Showing 6001 words to 9000 words out of 36837 words

Chapter 3 - BABBAN YARO Book 3

30 Jun 2024

18392

Mik'ewa take naji sha'awar shi ta kamani yana sanye da wata d'amammiyar vest ash color had'e da 3Queatr mai aljuhu na gaba da baya, fatar shi tayi wani fresh kwantaccan gashin da yabi lafiyyar fatar tashi shine yake gigita ni yake samun sha'awar shi... Baby ce take zillo sai taje gurin sa. Ya zura wayar cikin aljuhu ya karb'e ta daga hannuna yana dariya kamar bashi ba, sai wasa yake mata tana dariya, sai da suka gama sannan ya kalle ni babu yabo babu fallasa yace." Kun tashi lafiya."!? Kunya naji kadan abunda ya kamata ni in fara gaishe shi. Nace"Lafiya k'alau kaifa." ?


Baby yake wa wasa bai ce min komai ba, sai nayi nufin komawa dakin. Gyaran murya yayi na juyo a hankali ina kallonsa yace." Ke da waye ciki naji kamar sautin maganar mata a ciki." Kai tsaye nace "Su Aunt Hauwa ne." Wacece ita."? Ya fada cikin rashin sani. Na Dan ji babu dad'i ganin yanda yayi maganar babu walwala a tare dani nace"Aunt Hauwa zakace baka sani ba."? Jim! Yayi daga bisani yace. " Sorry nagane ta a maimakon kimin magana nazo in gaisa dasu sai kiyi shiru wato da ban tambaye ki ba baza ki fada ba ko."


Ajiyar zuciya na sauke nace"Zan fada mana yanzu ma na mance ne." Shuru yayi min yana kokarin shiga dakin. Naji kamar in jawo shi in hanashi shiga ciki dakin Saboda yanayin kayan jikinsa, wani irin kishin sa nake ji bana so ko su aunt Hauwa su ganshi haka.

Sakin fuskarsa yayi sosai suka gaisa dasu aunt Hauwa kana ya futo ya same ni inda nake. Bai ce min komai ba ya bar gurin kafadar shi sab'e da baby... Jikina babu kwari na koma cikin dakin inda na har sun mike suna shirin tafiya kamar in sanya kuka haka nake ji. Nayi diriduri Neman abunda zan basu nake na rasa da sauri na bude wardrobe din da naga ya bude jiya na fara bin cikin ta da kallo. Wasu dogwayen riguna na ciru a daure na Ciro Mayafai biyu Leda na sanya na biyo bayan su da sauri. Nan na Tarar suna sallama da granny na bi bayan su INA mik'a wa aunt Hauwa abunda ke hannuna. Karba tayi mukayi sallama idona cike da k'walla nace aunt ki gaida min da Umma don Allah.

Tana tafiya tace"Zata ji insha Allahu. " Rambo ne yayi musu magana yana nuna musu mota kai tsaye suka nufi inda motar take suka shiga Doh-doh yaja motar suka futa daga gate din... Ciki na koma zuciya ta babu dad'i kwata-kwata.... Na parlor na zauna kusa da granny dake kallon tashar sunnah tv malam Umar Sani fagge ba tambihi... Tace"Wannan yayyun naki suna da hankali da nutsuwa Asma'u. " murmushi nayi kurrum ta cigaba da cewa"Dama inaso in kara kwantar miki da hankali cewar don Allah kar ki d'aga hankalin ki kan abunda kika ji Suwaiba na fad'a jiya kiyi hakuri da abunda tayi kinji ko."! Murmushin takaici nayi nace "Babu komai granny Wallahi ni zuciya ta fes take wallahi ban sanya abun a raina ba, duk abunda ya faru dani nasan kaddara tace." Granny taji tausayin yarinyar ya kara shiga ranta tace"Yawwa haka ake son mutum me saurin fahimta." Sake wa nayi da granny muka dinga hira nake tambayar ta baby tace"Tana gurun babanta irin wannan lokacin suke bacci mutukar yana gida, shuru kawai nayi na kamo wani zancan.. Iyami CE ta shigo tana tambayar granny me za"a girka na abincin rana Granny tace." Ga matar gidanan Ki tambaye ta mana."
Dariya granny ta bani jin abunda tace, nace" Lokacin da banzo gidan ba ku ne kuka tsara abunku yanzu kuma sai ace a tambaye ni." Cikin bada kulawa tace"ai hakkin ki ne dole a tambaye ki, don ta k'ato ne mai sauki ne ba komai yake ci a gidanan ba dama kece zaki koya masa cin abunci a gida. " nace "Wallahi nima komai a dafa zanci." Iyami ta bar gurin tana mana dariya....... Kiran sallahr azuhur ne ya tada mu daga gurin kuma har lokacin su baby basu tashi daga bacci ba... Wanka na soma yi na dauro alwala na futo tsane jikina nayi sannan na shafe jikina da humra wacce k'amshin ta ya Riga ya kama jikina, duk kayana na gidanmu har da Wanda na dinka na futar buki don haka sai na rasa Wanda zan sanya.... K'atuwar wardrobe din dai na bude na fara dube-dube idona ya sauka kan wasu d'aurarraun Pakistan, da sauri na jawo su ina kwance wa Allah yayi ni da son Pakistan sosai da dogwayen riguna wani ne ya bani sha'awa pink coulor ya sha ado da stons sai daukar ido yake take na cire shi daga ledar shi na sanya a jikina gaban mirror na tsaya ina duba kaina, wallahi ni kaina nasan nayi kyau sosai ya kamani daga k'irjina dai-dai kuguna ya bude dalili akwai tsaga gefe-da gefe duk da wando k'ato ne bai hana bayyanuwar hips d'ina ba, sumar kaina na taje na hade ta tsakiyar kaina tayi tsini sosai sai na Dora net din da nayi futar buki dashi....jikina na kara feshewa da turare ko da wasa banyi wani fente-fente ba a fuskata saboda nasan ba kasafai nake yin kyau ba fuskata duk sai ta dame.... Futa nayi kafata sanye da wani takalmi plate, granny na samu zaune kan kujera da carbi a hannunta.


Ina zama tana shafa addu'ar ta tace"Ca nake bak'uwa mukayi daga k'asar Hindu ." Dariya NASA ina rufe bakina tace"Kinyi kyau Maman baby sai kace yarinyar nan ta hindiya ya ma take da suna."? Wai ni take tambaya Dariya kawai nake mata ganin da gaske take maganar.... Iyami ce ta shigo tace"Yauwa Iyami yama sunan yarinyar ta wannan film din mai yawan fara'a."!? Take Iyami tace" Johi chaula." Yanda Iyami ta fad'i sunan yayi mugun bani dariya dake wa kawai nayi nace"Granny ina ni ina wannan tsohuwar matar." Tace"Ai dama ba cewa nayi sa'ar ki bace cewa nayi kuna kama ko ba haka ba Iyami."? Iyami tace"Hakane Hajiya nima yanzu naga kammanin sun futo Sosai.."!

Ni dai ban San sanda na fashe da dariya ba take dimples dina duk suka futo Iyami tace"Wallahi har irin dariyar su ma gashi kumatunta yana motsawa." Ni dariya granny dariya nace"Ni kam Iyami ki daina had'ani da wannan tafi ni kyau nesa ba kusa ba ina ni ina ita ki duba da kyau don Alla.....Maganar tawa ta katse ganinshi ya futo daga bedroom din shi nayi saurin gintse fuskata ina kokarin kama kaina.. Iyami kuwa cigaba da k'od'a ni take wai nayi kyau har da rantse wa.
Kallonta yake tun daga samanta har kasan ta, tabbas ba karya Iyami tayi ba shima ya gani dressing din ya karb'a ta bai San me yasa pink din Abu yake mata kyau ba.. Sosai kwalliyar ta ta bashi sha'awa amma ko a fuska bai nuna ba, ya tsaya bakin k'ofa yana fad'in"Granny me yasa baku tashe ni ba gashi har lokacin sallah ya wuce uhumm!." Tace"Wallahi yanzu nake tunanin ince Asma'u ta shiga ta duba Ku Ashe baka tashi ba sai yanzu." Girgiza kansa kawai yayi ya koma ciki dakin jikinsa duk ya mace jin masifaffan k'amshin yarinyar.


Granny tace" Maza tashi kije ko da akwai abunda zaki masa." Mik'ewa nayi babu kuzari a jikina na nufi dakin... Wani irin sanyi da kamshin dad'i suka bakunce ni. Duk da cewa ba yau ne karon farko da na fara shigowa dakin ba, sai da gabana ya fad'i dana tuno abubuwan da suka faru tsakanina dashi shekarun baya..... Baby na kwance kan bed tana bacci na karasa Cikin dakin sosai zama nayi gefen bed din ina jin motsin zubar ruwa a toilet din... Wanka yake yi bed din nake kallo duk ya ya mutse ga baby a kwance bare in gyara masa, can na hango wani k'aramin frem hannu nasa na dauko ina dubawa.. Mimi ce tana dariya Lokacin tana da cikin baby da alama shine ya dauke ta a wayarsa don shi din take kallo tana dariya lokacin tayi wannan ramar da haske amma tayi kyau sosai..... Hoton na rungume a k'irjina hawaye suka fara zubo mun nace da na sani ban shigo dakin ba..kuka nake sosai domin na ma mance a inda nake jin motsin bude kofa yasa nayi saurin goge fuskata Ina kokarin mai da hoton in da yake Cikin tsautsayi ya fad'i kasa take ya tsage gida biyu... Wanda yayi dai-dai da futowar sa daure da towel ido muka hada dashi. Nayi saurin sunkyar da nawa saboda ganin yanda ya futo.. Hoton nake dubawa gabana na fad'uwa. Karasowa yayi kusa dani bai ce komai ba ya sanya hannu ya karb'i frem din yana dubawa naga ya b'ata fuska cikin tuhuma ya kalleni kana yace." Meye dalilin ki da zaki tsaga min hoto. "? Tambayar shi ta bani mamaki K'warai nace" Kamar yaya."!?


Babu walwala a tare dashi yace." Ina tambayar ki kina tambaya ta. Duba b'arnar da kika yi min lokaci guda shekarar abina guda babu abunda ya same shi sai dalilin ki."! Raina ya b'aci amma sai na danne zuciya ta kawai na mike da niyyar tafiya domin nasan laifina ne da na shigo masa daki har na dauki abun shi.. Tsaki naji yaja kasa-kasa yace." Ke akan kowa ma sai kin gwada kishi." Sai da na futa daga d'akin tukkuna na fara tunanin me maganar shi take nufi? Ni a kan kowa ma sai na gwada kishi! Idan na fahimce shi yana nufin kishin Mimi ne ya sanya na fasa hotonta Ikon Allah."!! Abun ya bani mamaki matuka Mimi ko tana raye a duniya Allah ya hada mu auran Namiji daya bazan yi kishi da ita ba, to ko zanyi kishi a kansa sai inyi da Wanda bana ganin shi baya Raye a duniyar ma gabaki daya.
Nafi minti a shirin ina tunanin wannan al'amari daga bisani na share maganar kawai domin dai ni nasan Mimi tafi k'arfin komai a gurina kuma ina zargin domin ya kuntata min yayi min wannan maganar.... Parlor na futo domun bana son tsohuwar ta fuskanci wata matsala amma nayi alk'awarin guy nan ya shigo gona ta zan gasa shi kamar yanda yake min wulakanci son ranshi, Granny tace"Dama yanzu nake tunanin kiran ki ki futo muci abunci ." nace gani na futo granny Daining muka nufa Ni da Ita. Ko da wasa ban kalli shi ba na fara hadawa kowa nashi.. Yana zaune da airpix s kunnen shi baby na jikin shi tana wasa tana ganina ta dinga kokarin saukowa granny ta dauke ta tana fad'in"Bari taci abunci tukkuna." Kuka tasa nace"Baby rigima Bari in gama zan dauke ki." Cikin sauri na had'a mishi abunci na tura gaban shi granny tace"Dauke ta ni na hada da kaina." 'Yar dariya nayi nace "Bari in karasa lada na." Lokacin kuwa baby har ta fara kuka abunda baya so kenan a rayuwar shi kukan baby a kufule yace." Malama ki dauke ta ki k'yale cin abunci mana dole ne."!! Granny tace"A'a!!! K'ato bana son son Kai ba, ji wani magana da kake cin abunci Dole ne mana idan bata ci ba ta yaya zata yi maka rainon yarinyar... Wayar tashi ya aje kan teble din yana kokarin karb'ar baby dake zillo sai tazo gurina, yaro kenan duk yanda take da Dadyn ta taki yadda dashi. Yaji kamar ya tashi ya gaggaura wa Asma'u mari a hasale! Yace." Asma'u wai ba dake nake ba ne."!? Idona na d'ago na kalleshi babu yabo babu fallasa nace" To." Daga haka nayi shiru ja goge hannuna da tissues na karb'i baby daga hannun granny barin gurun nayi raina duk babu dad'i tsaki yaja ya cigaba da danna wayarsa ko kallon abincin banyi ba... Parlor na zauna cikin kujera da baby granny ta biyo da plate din abincin a hannunta tana ta faman mita "Ni wannan rashin. Kawaicin naka akan baby shine yake bani haushi dai kai wallahi duk yanda mutum yaso ya kyauta ta maka sai ka kaishi k'arshe ka canza halinka Haba! Ina dalilin Wannan Abu."!!






*5/12/2019*
[12/6, 12:51 PM] .: *BABBAN YARO*
*75*


Shi dai shiru yayi mata yana latse-latse a waya ranshi nayi masa zafi domin har yanzu baby kuka take yi taki yin shiru Mik'ewa yayi ya karasa kusa dasu baby ya karba daga hannunta har
Hannunsu har yana had'uwa jikinta ya tab'awa yaji alamun zazzab'i, zama yayi kan kujera yana kokarin cire mata Riga jikinta ya kalli Asma'u da ta zuba musu ido shi da babyn yace." Ki duba dakin kan drowar akwai maganin ta dauko min." Asma'u ta mik'e jikinta babu kuzari, baby yake hurawa kunne yana rarrashinta granny tace"Zazzab'i ne yake damunta ko."? Gyada kansa yayi kurrum. Tace"Hak'ori zan sa Iyami taje ta had'o mata dauri tunda ga ba nono take sha ba ballanta yayi mata magani... Ina mik'a masa kwalbar maganin na bar gurin. Kuma har yanzu yarinyar bata daina kuka ba fafur taki karb'ar maganin daga hannunsa sai bugewa take duk jikinsa ya b'aci granny tace"Wacce dai ka karaina kake wa tsawa da nunawa iyaka ita din dai zaka je ka nemi taimakon ta domin nima kasan baby ba yadda take dani ba."


Shiru yayi mata yana matsawa baby tasha magani tana buge-buge dole dai ya mike da ita a kafad'a ya nufi dakin Asma'u da ita.... Ina zaune duk abun duniya ya dame ni ga kukan baby na damuna ka bakin cikin abunda yayi mun a kanta cikin wannan hali ya shigo dakin.


Kauda kaina nayi daga kansa domin wani irin haushin sa nake ji, Mik'o min ita yayi ba tare da tace min komai ba." Danne zuciya ta nayi nace"Me zanyi mata."? Kai tsaye yace." Ki bata magani tasha.'' Babu sauki s muryata nace"Kai da kake Ubanta baka bata sai ni 'yar karo."'" Hannu ya daga min da sauri yace." Ban nemi wata magana daga gare ki ba. Yarinyar nan tun da ta tashi bata yi kuka ba sai da kika zo gurin, duk kece sila kina ji ta fara kuka me yasa baza ki bar abunda kuke yi ba ki dauke ta, kece kika tunzurata take kuka har zazzab'i ya kamata."!! Cikin mamaki nake kallonsa ganin da gaske yake maganar nace"Kana nufin nice na d'ora mata zazzab'in kome. "? D'ora min ita yayi a jikina yace." Nifa ba haka nake nufi ba yanzu dai bata maganin sai muyi magana." Tsaki nayi niyyar inyi masa ganin rainin hankalin sa yayi yawa sai kawai na fasa na rike baby dake zura hannuta cikin rigata kamar me son tasha nono tana kuka da makyarkyata ban tab'a jin tausayin yarinyar ba irin na yau take wasu zafafan hawaye suka soma zubo min.......... Nace"Baby sannu kinji maganin ya mik'o min yace." Bata mu gani." Karba nayi na fara kokarin bata ta datse bakin ta.... Hannu na sanya na bude bakinta da sauri na d'ura mata maganin ta had'iya d'aga ta nayi ina girgiza ta sai shashsheka take yi ns rungume ta kam a jikina.

Yana tsaye a kanmu har Lokacin da nasamu baby ta sauke ajiyar zuciya bacci ya dauke ta, lura da yayi da hakan ne ya zare hannunsa daga cikin aljuhu ya fara kokarin d'aukar yarinyar dake rungume a jikina tana sakin ajiyar zuciya... Rike ta nayi kam a jikina ina hararasa Hankali nace "Zata tashi fa......... Bai ce min komai ba ya bar dakin na bishi da kallo cikin jin haushi kwantar da baby nayi na gyara ta sosai kana mike a hankali na shiga toilet domin dauro alwala, sallah nayi na kwanta kan daddumar bacci me nauyi ya dauke ni, Lokacin Amjad ya shigo ya tadda duk suna bacci daga ita har babyn sun bashi tws

Tausayi sosai Asma'u ya dauka kamar wata jaririya ya kwantar da ita kusa da baby hijab din jikinta ya ke kokarin cire mata ta bude idonta da sauri!! Mik'ewa tayi zaune tayi tana kallon shi. Ita yake kallo babu yabo babu fallasa yace." Ki huta kema naga kin bacci a kasa ne." Hannunsa ta kalla dake rike da hijab dinta yak'i saki..... Kauda kanta tayi tana kokarin sauka kasa dawo da ita yayi da hannunsa yana fad'in "Ina zaki je? Babu fuska tace" Zan shiga band'aki ne." Sakin ta yayi ita kuma ta sauko band'aki ta shiga cikin rashin sanin abinyi, kawai sai ta tsiri wanka, shi kam cikin shiri yake domin futa amma ganin yanayin Asma'u ya tada masa da sha'awa yana jin ko ya futa bazai iya komai ba dama daurewa kawai yake yi domin kar ya nuna mata zulamar sa... Zama yayi yana jiran futowar ta


Asma'u ta manta d'auka ya futa daga dakin sai ta futo daure da guntun towel iya cinya hankalin sa nakan wayarsa yaga futowar ta ta kasan idonsa da yanda tayi saurin komawa da baya.. Girgiza kansa yayi kurrum ya cigaba da latsa wayar sa. Kayan ta tayi saurin mai dawa ta futo tana b'ata fuskar ta... Hankalinsa kan wayar shi yace." Wanka me kikayi da rana haka." Shiru nayi masa kawai ni so nake ya bar mun dakin naga ma futa zaiyi daga gidan dama duk a takure nake zaman shi a gidan kwana biyu kacal. Yace."ko mafarki kikayi."?


Sarai na fahimci inda maganar sa ta dosa share sa nayi na zauna kujerar mirror a takure aje wayar yayi ya karaso gurin, k'amshin turarasa ya dabaibayeni rumfa yayi min hade da tsare ni da idonsa yace." Ina tambayar ki. "? Shiru nayi masa ina jin fad'uwar gaba.... Sunkuyowa yayi ya talfamo fuskata cikin tafin hannuwan sa ya kura min ido, ni kuma sai kauda kaina nake cike da fargaba. Bakinsa yake kusantowa dashi fuskata na rintse idona da k'arfi na mike, shima Mik'ewar yayi da sauri ya rike hannuna yana ya mutse fuska yace." Meye haka? Kike wani furgita da abunda kin San shi." Nace"Wai ba futa zakayi bane don Allah kayi tafiyar ka idan zakaje ni Wallahi na kan rasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login