Showing 3001 words to 6000 words out of 29438 words
tamkar ta fasa kirjinsa ta fito zama yayi a bakin gado ya fara cire safar'sa sannan ya cire agogon'sa a takaice dai daga shi sai boxer ya zauna ya dafa kansa ya zura hannunsa cikin sumar kan'sa yana al'ajabi ko a mafarki aka ce mai Aysha zata aikata haka zai musa wayar sa ce tayi ringing sai a Lokacin ya tuna da yabar ta cikin aljihun wandon'sa janyo shi yayi ya ciro'ta muzabfar ne ke kira ɗaugawa yayi ya saita nutsuwar'sa domin baya son ya fahimci halin da yake cikin yace
"wa'alaikassalam munatanan Germany.....,
dariya muzamfar yayi yace
"Barka da wannan lokaci mutanan Arewa....,
Kwanciya Asif yayi yace
"bakai karya ba wannan shine a salina...,
dariya muzamfar yayi yace
"ba shiri ka baro chaina da fatan dai an ga wa'yanda sukai wannan abun....?,
ajiyar zuciya ya sauke yace
"Har yanzu bincike nake....,
To Allah ya saka a gano ga yarka ta takura sai taji Muryar uncle sai dai uncle din'nata be fiye tunawa da ita ba ya bugo yaji lafiyar ta ba kullum busy work ya faɗa yana dariyar tsokana.....
wallahi muzamfar ka kiyaye ni bani ita salon kasa ta dena ganin girmana kasan yanayin aikin mu da naka ba ɗaya ba kai dan kasuwane nifa
zaɓin ka kabi ya faɗa yana miƙawa mufida wayar amsa tayi cikin maganar yara tace
"uncle good night....,
beautiful princess ya karatu
dariya tayi ta kalli daddy ta tace
"kullum sai nayi kuka bana son school....,
zaro ido Asif yayi kamar tana gabansa yace
"Maza tuba kinyi babban saƙo bakya so ki zama doctor.....?,
uncle ina so mana
to maza ki dinga karatu in bakya yi na dena kulaki uncle yayi fushi da ke
kukan shagwaɓa ta saka mai tace "Please uncle kai hakuri na dena.....,
duk kan wata damuwar'sa ne matar yayi ya rasa ashe daman ya'ya rahama ne lumshe idanunsa yayi a yanzu ya ji sha'awar daman tare yake da yaran'sa sun zagaye shi suna shirme yana biye musu har muzabfar ya ƙarbi wayar be sani ba sai da ya kira sunan sa maxaiwa yayi yace
"me i saka ka karɓa muna hira....?,
cikin takaicin halin dan uwan nasa yana cikin damuwa ba zai iya faɗamai ba suyi maganar matsalar yace
"Miƙo min tayi tace ka kashe wayar baka magana....,
shiru Asif yayi muzabfar ya ci gaba da cewa Wallahi tu da na kiraka naji Muryar ka nasan ba gajiya bace Asif Kai wa kanka adalci mana inna rantsai ko kaffara bazan ba wannan damuwar da kake ciki Aysha ce sanadin shigar ka ka ƙara aure ba duka mata suka taru suka zama ɗaya ba mata nawa ne suke binka suna so ita ta samu tana wasarere da damarta uwa uba rashin haihuwa amma kullum kana jibgawa kanka aiki dan ya rage maka damuwa alhalin ba shine mafita ba ina jiye maka ranar da za awa gari A'isha ta saka maka ciwon zuciya kuma wallahi guduwa zatayi ta barka dan batayi kama da macan da za ta dauki responsible ɗin ka ba tun huri kafin kane mowa Kan ka mafita
Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Ina jin ka ubana ci gaba....,
cikin dariya muxabfar yake cewa"ai na gama ƙi faɗi.....,
Kashe wayar'sa yayi ganin muzabfar zai cika mai kunne shiga toilet yayi yayi wanka tare da ɗauro alwala da yake an fara kiran sallar magariba cikin sauri ya xura jallabiya be san lokaci yayi haka ba feshe jikinsa yayi da turare ya tsane kansa ya dauki carbi ya janyo kofar sa ya fito ganoj bedroom ɗin aysha yayi a buɗe kai da kai yayi ya fita abin mamaki motar ta bata nan kenan yaji tayi a zuciyarsa yace
kyama dawo da kafafunki ya fita daga gidan masallaci ya jufa kamar ance ya juyi da sauri mutumin dake binsa ya laɓe tasbihi ya ci gaba dayi har ya isa masallaci zama yayi kafin a kira sallahi yana salati to har aka kira sallar Isha be fito ba sai bayan an idar yayi shafa'i da huturi ya fito again har yanzu binsa ake waya ya ɗauko ya fara danne danne ya tura saƙo ya zura a aljihu ya ci gaba da tafiya wata farar mota ce ta dallemai ido saka hannu yayi ya tare saboda hasken yana neman ya kashe mai ido ba zato ba tsammani yaji harbi.....
Cikin ikon Allah be samesa ba fitowa sukai duk fuskokin su a rufe abin da basu sani ba abuja ba kamar local unguwa ce tuni ko wanne security ya fito da sauri suka shiga Mota suka fita a guje Allah ya temake ku ba a kama suba Asif kuwa ɓoyayi da yake ya yi wa jami'an tsaro waya sun tare ko wanne get ba za su iya fita ba shiga cikin gida yayi kai tsaye bedroom ɗin'sa ya shiga ya dafa kansa ya zauna ba wannan ne karon farko da aka fara akai mai hari ba amma wannan yafi muni Allah ne yayi da kwanan'sa a gaba da tuni yanzu wata maganar ake matsantawar abokanan gaba tana ƙara tsanani ya zama me mai dole ya bar wannan kujera yana son aiwatar da gaskiya amma hakan baza ta yuhuba.... ɗaukan wayar'sa yayi ya soma lalubo contact din abba Saboda tashin hankali kasa ganinsa yayi abin mamaki duk wannan karar harbin da security ɗin gidansa da suka ji ba wanda ya fito tamkar da haɗin baƙin su zamansa a cikin gidan matsala ne dan haka ya ajiye wayar akwatin sa ya dauko ya ɗauki duk wani abu me mahimmanci da briefcase ɗinsa ya fita ta cikin kofar sirri sai gashi a waje wata mota ya shiga ya tada ita...a guje ya fata ba tare da mutanan gidan sun sani ba
kan titi ya miƙa bazai je hotel saboda duk kan wani motsinsa akan idon matane yake bazai iya basadar da ba za a iya ganesa ba dafa kansa yayi tunani yayi wa kwakwalwar'sa yawa a she daman taƙa wani matsayi kamar ka taka haɗarin rayuwar ka ne baka da kwanciyar hankali kowa ya matsoka ga ni kake cutar da kai zai yi ji yake daman ya dawo da agogo baya rayuwar sa ta da me cike da aminci....ba wanda ya damu da shi zai shiga cikin mutane ayi wasa da dare amma yanzu fa bazai iya ba...
bashi da tsayayyan gidan kwana ko mai nisan dare haka zai fito ya koma wani gidan ya kwana bashi da hutu na kansa wani lokacin ma baccin baya yuhuwa meeting ɗin na dare ne dole ya fito.....
*Washegari*
da kyar ta iya tashi zaune shima hakan da dabara ta tashi bata san rana ce ko dare ba ga gurin shuro baka iya jin komai kamar ba gurin ba wanda yake shiga in ansa Mutum a saka shine ba futowa haka ta raya a zuciyar ta
ba abinci ba ruwa a yanzu zuciyar'ta ta bushe kallon ko wanne dan adam take mara imani
*Kano unguwar kofar mata*
Alan guburo lafiya naga kana ta shiri yawa me barin ƙasar....uwani ta tambaye shi
Gyara zaman malin malin ɗin'sa yayi yace
"jiya na manta ban faɗa miki ba munyi shawara ni da manjagara da mahaifin dinana da na rabi za mu tafi Abuja ko za mu sami bilin wa'yannan yaran kinga yau kwanan su uku ba wani labari gwara mu bi sahun'su....,
taya akai kuka san a Abuja aka ajiye su
Malam hamisu ne ya faɗamin domin ya je headquarter su tanan an tabbatar mai basa nan saidai yaje Abuja
To Allah ya kai ku lafiya amma Ni ina jeye muku arba da wayan nan mutanan kar fa su nan naɗe ku su tura cikin cel
Ashsha kaji mugun baki
jan bakinta tayi ta tsuke tana yi mai fatan dawowa lafiya ba tare da an cire mai kafa ba domin ita ta tsorata da ganin mutanan nan ko ɗigon rahama babu a fuskarsu yanzu tasan duk wannan jikin na magajiya ya zube babu shi domin tasan sace shi za suyi tas to ga yan ƙari nan yan zuwa shishshigi su kuma Allah ya fitar da su....
gama shirin'sa yayi tas ya gama yace
"Bani dubu goma a cikin kuɗin cinikin ki....,
ba musu ta ɗaga kwanon da take jefa kuɗin cinikin ta dauko mai kirgawa yayi ya tura a aljihu ya dauki yar jakar'sa yace
"To mu mu tafi zaki iya ganin na dade domin dole inga Ak sardauna na bashi hakuri ya sakar min yarana.....,
abin dariya ya bata tace
"Allah shugaban ƙasa ganin irin mutanan nan bafa ganin limamin unguwar ku bane....,
be tsaya jinta ba ya saɓa jakarsa ya fita cikin addu'a a kofar gida yaga mahaifin rabi da na dinana sai manjagara saboda yayi zaman Abuja kai tsaye waha mota sukai a ka kai su tashar da zasu hau motar Abuja suka hau aka fara tafiya ƙara maƙale jakar'sa kahu yayi saboda ɓacin rana
wata uwar tusa na kusa da shi ya yi da sauri kahu ya tushe hancinsa yace
"Haba bawan Allah me maƙon kace a tsaya za kai uzuri wane be san uzuri ba sai kai mana tusa a mota salon cikin mu ya ɓaci....✍️
*GIDAN MAGAJI YA*
masu tambayar complete kuyi hakuri typing dinsa nake har yanzu
*EPISODE 25-26.....*
Wannan ai bura'ubanci ne in banda kai dan kwal'ubane taya zaka dinga cika cikin ka dabubuwa kana cutar mu.....
gyara zama wannan taton mutumin yayi yana aikawa da kahu harara kara karkace wa yayi ya saki wata tusar da sauri kawo yace
"Wallahi malam hamisu sai yau na fahimci karin maganar da hausawa suke yi na cewa tafiya yankin azaba a she wannan abubuwan sune azabar tafiya wallahi yanzu daje likita ya dubani ba mamaki ya ce min na kamu da cutar da ke damin wannan jibgegen mutumin domin fa cuta ya ke fitar wa.......,
shiru malam hamisu yayi domin bazai iya magana ba saboda zamansa da wannan mutumi cikinsa ta ɓaci gashi yana tsoron magana kar ya naɗamai duka tunda gashi suffar karfi......ya tushe hancinsa
maltina wannan mutumin ya ɗauko da biredi yana ci ga wasu kayan ciye ciyen da sauri kahu ya kwace yace
"Wallahi har mu sauka ko gutsure ba zaka ƙara ci ba al'ummar motar nan kuyi magana mana kuma fa yana cutar da ku bani kaɗai ba wannan wane irin mutum ne tun da muka shigo motar nan take zubawa cikin sa abubuwa.....,
haɗa baki sukai suna cewa gaskiya fa wallahi
Wartar abinsa yayi ya nuna kahu da danyatsai yace
"Kai tsohu ka fita a idona na rufe ko wallahi in kakkaryaka in watsaka ta cikin window din motar nan cikin ka ko nawa ka ƙara wata magana kaga kin ban rugurugu da kashin ka.....,
komawa baya kahu yayi ya rufawa kan'sa a siri domin bisa alamu tsab zai iya aikata mai hakan wallahi....
Sai karfe biyu ɗaya da rabi suka isa birnin tarayya Abuja bayan sun sha huya a cikin motar nan ban da manjagara da shi kamar ma warin maye ya sashi kai shayeshaye mugun ciwo Allah ka kare zuri'ar mu da shi.........
gyara zaman rigar'sa yayi ya fara tsayar abin hawa cikin sa'a suka samu suka kwatanta mai in da za akai su juyowa yayi ya kalle su yace
"amma a dan nesa da gurin zan ajiye ku dan wallahi bazan ƙarasa gunnan ba....,
Kahu ne yayi carab yace
"Haba dan nan ka gan mu nan gaɓoɓin jikin mu yawa an kunce mana ita wallahi ka temaka kai mu....,
Baba wallahi bazan ƙarasa yellow gidan nan ba ato kai ai ni ko a mafarki bana fatan in ganni a jikin gidan infa sukai huru huru suka ga me laifi bindiga za su dauko wallahi sai dai kaga kwakwalwar mutum tana yawo a ƙasa yawa tarwaɗa
wani mugun yahu su kahu suka haɗiye manjagara ya saka kuka yace
"to Allah i saka mu gani su ba su kashe su ba.....,
a fusace kahu ta buge mai baki yace
"tufar da mugun yahu falmata kaɗai ta rage min insha Allahu sai na dauki ya'yanta ai wahala bata kisa inhar da kwana a gaba......,
daga nesa ya tsaya suka sauka kahu ha bada kuɗi tafiya suka fara har suka isa get ɗin bisimilla kahu yayi ya fara bugawa yana ɗora hannunsa aka buɗe ja da baya yayi ganin wani katon mutum jikinsa duk a murɗa ga wata bindiga ta kusan rabin sa kallon su yayi sama da kasa cikin rawar murya kahu ya zunguru malam hamisu yace
"Tun da muka tawo ni nake magana dan haka kai da mahaifin Rabiu a yanzu ku za kuyi....,
Mahaifin rabi yace
"Dan Allah kai hakuri kayi...,
ganin kamar suna ce ce kuce ya fara rufe kofar da sauri kahu yace
"Hallaɓai mun zo ganin yaran mune da aka kama a kano Kai wa Allah kai wa annabi ka barmu mu shiga...,
kati ya miƙa musu ya basu hanya zare ido suka fara ganin kamar gurin ma'akata suna hada hada da sauri kahu yace "ku zo mu shiga nan binsa sukai me tsaron kofar ya kalla yace
"barka da aiki....,kallonsa yayi sama da ƙasa yace
"yauwa...,
dan Allah alfarma muke ne ma ka temaka ka kai mu inda za mu ga yaran mu da aka kama a garin Kano maza biyu mace ɗaya ko za ka kai mu gunsu...?,
Kallonsu yayi yace bani da alhakin nuna maka su ka tafi wani gurin kai kahu ya gyaɗa yace
"mun gode ku zo mu tafi....,
binsa sukai gaban wani haɗaddan wani gini suka tsaya iya tsaruwa ya tsaru kamar a ƙasar waje mutum suna kokarin tsallaka wani karfi wata tsawa wani jami'i yayi musu yace
"Ina zaku ku suwa ye maza ku dawo baya kunsan nan gurin gurin waye.....?,
da sauri kahu ya dawi baya suka isa gunsa tsugunawa kahu yayi domin ya gaji ga yunwa ga kumburin ciki yace
"dan Allah yallaɓai ka temaka mana yaran da aka kama a garin kano su muka zo gani.....,
wani kallo yayi wa kahu ya ɗauke kai yace
"Nan an faɗa maka kamar gidan yari ne ko ance maka ofishin yan sanda ne....baza ka iya ganin su ba tun huri ina maku shawara kafin kuma a jefa ku cikin su ku tafi in har basu da laifi aka gama bincike za ka gannu sun dawo.....,
Kuka kahu ya saka dai-dai fitowar Asif zai yi sallah lokacin salla yayi tare da habib da jabir suna magana da sauri manjagara yace
"Lah hantsi zarto....,
tun daga nesa daman sun gansu nunawa sukai kamar ba dasu suke ba maganar da suke kenan jabir ya nuna mai dattijon da yaƙe ƙasa yake kuka kahun falmata ne duk kan wani tarihin rayuwar su ba wanda ba su sani ba ba ƙaramin bincike suke ba tausayinsa ne ya kama Asif amma sai ya dauke kai ya ci gaba da tafiya cikin kuka kahu yace
"dan Allah yallaɓai ka nuna min wanda yake da alhakin kama su da kuma inda wanda akaiwa kidnapping ɗin matar tasa wallahi zan je har gida na basu hakuri yarinyar nan ita kaɗai ta rage min ita da ɗan uwanta yanzu haka ɗan uwanta ba lafiya yana kwance sai dai a ɗaga a kwantar bamu da yan uwa duk sun ƙare a faɗan boko haram mahaifiyarta ma neman ta mu muka rasa wata kila sun bawa karnukan farautar su sun cinye namanta kai wa Allah da manzon sa ka temake Ni.........
ganin Asif ya fito tare da su sir jabir da sauri ya sara musu tare da koma inda yake tsaro da sauran yan uwansa tunda ya faɗa mai be ji ba ya zai mai.....
Liƙen su manjagara yake yace
"Kahu kamar fa su hantsi nake gani...,
buge hannnunsa yayi da yasa a kafaɗarsa yace
"eh su ka gani saboda haka ta faɗa maka kwayar da kasha mutanan da suke yan daba ina su ina aiki anan.....,
wallahi kahu su na gani mahaifin rabi ne yace
"to jeka kai musu magana su sake su tunda abokanan harkar kune ai malam bulama ba a ƙin ta mutum yaje....,
wani yahu ya haɗiye ganin kallon da Asif yayi mai ya dauke kan'sa kiran salla akai tashi sukai suka fara neman gurin alwala suyi salla samin ruwa sukai suka ɗauro alwala a kofar masallaci kahu ya ajiye jakar'sa ganin wani ma'aikaci yayi mai alama da ya ɗauki abarsa ya saka
zuciyarsa kuwa ce wa yake da alama wannan gurin kurame sunyi yawa ba magana sai dai nuni ya shiga Masallaci domin har su malam hamisu sun shiga tsayuwa yayi kamar ance ya ɗago ya juyo yaga wannan dattijon a bayansa shi yana sahun gaba kusa da liman tare da su jabir.....
tada salla akai bayan an idar kahu ya dade yana kaiwa Allah kukansa kusan tare suka ɗago daga sujjada liman yayi salla kowa ya watsai tashi Asif yayi bayan ya gama lazumi kallon ida kahu yake yayi ya haɗa kai da gwuiwa su malam hamisu sunza gaur suna bashi hakuri....
kowanne ka dubi fuskarsa yana cikin mahuyacin hali Allah sarki iyaye Allah ka raya mu da su ya Ubangiji ka farantawa iyayen wa yanda iyayensu suka mutu Allah ya jikansu ya saka aljanna makomarsu wannan ita soyayya ta ɗa da mahaifi amma me i saka shi nasa iyayen basu damu da shi ba ko dan yana dan fari ne suke mai alkunya suna nuna kamar basu damu da shi ba hajiya ce rayuwar sa komai ita tayi mai har ya girma tafiya ya fara ya kalli jabir yace
"zuwa dare ka saki yaran nan tunda munyi bincike basu da hannu aciki amma ka yi wa su baba magana su zauna su tafi da su sannan ka kawi su office ɗina ina son ganin su gaba ki ɗayan su har na tsaran....,
Cikin girmamawa yace"to sir suka tafi da Habib jabir ya tsaya gurin sauran ma'aikatan suna tattaunawa turo wani jami'i yayi ya tafi da su baba aka basu gurin zama badai wanda ya kara ce musu wani abu suna zaune suna jiran ikon Allah
Jabir da wani suka huce su dakin da aka kulle su dinana suka fara buɗewa suna zaune sun jigum jigum ba abinci ba ruwa yau kwana uku kenan jabir yace
"Ku fito....,
Jikinsu har rawa yake suka fito ku je da su office director okay sir dakin da magajiya take ya buɗe ina bata san an buɗe ba tana kwance sai numfar fashi take Monica monica da sauri wacce aka kira tazo tace
"Gani sir....,
Cikin tausayawa yake kallon magajiya tuni ya tuno da alkairin da tayi musu yace
"Kamata ki kai ta office ɗin director...,
to tace ta fito da magajiya cikin muhuyacin hali tana ƙarasowa kahu ya tashi da