Showing 15001 words to 18000 words out of 29438 words
kallon wajan dining din turawa yayi ta buɗe corridor ne da yar baranda an ƙawata shi da flowers masu kyau har wani kamshi suke fiddawa ta cikin baranda ya shiga wani waje ga wata ƙatuwar glass door turata yayi tuni ta buɗe wani haddadan floor ne me kyau da tsaruwa dafa kansa yayi lokacin da ya tuna be fito da briefcase dinsa ba tana mota mutane sun gajiyar da shi tun da ya sauka ya huce government House sai da aka gama taron ya dawo haɗi da buɗe wani sabo. Aiki da gwamnar yayi na gina sabuwar gada wayar sa ya dauko ya kirawo Akram bugu ɗaya ya dauka cikin bada umarni yace
"Akram kazo dakina ka karbi key ka ɗauko min briefcase dina a cikin mota...,
Cikin girmamawa yace"to....,
Kashe wayar yayi yana kallon ko ina na dakin yana tuna rayuwar'sa ta yarinta sallamar Akram ce ta dawo dashi da ga dogon tunanin da ya waɗa ɗagowa yayi ya amsa ya mi ƙamai mukullin amsa yayi ya juya be wani ɗauki dogon lokaci ba sai gashi ya kawo mai amsa yayi ya ajiye yace
"Thanks...,
kasa kasa yawa me ciwon baki indai halin yaya ne inda sabo sun saba shi haka yake tashi yayi ya kulle bedroom ya shiga sai kamshi yake zabgawa da sauri ya fito..... yace
"Hajiya badai yaran nan ne ba suke gyara min ɗaki....?,
Wannan yaron ne Ubanka ne kabiru ke gyarawa ta bashi amsa a gatsai domin dazu ya ɓata mata rai da yaƙi cin abinci.....
komawa yayi ba tare da yace komai ba dan yasan yace zai biyewa Hajiya akwai matsala ita haka take so..
bedroom ya shiga ya fara cire kayan sa daga shi sai boxer ya shiga toilet cire boxer yayi sakarwa kansa shower limshe idanuwan'sa yayi da sauri ya buɗe sakamaƙon ganin fuskar falma'ta tanayi mai gizo......
Sauri yayi ya gama wankan Saboda ya tara gajiya yana fitowa kaya kawai ya ja blanket addu'a yayi sannan ya ƙarasa lulluɓa ya kwanta na dade'wa bacci yayi awan gaba da shi........
`Unguwar kofar mata`
Ina magajiya take da sauri magajiya ta ɗago ta kalli kofa wata mata ce da dattijuwar mace kallo ɗaya tayi musu tasan bada arziki suka zo ba tace
"Gani ko naci ban biya ba....?,
Ƙarasa shugowa sukai matar tace mata ke saurara tsohuwar kilaki zuwa mukai in ja miki kunne akan mijina
tashi magajiya tayi ta sheƙe da dariya tace
"Baki ƙarya ba danni nan da kika ganni tatatciyar yar iska ce duk da abin da kike zo dashi tofa ki shafa fatiha kin'samu dai-dai da kugunki......,
Ba shakka mama kinga ko ashe labarin da aka bamu zan zo na tarar da haka
tafi magajiya tayi tace
"Gaskiya tsohuwa sun cuce ku basu baku daidai ba....,
Salati tsohuwar nan ta saki tace
"Bilkisu bala ya dauko miki ruwan dafa kanki...,
Sai yanzu ta ɗauki haske ashe matar sajan Bala ce bilkisu tace
"Wallahi kika sake kika shigo gidana wallahi zaki ga bala'i da tashin hankali ganin idon ki.....,
to ai baki san nice bala'in ba da masifa har tashin hankalin duk nice ke je kijawa mijinki kunne ya fita harka ta inhar kin isa dashi ko da yake yace fa baki iya tarbiyya ba zai auro me mai wa ya'yansa tarbiyya ba irin ki ba tunda nima gashi nagani ba a sami tarbiyya tun daga gida inban da rashin tarbiya ace uwa ke rako ya' gurin budurwar siriikinta tir da halin ku ga hanya nan tun kafin in nuna muku irin nawa tashancin ku tattara yan'matan ƙafafuwan ku ku barmin gida ko in saka ayi ƙasa ƙasa daku
ta faɗa tana muci muci da idon'ta
Bilkisu zo mu tafi a'a mama wallahi yau sai naga wanda ya tsaya miki karuwa
dariya magajiya tayi tace
"Daga nan hotel hotel muke zuwa da mijin'ki yanzu waka ma ciki ne dani....,
Mama kinji ko innalillahi yowa kanta zata dake ta ji tayi an riƙe hannun'ta da sauri ta ɗago dinana yace
"Ke har wace zaki shigo har cikin gida ki ciwa uwar dakin mu mutunci wallahi kinci karya kin zo gidan da har gurin dass munje mu dawo balle ke matar ƙaramin alhaki dan sanda....,
Kuka ta saka tace
"Ta tabbata mama gidan karuwai muka zo....,
Sakin'ta yayi yace
"tantagarya kenan in kina neman gidan karuwai da ya amsa sunan'sa karuwai kika zo GIDAN MAGAJIYA sha fatiya da salatin annabi in da hali haɗa da kurhuwallahu three three in miki ta turawa....,
Kama hannun'ta mahaifiyar ta tayi ta goge kwallah tace
"Kema mace ce za ai miki abin da yafi wanda kikaiwa ya'ta....,
Komawa magajiya tayi ta zauna tace
"Da kar ku tafi wallahi in saka a karya muku ƙafafuwa....,
basu ce mata kala ba suka tafi.....
dariya dinana yayi yace
"Magajiya magajiya magajiya tamu wanda besan ki ba ya shiga uku a yau she sajan Bala yayi miki ciki......?,
juya wainar'ta tayi tace
"Kaɗan ka gani sun zo da bala'i ne sai suka tarar da wanda ya fishi....ko kahu....?,
zare ta gumin da yayi yace
"Falmata Allah ya kawo miki miji na aurar dake na huta kwanaki kin jamin bala'in dass gaba kuma bansan name zami jamin ba.....,
Hada rai tayi tace
"Alkur'an daman nasan zamu sha gori....gurin kahu...,
Rabi ce ta fito da ga bayi riƙe wando zanin'sa kuma a ƙafaɗa yace
"Magajiya anya kuwa da kafafuwa a jikina dan Allah ku duba min ko sun cire....kashi nayi me ciwo.......,
Innalillahi a'a ka gan'su nan a saƙale a kofar banɗaki kahu ya faɗa yana jifan shi da harara....
kallon kofar bayi yayi yace
"Ban gan'ta ba...,
kai karka raina mana hankali bana zaka fito ko sai na jefo ka......
ka dawo daga gidan yari dole ka dawo da iyashegen'ka dinana ya faɗa....
Aini kaga na rasa bakin magana deeni in banda tsohon iskanci yace a duba mai kafa a'a kai za a duba maka cewar magajiya.....
Kyale dan kut..tumar uba jira nake ya ƙaraso na danfara Shi da ƙasa zai yi explainesha (explanation) dala dala nine har da tafiya Abuja cikina duk ya kunbura dama ba muje ba sun harbe maka kafa da hannu ka shanya su da hujja manjagara ya faɗa yana zare ido irin na tsofaffun yan daba
aaa wannan kuma har damu kake manjagara kafi to fili kace mun ishe ka tsohon dan wiwiii....dinana ya faɗa
zaman dirshan rabi yayi yace
"Wayyo ƙuguna na shiga uku zan rasa kugun haihuwa.....,
Iccen hutar magajiya kahu ya ɗauka ganin kamar kahu gunsa yake yowa ya tashi ya fita a guje yabar zanin'sa kahu yace
"Kun ga dan iskan karya ko da ya tsaya na babbaka mai kafafuwa sai ya faɗa mana tana jikin'sa ko kuma tana saƙale a kofar bandaƙi.....,
Gafaran ku dai masu gida ba'a rasa ku da tashin hankali asho ya faɗa yana shigowa
harara magajiya tayi mai tace
"To gama abin ka wallahi bazan bada bashi ba...,
kuɗi ya zaro yan hamsin hamsin yace
"Yau da gwarina nazo.....,
Dariya su sauda suka saka suka daka ta da cacar da suke to yan bani na iya kuji da abin da yake gaban ku....
kallon'sa ba suyi ba suka ci gaba da buga cacar da suke kujera ya ja ya zauna ya miƙa mata yace
"Bani ta duka....,
Kirgawa tayi tace
"Naira dari biyu ce fa....,
Kinga kina gallakaikai da kudin nan nasan darajar'su in ba zaki bani ba bani kuɗi na ina gangarawa Yakasai zanci ta hadiza uwar yan daba...
dariya ta sheƙe da ita tace
"Dinana jiye min wannan magana.....✍️
Ana ta payment fa me kuke jira zuwa 50 na gama book 2
*8141785374 Amina alhasan Muhammad opay*
*Ku turo receipt kai tsaye ta wannan number 09061890481*
500
Yan nijar Cameroon Katin VTU ta wannan number 09061890481 yan nijar katin Airtel na 300fcfa ku ɗauke shi kuturo ta wannan number 09061890481
*Only WhatsApp*
*Dan Allah in baku shirya ba kar kuyi min magana*
*GIDAN MAGAJIYA*
EPISODE 37-38
Kaf faɗin unguwar nan wacce waina ce me dadi sama da tawa....?
Wallahi babu uwar ɗakina ko zaki temaka ki bani ko fefe ɗaya ce da shinkafa da taliya da miya har da bama in dan na samu kyamini total na biya....
turo ɗaurin'ta gaba tayi tace
"Banji me kace ba mai mai'ta injiii....,
ba sai ya maimaita ba kawai kice bazaki bayar ba sai zaman kashe wando ba sana'a wallahi ka cuci kanka mu da ake ganin mu gamu ga munan to mu ke sana'a har mu samu abin sakawa a maƙoshi bama maula
Maza zuby tofar da mugun yahu da inyi wannan sana"ar taku ta karuwanci yasin gwara in mutu banci ba lallai yarinyar nan kin ma raina min hankali ai kuwa zanyi maganin'ki ya faɗa yana kokarin ciro reshen bishiya ihu ya saka sakamaƙon kaɗan gare da ya hau jikinsa ihu ya saka da sauri kowa ya fara neman hanyar gudu har magajiya duk son wainar'ta da take haka ta tsallake ta barta kawu da yake cikin bayi ya na ƙoƙarin rufe wa dinana yayo kansa ihu ya saki yana cewa na shiga uku karka sake ka.....shigo min be ida rufe bakinsa ba ya shigo fita kawu zai yi amma ina dinana ya riƙe shi yana kuka rasa yadda zai yi saboda tashin hankali.... cikin ikon Allah ya sauka daga jikin dinana yabi ta tarariyar banɗaki ya fita......
duk da haka dinana be saki kawu ba sai ma ƙara rukunkume shida yayi....tun ƙuɗashi kawu yayi ya waɗi.....
taka wa shege ruwanci ki rabi ya faɗa daya shigo yanzu....
Tashi dinana yayi yace
"To dan kumbura masifa zo kai ka taka min ruwan ciki kaga yadda ake bura....uba wallahi.....,
Rabi aini na rasa bakin magana me yahana Kai da ka shigo ka taka min huyan'sa so yayi ya rungume'ni mu mutu tare da yake Allah almusawweru ne kuma adalu sai ya ƙara ruƙunƙume shi ya kasa barin jikinsa.....
Dariya rabi ya dinga yi harda riƙe ciki ya gyara daurin zanin'sa....yace
"Allah ya temake ni bani da rabon huya kawu kawai harsaso yadda gudun ƙadangaran da kuke nake....,
tsaki kawu yayi ya huce shi bin kawu yayi yace
"Kawu dan Allah wai yau she zaku koma Maiduguri....,
Lokacin da uwar... ka salamtu ta shirya dinana ya bashi amsa tsaki ya ja ya murguɗa baki yace
"Bandai kasa da mutum ba balle ya dauki kaso shege dama director na DSS ya harbe maka kai kowa ya huta haka ya dinga damuna da kuka yana face majina....,
Zama dinana yayi a kan farin botikin uwani zame shi uwani tayi tace
"Sau nawa zan faɗa maka ka dena zaunar min a kan botiki kaƙi to wallahi haka zan dinga yi maka kana zama ba magana zan zame ka ko ka yi hankali.....,
tab har abada wannan dai bazai hankali ba to ma duwawun nasa nawa yake da har zai fasa miki botiki da kinyi hakuri ko ki saka kunama yana zama ta sheme dan iska........kowama ya huta yayi jinya ko ta kwana ɗaya ce ko ma sarara
KAWU Ka lura ka gane duk inda ka saka sabga da dan daudo ana tare da rashin nasara Ubangiji ne fa yayi hani da daudo shikkenan KAWU munga ta kanmu baka bina bashin rantsuwa yanzu haka jarin da MAGAJIYA ke baka yana rushewa nima yar sana'ar da na fara abun yaƙi arzki ba mamaki Ubangiji so yake ya ganar damu illar abota da fasiƙi amma munƙi fahimta duk inda ƊAN DAUDO yake to aminin KARUWAI NE....
Karuwa tana gidan malam hamisu zubaida ta faɗa tana wani girgiza haɗi da taunar chingum tana yi mai kallon tara saura kwata....
Dariya Rabi yayi yace
"Dadina da gobe saurin zuwa godiya nake zuby ta waje na....,
mayafin'ta taja a igiya ta kalla mai harara tace
"Da hallacan matsamin zan huce uban haɗa husuma wallahi rabi kaidai anyi munafiki....,
Kai tab gaskiya na lura ba a cikin hayyacin ki kike ba kin dawo wacce ta fi karfin ki yar tasha zo ki huce....
fita tayi har taje soro ta leƙo tace
"Inka isa ka biyoni...,
banza yayi mata dariya dinana yayi yace
"Anayi muna jin dadi a hayye rasss...chasss warrrr Sai kawulliya namu na gargajiya
Kawu ne ya magantu yace
"Dinana ina jin ka ƙarasa sai akai yaya daman ni na dade da sanin cewa mutanan nan da falmata ke haɗawa abin da suke zunubin har dani....,
Au kawu baka da labari tab makaranta nakoma ta addinin Islama kaga muwadda maliki a koya mana sai wannan abin ko uhmm na manta nafi dai riƙe muwadda maliki din nan yauwa Riyadursahali magajiya yama ƙarashen....sa?
kaga kar ka sake ka sani a cikin wannan shirmen naku gabaki ɗaya ba daidai ka faɗa ba ka tubarwa Ubangiji.....
Hhhh chass wayyo dad'i kaga ulama'u magada annabawa KAWU ka fahimta ko inyi maka bayani dala dala
tashi KAWU yayi ya shiga daki ba tare da yace ƙala ba sosai rabi ke dariya yana cewa ulama'u masu aiki domin Allah wa'azi bako sisi kwafaɗawa mutum Allah yace annabi yace......
abin dariya ya bawa magajiya ta taya shi suna ciwa DINANA mutunci.....
kuwai wallahi me iya muku sai Allah baku da gwani wallahi Allah ya shirye ku UWANI ta faɗa tana tur da halin su
UWANI dadina dake kwai faɗar TRUE wallahi yanzu dai tela musu suji yadda ake zaman duniya RABI ya faɗa sanin hali ba mutunci ne da su ba yanzu zasu haɗe mata kai su dawo kanta sai ta ja baƙin'ta ta tsuƙe tana yi musu fatan shiriya in suna da rabooo...
✷✷✷✷✷✷✷✷SOKOTO BIRNIN SHEHU
Nabeela nabeela wani kallon hadarin kaji tayi mai tace
"Na'am ina jinka....?,
Kai ya gyaɗa yace
"Na lura kullum rashin mutuncin ki ɗaga gaba yake nagane abinda kike nufi saidai har abada baza ki samu ba .....,
dariya tayi har da tafi tace
"Ai Allah kalle ni da kyau haladu nafi karfin ka na huce a jikin ka da ka amshi kuɗin ka da kar ka amsa duk uwar....su ɗaya ka saka a ranka kamar na auri ASIF ne na gama....,
Haka kika ce....?
Juyawa tayi ta fara tafiya komai ta tuna sai ta tsaya tace
"Wannan shine kashe di na karshe da zan maka haladu kar ka sake in ƙara ganin wa yannan matattun ƙafafuwan naka sun zo kofar gidan mu in ba haka ba wallahi sai na saka yan iskan garin nan sunyi gunduwa gunduwa da naman ka ka kalle'ni celebrity dani kace ni zaka aura ni wallahi bansan hau din da ta hauni ba har na'amin ce da ka turo gidan mu.......,
gyara zaman hularsa yayi ya tsura mata ido har ta gama maganar'ta ta shiga cikin gida tana wata iriyar tafiya ajiyar zuciya ya sauke ya tafi yana mamakin nabeela
Cikin gida kuwa inno ce tsaye a tsakar gida sai kai kawo take nabeela na shigowa tace
"Ta gaban mota ya kukai kin kora mai bayani da manyan baƙi ko yaya....?,
cire maya'fin'ta tayi tace
"Inno wallahi sai mun haɗa da bokaye ayi mana farraƙu dashi har fa yanzu yana kan bakan'sa kinga kuwa a kwai gagarumar matsala...inno na aure ASIF wallahi bake ba har kaka sai ta huta kuɗine ba iya ka lokacin da naje Abuja fa inno kinga company sa .....hmmmm abin ba a magana makkan nan da take tsada inno ki ɗauka kinje'ta kin dawo.....,
Dan Allah nabeela.....?
Hmmm babban fa mutum ne kedai kawai ki tayani da addu'a kwanaki da naje Abuja ban ganshi ba wallahi
To Allah ya temaka
Bazai taɓa temaƙon ku ba akan muguwar niyar'ku wallahi sha'awa kin ban mamaki me maƙon ki ɗorata akan turɓa ta gari kece me ƙara ingiza ta gurin aikata ɓarna ita ba duniyar nan dakike gani a yadda ka ɗauke ka haka zata ɗauke ki in ta tashi juyi dake ta faɗo dake a tsakiyar rana.....
haɗa rai tayi nabeela kuwa tashi tayi ta bar gurin tana ƙunƙuniiii.....
Sha'awa magana fa nake kinyi shiru
ɗagowa tayi kamar wanda wani abu ya tsikare'ta tace
"Uhmm malam me kace ban jikaba saboda abin duniya ya isheni.....?,
ƙwafa yayi dajin wannan rainin hankali irin na sha'awa ya fita daga cikin gidan yana yi musu fatan shiriya Allah ya ganar dasu gaskiya da basu ikon bin'ta..........
OSOKORO ABUJA
Gaskiya A'isha abin da kikai baki daidai ba wannan fa zunubi ne babba da auranki ki dinga soyayya da wani a waje har kuna kokarin kulla aure in hankali ya gushe tunani be kamata nima nawa ya gushe ba in bi son zuciyar ki mata wane ne suke neman damar ki basu samu ba mata nawa suke bin mijin ki...be basu dama ba saboda yardar dayayi miki amma gashi Saboda son abin duniya zaki watsa mai ƙasa a ido mene ASIF be miki a rayuwa ba wallahi kin ban mamaki inza ki fita daga harkar Alhaji manneru ki fita dan wallahi kai ki zai yi ya baro ki amfani yake dake a lokacin da kika gamemai aiki keda banza duk ɗaya......
Hafsah kin gama nace kin gama
tashi tayi tsaye ta ɗaga hannun tace
"Yi min shiru munafuka ban saka da ke ba inhar ba zaku faɗa mata gaskiya ba be kamata Ku zugata ba wallahi tunda nake banta ɓa ganin wannan tashin hankali ba ba mamaki bokan'sa ne ya sa shi ya nemi matar Aure ko da yake Alhaji shi kansa shu'umin kansa ne kina kuwa da hankali ki bincika ME YA SAKA ASIF YA KAKA ALHAJI MANNIRU SAI DA WANNAN GWAMNATIN TAZO TA FITAR DA SHI.....,
tana kaiwa nan ta dauki jakar ta kamar kububuwa ta fita a fusace
gyara zama Aisha tayi tace
"Wallahi bestie sai yau na gane halin Hafsah ashe maƙiyata ce ban sani ba tana yi min baƙin ciki dan nabar ASIF saime...shidin autan maza ne matan da suke son'sa Suma dan basu san waye shi bane da sun sani wallahi baza su so auran'sa ba
A'a a'a bestie banda sharri ko munan fa muna sha'awar ki wallahi ba zaki gane mene rayuwar zawarciii sai kin fito zaki fahimta kingani ina da kudi dai-dai musali amma abin tashin hankalin shine kowa da irin kallon da zai maka wani ma tahin wulakanci zai maka musamman wannan mazan namu da muke aiki tare abin da hafsa take faɗa miki gaskiya ne.... wallahi hajiya ni'ima zata iyayin komai dan ganin ta sulwantar miki da rayuwa kin san kuwa bata barin kowa ya raɓi mijin'ta ko ni da nake matemakiyar'sa Hmmm kallon hadarin kaji take min
Wallahi ta dade batayi ba kinga nifa ba gudu ba ja da baya suka tafa da wata ta kusa da ita
Allah ya ganar dake wace rufaida shedaniyar mace ce in baki sani ba yau ki sani yanzu haka ba mamaki kan'ta take yiwa wannan faɗan daga ta kautar dake saidai kiji ana buɗa....rayuwar yanzu ba yadda kowa mugun kansa ne ƙalilan ne