Showing 18001 words to 21000 words out of 29438 words
na Allah
Da kata MUSEENA tunda kuka shigo cikin wannan gidan nawa kuke fadar duk abin da ranku ya ga dama amma wallahi bazan yarda da cin mutunci ba zo ki fitar min daga gida
ba saikin ce in fita ba daman fitar zanyi ke kuma A'isha Allah ya ganar dake ke da mahaifiyar ki idon ku ya rufe kun kasa ganin gaskiya ASIF garzone ko a cikin mazaje tana kaiwa nan ta fita dariya suka sheƙe dashi suka tafa........
*KANO TA DABO TUMBIN GIWA*
N.N.D.C quarters
KARFE 9:30 na dare
Dan Allah Asif, please give me the address of their house, if you do not accompany me, I will go alone.....
tamkar MUZABFAR da dutsai yake domin ci gaba yayi da aikin da yake a cikin laptop a zahiri kenan amma a baɗini shi kaɗai yasan irin bugun da zuciyar sa yake yi yana danna keyboard ɗin laptop din ne amma besan me yake ba rubuta wa ba ji yayi kunuwansa sun toshe ba abin da yake iya ji sai maganar MUZABFAR ina zai saka kansa in hakan ta faru shi kawai ko wani ne ya aure'ta amma ban da MUZABFAR komene dalili wata zuciyar ta tambaye shi I dont no shima be sani ba Amma duk wani bugu da zuciyarsa keyi tare da tunaninta take yi mene dalili anya kuwa ba ɗaukar fansar abin da yayi mata ba za tayi...............
Yan aljanna me ke shirin faruwa
Domin samin amsoshin ku kudai ku ci-gaba da payment a yadda naso ina gamawa in dora book 3 hakan bazai yuhuba sai kun ci gaban da payment wasu jiran document suke Please zan da masu jiran document da masu pages Ku biya ba lallai ne ma in bude group ba wata kila kafin na gama book 2 zan kammala book 3 amma sai kuna karfafamin gwuiwa ta hanyar payment
Zaku ga kwana biyu bana yi da yawa ace duk son da kukewa GIDAN MAGAJIYA MUTUM BIYAR NE SUKA FARA PAYMENT haba yan aljanna ku nuna min so na karshe mana daga wannan fa hutu zan tafi......
Shi yasa ka na tsaya nayi dogun tunani domin faran ta muku da wa'azantar da ku ta hanyar nishaɗantar'wa
Ni Fatahiyyah Muhammad yakasai nake cewa mu huta lafiya 09061890481
Domin biya ta kai tsaye ku sakamin a wannan asusun
8141785374 Amina alhasan Muhammad opay
Ku turo da sheda ta wannan number
09061890481
Dan girman Allah in baki shirya ba kar kiyi min magana
*GIDAN MAGAJIYA*
PERFECTLY PEN'S ✊
https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k
EPISODE 39-40
ASIF tunanin me kake yi.....?,
kodai kana shawara ne ka rakani ko kar ka rakani dan girman Allah ka raka ni ka temaka min ka ceci rayuwata kasan kuwa saboda kai'ta na bar Abuja na tawo....?
tashi ASIF yayi amma ina ji yayi baya ganin komai dafa bango yayi ya runtsai idanuwan'sa yace
"Please MUZUBFAR ka fita hutawa nake so nayi maganar ka tana damuna...,
ASIF kana son FALMATA amma kafiyar'ka ta hana ka gane inza ka farka ka farka wallahi ina guje maka randa zaka wayi gari ace maka tayi aure lokaci ya kure ba damar maida hannun agogo baya....
Fita yayi daga daƙin ya bar MUZUBFAR a tsaye da sakakken baki yana mamakin hali irin na ASIF ga gaskiya nan amma yana kokarin karyata zuciyar sa da hana'ta abin da take so... bin bayan'sa yayi samun'sa yayi a zaune akan kujera ya dafa kan'sa da hannuwan'sa biyu zama yayi a kusa dashi yace
"ASIF....,
a fusace ya tashi yace
"Kai baza ka mai dani dan iska ba wacce budurwa ce za'a je mata karfe tara ta fito indai tana da makwaɓi.....?,
ajiyar zuciya yayi ganin ya sauko be yi tunanin abin da zai fito daga bakin'sa ba kenan yace
"Eh naji mu tafi in bata fito ba shikkenan sai mu bari gobe maje amma fa....,
Saurin tarar numfashin'sa yayi yace
"Wallahi kana magana na fasa...,
Yi hakuri oga muje harara ya banga mai ya shiga bedroom ɗin'sa jiransa MUZABFAR yayi har ya ƙosa kamar ance ɗago kansa dai-dai da fitowar ASIF sanye da riga red colour da wando baki yan gidan TOM FORD haɗe da P-cap Black color ha saka face mark dariya abin yaso ya bawa MUZUBFAR amma sai ya mazai daukan keys yayi binsa a baya MUZABFAR yayi har suka isa gun ya ajiye motar'sa Allah ya temake su Hajiya bata ga fitar'su ba domin data gansu tsare su za tayi da zance....
Wajan driver MUZABFAR ya shiga ASIF ya zauna gurin me zaman banza kome ya tuna har ya shiga ya fito ya dawo gaba wayar'sa ya fito da ita yana dan-dan nawa da alamar wani abu me mahimmanci yake yi sai da suka fara hawa kan-titi tukunna MUZABFAR yace
"Allah ya ja daran oga mun hau titi fa yanzu ina zamu....?,
Ba tare da ya ɗago ba yace
"kai daman baka sani ba....shine ka jawo'ni....?,
daman da address ɗin da su HABIB suka turo maka dashi zamu ni ban sani ba ranka ya dade oga...
okay muje Unguwar sai ka tambaya be cemai kala ba ya ci gaba da tafiya har suka iso asibitin MURTALA ci gaba yayi da tafiya har suka iso kofar mata be mai magana ba ya fito wasu mutane ne zaune masu saida mai abakin titi sallama
amsawa sukai sannan yace
"Dan Allah tambaya nake.....,
Wani da yake gyara jarkar mansa yace
"Allah ya saka mun sani....?,
Amin GIDAN MAGIJYA nake nema
da sauri wani yace
"Kaga wannan shagon to in kuka miƙe zaku ga wani gida kofar'sa a cire da mutane nan ne gidan...,
Godiya yayi musu ya juya baya yana ji wani yana cewa tab yau magajiya ta ɗebo ruwan dafa kanta jar ubancan anya kuwa ba mutanan da suka kamata bane suka dawo....ba
Juyawa yayi ya buɗe mota ya shiga suna ta ce-ce kuce ko kallon arziƙi be samu ba shi abin nasama dariya yake basa gudun samin matsala sai ya danne tada motar yayi suka shiga cikin layin ya gane gidan tun daga nesa a kusa da kofar gidan yayi parking yace
"Oga Munzo fa.....,
Sai a lokacin ya ɗago yace
"ka fita mana dole sai na raka'ka....?,
ajiyar zuciya MUZABFAR ya sauke yace
"ASIF kai fa na kawo....,
da sauri ya ɗago dai-dai saukar MAGAJIYA daga kan mashin sanye take cikin doguwar riga me haɗe da mayafi amma mayafin bata rufa ba yana kafaɗar'ta sai hular chetili da tasaka ta rataya ta jirgita ta tazo mata har ciki shiga cikin gidan za tayi me mashin ɗin ya kashe mashin dinsa da sauri ya tare kofar da sauri MUZABFAR ya kalli inda ASIF yake kallo da yake unguwar da wadatar haske ko ina da kwan lantarki su kuma ba'a iya ganin'su saboda motar me tinted glasses ce ASIF yayi yace
"Malam in baka da abinyi ni da shi....,
ASIF kamar fa faɗa suke da me mashin ɗin nan
a'a dambe suke da hallacan ka jamu mu bargun nan wallahi bana kaunar ganin mata marasa kamun kai jibe'ta
ASIF shigar da tayi kabaƙi ɗaya ba shigar banza bace me tayi na rashin kamun kai hawa mashinɗin da tayi ko kuwa faɗan da suke dame mashin ɗin kasan me ya haɗa'su wata kila ita ce da gaskiya ko shine.....
banza yayi mai ya balle murfin motar ya fita yana ƙarasawa ta ɗaga hannu ta mari me mashinɗin tace
"Narantsai da Allah wannan ka ɗan nayi maka harni zaka kawowa maganar banza nayi maka kama da irin wa'yannan matan ne saboda tsabar rainin hankali nace ka kawo ne gida zan baka dubu ɗaya saboda karfe goma tayi an saka doka shine zakai amfani da wannan damar ka ce min 2500 kabi a hankali wallahi baƙaramin aikina bane ince bazan bayar ba.....,
Kika mareni....?
Juyowa tayi ta kalli ASIF cikin tsuwa tace
"Malam lafiya kazo ka tsaya mana wallahi kome zaka ce bazan bayar ba dubu ɗaya zan bashi tun daga zoo road ka dauko Ni kace sai na baka 2500 ban da uwar a sara da na tabka me ɗinkin be mini ba....,
Wayyo Allah wai ita wannan wacce irin mace ce haka haka ya faɗa a zuciyarsa afili kuwa ciro kuɗi yayi a cikin aljihun'sa dubu uku ya miƙawa me mashin yace
"Gashi tafii...,
ba musu ya amsa yace
"Wallahi kinci darajar wannan bawan Allah da yau zaki san ke mara kunyar karya ce.....,
bisimilla zo wallahi Allah in Ka fita da kafarka Ka godewa Allah domin sai na saka anyi maka dukan tsiya irin kune kuke kuntatawa talaka in kunsami dama Allah ne yasan manufar jaki dabe mai ƙawo ba
yowa kanta yayi da sauri MUZABFAR ya riƙe shi yace
"Dan Allah malam bafa girman ka bane ka tsaya kana faɗa da mace jeka....,
Burga mashin ɗinsa yayi ya yafi ko sai yanzu take tunani inna tasan wannan kamshin turaran tsaki taja a zuciyar'ta tace"ko ina ruwana da su owo afili kowa tace
"Nagode amma wallahi daba ku bashi ba maceci ne a zoo road fa ya dauko nii amma yace 2500......,
murmushi MUZABFAR yayi yace
"Ba komai....,
juyawa tayi zata shiga gida KAWU ya sawo kai zai fito tsayawa tayi ya fito yace
"FALMATA lafiya nake jin hayaniya tun ɗazu nake jiran dawowar ki amma shiru me kika tsaya yi harkika dade daga zaki amso ɗinki..?,
KAWU me ɗinkin ne baya nan na tsaya jiransa da ya dawo kuma beyi ba dakyar na samu abin hawa....
To shige Allah ya shirya ki bana son wannan faɗan dakike yi da maza amma bakyaji FALMATA
shiga tayi ba tare da tace ƙala ba kallon su MUZABFAR yayi Allah yayi mai gane mutane dan haka lokaci kalilan ta gane su cikin tashin hankali yace
"Ranka ya dade badai ku tayiwa wannan diɓan albarkar ba dan girman Allah ku rufan asiri kar saka a kama'ta kuyi hakuri....,
Runtsai ido ASIF yayi ganin babban mutum yana me wannan magiyar da sauri MUZABFAR yace
"A'a baba wajan'ta muka zo a bokina na rako....,
da sauri ASIF ya buɗa baƙi zai magana KAWU yace
"Allah ya saka lafiya....ba kamasu kuka ƙara zowa kuyi ba....,
Ji ASIF yayi yawa ya ɗora hannu aka ya kurma IHU ko yaji dad'i gashi kamar an kulle mai baki ya kasa magana be tsinke da lamarin MUZABFAR sai da yaji yana ce baba daman wani babban lamarine ya kawo mu baba alfarma muka zo kai mana tun lokacin da kuka bar Abuja muke so muzo amma aiyuka summana yawa ASIF yana son yar gurinka FALMATA mun zo tambaya Allah isa ba aimata miji ba
suman tsaye ASIF yayi ya kasa tantance me kunnuwan'sa suke ji mai muryar KAWU yaji yace
"Babbar magana yanzu dai ga wayata ku samin number ku zan neme ku inde na gama bincike...,
da sauri MUZABFAR ya amsa ya saka mai sallam sukai mai suka shiga mota har a wannan lokaci ASIF yaka sa tantance me ke shirin faruwa me i saka be dakatar dashi ba....amsar da ya kasa bawa zuciyar'sa kenan
har suka isa gida ba wanda ya ƙara magana fitowa yayi ya shiga shashin nasu kiciɓus yayi da HAJIYA a kofar shiga part ɗinsa tana zagaye da waya a hannu da sauri ta juyo tace
"Kai kuwa ASIF ina kasamu gun shiga tun dazu hajiuya kattime me dalilin aure wannan wacce gidan tv suke tallan'ta ta kawomin zuƙa zuƙan mata ka zaɓa amma shine kake ƙoƙarin watsa min ƙasa a ido na kirawa wayar ka tana faɗa min wani shirman banza.....,
MUZABFAR da shigowar'sa kenan dariya zancan Hajiya ya basa yace
"Hajiya Allah ya bar mana ke....,
Amin inda gaske kake kai kuma na dawo kanka dan wallahi bazan laminci ka zauna da wacca juyar'ba ba tare da ka auri me kwan haihuwa ba.....ga kanan marabar ka da gauro kaɗan'ce kamata yayi lokacin da zaka tawo ka tawo da me zubin taliya yar murji amma ka tawo kai kaɗai ni shigo ka zaɓa ka darje....
dabara ce ta waɗo mai yace
"Hajiya yanzu daga gunta nake....,
washe baki tayi tace
"Dan Allah nasan Baka karya da gaske....daga gun jikartawa kake hakane MUZABFAR....,
Eh Hajiya
Shiga Hajiya tayi ɗaki ba tare da ta ce musu komai ba shiga part ɗin'sa yayi shikuwa muzabfar sai ya gano karshen wannan chapter dan haka bin Hajiya yayi dariya ce ta kusan kuɓucce mai dannewa yayi ganin yan mata sunci ado sun fi su goma sha wayyo Allah rigimar Hajiya ko salla bata yi..,
da sauri Hajiya kattime me dalilin aure tace
"Zaɓi ka darje ko wacce da ka ganta nan kwalin degree ne da ita wannan ita kuma master's degree ne da ita ta nuna wata tasha fenti a fuskarta sai taunar chingum take a ƙa'idar ungiyar mu photo muke bayarwa a zaɓa so lokacin da tayi min magana ta dauki number ta ne a television ne daga cewa babban mutum ne kai shi ya saka ma na kwaso su muka tawo akwai zaurawa a cikin su amma wallahi zam zam suke ciki da waje yasha gyara baza ma kace anyi ba ga yar shela can sabuwa ce fil Ranar auranta mijinta ya mutu....
kurɓar lemon da Hajiya ta saka yar aikin'ta ta kawo mus da snacks ta gutsire cake ta ƙara korawa da lemo tayi fari da idon'ta tare da yarfe hannu awarwaron da ta saka suka bada wani sauti tace
"Dan samari zaɓa ka darje wallahi zasu zame maka aljihu kai saboda tsabar biyayya zasu iya kwantawa kabi ta kansu domin sun horu ba ƙaramin training na yi musu ba danni ba yau na saba harkar nan ba na dade a cikin'ta....
Zaro ido MUZABFAR yake tabbas Hajiya ta ɗebo abin da yafi karfin masifar'ta koya zasu kaya da wannan yar duniyar tab......
Nima zan so inga yadda zasu kaya
*akwai rikice fa hmmm kudai Ku ƙarasa payment domin jin yadda zata kaya yau na buɗe paid group WA yanda suka biya zasu gansu a ciki.....*
Sauran page 5 na gama book 2
09061890481
Only WhatsApp
Nainarh kid's:.captain Ayusherh
Queen Kainat:.shiryayyiyar kaddara
Oumyasmeen:.gidan magajiya
*GIDAN MAGAJIYA*
EPISODE 41-42
Ina me dalilin Aure ajiye kofin hannunta tayi tace
"Ranki yadade gani...,
Hajiya tayi tace
"ina me baki hakuri yaron nan yace min yana da wacce yake so ....,
Hajiya ban gane mekika ce ba haɗa rai Hajiya tayi tace
"Abin da kunnuwanki suka ji miki shi nace....,
tab wallahi baza ta saɓuba saida na kashe uban kuɗi ki zomin da maganar banza kar ki ganki uwar manyan mutane narantsai da Allah yanzun nan sai mu lakaɗa miki duka iya karkarinta ace an kai mu gidan yari wannan kuma ba yau muka saba shigar'sa ba ya zame mana tamkar ɗakin uwar mu in banda rainin hankali na tako tun daga Sokoto na tawo kice min wai kun fasa muna dura a garin na ko hutawa bamuyi ba muka yo nan....
Ke daka tamin amma ke dai anyi mara mutunci ki dubeni tsofe tsofe dani ki dinga faɗan wannan magana bakya tsoron Allah ya kwashe miki albarka
Sannu uwata nace sannu uwantale wallahi ku daka ta nawa ne abin da kika kashe....?
MUZANFAR ya faɗa kama kugu tayi tace
"Dubu dari uku domin jirgi muka hau....,
Okay bani account number din ki karanto mai tayi ya saka ba dadewa ta ga alert tashi sukai ba wanda yayi wa Hajiya sallama ƙasa tafiya nabeela tayi ji tayi baza ta iya barin gidan nan ba Hajiya kattime ta roƙo hannun ta domin tasan damuwar'ta tace
"Mu tafi zaki gwada min son zuciyar ki....,
ba yadda ta iya haka ta bisu tashi Hajiya tayi zata shiga bedroom dinta dariya ce ta kubbu cewa MUZABFAR ya dinga yi harda riƙe ciki leƙowa Hajiya tayi tace
"Innalillahi MUZABFAR kardai kaima ka haɗu da wannan ciwo na zamani mental processing da naji a radio....,
be cemata ƙala ba ya fita shashin'sa ya nufa tura kofa yayi kamar yadda yayi tsammani haka ce ta faru tana zaune ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya tana girgizawa ta na kallo agogo my juyowa tayi tace
"Habibty 11:39 fa .....?,
rungumeta yayi yace
"Zance...?,
Dariya tayi tace
"Masha Allah ina picture kanwar'tawa nunamin....,
Wayar'sa ya zaro ya shiga cikin gallery din'sa ya miƙa mata dariya tayi ta rankwashe shi aka tace
"Wannan photo na ne ai na kanwar'tawa nake nufi.....,
amsar wayar'sa yayi yace
"Tunda baki yarda ba shikkenan....,
dariya tayi tace
"Uhmm...,
ABUJA OSOKORO
Kamar an jefo'ta haka ta shigo cikin gidan tana haƙi sai zare ido take tana wai waye domin yau taga bala'i ganin idon'ta hurjanjan ta shigi cikin dakin mahaifiyar ta da sauri hajja ta tashi tace
"A'isha lafiya tun dazu nake neman ki amma wayar ki a kashe kin ɗaga min hankali.....,
kasa magana tayi sai ruwa da take cewa miƙo mata tayi ta sha bude wardrobe tayi tana zuba kaya a akwati..
A'ishah lafiya kike haɗa kaya tamkar wacce za tayi hijira....?
Hajja gidan mijina zan koma ni wallahi na fasa auran wannan shegen mutumin ɗazu kinga tujarar da matarsa ta aiko akai min har da cewa zata buga sunana a jarida da photo na ai kinga ta kunyata ni a idon duniya harfa barazana tayi min da rayuwata
to shi yanzu Allah isaka be sakeki ba
Hajja ko ya sakeni wallahi sai ya mai dani
yanzu dai ki bari sai gobe kya tafi dare yayi 12:00 fa
Hajja da zafi zafi ake bugar karfe gwara natafi tun da zafin abin Abuja ba kamar sauran garuruwan ce ba a kwai tsaro zan isa lafiya ina zuwa zan faɗa miki kar ki damu ta faɗa tana jan akwatin ta
Allah ya tsare ki
Amin hajja ta ɗaga labule tafita inda ta ajiye motar'ta ta nufa buɗe'ta tayi ta saka akwatin'ta ta rufe za gayawa tayi wajan driver ta shiga kye tayi mata ta tashi horn tayiwa me gadi ya buɗe mata get ta fita hawa kan titi tayi zuciyar'ta cike da tunani kala kala har ta isa gida horn tayiwa masu ɗaya daga cikin masu tsaron gidan ne ya fito riƙe da bindiga a hannunsa ganin ita ce sai ya koma ba dadewa sai gashi me gadi ya buɗe get ɗin....
shiga ciki tayi da gudu daidaita parking din'ta tayi ta fito ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya zo ɗaukan akwatin'ta yayi har kofar da zata sada ta da floor'ta ya ajiye mata da yake yasan dokar ogan'nasa dauka tayi ta shiga ajiye akwatin tayi a floor ta zuba ta gumi....tana tunani
KANO N.N.D.C QUARTER
tunda ya shigo ya kasa zaune ya kasa tsaye ya rasa abin yi ko dan Hajiya ya yi AURE amma wannan ta dace da ta zama uwar ya'yansa.....?wacce irin tarbiyya za ta bawa ya'yansa anya kuwa ba auran