi ya fada cewa ka girmama bakon ka. Sai da suka shiga jirgi sannan 'yan rakiyar suka koma gida cike da kewar su. To suma nasu 'b'angaran sunyi kewar su sosai haka rayuwa take dama.


******
Granny sai da tayi wata uku sannan ta dawo lokacin cikin Asma'u ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe a lokacin ne Kuma ayyuka suka tsananta ga governor domin ba k'aramin b'arna Alkanawi Yayi ba yanzu sun mai da hankali gurin ganin sun dai-dai ta komai a jahar kano.


Umma sau daya tazo gidan gomnati taga Asma'u ta sanya mata albarka tare da yi mata fatan sauka lafiya ta tafi cike da kauna da son yarta a zuciyarta


Aunt Hauwa kuwa ai tazo gidan yafi sau biyar duk da cewa akwai tsaro sosai amma babu yanda suka yi da aunt Hauwa domin wani sa'in gayya take yo wa ita kawayen ta lallai sai ta nuna musu itama babbar macace kanwarta tana auran governor.



Innah Suwaiba da Hafsa sunzo gidan ya kai sau goma securitys sun hana su ko da ra'bar gate din Saboda rashin sani har kuka sai da Innah Suwaiba tayi musu tana yi musu bayanin cewar ita mahaifiyar mai gidan ce suka ce basu San wannan tayi hakuri sai ya dawo tukkuna a lokacin suna Chadi....Haka suka koma gida jikinsu suk a mace zagi kuwa babu rij Wanda Innah batayi wa securitys din tana fad'in " Idan governor ya dawo zai nuna muku matsayi na a gurinsa shegu tsinannanu.!


Da ta samu labarin dawowar shi sai ta sanya Hafsa ta shirya sosai suka nufi government house din zuciyar cike da kudure-kudure a cewar ta sai ta sa Amjad din ya kori wannan masu gadin da suka yi mata wulakanci sannan ta umarce shi ya sanya ranar d'aurin auran sa da Hafsa.: Ko da suka isa gidan sai suka yadda securitys har sun fi na kwanaki yawa tabbatar cewar mai girma governor yana ciki bai futo ba, taje ta tsaya tana musu magana dukaninsu Hausa bata ishe su ba domin kadan ne daga cikinsu hausawa turanci suke mata suna zare mata ido! Inna ta tsorata sai ta koma gefe guda tana haraarau Hafsa da ta tsinci kad'an daga abunda suke cewa tuni ta tsure! Domin cewa suke maza su bar gurin idan ba haka ba zasu Zane su da bulala! Inna na gama jin abunda Hafsa take cewa kawai sai ta fashe da kuka Wanda yayi dai-dai da shigowar Aunt Hauwa cikin gidan cikin dalleliyar motar ta. Ga mamakin Inna taga aunt ta bude mota ta futo kuma kaitseye ta durfafi securities din babu wani fargaba ko tsoro sai ta dunga mamakin ita kuma wacece ita? Gani tayi suna gaishe ta suna mata magana da turanci hade da nuna su da hannu abunda suke cewa shine wai tasan da zuwan su Innah ko kuma tare suke domin sun San ta saba zuwa gidan da jama'a .

Juyowar da aunt Hauwa tayi sai da gaban Innah ya fad'i ganin suna kama da Asma'u a zuciyarta tace"Babu shakka wannan yayar ta ce aikuwa hafsa tace"Yawwa inna ga aunt Hauwa nan sai tq shiga damu gidan." Innah Suwaiba Tayi sakato da baki har aunt Hauwa ta karaso gurin ta gaishe ta cikin mutumci sannan tace"Kuzo mu shiga ciki gashi munyi sa'a duka mai grima governor yana nan bai futa ba." Simi-simi suka bi bayan aunt Hauwa tayi musu jagora har katafaran parlor mai girma matar governor hamshakiya mandiya Asma'ulhusna.


Suna zaune a parlor ita da granny suna shira granny na saman kujera Asma'u na kasa kan wani irin lallausan kafet ta mike k'afafunta Shi kuma ubangayyar yana matsa mata granny tana fad'in "nauyin cikin ne yasa k'afar taki tayi kumburi nace anya kuwa Wannan cikin naki bana tagwaye bane." Fad'ar maganar granny tayi dai-dai da shigowar su Innah Suwaiba cikin parlor
Innah Suwaiba tayi turus ganin abunda yake faruwa Amjad gurfane kamar wani bawa yana aikin mammatsa k'afafun Asma'u dake zaune da ciki turus a gaba daga ita har Hafsa jikinsu mugun sanyi yayi tuni Hafsa ta tabbatar wa da zuciyar ta cewar Asma'u tayi mata nisa kuma tayi mata fintikau ya kowa ne b'angaran tasan ko inna ta sanya Amjad din ya aure ta to tasan itace zata sha wahala a gidan Saboda tasan irin son da Amjad din yake wa Asma'u bana wasa bane jikinta yayi bala'in sanyi kamar yanda na innah yayi sanyi cikin sagewar gwiwa suka karaso cikin parlor granny tana musu barka da zuwa


Ita kuwa aunt Hauwa kunya ce ta ishe ta bata tab'a jin nadamar zuwa gidan ba irin na yau governor da kansa yana yiwa kanwarta tausa lallai babu abunda zasu cewa Allah tabbas yanzu ta k'ara tabbatar da cewar kauna da so tsakanin kanwarta ta dashi Amjadu din ajininsu yake. Bayan sun gaisa da granny dashi kanshi uban gayyar ta wuce dakin Asma'u cikin kunya.


Ita kuwa Asma'u a ladafce ta gaishe da inna Suwaiba dake faman ya'ke tana satar kallonta a fakaice har ta samu damar mik'ewa tsaye a daddafe Amjad din yana taimaka mata sai da ya kaita kofar d'akinta sannan ya sake ta ta shiga gurin aunt shi kuma sai sannan hankalinsa ya dawo jikinsa ya dawo cikin parlor Innah Suwaiba tayi muzu-muzu tana jin Shakkar ta fada masa abunda ya kawo ta gidan saboda yanda yayi mata mugun kwarjini a ido haka suka gaisa dashi jikinta sai kyarma yake yi Hafsa kuwa ba yarda ta hada ido dashi ba. Saboda kwarjini gami da tsoro duk masifar da Inna tazo dashi ta neme shi ta rasa sai ta fara jan granny da hira cikin rashin abinyi Ita kuwa granny biye mata tayi suka dinga hira kamar wani Abu bai faru ba.... Sunanan zaune Amjadu din ya futo cikin shirin futa...ya tsa Yana fadin''Innah zan futa ofis babu wata matsala ko."! Baki na rawa tace"Babu komai Dan albarka Duk ka cika mu da abun alkairi wallahi bama bukatar komai mungode sosai Ubangiji Allah ya jikan mahaifiyar ka." Ya amsa da ""Ameen kana ya futa yana mamaki innah da bata yi masa wani k'orafi ba sai yaga ma kamar tsoransa take ji..shu kadai ya ke dariya cikin mota Rambo dake gefan sa yana taya shi murmusawa hummm Rayuwa kenan Amjadu bai zubar da bodyguard dinshi ba a yanzu ma sune suke take masa baya kasamcewar duk wata gwagwarmaya tare aka sha dasu.




******
Bayan shekaru hudu abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa har da haihuwar Asma'u inda ta haifi twins duk maza masu kama da mahaifin su Allah bayanda baya al'amarin shi ana ya gobe suna Hassam din ya rasu sakamakon shakewar nuffashi dalili lokacin an haifi yaran da sanyi a jikinsu Amjadu sai da yayi kuka saboda ya yana son Hassan din kasamcewar ya Dan d'auko kamanin Asma'u kadan a lokacin sai Asma'u tafi shi dauriya. Hakadai ya 'karaci kukan shi ya gama ya barwa Allah to da yake ubangiji sami'uddu'ai ne sai ya kara bawa Asma'u cikin tagwaye lokacin Husaini na wata goma sha daya ta haife su duk mata kuma masu tsananin kama da ita sai dai daya tafi daya haske Hasana farace tas kamar ubanta ita kuwa Husaini kamar Asma'u tayi kaki ta tofar har yanayin jikinsu da saurin bakinta gami da zafin nama irin na uciki Amjad ya Dora mata son duniya komai Husaina komai Husaina gata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login