Showing 30001 words to 33000 words out of 36837 words
abunda kunnen ta yaji ye mata gaskiya ne.
Zuciya ce ta ciyo tace"Wallahi INA sane da masu sona da wa'inda basa so na Ni a rayuwata babu abunda zan cewa granny domin ta nuna mana 'kauna dani da 'yar uwata Mimi Allah ya. jikanta, duk abunda wannan matar take yi min baka cewa komai babu irin 'kazafun da bata yi min ba dukol kayi shiru. To ni kuma nace bazan zauna da 'yarta ba wallahi sai dai ka zab'i guda cikiin mu kuma duk wani Abu da take min taje na barta da Allah zai saka min."
[12/13, 10:03 AM] BintuUm@rAbb@le Fuskar sa a had'e ya d'ago kansa yana kallonta "Kina da hankali kuwa Asma'u? Innah kike kokarin fad'awa magana a gabana uhumm."!? Ya fad'a muryar shi babu dad'i!
Ba tare da na damu ba nace" Ai itace ta jawo meye ruwan ta dani a gidan mijina a matsayin ta na babba bai kamata ta shiga hurumin da bana ta ba tun da tazo gidan nan take zagina." Cikin kuka take maganar....
Ido ya tsira mata fuskarsa babu wasa yace." Ke Matsalar ki kenan tsaurin ido! Shiyasa kowa ya tashi zai fad'i aibunki ke baki bar yara ba baki bar manya ba uhumm ? Idan da mutumci ya dace ki fad'awa Innah Suwaiba wannan maganar ko da kuwa cewa tayi in auri mata uku a lokaci guda ai tana da iko dani ne."
Asma'u taji kamar ya watsa mata barko no a ido idonta a rufe tace." To sai me idan tace ka auri Hafsa bayan ita ka 'kara da wasu biyu ko a kwalar rigar Asma'u wallahi ni dai nasan ta siya maka tashin hankali a cikin gidan ka, Wanda nasan idan Maman ka ce ita ta hak'ika baza ta so kayi rayuwa cikin tashin hankali ba, ita dai akwai wata manufar ta ita kad'ai ta sani."!!! Sama-sama take maganar....
Babu wasa a maganar shi yace." OK da kike yin wannan fuffukar kina tunanin zaki hanani abunda nayi niyya ne? Ko kina tunanin zan bujerewa maganar Inna Suwaiba akan taki, Wallahi ki shiga hankalin ki ni nan da kika ganni bana daukar raini gurin ko wace mace zan 'bata miki rai Wallahi! Daga yau sai yau ki San irin maganar da zata dinga futowa daga bakin ki akan Inna domin duk rintsi Uwata ce ke ma haka dole ki girmama ta kamar yanda nake yi "you have to be serious."! Ya fad'a cikin 'bacin rai!
Asma'u kuka kawai take yi cikin zuciyar ta kuwa babu irin addu'ar da bata yi wa Innah Suwaiba Allah yayi mata katangar k'arfe da sharrin ta ubangiji Allah ya rusa maganar tun kafin aje ko ina ita tana ganin idan abun ya tabbata to babu shakka Zama Lafiya ya 'kare tsakaninta dashi tana mugun sonsa Wanda shine ya jawo mata tsanin kishin sa.
Sosai take kuka Yana jinta Yayi mata shiru kurbar Coffe dinshi yake gefe guda kuma yana latsa wayarsa a zahiri ka kalleshi sai kace kukan NATA baya cin ransa cikin zuciyar sa kuwa shi kadai yasan yanda yake jin zafi da kukan ta, ranshi ya 'baci ne da jin irin bak'aken maganganun da take fad'awa Innah Suwaiba ko kunyar idonsa bata ji ba, idan da zai bude mata zuciyarsa ta gani zata yi mamakin girman son ta da kaunar ta a ciki kawai yana dannewa ne saboda sanin halinta, shafa ya amsawa Inna ne kawai amma Sam bai shirya auran Hafsa ba yanzu bai sani ba ko nan gaba.
Asma'u ta gaji da kukan ta bacci me nauyi ya d'auketa cike da mafarkin 'yan gidansu musamaman Ummansu ta ganta cikin farin ciki da walwala.
Jin saukar ajiyar zuciyarta ya gane tayi bacci shima ajiyar zuciyar ya sauke kana ya kashe wayar sa toilet ya shiga ya wanke bakinsa ya futo kai tsaye bed din ya nufa ya kwanta hade da shiga blenket din ya rungume ta jikinshi yana sauke a ajiyar zuciya k'amshin da jikinta yake futar wa ne ya gigita shi tuni ya fara ya mutsata yana kaiwa ko wanne shashe na jikinta kisses masu zafi! A rikice yake kokarin cire mata Riga... Furgit ta bude idonta ta ganshi yana kokarin hawa jikinta da sauri tayi nufin tashi ya mai da ita da hannu daya daya hannun kuma ya zare mata rigar jikinta tuni ya gigice ganin lafiyayyun Brest dinta masu gigita shi take ya rungume ta a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya.
Asma'u duk buge-bugen da take yi. Sai da Amjad yayi nasara a kanta ya samu biyan bukatar shi.
*13/12/2019*
[12/13, 10:27 PM] .: *BABBAN YARO*
*88*
Haka suka tashi da safe ita dashi kowa na d'acin rai! Tunda ta gaishe shi bata 'kara kula shi ba shine ma yake janta da hira tana basar dashi haka suka had'u suka yi breakfast har shi uban gayaar ya d'ora baby a cinyar sa sai shirme suke yi shi da ita ya koma kamar wani 'k'aramin yaro yana biye mata sai faman dariya suke kyalkyalawa.
Granny bayan tagama karyawa mi'kewa tayi ta nufi d'akin da take suka bita da kallo Sam basu kawo komai ba, minti biyar tsakani sai gata ta futo cikin shiri ta yafe jikinta da mayafi kirif tayi hanyar futa ba tare da tacewa kowa komai ba."
Da sauri na mike naje na tari gabanta ina marairaice fuska nace"Granny ina zakije inace jiya mun gama magana dake kince kin fasa tafiya."
Jin abunda Asma'u take fada ne yasa shi mik'ewa da sauri ya karaso gurin yana tambayar menene."?
Granny tace"Dama yau na shirya tafi gidana." Amjad ya 'boye dariyar da take 'kokarin subce masa yace." Wani abu aka miki a gidan. " ? Gyada kai Tayi tace"Ba'ayi min komai ba kawai zan baku guri Ku wataya."
Dariya yasa ya kama hannunta guda yace." Rayuwata baza ta tafi dai-dai ba idan babu ke a gidan uwargidana ta kaina idan mun yi miki laifi ki hak'ura. "
Granny tace" babu laifin da kuka yi 'k'ato nice naga ya dace in tafi." Amjad yace." Ni kuma ban sallame ki ba sai kiyi hakuri idan kuma kika ce dole sai kin tafi kin San kina futa zan sanya a saki karnuka sai muga ta inda zaku tafi."
Cikin sababi! Granny tace." Sai kace zaman nawa dole ne iyi yanzu nace nafi son zama a gidana nagaji da jin iface-iface! Cikin dare."
Saurin barin gurin nayi ina mamaki tsohuwar ko me take nufi oho.! Ina Juyawa Inna Suwaiba ta watsa min mugun kallo tana gyada kanta... Bedroom dina na shige ina fadin"Allah Yayi min gatangar k'arfe da sharrin ki."
Kwanciya nayi kan bed din ina sa'kawa da kwance wa har bacci me nauyi ya d'auke ni.....a takaice dai ban San sanda su Inna Suwaiba suka bar gidan ba domin bacci na shirga sai daf da sallahar azahar na tashi a gurguje nayi wanka da alwala na futo simple make up nayi na zura doguwar Riga mai hula humra na shafa a jikina sannan na hau dadduma na tada sallah
Ko da na futa parlor granny kad'ai na gani zaune suna hira da Iyami na saki wata irin ajiyar zuciya mai sanyi, yanzu na tabbata Innah Suwaiba sun bar gidan cikin zuciyata nace mata 'yar bala'i kurrum tazo zata d'aga mana hankalin gida. Zama nayi cikin kujera cikin sakin fuska na dinga sanya musu baki a hirar tasu kafin mu zauna cin abunci granny kam cewa tayi Iyami ta had'a mata ta kawo mata inda take domin baza ta iya zaman daining ba. A cewar ta 'kafar ta tsami take ni da Iyami muka sanya mata dariya... Yanzu wani irin nishadi nake ji a zuciya idan na tuna cewar me takura min tabar gidan wallahi d'an zaman da Tayi na kwana biyu jina nake yi a takutey gefe guda kuma idan na tuna al'kawarin da Abban baby ya daukar mata sai gabana ya dunga fad'uwa.
*******
Al'amura sun tsananta ga me girma governor gobe wato *Amjadu AbulAbbas mainasara* Yanzu kwata-kwata baya zama a gida kullum suna can suns taron siyasa ya tsai da mataimakin sa Engineer Jabir Hamid shine ya yarda da alkairin sa da kulawar sa kana da yanda ya tsaya tsayin daka akan jam'iyyarsu tabbas Engineer Jabir Hamid tsohon d'an siyasa ne Wanda yake da a 'kida Amjad tun yana da 'kananun shekaru yasan da mutumin domin. A haife ya haife shi idan kididdiga ma za'ayi ya girmi mahaifin shi, to dashi ya yarda ra'ayin shi shi jama'ar jahar kano suke bi lokaci guda al'amura suka dai-dai ta yayin da 'yan bakin ciki da hassada suka 'kara yawaita sharri kullum yin sa ake yi ga amjadu amma yak'i tasiri jama'ar jahar kano sun Riga sunyi nisa a 'kaunar sa, Nima nace tabbas zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shawo sai yayi Amjadu sai dai fatan alkairi
Kullum zai dawo gida cikin dare a gajiye amma saboda tsabar futuna komai baccin da Asma'u take yi sai ya turme she ta ita kuma tayi ta masa sangarta da shagwab'a salo-salo abunda yake 'kara gigitashi kenan yake 'kara dilmiya cikin kogin sonta, sun ringa sun saba ita dashi kullum sai sunyi sex kuma basa tab'a yin sau d'aya a rana duk rintsi kafin ya futa sai 'kara wani da safe ko da asubah.....aikuwa Asma'u tayi wata irin lafiyayyar 'kiba fatar ta murje sosai Sam bakye ce mata baka saboda tana samun kulawa kullum oga nayi mata feshi tayi 'kiba sosai ta samu Lafiya ita dashi duk sun mance da wani zancan Inna rayuwar su suke yi tsaftacciya....Asma'u da kanta ta fuskanci tana da ciki domun wata biyu kenan bata yi al'ada ba kunya ta hanata fad'a masa, shi kam gogon NAKU hankalinsa ya d'auke gurin harkokinsa Sam bai fahimci komai ba tabbas yasan dai Ta 'karayin Sugar ta inda Idan yana sex da yake iface-ifecn da ya saba Wanda Granny take 'k'orafi akai Asma'u ce take rufe masa bakin sa wani sa'in amma Amjadu hauka ne kurrum baya yi mata a gado.
****
Granny ce ta fahimci abunda yake faruwa aikuwa farin ciki duk ya isheta shiga futa d'ari sai tayi zancan ciki motsi kad'an Asma'u zata yi zata hau fad'a wai ta dinga yin komai a hankali da nutsuwa ita dai sai dai tayi dariya kurrum...cikin wannan yanayin za'be yazo gari ya hargitse ya hautsine ko ina ka duba police ne sosai aka sanya matakan tsaro a garin na kano, ana ya gobe za'be Alhaji Hashimu da Yarshi Hibbah suka shiga gidan redio domin ayi hira dasu.
Dama tun safe ake maganar cewar za'ayi hira da tsohon d'an kasuwar nan Wanda yaga jiya yaga yau a fannin kasuwanci wato Alhaji Hashimu mai citta mutanan gari suka dinga dariya suna fadin ko me zai fad'a oho kowa ya 'kaugauta lokaci yayi ya saurari hirar har shi kanshi Amjadu wayar sa na hannun Rambo yana jiran lokaci ya kunna masa.
Alhaji Hashimu mai citta ya zage yana shirya karya kan Amjadu har da fad'in cewar mahaifin sa da bashin mutane ya mutu kuma bayan haka shi ba d'an gari bane yazo gari zai mulke su yana da kyau jama'ar kano su farka kar su zab'i bara gurbi Wanda zai tarwatsa jahar kano daga k'arshe ya koma garin su na gado maganar 'k'arshe da ta girgiza mutane shine abunda Alhaji Hashimu yace."Amjadu yayi wa yarshi ciki gashinan wata hudu a jikinta suna da shadar haka koda jama'ar gari zasu karya ta...... Wannan zancan ya jawo kace nace a garin inda kowa yake fad'ar ra'ayin da akan Amjadu dim wasu suna ganin hakan zata iya faruwa tunda dama tsohon Dan bariki ne yana da hotel har guda biyu tabbas ba asan iya adadin matan da ya lalata ba......wasu kuwa a take suka karya ta maganar tare da cin alwashin sai sun ragargaji mai citta shi da shegiyar yar tasa sai ta fada musu Wanda yayi mata ciki da bakinta, a rake su ka dauki gorori cikin shirin ko ta kwana suka nufi titin gidan redio na *Komai da ruwan ka* lamfu suka yi daga nesa suka hango motar Mai citta ta futo daga cikin gidan redio aikuwa suka futo da gudu suka tsaya kan titi... Cike da tsoro mai citta ya ci birki hankali a tashe! Yake kokarin bude motar ya futo Hibbah kuwa har ta saki futsari a wando tsabar furgita da tayi kafin su Ankara suka ji taratsatsa!!!! Gilashin motar ya fashe d'aya daga cikin matasan ne yake dukan gilashin motar yana fad'in "Futo tsohon banza da shegiyar kilakin 'yarka ogon namu zakuyi wa 'azafi duk bakin cikin Ku k sai ya zama governor!
Mai citta ya futo daga mota a gigice! Yana sa'be babbar rigar shi da ta gama jikewa da gumi fad'i yake'" kuyi hakuri don girman Allah kar Ku tab'a min Lafiya ta kar ki dake ni don Allah kuyi hakuri."
Mari!! Wani daga cikinsu ya kaud'a masa! Cikin tsawa! Yace." Cire wannan babbar rigar ta jikinka ko yanzu muyi maka zigidir."
Da sauri! Ya cire babbar rigar ya jefar yana goge gumin fuskarsa, d'ayan yace." Yi mana tsallan kwad'o."! Babu musu mai citta ya dinga buga tsalle a kan titi shi kuma matashin na haurin sa da k'afar shi Mai citta sai zufa yake yi gwanin tausayi dukan shi yake yi a d'uwawu yana fad'in "Maza!!! Tsallan kwad'o da sauri! Allah sarki me citta ya dinga buga tsallan kwad'o yana nishi su kuma suna tayi masa dariya had'e da d'aukar shi vedio a wayoyin su domin sunyi nufin tozar tashi shi da 'yar shi mara tarbiyya........ Kasancewar jajiberan za'be ne yasa garin yake a hargitse babu Wanda ya fahimci abunda yake faruwa a gurin kowa na hidimar gaban shi dama kuma dare ne motoci jefi-jefi ne suke wucewa a titin sai da suka tabbatar da mai citta ya galabaita sannan suka k'yale shi suka dawo kan Hibbah da ta kusa suma saboda fargaba da tashin hankali..... Cikin iskanci suka jawo ta ta k'arfi ta fad'o kasan mota d'ankwalin ta ya kwance ta dauka zata d'aura suka take cikin tsawa dayansu yace." Ke 'yar iska ko wato kin shiga gidan redio zakiwa Governor mu k'azafi ko tom sai kin fada mana uban da yayi miki ciki kika lakabawa bawan Allah....... Hibbah tana kuka take basu hakuri babu Wanda ya saurare ta a cikinsu sai iskanci suke mata gashi suna kokarin yi mata tsirara a titi.
Cikin kuka tace." Don Allah kuyi hakuri zan fad'a muku." Take suka saurara mata mai babbar wayar ne ya sai ta camera yana daukarta tace." Wallahi bashi bane sharri nayi masa domin. Ya aure ni." Suka ce tom ki fad'i sunan Wanda yayi miki cikin." Take tace" sharri ne ba gaskiya bane mun shirya maganar ne nida mahaifina muna ganin I Dan muka shiga gidan redio muka fada to zamu 'bata masa suna."
Mari suka dunga gaura mata suna harbin ta da k'afafun su... Daga bisani suka sakata tsallan kwad'o kamar yanda suka saka mahaifin ta..... Hibbah na kuka take tsallan kwad'o har ta isa gurin Baban nata da yayi mutukar galabaita tana kuka shi kuma yana share gumi.
Su kuwa matasan tuni sun bar gurin kai tsaye gidan redio komai da ruwan ka suka nufa domin. Kai musu rahoto suji kuma su gani duk maganar fa mai citta yazo Yayi karya ne...... Take suka fara turawa a wayoyin mutane a'lamarin ya watsu a media kafin Safiya kowa ya gane gaskiya mutane sai tur da Allah wadai suke yi da masu irin hallin mai citta.
A ranar Asma'u da Amjadu kwanan rigima suka yi gashi dai ranace ta farin ciki a gare su tunda Allah ya baiyana gaskiya.... Matsalar daga Asma'u ne ta inda take tayi masa shan'kam shi da yada masa magana cewar duk abunda ya faru laifin sa ne shine ya jawowa kansa raini da neme Neman matansa na tsiya...
Amjadu kam lallab'ata yake mussaman da fuskanci tana da ciki Bini Bini sai ya bude cikin yayi ta mata sambatu wai nan hira yake da babyn shi addu'a kuwa kullum sai yayi Allah ya bashi da namiji shi idan San samu ne ma Asma'u ta haifi 'yaya uku lokaci guda.... Ni kuwa nace"Amjadu komai na Allah ne domin shine mai bayarwa da hanawa.
*13/12/2019*
[12/14, 11:48 AM] .: *BABBAN YARO*
*89_90*
Ga maibukatar cmplt. Sai same ni a wannan numbars *08089965176_07084653262*
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
```Wannan pege d'in sadaukarwa ne ga duk wani d'an kwankwasiya Amana Mussaman Madugu uban tafiya Dr Rabi'u Musa kwankwaso```
⛑⛑⛑⛑⛑⛑⛑
Alhamdullahi anyi za'be an gama lafiya yanzu sauran zaman jiran sakamako, to abun dai ba sai an futo an fad'a a zahiri dai Amjadu duk yafi ko wane d'an takara yawan 'kuri'u jama'ar gari sai murna suke yi domin suna ganin sun Riga sun gama cin za'be, Amjad kuwa yana gida tun bayan da ya futa ya sanya 'kuri'ar shi ya dawo gida ya futini Asma'u yini yayi yana abu d'aya duk ya jigata ta, ya zamana da 'kyar take motsa jikinta aikuwa ta dinga kyalaya amai! na futar hankali Wanda tun da ta samu cikin ba tayi irin shi ba, granny ta dinga fad'a kamar ta ari baki, dama tun daga ya'ki futa take fad'a tana cewa"Shikkenan ya 'ki ya futo ya sanya yarinyar mutane a d'aki yana sasakarta ko tausayi babu." Ita dai Iyami dariya kawai take yi tace "In banda abunki granny yau sharabon da kika ganshi ya zauna a gida irin yau, yau d'in ma dalili ne kuma kinga baza ki hanashi ya kusanci iyalinsa ba." Granny tace"Duk da haka dai wallahi Iyami futunar 'kato yawa gare ta, ace ka shiga d'aki ka kulle tun safe Dan jaraba ko yunwar cikinka baka ji humm Allah dai ya kyauta."!
Iyami dariya takewa granny ta 'mike tana fad'in "Granny kenan ko dai kishi kike yi ne." ? Da sauri Granny tace" Babu wani kishi ina tausayawa baiwar Allah ne." Cikin dariya Iyami tace"To ai aikin lada take yi kuma idan bazan manta ba kwanaki da bakin ki naji kina mata magana cewa ta tsaya ta kula da mijinta ta bashi hakkinsa saboda kar ya futa yabi matan bariki."
Granny tace"Ai Ba irin wannan nake nufi ba Wato Iyami kema na lura kina goyon bayan 'kato ko."? Iyami tasa dariya tana fad'in"Dole ne in goyi bayan ubangidana shugaba mai adalci ubangiji Allah ya