Showing 18001 words to 21000 words out of 55849 words

Chapter 7 - Auren Shehu 2 Complete Hausa Novel

TAKORI   

01 Oct 2025

21

ta ci kukan ta ta koshi ne yunwa ya sako ta gaba, gashi bayan abin da Usman ya sheda mata ko ruwan Rugar Shehu ba ta sha'awan sha. Duk yanda ta so ta roki afuwan Usman da ya mata rangwame ya mayar da ita gida taurin kai ya hana ta. Sai da la'asar ta yi sannan ta sauko daga kan gadon karar, ta ci sa'a kasa ta shanye ruwan wankan ta, sai dan ragowa da ba a rasa ba. Daga can gefe in da dama be jike ba ta shimfida ledar dakin ta yi sallah.

Rabon da ta yi sallah mai cike da nutsuwa kamar ta ranar tun tana jami'a sai yanzu da Usaman ya kawo ta Rugar Shehu. Gun Allah ta kai karar shi, ta na mai rokan Allah ya fitar da ita daga hannun shi ya kuma mata sakayya da gaggawa. Kukan yunwan da cikin ta ya ke mata ya sa ta tuna da ajiyar kwararen da ta tura karkashin gadon, ta na adduar Allah ya sa ta sami abin da za ta iya ci ba tare da ta tuna kalaman Usman ba ta janyo su waje. Ganin dafaffen kwai ta yi hamdala, dan kuwa shi ta ci sai da cikin ta ya dan tasa sannan ta yi hamdala ta na mai duban ruwan shan da aka aje mata. Ko dan daukan fansa dole ta rayu, dan Usman dai sai ta ga bayan sa matukar ta na numfashi, kudirin da ta ke yi a ranta kenan yayinda ta daga kwaryar ruwan ta kai daidai saitin bakin ta ta na mai zubawa ba tare da ta yarda kwaryar ta sauka bakin ta ba. Sai da ta kusa kwarewa ta aje, azahiri ta na furta
"Idan har ban ga bayan wannan almajirin ba ban isa Zeee ba!"

******

Yanda Zainab ta ga rana haka ta ga dare, itacen korar sauro da Usman ya kunna mata a bukkar be sa Zainab ta iya bacci ba saboda zugin da kafarta ta ke mata duk da kumburin ya ragu, da kuma taurin gadon karar Usman da yake ikirarin ta godewa da ta samu ya iya bar mata.

Duk yanda ta so musgunawa Usman ko ya ji haushi ya mayar da ita abu ya ci tira, haka kuma ba ta fasa yi masu kashi ko wanka in da ta so ba, Usman na dauke kai ya sa yara su gyara. A haka har Zainab ta yi kwana uku Rugar Shehu, gaba daya ta fita hayyacin ta, kafa kam Alhamdulillah ta warke sosai ta bar zuciyar Zainab da jinya, tun tana kuka har hawayen ya sauke sai dai na zuci.

Da Safe bayan ya tashi daga zaman fada, ya zauna wajan bitar karatu da ya saba yi tare da yara maza. Zaune su ke tsakar gida, sun saka Usman tsakiya kowannan su dauke da alqur'ani ko kuma allo sanadiyar rashin wadatuwar alqur'ani cikin Rugar. Kai kawo da Zainab ke yi a tsakar gidan na ba gyara ba dalili ya sa Usman kasa nutsuwa. Sanye ta ke cikin daya daga cikin doguwar rigunan da ta zo da shi, ramar da ta yi be saka kirji ko hips din ta raguwa ba, illa dai kashin wuya da tsayin wuya da ta kara, ba sururu Zainab kadai ba hatta tafiyar ta ma abin sha'awa ne ga duk mai kallo, duk sanda ta gifta sai ya bita da idanu hatta daliban na sa sai da suka fahimci hankalin Shehu yau dai ba ya gare su.

Sallamar Bello da kuma ganin wanda su ke biye da shi ne ya sanya Usman hade rai kamar hadari yaAuren Shehu 2


6


HaWe ran da yayi bai sa sun fasa ?arasawa har in da su ke ba, su uku ne namiji Waya da mata biyu da za a iya cewa miji, mata da ?arsu ne don ?ar ba za ta wuce shekaru goma ba.
"Me ya kawo ku nan Tanko"

usman ya faWi cikin tsawa, ya kara da

"Bello me kake nufi kenan? So kake ka nuna ka isa a Rugar nan ko me ye dalilin ka na shigowa da wainnan iblisan?"

Ya cigaba da faWi yana mai kallon Bello wanda ya sha jinin jikin sa jin lafazan Usman. Gyara tsayawa zainab ta yi cikin nishadi wanda ya kira jinin sa ya mata aikin da ta dade tana yi baya kama shi, amma kuma kallo Waya ta yi ma wanda ya kira da Tanko ta hango kamanni na jini tsakanin su sai dai shi din baki ne, sabanin Usman da ya ke farar fata. Duk da ba jin yaren ta ke yi ba za ta tsaya ta kalli dramar da za a yi.
Haka ma sauran jama'ar gidan su ka fito suna mai kallan Tanko cike da mamaki da al'ajabi, dan kuwa babu wanda be san mugun halin Tanko ba. Daliban Shehu kuwa musammam kanana cikin su har rawar jiki su ke ganin yanda Usman ke bambami.

"ka dubi girman Allah Shehu, ka dubi nasaba da martaban ka, ka dubi darajan yarinyar nan Cangwai da ta fito daga tsatsonka ka yafe mana"
Macen ta faWi tana mai share hawaye.
"Baffa Allah ya masa cikawa bayan kun baro sa, ba mu da kowa shi ya sanya muka ce mu zo cikin ?an uwa mu zauna, wallahi duk wani mugun abu na bar shi a dajin falgore, Tanko mai kyawun hali ne nan, ka yafe mana"

Tanko ya caSe cikin fullanci yana mai rusunawa kamar zai yi sujada. Cikin lafiya da nuna rashin tausayi Usman ya furta

"Rugar nan tsarkakakke ne babu Wigon mugun aiki a cikinta, saboda haka baku da matsuguni ku fice kafin na saukar da fushi na akanku"
yayi maganar ya na mai nuna masu hanyar ficewa daga Sangaren nasu. Daga Tanko har matar shi zubewa su ka yi gwiwowi biyu, hawaye na zuba daga idanun sa ya ce

"Ka taimaka Shehu, ba mu da matsuguni Shehu, duniya ta juya mana baya, idan ma ba za ka karbe ni ba ka duba Rahila da Cangwai, Raliya diya mace ce, ko ba komai Cangwai diyar ka ce...."

"Cangwai ba diya ta bace!"
Usman ya katse shi cikin tsawa yayinda ya kai kallan sa ga yarinyar da Tanko ya kira Cangwai, be gushe ba ya kara da

"Na sani! Ka sani! Na san ka sani! ku kama hanyar ku tunkafin rai na ya fi haka baci"
Maimakon su juya Tanko ya shiga waige waige yana mai rokon mutanen da ke wajen da su sanya baki Shehu ya yafe musu a nan ne ya hango zainab da ke tsaye. Ba shigar da tayi na doguwar riga kaWai ya Wauke hankalinsa ba har da bambamta da tayi da sauran matan rugar, in bai yi ?arya ba irin matan birni da su kan sace don neman kudin fansa ne.
'toh me ta ke yi a rugar shehu' ya tambayi kansa. Gaba Waya ta manta abin da ya ke yi ya saki baki yana kallon zainab tare da zantawa da zuciyar sa. Yanda ya saki baki ya na kallan ta ne ya sa Usman ya kai kallo gare ta, ganin Tanko ya sa shaf ya manta da ita. Wani irin bakin kishi da tun da ya zo duniya be taba jin irin shi ba ya taso masa har kahon zuciyar ta, musammam da ya lura Zainab din ma Tankon ta ke kallo

"Me kike yi a wajen nan? maza shige?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ciki!"

Shehu ya daka mata tsawa da firgici ya hana mata musawa cikin sauri ta shige bukkan, sai da ta shige sannan ta ji haushin kanta na yin biyayya da ya daka mata tsawar. Daga bakin assabari ta laSe tana kallon yanda mutane ke ro?on usman yana botsarewa.
"Kai an yi azzalumi! komai aka yi wani zalincin ya ke aikatawa! Wannan masifa har ina! Ina ma ina jin abin da su ke fada! Ya Allah idan har wannan bawa zai iya aikata sharri da zalinci ga jinin sa, Allah kai kadai ka san irin zalincin da zai iya aikatawa kai na, ya ke kuma kan aikatawa, ya Allah ka mana maganin shi.

"Zan iya karbar Rahila da kuma diyar tsohuwar mata Cangwai saboda raunin su na 'ya'ya mata! Wajan ka dai babu shi Rugar Shehu, idan har hakan ya maka toh, idan be ma ka ba su ma din kana iya tafiya da su!"

Cewar Usman wanda kallan da ya ga Tanko ya na yiwa Zainab ne dalilin shi na biyu na rashin yarda ya zauna a Rugar Shehu. Rahila matar Tanko ta na ji tana gani Tanko ya mata sallama tare da mata alkawarin zai dawowa da ya sami matsugunni. Kukan Rahila da Cangwai be sa Usman ya tausaya ma su ba, sai ma sallamar yara da yayi daga karatu, shi da Bello su ka tasa Tanko gaba, sai da su ka tabbatar yayi nisa da Rugar Shehu, sannan Usman ya ce da shi be hana shi zaman dajin ba matukar ya kiyaye kusantar Rugar Shehu.

Tuni labarin zuwan Tanko ya kadaye Rugar, ranar da jimamin abin da ya faru aka wuni, ita kan ta Zainab sai da zuciyar ta ta dan yi rawa sanadiyar ganin rikidewar Usman cikin kankanin lokaci duk da sam ba ta fahimci ainihin abin da ya gudana a tsakar gidan ba.
Usman kuwa tun bayan da ya tasa kyeyar Tanko, haka kuma ya tabbatar ya ja kunnan Bello be iya komawa sashan shi ba gudun kar ya kara saka Zainab a idanun sa, wani irin bacin rai ke addabar zuciyar duk sanda ya tuna yanda Tanko ya shagala ya na kalle Zainab, wacce ta tsaya kerere da ita ko mayafi babu.

Sai bayan da ya idar sallar ishai sannan ya koma gida ya tarar Zainab na zauna sai surutai ta ke. Fadi ta ke

"Babu ruwa, babu wuta, babu bandaki, babu siturar arziki! Babu waya! Babu club! Babu mai jin hausa! babu Jin dadi! Babu babu babu, babu civilization! bambamcin wannan daji da kabari shi ne can lahira ne! wannna wani irin rayuwa ce!...Ammy in ma ke ce ki ka kullace ni dan Allah ki yafe min, Dady.... Dady ka mutu ka bar ni da masifa Dady! Auren Shehu masifa ne Dady!"

"Akwai maza amma ko?"

Da sauri ta kai kallan ta ga Usman sam ba ta san da shigowar sa ba, tsaye ya ke jikin bango hannu sa harde a kirjin sa, yayinda hasken acibalbal ya haske fuskar sa, idanun sa har kyalli su ke tsabagen bacin ran da ya ke tattare da shi.

"Na'am?"

Ta mayar masa cikin rashin fahimta. Maimakon ya bata amsa, sai ya wuce ciki ya dauko wasu acibalbal har biyu, ya kunna haske sosai ya gauraya dakin, sannan ya dawo ya tsaya gaban ta, idanun sa cikin na ta ya furta

"Maza da ki ka fi so a rayuwar ki, akwai su ko? Na ga yanda ki ka kasa boye maitar ki sanadiyar ganin Tanko...."

"Tanko? Wanene Tanko?"

Zainab ta tambaya dan kuwa gaba daya kan ta ya juye ta kasa gane in da Usman ya dosa. Zainab na murmushi bayan ta gano bakin zaren ta ce


"Ya ba zan nuna maita ta ba bayan na ga namiji iya namiji? Ai wannan dajin kaf babu namiji da ya amsa sunan sa namiji kamar wannan....ya ma ka kira sunan sa?"
"Zainab!!!!"
Ya daka mata tsawa ya na mai kiran sunan ta na ainihi a karo na farko cike da gargadi, duk da hantar cikin Zainab ya kada ba ta fasa fadin
"Ga shi baki, ga faffadar ka fada....."
"Zainab!!!!!"
Ya kara daka mata tsawa tare da daga hannu kamar me shirin marin ta, har ta kai ga runtse idanu. Jin ba ta ji saukar marin ba ta bude idanun ta a hankali ta kai kallan ta gare shi. Idanun sa sun yi jajur sai huci ya ke
"Me ya sa ka fasa? Ka mare ni mana! Ka dake ni! Idan har ba ka daga hannu ka dake ni ba Usman ba ka isa namiji ba!"
Murmushin mugun ta ya sakar mata kana ya na mai ja da baya ya furta

"Idan har duka shi ne zai gwada mi ki isa ta namiji, Ni kuwa zan dake Abu, Amma duka mai dadi Abu ba irin wanda ki ke tunani ba, Irin wanda za ki dena maitar duk wani damiji face ni Usman..."

Ya na gama fadin haka ya fice da sauri dan kuwa yanda ya ke ji zai iya aikata abin da zai zo yayi dana sani.


*Khadija Sidi*
Auren Shehu 2




7



Ta na mai nana ta maganar Usman cikin ran ta yanda ta ga rana haka ta ga dare, dan raban da ta sami ishesahen bacci tun ranar da aka wayi gari a Rugar Shehu.
Kamar yadda kowa ya kwanta da sanyi jikin zuwan su cangwai rugar da tsoron abin da Tanko zai iya aikatawa saboda korar da aka masa haka aka tashi washe gari, hakan bai hana mata dakan hura da zuwa tatsar nono asubahin fari ba. Bukkar da ke kusa da ta Atuwayye , matar taubashin Shehu ya sauke Rahila da Cangwai saboda aminta da yayi da ita sannan zaman da su ka yi a ?asar Benue da mijinta lokacin da su ke ganiyar kaWe shanu ya sanya ta Wan fi sauran wayewa.
Duk wannan kai komon da ake yi da Rahila ake yi, sakin jiki tayi tana aiki tana lura da rugar sosai, cangwai kuwa tuni ta shige cikin yan mata sa'annin suna ta hidimar gaban su.
Ko da aka kammala girki, Raqiba aka kwalawa kira don ta kai ma Zainab nata.
"Iyalle barshi zan kai"

Rahila ta yi saurin faWi don dama neman hanyar shiga sashin Shehu take.
"Ayi haka, tun safe kike aiki fa, Allah ya miki albarka" faWin Iyalle ta na mamakin sauyin halin da ta gani a tattare da Rahila.

"Ba komi Inna, ai mu masu laifi ne, duk abin da zamu yi don mu rage nauyin zunubinmu za mu yi"

"Aikuwa dai Shehu na son debbo ma, ga ta KaWo maras daraja" .

Hansai ta caSe tana mai taSe baki

"Kinga ki iya bakin ki, ba da ni za a yi shari'a ba, in bai so ta ba wa zai so, da gani ai ka san yar birni ce"

Cewar Iyalle tana mai tashi daga wajen. Kalaman nan ne su ka ?ara sanya Rahila son zuwa ko don ta gane ma idon ta matar da kyau, gashi dai zuwan su jiya ta shaidi cewa yana kishin ta.
Da tunanin nan ne ta nufi hanyar sashin Shehu, da sallama ta shiga bukkar ba tare da ta jira an amsa ba duk da cewa zainab ba amsa sallamar su take ba.
Zaune ta iske ta ta baje kayan ta a saman gado tana Waga su, neman mai gwara gwaran da za ta sanya take yi kasancewar duk sun yi datti.
Buga wayar ta take a tafin hannun ta kamar hakan zan sanya ma batirin charji har ya kawo

"A ce mutum ya zama kurma a ?ungurmin dajin nan ta ina zai fara ga waya a kashe ba charji"
Tace tana mai jan tsaki daidai lokacin da Rahila ke kai bakin ?ofa za ta fice daga Wakin. Jin haka ta juyo tana mai kallon hannun zainab, ko da ta shigo bata maida hankali ga hannun ta ba illa suturar da ta gani zube a gado musamman gajeren wandon zainab.

"Laaaaaaa!!! Wallahi irin abin da mai gidana ke magana da mutane in sun yi kinnafin, salla ko me ma sunan"

Tace tana Singere baki, duniya in akwai abin da ke birge ta yana bayan waya, don ta so Tanko ya bata Waya wata rana da ya shigo da su ya ce mata ai kudi ne ma?udai in ya siyar da su

"in sun yi mene? Ya aka yi ke kika iya hausa"

Zainab tace cikin firgici da farin ciki. Firgicin ambaton kidnapping da kuma farin cikin wacce ta ke jin hausa, hakan ya sa Rahila ankarewa da subul da bakan da ta yi, ta yi saurin gyara maganar ta hanyar fadin

"A'a wai in sun dawo daga wajen Sana'a na ke nufi..."

"Laaaa hausa ki ke min? Ki na jin hausa? Kin iya hausa?"

"Ai kusan rabin matan rugar nan in ba ma fiye da rabi ba suna jin hausa, Ce mi ki su ka yi ba da ji?"

Cewar Rahila ta na mai duban Zainab wacce alamar mamaki ya bayya na a fuskar ta, kafin bacin rai ya maye gurbin mamakin, murya kasa kasa ta ce

"Babu mahalukin da ya taba min, ko na mu su magana ba su nunawa sun gane bare su amsa, sai tsinannan dariya kamar mahaukata!"

"Hmmmm kadan daga cikin aikin Usman kenan!"

Cewar Rahila ta na mai jinjina kai na.

"Usman kuma, akan wani dalili"
zainab tace cikin Sacin rai

"Zalunci! Ai babu azzalumi sama da Usman, Kinga da mahaifin Usman da na Tanko miji na uwa daya uba daya su ke, Amma Usman ya tunkude siriki na daga sarautar Rugar Shehu, haka kuma ya haye kujerat tare da haWe dukiya gaba Waya, ya kada shanu kaf be bar mana ko daya ba ya tai dajin ga, ya bar mu ba cin yau bare na gobe, bakin cikin haka ya kar siriki na har lahira, dole ta sa mu ka bi sahun Rugar Shehu, gaban ki dai aka yi komai jiya....."
Ta kare maganar ta matsar kwalla. Cike da tausayawa Zainab ta furta

"Lalle ya cika azzalumi na gaske, tun da har ya iyayiwa jinin sa haka, ban yi mamakin abin da ya aikata gare ni ba......"

Nan ta kwashe komai ta fadawa Rahila, ta kare da

"Ni ban san yanda aka yi ba, zan dai tuna sanda na gama karatun jarabawar da zan zana, kawai sai wayar gari na yi na ganni kurgurmin daji hannun wannan azzalumin!"

"Surkulle kenan! Ai kiranye ya mi ki!"

Cewar Rahila ta na mai hango tarin dukiyar da Tanko zai samu ta sanadiyar Zainab, Dan kuwa kifi ne daga sama gashesahe, za su yi amfani da Zainab ta hanyoyi har biyu, na farko su kwaci Rugar Shehu ta hanyar hada baki da ita, Dan kuwa tun jiya ta gano Shehu na so da kishin Zainab, Zainab din ce dai ta kasa fahimta, haka kuma bayan sun kawar da Shehu su karbi kudi makudai na fansar Zainab, dan kuwa dai ba ta ga dalilin da zai sa Tanko ya ga Zainab ya mayar da ita salin alin hakan nan ba.

"ikon Allah, yanzu dai tun da na same ki baki munafunce ni ba kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login