Showing 39001 words to 42000 words out of 55849 words

Chapter 14 - Auren Shehu 2 Complete Hausa Novel

TAKORI   

01 Oct 2025

32

kallo ba, sanyin da ya ziyarci fatar har ya kai ga sanya ta dan rawar dari da kuma yanda ya zuba mata idanu ya saka ta yi saurin shigewa jikin sa, Usman ya runtse idanu lalle zuciya ba ta da kashi, ganin Zainab da kuma yanda ta kamkame ya sa gaba daya gwiwarsa ta yi sanyi. Cikin zafin nama ya zare ta daga jikin sa, yayinda ya ke kokawar danna rigar kan ta, Zainab ta dada bijirewa ta hanyar yin rawa da kanta, ta na samin damar kwatar kanta ta yi saurin sake shigewa jikin sa, ta rungume shi kam kamar me shirin shigewa jikin sa, cikin kuka ta ke fadin

"Dan Allah kar ka bari a tafi da ni, ba zan iya komawa gida ba"

Usman ya runtse idanun sa cikin karfin hali, shi kan shi ya na jin zafin tafiyar ta, Amma bayan abin da ya faru ta tabbatar ma sa ba ta da makiyi da ya wuce shi, ta kuma tabbatar masa yanayin tsanar da ta masa da kuma tsanar zama da shi a Rugar Shehu....

"Ka riga ka gama bata min rayuwa shi ne za ka yada ni, wallahi ba ka isa ba....."

Maganar da ya dawo da shi cikin hayyacin sa kenan, yayi saurin banbare ta daga jikin ta, ya tashi tsaye, a dake ya furta

"Ki shirya nan da awa daya Bello zai tafi da ke....."

"Na san ka so ni Usman, ka fada min kuma na gani a idanun ka, me zai sa ka guje ni? Na san na ma ka laifi......"

Hannu ya daga mata tare da fadin

"Ba na son ki! Dama na dauko ki ne ina cikin magagin bakin cikin rashin mahaifiya ta, wacce a sanadin ki ban gana da ita ba, yanzu kuma na huce ba kuma na bukatar ki!"

Wani irin zafafan hawaye ne su ka gangaro daga idanun ta. Zanin jikin ta ta kunce domin janyo shi samai yanda za ta rufe kirjin ta, ta tashi ta yi ta sha gaban sa ta na mai kokarin sanya idanun ta cikin na sa, murya kasa kasa ta furta

"Ba gaskiya ba ne, ka ce min ka yi nadama, ranan a bakin ruwa, ka ce min ka na so na......"

Ya na mai girgiza kai yayinda maganganun sa da Tanko ke kara saka zuciyar sa radadi su na mai masa ya yawo a kunne


"Zainab me ya sa? Duk zaman nan da mu ka yi da ke, duk kwanciyar hankalin da mu ka samu.... Zainab... Zainab me ya sa...? Dama kin yi ne dan ki cutar da ni?"


"Ta yi ne domin haka na ce ta yi! Kai a tunanin ka yarinya kamar wannan za ta taba san gidahumi irin ka? Ai ka godewa Allah ma ka sami raban ka!"

"Ki manta da abin da na fada mi ki rannan na fada ne bisa kuskure.......ba na san ki....."

Maganar ya soke ta tamkar takobi. Cikin dauriya ta furta

"Ka na so na Usman, fushi ka ke da ni kawai in ka huce komai zai wuce.."
Kai ya girgiza mata, kana ya ce

"Ba zan iya zama da ke ba......"

"Ko da kuwa ina dauke da juna biyu?"
Kallan ta ya ke cike da bakin cikin karyar da ta ke sharara ma sa, har ta kai za a iya karya ciki, maganar Tanko ya kara ratsa zuciyar sa na

"Ta yi ne domin haka na ce ta yi! Kai a tunanin ka yarinya kamar wannan za ta taba san gidahumi irin ka? Ai ka godewa Allah ma ka sami raban ka!"

Ya sake juyawa zai fice Zainab ta dakatar da shi ta hanyar fadin

"Ka sake ni toh! Idan har za ka mayar da ni gida ka sauwake min wannan auren na masifa!"

Ga mamakin ta sai ga shi ya juyo, hannu ya sanya cikin aljihu ya fitar da takarda, ya na mai ruko hannun ta ya sanya takardar tafin hannun ta. Ba tare da ya bari sun hada idanu ba ya juya zai fita, har ya kai kofa Zainab ta furta

"Ka yi min yanda ka yi sanda za ka dauko ni, dan Allah ka gusar da hankali na Usman....."

A sanyaye ya juyo ya na duban ta, sai a sannan ta lura da yanda idanun sa su ka yi jajur. Cike da nadama ya furta

"Ina fatan za ki yafe min...."

Ya fice da sauri in da ya bar Zainab durkushe hannun ta rike da takardar da ya bata ta na kuka mai tsuma zuciya.
AUREN SHEHU 2


Bayan ta yi mai isar ta, ta tashi ta fara hade na ta ya na ta, tsoron abin da ke cikin takardar da Usman ya bata ya sa ta kasa budewa bare ta karanta, dan kuwa idan ta ga saki uku za ta iya zarewa. Kayan da Usman ya kawo mata ta sanya, kafarta sanye da silifas ruwan dorawa. Kallo daya za a mata a danganta ta da fulanin daji.

Idan aka dauke Raqeeba babu wanda jikin sa be yi sanyi ba ganin Zainab ta fito dauke da akwatin ta, tsakar gidan Shehu cike da jama'a manya da yara sun zo mata sallama, su Iyalle kuwa cikin su har da ma su kuka. Zainab ta karaci waige waigen ta ko za ta ga Shehu, hakan ya sa Bello fadin

"Tun dazu ya fice.....ya ce ba sai mun tsimaye shi ba"

Kai Zainab ta gyada kawai ba tare da ta iya furta komai ba. Ta na kuka su Iyalle na kuka tare da neman yafiyar juna, har su ka mata rakiya daidai mararraba da Usman ya taba aje Tanko sannan su ka juya cike da alhini.

Tafiya ce mikakkiya Muhamadu Bello da Zainab su ka yi, duk sanda ya nemi su zauna ko dan Zainab ta samu ta huta, sai ta ki, gaba daya a tafiyar ta ke sauke fushin ta, ganin haka duk sanda lokacin sallah yayi Muhamad Bello ya ke bata lokaci ko ya samu ta huta.

Ta ki ci, ta ki sha sai kuka. Sai yamma likis su ka Isa Mambila, dake sun saba sosai da Bello sun sami tarba na karamci, in da aka ware ma Zainab daki na musammam dake wasu daga cikin su ba su mance Zainab ba. Ita kuwa sam ba ta iya tuna komai bare ma ta gane su. Da adduar Allah ya sa Usman ya biyo sahun su ya ce ta dawo ya fasa mayar da ita ta kwana cikin ran ta. Ba ta yanke zato ba sai da washagari da sassafe Bello ya sanya ta cikin motan Taraba. Makudan kudin da Usman ya ce a bata, kulle cikin bakar leda Bello ya aje a kan kafarta bayan yayi yayi ta karba, ta ki.
Har zai juya ganin halin da Zainab ta ke ciki ya sa ya kasa tafiya ya bar ta kamar yanda Usman ya ce, tare su ka karasa Taraba. Wajan kwana ne ya gagara sai da Allah ya taimaka wani driver ya kai su wani dan karamin hotel wanda za a kira shi da ba yabo ba fallasa, Bello ya kama mata daki guda, tare da siya mata abinci. Ya sheda mata shi ya na daga can waje kila ya kwana wajan masu gadi dan kuwa shi be saba da rayuwa mai tsada haka ba.

Abincin na su babu laifi, Amma kasancewar ta na cikin bakin ciki da kewar Usman da kyar ta dan caccaka sannan ta yi sallah ta na mai rokan Allah mafita. Kasancewar Zainab ta kwana biyu ba ta kwana kan katifa ba, sai ta ji gadon ya mata wani irin, ta gwammaci ta yi kwanciyar ta bisa dadduma duk da ta san baccin ba zuwa zai yi ba.
Da sassafe wajan karfe Shida ya sanya ta motar Kano, Zainab na masa magiyar kar ya barta shi kuma Bello ya na bata hakuri, har ta kusa tara masa jama'a ciki har da masu cewa

"Toh ana tafiya dole ne? Tun da ta ce ba ta yi a rabu da ita mana"

Wani kuma fadi ya ke

"Kai kuwa ka juya da ita mana"

Cike da rarrashi Bello ya furta

"Ki yi hakuri uwar gida, ban san takamamman dalilin da ya sa Shehu hakuri da ke ba, bayan jaddada soyayyar ki da yayi a gare ni, Shehu na kaunar ki matuka kusan sai na ce ke ce diya mace dal tilo da zan iya bugar kirji na ce Shehu ya so, so daya tal! Shehu ya zabi barin mu, barin Rugar Shehu da komai na shi domin ya dawo birni ya rayu da ke. Dan haka ni sai dai na ce ki yi hakuri, wannan al'amari na ku da daure kai ya ke, Allah ya saka hakan ya fi zama alkhairi, Allah ya sada mu da alkhairin sa, bissalam"

Ya juya ya na mai matse kwalla, in da ya bar Zainab cike da da na sani iri iri, musammam na kasa rokan Usman da ta yi, da ta sani da ta nemi yafiyar shi, da ta san zai ce su dawo birni da ba ta ji zugar Rahila ba, da kuma ba ta bari zugar Raqeeba ya rude ta ba, duk da a lokacin neman hanyar tafiya ta ke Ido rufe, yanzu gashi Allah ya yassare mata lokacin da sam ba ta bukatar komawar ta gidan. Gaba daya rayuwar ta ta sauya cikin watanni kalilan, shin ina ta dosa? Daga ina za ta fara? Tunanin da ta yi ta yi kenan a hanya.

Ba kamar da ba duk check point in aka tsaya sojoji sai sun tanka ta, wannan karan babu wanda ya lura da ita saboda shigar fulanin da Usman ya sanya ta tayi, da kuma wannan shekin da fatar ta take gaba daya ya tafi. Sanda su ka isa Kano Magarib ta yi, dan sahu ta tara ya kai ta gida. Amma ko da ta doshi kofar gate din gidan Malam, gaban ta na faduwa ta shiga bugawa, wani saban maigadi ne ya bude. Ganin mace tsaye bakin kofa ta yi dagaje dagaje da ita cikin kayan fulani ya dube ta ya ce

"Lafiya? Ku barar ku ba dare ba rana?"

Cike da bacin rai Zainab ta furta

"Na ma ka kama da yar bara? Kai wanene ma?"

"Kut! Kanin uban ki ne ni! Ja'ira! Sai ki ta zama a nan tunda ke abin na ki ma har da rashin kunya!"

Baki Zainab ta bude, duk tsiwar ta yau sai gashi ta rasa ta cewa, wai ita ake kira almajira a gidan uban ta. Katan dutse ta dauka ta shiga buga kofar da iya karfin ta. Isowar mota tare da fitowar Jauro da saban maigadi wanda bugun da Zainab ta ke yiwa gate din ya sanya su fitowa a fusace lokaci guda ne. Motar ce ta dalle Zainab wacce Jauro ya hau da fada da shi kan shi be gane ta ba, fadi ya ke

"Wallahi sai mu yi kasa kasa da ke a wajen nan! Kofar gidan uban ki ne za ki kama da bugu ko akwai wanda ki ke bi bashi? Kai muntari ko wani ya siyi nono gun ta ne be biya ta ba?"

Cike da takaici Zainab ta furta
"Kai din gidan uban ka ne ai! Ba nono ba Shanu ya sa siya! Wallahi duka sai kun ci uban ka ni Zainab sai na yi maganin ku!"

Jin Murya irin ta Zainab Jaura ya bude idanu ya na duban ta, gaba daya ya ma manta da motar da ta tsaya ta na shirin a bude kofa su shiga. Muntari da har lokacin be gano komai ba cewa yayi

"Wallahi ban taba siyan nono gun ta ba, kai ni yau ma na fara ganin ta...."

"Hayaniyar me ku ke mana ne da ba za ku zo ku bude mana kofa ba?"

Cewar Falmat wacce ta gaji da sakarcin su Jauro, ta sauke gilashi cikin neman ba'asi. Gefan ta Halitta ce zaune, da ke sa'ad da su ka je umara ta makale lalle sai da Sudais ya bari ta biyo su Nigeria, za ta yi wata guda ya zo ya dauke ta.

Tsayawa Zainab ta yi ta na duban motar cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa, dukan su biyun ba su lura da ita ba, musammam Falmat wacce ta ke bambamin sun ki su bude mu su gate su shigar da mota.

Cikin inina ya na mai nuna Zainab da yatsa Jauro ya furta

"Ran-ran-ki ya da-de ina ga fa kamar dai Hajiya Yakura ce......"

Sai a sannan su ka lura da Zainab, Halitta ce ta fara fitowa da sauri inda Falmat ma ta bi bayan ta, gaban ta su ka karasa idanun su kan Zainab yayinda ita ma din su ta ke kallo, shigar su, yanayin su da kamai na su yayi daban, musammam Halitta wacce ta yi jajur kamar balarabiya cikin bakar abaya. Sai Zainab ta ke jin kan na ta tamkar almajira kamar yanda saban mai gadi ya yi zato, hawayen da su ka dade ba su zuba daga idanun ta ne su ka fara shirin zubowa, ta yi saurin kawar da kai gefe.

"Yakura.........."

Cewar Halitta yayinda ta rungumo ta da sauri, kamshin turaren ta ya maye warin ranar da Zainab ta kwaso, ta ma rasa yanda za ta yi, murnar ganin Yakura ko kuwa kuka za ta yi, Falmat kuwa rugawa ta yi ciki ta ihu fadi ta ke
"Yakura! Yakura ce! Wallahi Yakura ce! Ammy Allah ya karbi adduar mu!

Halitta ta janye Zainab ciki dan kuwa yan unguwa har sun fara tsayawa ganin ba'asi. Ammy ba ta gasgata maganar Falmat ba sai da ta ga Halitta ta shigo hannun ta rike da na Zainab, nan ta zube ta yi sujjada na godiya ga Allah sannan ta tashi ta rugume Zainab, dukan su hudu kuka su ke, aka rasa wanda zai rarrashi wani, musammam Zainab wacce ita na ta kukan biyu ne, har da na rashin Usman.

Sai da su ka dan nusta ne Falmat ta fita shigo da mota, Halitta zaune kusa da Zainab har lokacin ta kasa sakin ta, Ammy ce ki ta kiran yan uwa da abokan arziki ta na sheda mu su Allah ya dawo da Zainab, Yakura ta dawo. Anty Sauda kuwa cewa ta yi da Yakura ta huta Ammy ta fara tambayar ta in da za a samo tsinannen almajirin nan da kuma in da ya kai ta, idan Allah ya wayi gari ita za ta zo.

Duk yanda su ka so Zainab ta fada mu su daga in da ta ke, ko kuma yanda aka yi aka tafi da ita, da kuma wanda ya tafi da ita sai Zainab ta sa mu su kuka. Hakan ba karamin dada tayarwa Ammy da hankali yayi ba, dan haka ta ce kada wanda ya kara tambayar ta komai, a bari ta huta tukunna ko zuwa gobe ne.

Ruwan wanka aka hada mata, bayan Falmat da kan ta ta gyara mata daki. Sai ta ke ganin komai daban musammam da ta shiga bandaki, wai itace cikin tangaran maimakon zagayen kara da Usman ya sa aka mata, cikin kokarin tsayar da hawayen ta yi wanka ta fito. Cikin kayan ta da ta bari a gida ta sami wata doguwar riga mara hannu ta sanya. Gaba daya jin ta ke tamakar bakuwa, komai na gida ya zame mata tamkar sabon abu, gadon katako maimaikon gadon karar da ta saba, carpet maimakon tabarma ko ledar da ta saba, tiles maimakon kasa da tsakuwar da ta saba takawa.

Ta idar da sallah kenan sai ga Halitta dauke da farantin abinci, ta aje gaban ta tare da fadin

"Yakura ki daure ki ci abinci"

Zainab ta yi mata shiru kawai ta na duban ta. Ganin ba ta da niyar bude kolar ne Halitta ta bude ta fara zuba mata, shinkafa ce jellof ya sha bushesshen kifi, yanayin turirin da ke fitar da kamshin kifin ne ya daki hancin yakura, tun ta na iya jurewa har ta kai ga toshe hanci da hannu, cikin ta ne ki hautsinawa sanadiyar rashin abincin da ba ta ci ba tun safe, ba ta ankara ba sai ji ta yi amai ya taso mata, ta tashi a guje ta shiga bandaki. Nan ta yi ta amai kamar wacce za ta amayar da hanjin cikin ta. Hankali tashe Halitta ta kira Ammy.

Cike da tsoran abin da zuciyar ta ke ayya na mata Ammy ta furta

"Yakura ayya kuwa? Tun da na gan ki na san ba ki da cikakkiyar lafiya, tin kafin dare yayi mu tafi asibi..."

"Ammy gajiya ce kawai da yunwa, tun safe ban ci abinci ba hanji na ya kulle, da na sha ruwan zafi I will be fine"

"Duk da haka gobe sai mun je asibiti Yakura....."

"Allah ya kai mu"

Cewar Zainab cikin kaguwar su tafi ko ta samu ta huta. Ammy ba ta barta ba sai da ta tabbatar ta sha ruwan bakin shayi kamar yanda ta bukata, bayan shi ba ta iya cin komai ba, dole haka su ka bar ta ta kwanta.

Tun da su ka fita take juyi kan gado, Baccin gaji ya ke diban ta amma hakan be sa ta dena ganin Usman da ke mata gizo cikin idanun ta ba. Filo ta ja ta rungume tamkar shi ne Usman cikin magagin bacci ta furta
"Ina san ka Usman, ba zan iya rayuwa da wanin ka ba, dan Allah ka rufa min asiri ka dauke ni daga nan......."

Inda Zainab ke cikin radadin san Usman, shi ma a nashi bangaran gaba daya ya rikicewa su Iyalle tun bayan da ya dawo ya tadda Bello ya cika umarnin shi ya tafi da Zainab.

Ko zaman cikin Rugar baya iya yi bare ya yarda ya shiga bukkar sa ko wanda Zainab ta koma bayan ya farfado da ga ciwo. Kamar yanda ya ke mata gizo shi ma din gizo ta ke masa. Fatan shi Allah ya sa ta isa gida lafiya gashi be da hanyar da zai gane hakan.

***

Anty Sauda tare da Ammy da Halitta ne su kai Zainab asibitin premier washagari da azahar bayan isowar ta, tare ta ke da sojoji wanda a fadar ta su ne za su rubuta statement din da Zainab za ta ba su bayan sun dawo daga asibiti, ta sha alwashin kama Usman da duk wani da ya ke da sa hannun dauke Zainab. Babu gwajin da ba a yiwa Zainab ba, ciki har da na HIV, hepatitis da na juna biyu.
Bayan an gama gwaje gwajen suna zaune jiran fitowar sakamako Zainab ta yi zaman ta can gefe a reception, ba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login