Showing 6001 words to 9000 words out of 29871 words

Chapter 3 - ETERNAL-LOVE COMPLETE HAUSA NOVEL

fams   

05 Dec 2024

5945

mata yaga anasa ummi a adaidaita Hakim ya dauketa .
Mai yasami ummin ne?
wallahi maman nabil daga kwanciya tace mana zata dan kwant¨¤ kanta na Sara mata shikenan Aida taje ta tasheta ganin magrib tayi tasamai ta a wanan halin Dama Bahama warkewa tayiba tafada tana nufarsu Hakim dake jiranta cikin sauri.
Oh Allah sarki Ummi!
Allah ya bata lafiya Nima zanshigo anjima in baban nabil ya dawo.
Bakomai maman nabil saimun dawo tashiga Hakim Kuma ya zauna gefen adaidaitan.
malam Dan Allah kayi sauri kamar bata numfashi general hospital zaka kaimu .Gudu yakara Allah yabata lafiya .
Allah ya taimakasu weekend ne ba goslow sosai da isarsu general hospital Hakim ya sauka,yai cikin asibitin wajen da nurses suke zama ya nufa don neman agajinsu, da wani labura suka hadashi dashi, ya dauko wheel chair suka koma wajen asibitin inda su Nuzla suke aka daurata kan wheel chair suka shiga ciki yayinda Mai adaidaitan kemasu Allah ya Kara sauki.
A office din Dr gabadayan sunyi tsuru tsuru suna sauraran abunda zaice masu.glass din dake idon shi yacire ya ajiye kan table Sanan ya Maida dubansa kansu Aida zaku Dan bamu waje zanyi magana da sister dinku, mikewa sukayi suka fice daga office din.
Iskar bakinsa ya faisar sanan yace ya kike da wanan patient din da kuka kawo?
She's my mother!
Shiru yayi na Yan secanni Yana kallonta kamar ba zai ce komai ba,can yace Am sorry to say but tana fama da brain tumor Wanda a halin y¨¤nzu take bukatan surgery, gashi ta shiga coma , akwai medicines damuke bukata da zaa fara mata amfani dashi before we undergo the surgery.
Tunda ya ambaci brain tumor take ambaton Inallilahi wa ina illiaihi rajuin hawaye na kwararowa daga idanunta.
Dr nawa ake bukata kudin aykin? Tafada tana share hawayen daya wanke mata fuska.
Wata paper ya dauko ya Mika mata, aibatasan lokacin data mike tsaye ba hannun ta na rawa 1.5 million Inallilahi wa ina illiaihi rajuin ina zasu Sami wayannan makudan kudaden da zaayi treating ummi dasu.
Dr ba wani taimako dazaka iya mana wallahi bamu da inda zamuyi sourcing kudin.
Am sorry this the only way to save her life ,muna bukatan ay mata surgery very urgent.
Tashi tayi da kyar tana kuka yayin da take fitowa daga office din, girgiza Kai kurum doctor yayi what's a pity ya tausaya masu sosai.
Da sauri Hakim da Aida suka tareta.
What did the doctor y? Cewar Aida, kukan datake ne yahana ta magana.
Is she going to be alright? Nan ma shiru
Dan Allah kayi mana magana mana kina daga mana hankali cewar Aida.
Doctor yace tana dauke da brain tumor!
What!suka fada atare har suna hada Baki.
Yes! He said we need the sum of 1.5 million for her surgery.
Aida batasan lokacin data zame kasa ba ta zauna tareda kifa kanta akan ciya tashiga raira kukaba 1.5 ina suka gansu, yayinda Hakim ya kifa Kansa jikin bango hawayen ma sun kasa fitowa don tashin hankali ina zasu Sami kudin da zaayi treating ummi shine duk abunda yafi tsaya masa a Rai.
Jin hannun Nuzla yayi a hankali ya dago idanuwan shi da sukayi ja dasu Yana kallonta girgiza masa Kai ,sanan ta duka wajen Aida tareda dagota ta rumgume stop crying Aida everything will be alright muyi mata adua,insha Allah ummi will be back on her feet tafada yayin da take goge mata hawayen dake face dinta,hannunsu ta kama suka tafi dakin da aka kwantar da ummi.
Kwance take jikin yazama stable unlike lokacin dasuka kawota duk da y¨¤nzu ma a coma take.
Gaban gadon suka karasa ,Nuzla ta tsuguna daidai fuskarta tareda dauko hannunta ta hada da nata,Allah ya Baki lafiya please karki tafi ki barmu kamar baba I promise you duk inda kudi suke zanje na Nemo for the surgery kukane yazo mata ,da sauri takifa kanta akan bed din kar su Aida su gani, itace babba she has to be strong for them, Intana kuka agabansu zatana karya masu zuciya ne kawai.
Har dare suna Nan Basu tafiba,maman nabil da baban nabil ma sunzo harta kawo masu abinci.
Doctorn dazu ne yashigo Yana ganinsu yace I think you should leave,kukoma gida ku huta .
But Dr wazai zauna wajenta? Karku Sami damuwa akwai masu kulla marasa lafiya anan saidai ku rinka zuwa da safe Kuna ganinta,shiru sukayi basuce komai ba,har ya gama abunda zaiyi ya tafi.
Har Aida ta fara Gyangtadi Nuzla ta tasheta Saida ta shafe ummin da aduain tsari sanan suka fice daga asibitin.
Koda suka dawo gida Daman basa Jin yunwa sunci abinci a asibiti, don haka wajen kwanciya suka gyara suka kwanta.
Yau satin ummi guda a asibiti bawani improvement kullum sai sunje sai dare suke dawowa,ganin kudin hannunsu yafara yin kasa yasa Nuzla fara tunanin inda zata Sami ayki tabuga tabuga Amma baa Dace ba har ta fidda Rai wata ranan talata maman nabil tazo mata da albishiri cewa wanan shararran restaurant Dinan wato pLG na neman maaikata wani abokinsa ke sanar dashi baban nabil din Bai ,aikuwa Bai kasa a gwiwa ba yake bashi labarin Nuzla, aikuwa ya tausaya mata Kuma yay masa alkawarin Yi mata hanya tasamu ayki awajen Dan samun ayki a PlG sai kana da hanya.aikuwa sunyi murna ba kadan ba,har gida suka shiga gabadayansu sukai masa godiya.wanan shine dalilin fara ayin Nuzla a PlG restaurant.
[2/6, 6:52 AM] +234 806 235 2006: ETERNAL LOVE
SOYYAYA TA HAR ABADA
4??
??
yau tunda ta tashi take jin kanta na Sara mata a daddafe tayi wanka ta dauko kayanta ta shiga shiryawa cikin uniform dinta white and black Mai dauke da logo din PLG restaurant sai sunanta a gefe.
Aidace ta shigo dakin hannun ta dauke da plate sai cup din tea ta ajiye mata ,Nuzla ga breakfast dinki ki maza kici kar kosan yay sanyi da zafinsa iyabo ta zubamin Allah yaso ba layi sosai .
Zama tai kan mattress dinsu ta dan kwanta tare da rufe idanuwanta hannun ta dafe dakanta .
Mainene bakya Jin dadine ? cewar Aida tana taba wuyanta donjin temperature dinta .
No kainane yake Dan min ciwo na kwantane ya lafa .
To ki hakura mana da zuwa restaurant din yau man tunda ba kyajin Dadi sai ki kira ko Ahmad ne ki fada mishi .
Tashi tayi ta gyara zaman ta yauwa yama lafamin kinga bani abincin naci natafi kar na makara don madam ba mutuncine da ita ba ,tafada tana Mika mata hannu.
cikin tausayin yayar tata Aida ta Mika mata kosan sannan tafita ta dauko wani cup din tana fifita mata don ya huce ko rabi bata Shaba ta mike .
Wai kina nufin Harkin koshi Dan wanan da kika ci? tafada tana kallonta .
Kumatunta taja don't worry am ok in inajin yunwa zan nemi wani abun naci am not a kid okyyy.
bayanta ta dauka ta daura kan uniform din sai taje can zata cire .
Hakim ne yashigo Yana Waka as usual.
Oops sorry yafada Yana juyawa girgiza Kai kawai Nuzla tayi kullum fa sai Ammasa magana akan sallama Amma hakan Bazai Hana ajima ya shigo Yana Waka ba .
salama ya rinka wada masu da gayya ,dallah malam kadamemu kashigo cewar Aida kadai ji kunya kullum sai an maka magana akan sallama Amma kamar wani ibli....
ya isa haka Nuzla ta katse ta don tasan y¨¤nzu zai koma fada .
Hakim da Allah karka fita ka bari na dawo ,kayi mana girki kaga Aida zata asibitin wajen ummi .
Kuma Kai mana Mai Dadi sunan wani wai hajara Aida tafada tana dariya ,malama ki bar ganinkin bani shekara daya wallahi zan gwabje maki baki.
Au haba Bismillah to tafada tana matsowa .wai ku Dan Allah kullum sai kunyi fada hankalinku yake kwanciya ? to kina Jin dai itace take takalata da fada cewar Hakim,
kaikuma dayake baka da .....Dan Allah ya isa haka kubarni inji da abunda damuna karku sani makara please tafada tana daukan handbag dinta ,1k ta Ciro tamikawa hakim gashi ka Samo chanji ka dau dari biyar kayi mana wake da shimkafa ay munada ragowar waken ko ? Kallon Aida yayi dake kunshe Dariya malama ana tambayarki akwai wake ko Babu Akwai mana ,saika bama Aida chanjin tayi kudin mota .
Saina dawo !
A dawo lafiya
Andaiji kunya namiji da aykin mata tafada tana dariya ,to saimai tunda nasan ni ba Dandaudu bane.
tadan makara Dan Allah ya taimaketa madam taba karaso ba don ba mutuncine da ita ba ,idan kayi fashi koka makara saita cire Maka dari biyar acikin salary dinka ,gashi Kuma da aykin Nan ta dogara don ba laifi ana rufawa Kai asiri .Matsalarta dayace yadda zata Samu ta roki madam ko zata bata loan ne sai ta rinka cira a albashin ta tasamu takai ay ma ummi ayki take tunani .
Nuzla!Nuzla !
Naam ta amsa a firgice don tayi nisa a tunanin.
Wai tunanin Mai kike ina tayi maki magana cewar Ahmad Wanda yake daya daga cikin staff dinda ke ayki a wajen . kije table 6 please akwai customers kije ki taking order Cewar Ahmad .
Ok tafada tana mikewa ,girgiza Kai kawai yayi yarinyar tana burgeshi bata jima da zuwa wajen ba Dan akalla zatayi wata biyu amma har sun saba,batada zakewa kamar sauran staffs dinsu mata ba insunga customers maza sunta Kai Komo kenan ana kararraya.
Tafiya take a hankali saboda kan nata dake Dan Sara mata, Dama tabi shawarar Aida ta zauna yau a gida don dai karta daga masu hankaline tace masu da sauki zata iya zuwa, Amma da kwanciyarta kawai tayi.
wasu yanmatane guda biyu zaune a table six ta karasa wajensu daya tayi dressing cikin abaya maroon yayin da dayar ke sanye da English wear sai wani Dan mitsitsin mayafi data daura Akai kanan yaci atteach ga nails din ta datayi panting kamar ba musulma ba .
Vanilla ice tana danna wayanta
ok ma'am anything Nuzla ta tambaya politely.
Wow Anty Mimi kiga waitern Nan tana da masifar kyau, I like her taima dayan whispering. Sai a sanan wacca aka kira da Mimi ta dago Kai ta kalleta jitai gabanta yafadi, batasan Mai yasaba Amma ji tayi batasan yarinyar.
Kallon ta tayi sama da kasa tana wani yamutsa fuska No you can leave ta fada tana mata kallon banza.
Haushine ya kama Nuzla don a rayuwarta ba abunda ta tsana irin wulakanci Amma ba laifinta bane don tasan yar wani ce ita shiyasa suke wulakanta talaka yadda sukaga Dama da tana da gata aybata isa tamata kallon banza ba ,ba yadda ya iya don aykinan shine rufin asirinsu shiyasa take jurar duk wani wulakanci da cin kashin da customers dinsu masu ji dakai suke mata .
Wajen Ahmad ta nufa two vanilla ice tace masa sannan tasami waje ta zauna,hadawa yayi yabawa wani waitern yakai ganin kamar bata Jin dadi.
Nan ta zauna wajensa dayake chef ne tana kallon abunda yake suna Hira sama sama tana kallon yadda yake hada wani snacks .
Yau ko madam bata shigo bane naga Banga motarta a wajeba?
Tashigo mana yafada Yana daura coffee a tray Yana mikawa wani waiter ,kinsan yau ta makara shiyasa baku haduba, zatayi magana kenan telecom dake wajen yafara Kara.
Recieve the call Ahmad yace mata!
Dauka tayi hello Ana bukatan waiter a table 4 madam tayi instructing, ok ma'am tafada tana hanging call din.
Ahmad bari inje nai taking order madam ce takira.
Tashi tayi saikuma ta zauna da sauri saboda wani jiri dataji, da sauri Ahmad ya tareda gudun karta Fadi.
Ki zauna kawai bari nasa wani yaje yace mata.
No ba komai zan iya zuwa!
Are you sure? Ya tambayeta ,gyada masa Kai tayi sanan ta mike a hankali.
Tun daga bakin kofa r da zaka shiga bangaren VIP ta hango securities guda uku cikin bakaken suit sanye da Bluetooth a kunne kowanensu ,fuskar Nan a hade kamar an Aiko masu da Sakon mutuwa daya na tsaye a entrance din Vip yayinda sauran ke tsaye a main entrance din.
Tunda ta tunkari wajen take jin gabanta na faduwa, ganin wanan bodyguard din Nan Saida ta tsorata . lallai yau koma waye yazo toh babbane, zata shiga ya dakatar da ita fuskarshi ba faraa yasa mata scanner, kut ta hadiyi wani yawu Bai yadda da itaba wato karta cutar da boss dinsa, Nan taji tarafa fargaban haduwa da koma waye shugaban wanan mutumin.
Hanya yabata ta wuce, a hankali take tafiya yayin da gabanta ke cigaba da faduwa Wanda ta Rasa dalili .
Kai tsaye ta nufi table 4 and guess who was sitting there?
The youngest billionaire bachelors in town wato Murda da kaninsa Muneer.
Da kyar ta hada kalmomin bakinta bayan ta hadiye yawu.
Good morning sirs,may I have your order please? ta tambaya muryarta na Dan rawa, Dama in ba a irin Nan ba ta Isa tazo har kusa dasu ,saidai gani a TV.
Murad ko ,kodagowa Bai ba Yana magana a phone Kansa na kallon kasa as usual sanye yake da p cap dinshi Wanda ya rufe Rabin fuskarshi , jikinshi sanye da wata bodyhug ta maza wace ta fito da surar jikinshi na karfi don ana ganin six packs dinshi yana waya a hankali bakajin maiyake cewa, hannusa tabi da kallo Wanda ya rikeda wayar ,gashine kwakkwance ajiki kana ganinshi kaga Dan Hutu,tayi nisa a kallonshi taji gyaran murya.
Um um da sauri ta Maida kallonta kan dayan ,shaf ta manta abunda ya kawota tashagala da kallon Murad.
Sorry sir,
Murmurshi Muneer yayi please hot soup and a medium cup of tea.
Yes sir tafada tana taking down jitai idonta na blurry little by little Amma tana kokarin maintaining balance dinta.
I need to be strong tace ma kanta.
kallonta tamayar kan Murad daya gama waya.
" What about you sir? What would you like to order? Ta tambayeshi tana giran Amsa.
Amma to her suprise the idiot is busy with his phone kamar Bai jita ba .
Rolling idonta tayi yau batasan maike damun customers dinta ba, they kept ignoring her kamar wacca taimasu laifi, wayoyinsu sunfita mahimmanci kenan.
Muneer ne ya katse mata tunani ,just coffee! Nodding Kai tayi sanan ta juya tabar wajen.
Wajen Ahmad ta nufa ta sanar Mai abunda ake bukata, nan da Nan ya hada mata first tray din ta dauka takai masu sanan ta koma ta dauko na coffee din Saida tazo dab dasu lokaci guda ganinta ya dauke yakoma blur wani jiri ya kwasheta kamar kiftawar Ido taji tafadi bata saniba ko akan wani ta fada Amma da alama abunda ke hannunta ya zube.
Kamar wani magic Nan take taji ganinta ya dawo.
Gabantane ya Bada Dam, Ashe Murad ta juyewa coffeen ajiki.
Nan da Nan jikinta yafara bari.
" What the fuck" yafada ranan a hade tareda mikewa Yana kallon yadda jikinshi ya Baci da coffee.Numfashinta ne yanemi daukewa lokacin da narkakkun idanuwansa suka sauka a kanta
Da sauri guard dinshi dake bakin kofar yashigo thinking that the waiter wants to harm his boss tareda zaro pistol daga aljihunsa ,hannu muneer ya daga masa tareda masa alama ya koma bawani Abu.
Cikin in ina tace tace I'm ....I'm sorry sir gabadaya ta rikice tissue din data gani kan table dinsu ta dauka tana kokarin goge masa hannunta tana rawa.
Hankade ta yayi tai baya sai gata a kasa,Amma duk da haka tatashi tana cigaba da bashi hakuri.
Dan Allah kayi hakuri Bada sanina Nayi Maka haka ba tsautsayi ne please forgive me.
Madam ce tashigo da sauri saboda wani waiter daya Kai mata tsegumi ,Allah yasota ma Vip ne da ya tara mata jamaa.
Please Murad am sure ba tana sane tayi Maka haka ba ,it's just a mistake cewar Muneer trying to caim his brother.
You fucking call this a merely mistake ?!
How about this? ya fada ,kafin Nuzla ta dago saijin saukar soup a jikinta harda coffee din .Gabadaya kayanta musamman white top din yayi staining.
Inda Allah ya taimaketa miyar batada zafi sosai Amma dukda haka tana Jinta a skin dinta .
Rufe idanta tayi wanan shine worst expirence daya taba samunta a rayuwa . tana tsaye a wajen kamar status tana ruwan hawaye don tsoran magana ma take .
Murad Mai haka please take it easy muryar Muneer taji .
I'm sorry!
You're just so fucking stupid ,he cured.
Madam ce ta shiga bashi hakuri har tana tsugunawa ,Nuzla ta Kalla tsuguna ki bashi hakuri cewar madam .Amma ga mamakin madam tana tsaye taki bashi hakuri.zuciya ta ciyota .
Ganin haka madam tai kneel down tana magiya .
Damn it ! Fire her her away .
What madam tace tana mikewa .
Don't you get it I said fire her or this building will be demolished yafada Yana juyawa tare da barin wajen yayinda guard dinshi ya take mashi baya .
Hannu madam ta daura Akai tana ihu.
[2/6, 6:52 AM] +234 806 235 2006: ETERNAL LOVE
SOYYAYA TA HAR ABADA

Gamai son update Akai akai zai biya 200 a wanan Acct number 3078411837 first bnk Then message me on my WhatsApp number 08062342006 Banda kira please .

5??.

??

fashewa tayi da kuka , Muneer ne yabi bayan shida sauri yasha gabanshi .
Murad this is not fair,how can you get her fired, just look at the poor girl she tried to apologize to you several times but kaki bata Dama ,why are you so mean to the poor girl.cewar Muneer da ransa Shima Bai masa Dadi ba da abunda Murad yaiwa yarinyar dispite hakurin the ta bashi.
kagama ? to bari kaji nasan irin wayan Nan girls din ,
They are slut da sauri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login