Showing 9001 words to 12000 words out of 29438 words

Chapter 4 - GIDAN MAGAJI YA book 2 HAUSA NOVEL

25 Nov 2024

3812

number 09061890481 yan nijar za ku iya turo da katin 300fcfah

Yanzu wasan ya fara ba a fara ganin komai ba
*GIDAN MAGAJIYA*

*EPISODE 29-30*

*Book 2*


Wayyo Allah gadon bayana na shiga uku da sauri kowa ya fito ban da hajiya jamila da ta leƙe ta sama taja kwafa tace kaɗan kuka fara gani ni daman na dade da dawowa daga rakiyar wannan tsohuwar...

Cikin mamaki umma ke tambayar izzatu hararar umma tayi ta miƙe tana karkaɗe rigarta dafe da kugu tace

"ta Allah ba taki ba kinga na miƙe ba mamaki ke kika laɓe kika bugan sanda....,

umma mace ce me hakuri dan haka ko a fuska bata nuna taji me izzatu tace ba ta juya zata tafi hajiya ta fito tace


"To rasa kunya ina jin irin rashin arzikin da kike wa umman yaya ke wai izzatu wacce irin macece ai Asma'u dama da kika tarar da ita a kwance ki daddage ki dauki tsabga ki ruɗa mata jiki da duka da wallahi ko kallon banza aka ce tayi miki ba zatayi ba ki ruɗawa yar iska ba yadda zata kasa kwanciya ta tsawon sati biyu ba yawo.....,

sosai zancen hajiya ya bawa mamy dariya da take gefe ita kuwa umma bata tsaya jin wani zance ba tayi gaba inde hajiya ce yanzu zata iya dawowa kanta ba abin dad'i bane ta ci mutuncin dan uwanka kayi murna anjima naka zata ci salati hajiya ta saki ta kalli mamy tace

"Hamziya ina magana kina dariya saboda ga yar iska ko.....,

girgiza kai tayi tace

"Allah ya hucu zuciyar ki hajiya....,

Au da keki Ka kunna min huta a zuciyar tawa shine yan zu kike so tayi sanyi anya kuwa hamziya kina so kika annabi salim alim ba tare da ankwashe miki fatar baya ba Ubangiji yayi miki azaba


Sosai drama hajiya take bawa faisak dariya dan haka ba abarsa a baya ba ya tuntsure da dariya ganin hajiya ta jiyo dariyar'sa ya koma cikin daki kar faɗan ya shafe shi hajiya jamila ta maida hankali kan fadan nasu bata san hajiya ta juyo ba sai ji tayi tace

"Muna fuka ƙaremin kallo to wallahi Ubangiji yace hutar munafukai daban take kina sama yawa jemage da fuska a jeme kina munafur wallahi har na gano an dilmiya wannan fuskar'taki a dalma ta kwakkwaɓo in banda tsabar kin kware a munafurci har na juyi baki sani ba kina dariya rai yayi fari tas anci mutuncin faccalolin'ki me zubin kafurawan farko shi yasa ka Asma'u ke birgeni wallahi ba ruwanta da wannan baƙin halin kai Asma'u yar aljanna ce...,

juyawa Hajiya jamila tayi ba tare da tace ƙala ba faisal ta tarar a floor yana cin abinci a tsawaya tayi akansa tace


"Kaga masifar da kaja min ko har ubanka ya dawo ba zata dena wannan maganar ba kai Allah ya kashe hajiya mu huta.....,


tare da ke

da sauri ta ɗago tace

"Faisal niii mahaifiyar ka...,

Mom ai ita ma mahaifiyar wasu ce yanzu in Mala'iku suka amsa miki addu'ar ki har dake zasu haɗa wallahi dan naji wani wa'azi ɗazu a she akanki zai aiki ban'sani ba duk fatan da kaiwa ɗan uwanka wala na alkairi ko akasin haka akwai mala'ikan da zaice Allah ya yayi maka misali in kace Allah ya jikan wane sai yace kai ma Allah ya jikan'ka

Da hallacan rufan baki shashasha kawai har wani karatun addini ka iya in banda shashanci Hajiya tana mutuwa gado mahaifinka zai ci me tsoka mu ware kan mu ban masifar tsohuwar nan ta ƙi bari kowa ya ware ya zauna ai bata ƙarasa ba hajiya ta shigo cikin ɗakin tace


"Ya ware ubanki....jamila wallahi kikiyaye'ni tab Allah ya ragewa aya zaƙin ta jiya ba yau bace da ke bama zaki iya yimin wannan maganar ba ko da abayan idona ne ban gurce miki baki ba in saka Mustapha ya auro wata ya sake ki to daman mene amfanin auran ki ɗa ɗaya kwal kika haifa shima gashi nan ga shina ba tsiya ba arzƙi....,

hajiya cikin sauri ta tari numfashin'ta tace

"Rufemin baki bana son dogon turanci...,

ƙasa tayi da kanta zuciyar'ta kamar ta fasa kirjin'ta ta fito to wallahi tun huri ki canza taku domin wannan na dade da gano shi har ina magana da yake ba tsohuwar ki bace ki tafi ki barni


Dan girman Allah hajiya ki hakuri wallahi Ni nayi dariya ba ita ba faɗa take min shine na koma Please............

Faisal ya faɗa yana haɗa hannuwansa alamar ban haƙuri

wallahi taci arzikin ka da yau kwanan gidan alhaji Nuhu za tayi aje can sai kin gyara hali kya dawo ta faɗa tana kokarin fita daga ɗakin zama Hajiya jamila tayi zuciyar'ta na mata suya a kullum kashe kuɗi take akan matar nan amma har yanzu bata tsira da mutuncin'ta ba

Mom Dan Allah Kar ki damu da halin Hajiya

harara ta watsai mai tace

"Wallahi duk kai ka jamin wai yaushe zaka shiryu ne ko kishi baka yi jibi Ayman Akram muzabfar uwa uba Asif ha kamis amma kai har yau jiya i yau sai iskanci ka saka gaba ka ɗauki yan mata kuje club anya kuwa Faisal gashi ka ƙi bani haɗin kai da tuni mun kawar da Asif.....,

tashi yayi yace

"Mom kiyi min addu'a nima bajin dad'i nake ba wallahi amma maganar nan dan Allah ki barta haba mom abin da yaya zai bawa umman yaya shi ke baki ya bawa kowa baya warewa ko cin zarafin mu wallahi be yarda wani yayi ba matar sa kuma akwai abin da ya hada mu itama tarata nake ina gab da fasa kwai danni nasan wace ita tayi haka ne dan nayi zuciya na bar gidan to gobe zan koma.... Abuja zanbi jirgin yamma....,

da sauri ta ɗago tace

"Dan Allah faisal bani labari me zaka tona....,

Kinga tafiya ta in lokaci yayi za ki ji.....

Kiransa ta shiga yi amma ina tafiya yayi ya barta cikin takaici....

*_* *_* _*_*......osokoro Abuja.....

*_* *_* _*_*......osokoro Abuja.....


Aysha inhar kika kashe auranki wallahi ba abin da bazan miki ba babban burina yau in baƙanta zuciyar Asif kamar yadda ya baƙanta min Alhaji munner sani jos ya faɗa


cire glass ɗin ta tayi ta ɗora akan coffe table ɗin tace


"Alhaji ke nan badan Allah kake sona ba dan ka kuntatawa Asif....rai zaka aure ni....,

ajiyar zuciya ya sauke yace

"Aysha kin sani cewa ina son ki faɗama ɓata baki ne in har kikau abin da nace to wallahi zaki shiga jerun manyan mata me yake dashi me yake baki mace kamar ke tana hawa ƙaramar mota wacce kuɗin'ta befi na miliyan talatin ba.....,

Kanta ne ya ƙara girma tace

"Allah Alhaji wato dai nafi karfin wannan....?,

baƙin ciki yake miki lokacin da nasaka aka baki ministan ilimi ai be goyi bayan ki ba saboda baya so ki ci gaba


wallahi wannan maganar taka gaskiya ne amma ka bani lokaci in ƙara shirye shiryen da nake dan sai na tsiyata shi tas tukunna zance ya bani takarda ta yanzu ma haka bana gida jiya ya mare ni

da sauri Alhaji ya ɗago yace

"Mari kamar ke....

hmmm kai ma ka faɗa wallahi marina yayi

tab ki ajiye duk wani hulakanci da yayi miki akwai ranar ramawa yanzu boom din da nake na haɗa mai shugaban ƙasa ya cire shi a kan matsayin'sa muga dame kuma zai yi kafafa ya faɗa yana buɗe wata a ƙwati

Zaro ido aysha tayi tace

"Alhaji wannan dalar fa....,

ta kice
ya faɗa yana tura mata rufewa tayi tana wani irin farin ciki burin'ta kuɗi kuma ta samu tace

"Nagode sosai alhajina...,

bana son godiya kinsan mu yan siyasa kudin nan abanza muke samu ya fada yana gyara babbar riga yace

"Sai kin gama yanke shawara...sai ki kirani...,

Ajiyar zuciya ta sauke tace

"Babbar matsala'ta matar ka.....,

dariya yayi yace

"Hajiya ni'ima ba ruwanta dake balle nihila ko Hanifah....,

Allah ya sa ta faɗa tana gyara mayafinta a kafaɗa glass ɗinta ta dauka haɗe da jakar da ya bata ta fita ta baya shi ya fita ta gaba.......

*********

Joseph, until you come back to the truth, hurry up

Dariya Joseph yayi yace

"By the way, I was also quick to come back, she said, is too mahaukasii she gave me trouble until you took a photo and she saw that I was stopping her from walking....,

cikin mamaki Asif ya gyara zaman'sa akan kujerar da yake kashe tv yayi yace

"who is mahaukaci among them but this woman did not say your name like that....,

Domin yasan ita kaɗai zata iya aikata haka

Cikin tabbatar'wa Joseph yace

Yes, her name is crazy

Kai Asif ya jinjina yace

"You can go, but not her name, not her name....Falmata....,

so this old man said to thank you

Okay kawai Asif yace ya kunna labaransa ya ci gaba da gani amma abaɗini tunanin ne yayi mai yawa waya ya ɗauka ya kashe kallon ya nemo number umma har ta tsinke ba a ɗaga ba ƙara kira tayayi sai a wannan karon ta ɗaga ajiyar zuciya ya sauke yace

"Assalamu alaiki umma Barka da dare..,

wa'alaikassalam barka dai

limahe ido yayi ji yayi duk wata damuwarsa ta yaye jin muryar umman'sa da yayi yace

"ya kowa da kowa da fatan kuna lafiya Insha Allahu a cikin satin nan zan shigo aiki ne yayi min yawa...,

Kowa lafiya Allah ya kawo ka lafiya Allah ya temaka ya naka iyalin

Amin ya Allah Alhmdllh lafiya qalau ki cigaba da yimin addu'a kasar nan mara gaskiya ke tsira me gaskiya yana cikin wahala umma

Kullum cikin addu'a muke maka Allah ya tsare ka ya ƙare ka daga sharrin abokan gaba

Amin ya Allah
Sallama sukai ya kashe wayar kiran muzabfar ne ya shigo ban za yayi dashi domin sai ya sashi ciwon kai be dena kira ba har sai da ya gaji ya ɗauka yace

"Wai kai muzabfar naci bashin kane.....?,

Asif Ka ganni nan naka cin abinci photo yarinyar nan nake gani tana yi min murmushi Joseph ya dawo ne zai gane gidan gobe fa zani zaka rakani

Ba shiri ya kashe wayar zuciyarsa na tafasa wani irin gumi ne ya shiga yanko mai duk kuwa da AC da take aiki a floor ji yayi kamar an saka shi a huta to me ke damun sa ne daga wannan maganar ya juya lokaci ɗaya jin dafin maganar muzabfar yayi tamkar ɗigar dalma a kunnan sa zuciyar sa tamkar an zuba mata fetur an saka mata ashana an kunna...ta........✍️

Akwai cakwakiya fa kudai ku kasance dani a book 3 domin in warware muku ita an fara fa payment Ku hanzarta yi domin mallakar document zan yi sauri na gama tun da bakwa son paid group

*GIDAN MAGAJIYA"

EPISODE 31-32

Jefar da wayar yayi numfashin'sa na sama yana ƙasa da kyar ya dawo hayyacin'sa cije lips ɗin'sa yayi rasa me yake shirin faruwa da shine tashi yayi zaune ya ɗauki wayar'sa ya tashi bedroom ɗin'sa ya shiga kwanciya yayi a kan gado text message ne ya shigo mai amma sai yayi banza da shi can sai ga wani a jere har guda uku buɗe wayar yayi ya duba biyu na Aysha ne ɗaya na wata baƙuwar number ce zaɓar ya fara duba na aysha yayi buɗewa yayi kasa tantance anya kuwa idanuwan'sa gaskiya suke faɗa mai ko mai karantawa yayi a fili tamkar me koyar karatu ASIF tun kafin in kawo maka sammaci da kotu ka sakeni na gaji da auranka tunda har ka fara saka hannu ka dake ni wata ran duka za kai min wallahi Asif na gama auran

Da sauri ya shiga ɗayan message din tun huri kafin in tozarta a idon duniya ka sakeni ......... kafin ya ƙara karantawa yayi sauri a fita zuciyar sa na tsananin bugawa tabbas zai nuna mata ya cika dan halak ashe daman haka halin dan Adam yake ya janyo'ta inuwa tana kokarin kai shi rana ta ɓata mai suna cije lips ɗin'sa yayi ya ɗauki wayar hannunsa na rawa ya fara rubuta mata saki kamar haka

*NI ASIF KABIR SARDAUNA NA SAKI MATATA AYSHA SAKI UKU.... SAKAMAKON ITA TANE MA DA KANTA.....,*

ajiye wayar yayi bayan ya tura mata kasa kiran mahaifinsa yayi ya sheda mai dan haka ya kwanta zuciyarsa na yi mai ɗaci daga nan bacci ɓarawo ya salallaɓo yayi awan gaba da shi ba tare da ya shiryawa hakan ba

Washe gari da sassafe yayi booking ɗin jirgi saboda yana so ya je kano cikin Sa'a ya sami wanda zai tashi karfe ɗayan rana bayan ya gama ya ajiye wayar'sa ya ci gaba da aikin office a gida bayan ya gama misalin ƙarfe sha ɗaya ya shirya cikin ɗanyar shadda gezner ash colour an mai aiki monogram hula ya saka da agogo da suka dace da kalar kayan'sa sannan ya feshe jikinsa da turare me dadin kamshi da sanyaya zuciya ko breakfast be yi ba sai ruwan black tea da ya sha da wainar kwai sune har yanzu a cikin sa......

wayoyinsa ya dauka sai briefcase ɗinsa sannan ya saka baƙin glass fitowa yayi ya kulle part din nasa daman Joseph na jiransa yana fitowa buɗe mai mota yayi ya shiga jaridar da ya ajiye mai ya soma karantawa sosai aikin da wannan gwamnati keyi yake burge'sa shagala yayi da karatun jaridar har aka'zo Airport be sani ba sai da Joseph ya faɗamai ajiyewa yayi be jira Joseph ya buɗe mai ba ya buɗe da kansa ya fito rike mai briefcase dinsa yayi har suka isa reception


Abin ka da babban mutum nan nan suka dinga yi dashi kowa kokari yake ya faranta mai kafin ya lokacin hawa jirgi yayi guri suka bashi ya zauna tare da drinks kala kala da snacks wayar'sa ya ɗauko kamar ance ya shiga gurin text message dafa kansa yayi lokacin da ya ci karo da text message din da ya yiwa Aysha be shiga ba be ƙara resending ba ya goge......be kamata ace ya sake'ta yanzu ba kamata yayi ya ƙaro aure taga be damu da ita ba tun da anata tunanin gani take bazai iya rayuwa in ba ita ba


ci gaba yayi da operating wayar sa har lokaci ya cika tashi yayi be ci ko abu ɗaya da suka kawo mai ba da sauri Joseph ya tashi yabi bayan'sa karɓar jarakarsa yayi sukai sallama da Joseph ya fara taka matattakalar jirgin hawa yayi sai da Joseph ya dena ganin da ya juya ya tafi yana yiwa ubangidan nasa fatan nasara a special prevent seat ya zauna....... dauko wayarsa yayi ya saka a play mode ya ajiye ta magazine din da aka ajiye mai ita ya ɗauka labari mafi munu ya fara cin karo da shi....


Cire glass dinsa yayi ya ya ɗauki tissue ya goge idonsa ba raguwar zuciya gare shi ba amma musgunawa talaka da ake a ƙasar nan ya fara yawa sai yau she arewa zata zauna lafiya mutane basu da kwanciyar hankali a garuruwan su sosai ya kurawa gawarwakin da akai musu salla a jahar katsina wa yanda yan bindiga suka harbe ajiye wa yayi..........

ya shiga tunani wata kila wa yan nan da aka kashe akwai masu aure a cikin su kuma suna da ya'ya ya ya rayuwar ya'yan da suka bari zata kasance an hana matasa karatu babban burin su suyi wasa da kwakwalwar matasa lokacin zaɓe su fito su basu yan kuɗi kalilan su tada hankalin mutane wannan abin bazai yuhuba sai da rashin ilimi su basu kwaya hankalin su ya gushe su aikata abin da za su zo suna dana sani mara amfani rayuwar su ta ƙare a gidan yari ba batun cin ma muradin rayuwa.....

yan zu a ƙasar nan ilimi na nema yafi karfin takala ga matsin rayuwa takai ta kawo yanzu zaka ji fara shi in anjima ya tashi ga man fetur din nan a ƙasar mu ake haƙoshi amma yana nema yafi karfin talakawa hutar lantarki daman ba'a maganar'ta......yan handama da baba kere sunyi oder sola suna so ta tafi in da tsayuwar huta ba batun siyan huta me amfani da hasken rana.....

ganin wayan nan ire-iren tunanin za suyi mai yawa ya fara neman ɗauki gurin Ubangiji yana tasbihi belt ya saka sakamakon ji dayayi an sanar jirgi zai tashi a hali jirginsu ya fata tafiya har ya ɗaga sama.........

Unguwar kofar mata*

Ashe gida rahama ne tab ai sai yau na tabbatar da haka dinana da nayi bacci cikin kwanciyar hankali kai Allah ya sakama mana nifa ba fuskar da na tsana a duniya sama da wannan me kama da bishiya


Dariya dinana yayi yace

"Yanzu dai besan kina yi ba tawo muje in raka ki Abuja sai ki faɗa mai.....,

Banza tayi mai rabi ne ya sheƙe da dariya yace

"Na'rantsai da Allah da kuwa in ta shiga ba zata fito ba sai sun ya galgala naman ta ai ni a gurin na gane Ni dan iskan karya ne ina washe garin mu ka kwana kana ga zuwa yayi cikin wannan cel din da ke kallo mu ya harbe wani....,

zaro ido magajiya tayi tace

"Kace har kisa yana yi haba shi yasaka Ubangiji ya ɗauke mai rahamar fuskarsa ba rahama a fuskar sa ko ɗaya nifa daman can baya burge Ni mutane suyi ta yaban'sa ai shi adalin shugabane.....,

Magajiya nifa nayi mafarki mun sha biki ya aure ki dinana ya faɗa yana danne dariyar'sa

Wainar da ta zuba mai ita ta fara ƙoƙarin juyewa da sauri ya saka hannu ya ɗauka yace

"Ya kyauta da zobe...?,

harara ta watsai mai kahu da yake zaune yana jin su yace

"Allah ne ya rufab asiri da tuni dani za a kama..,

Allah ya rufa maka asiri kahu bulama da kaga baƙin tashin hankali wallahi baka da rabon fige kazar hawala da ka dauki darasi mai girma.....

Hmmm Allah ne ya fidda a'e daga rogo

Dariya dukkan su suka saka ban da magajiya da tun da abin da dinana ya faɗi ya ɗauke mata annurin fuskarta

Radio ya ware kamar kullum domin jin labaran duniya ya tarar ma har an kusan gamawa sai karashe A wata majiya me karfi a yau ne shugaban hukumar Dass zai kawo ziyarar ba zata kano in zai taya gwamnan jihar Kano buɗe sababbin aikin da yayi.....
Garin nan ya cika da masoyan sa domin tarbar'sa duk da be sanar da zuwan'sa ba a safiyar ranar Laraba ne aka kai mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login