Showing 78001 words to 81000 words out of 88219 words

Chapter 27 - TSUTSAR NAMA ONE by Bilyn-Abdull

29 Jun 2024

18184

ɗakin yayi datti ina jin ƙyanƙyami”.
    Dukansu sai da suka ɗago suka kalleni. Yayinda Gwaggo ta riƙe haɓa da faɗin, “To kaji kuma wani sheɗancin kuma, yanzu duk waɗan nan zagada-zagadan ƴan matan uwa wa ƴan matan amarya a gida ashe hotiho suke. Yo ni dama tunda na shigo naga gidan yamun wani harmutsai a ido nasan ana ƙwaɓa hauka dan har bashi-bashi da tsami-tsamin dauɗa nake shaƙowa ma. Yanzu ke Julaila kike ko mima oho miki bayan koyama ƴaƴanki rashin kunya abinda zai taimaki rayuwar tasu ma kin tauyesu basu iya ba. Komai kun tattara akan marainiyar ALLAH. To wlhy ba mugunta kikai mata ba idan ma ke haka kike tunani, su waɗan nan da kike gani ƴan hutu a gabanki su kika kashewa rayuwa, dan su zasu gurji kan ubansu nan gaba kaɗan. Zaku ma ki tabbatar da hakan ke da su ranar da tusa ta ƙarewa bodari, ɗiya mace bata iya komai ba ai bata cika mace ba wlhy, babu kuma namijin da zai juri zama da ita, idan ma ya haƙura ya jure dan yanada kuɗin biyan wasu suyi to bazata taɓa daraja a idonsa ba dan wataran ko shine ƙaruna akan kuɗi zai so matarsa ta masa hidima. Kai ai wlhy baki birgeba kuwa. Ashe ma fuggukar taki da ɗaga hanci kamar ƙofar gora na wofine” ta ƙare faɗa a fusace. Bibaa ta nuna da Baby “Ku dan ubanku Imamu ku tashi ku ɗakko kayan shara, ke kuma zoki zauna anan wazai barki kiyi wani aiki kina fama da kanki. Zakiyya ma na hanya gyaran jiki zata fara miki yau ɗin nan dan duk da gaki nan fes da ke ga kuma ƙarancin lokaci bazai hana nasa a kwaskware min ke ba dan kowa ya sake tabbatar da amarya ƴar gata zan kai”.
      Sosai Bibaa da Baby ke kallonta ransu a ɓace, sai kuma su kalla Mum da taƙi cewa komai. Tsawa ta daka musu, babu shiri suka miƙe a zabure kuwa. Nayi mamakin shirun Mum dan nasan yanda suke ƴar tsama da Gwaggo Gudidi, rashin jituwar tasu ma ce tasa Gwaggon daina zuwa gidan gaba ɗaya. Amma dai dole a wannan shirun nata akwai ayar tambaya.
     Su Baby naji na gani Gwaggo ta turkesu sukai gyaran ɗakin, sau biyu tana maidasu su maimaita wai bai mata ba. Bayan sun kammala sunata zungure-zunguren baki tasa Bibaa ta tattara kayanta ta maida ɗakin Baby. Shima auta aka haɗa masa nasa aka sanda shi ɗakin Mum. Acewar Gwaggo nan sune zasu zauna har sai biki ya tashi. Ni dai dariya ma abin ke ban. Dan Gwaggo Gudidi fitinanniya ce sai dai idan bataso ba zaka ga ta watsar da kai kamar mai shiru-shiru. Halin namu dai na kamanceceniya sosai, ƙila dai ita na gado ma (🤣). Fuu Mum ta tashi batare da tace mana komai ba ta bar falon, mu duka da kallo muka bita, sai dai babu wanda yace komai.

“Mum na shiga ɗaki waya ta ɗauka, sai faman huci take da jan numfashi, kai daka ganta kasan dama danne komai take da ƙyar kawai. Ko sallama balle gaisuwa batayi ga wanda ta kira ɗin ba ta fara magana a hasale. “Mama magana ta gaskiya bazan iya haƙurin da kikace da wannan tsohuwar ba. Kinga daga dawowarsu yanzu tabi ta addabar min yara. Nidai bazan iya ɗauka ba. Wannan plan ɗin naki na fara jin kamar bazan iya juresa ba. Ina dalili yara tun suna ƙanana sun tare min komai yanzu kuma an saka min ƴaƴa a gaba duk da kwacen saurayi da akaima Baby”.
Siririyar dariya akayi mai sauti daga can. Sai kuma dattijuwar murya ta fara faɗin, “Jalila wani lokacin idan kina wani shashancin sai nake ganin kamar bani ce na haifeki ba. Ke matsalarki baki iya ɓoye abu aranki. Shiyyasa tun farko ko riƙon yaran nan nace ki yi na siyasa ta yanda koshi mijin naki bazai fahimci baki ƙaunarsu ko son zama daku ba. Amma ina kin kasa. Yanzu kina ganin matsala ta taso kaso biyu bisa uku na mutane har yanzu ke suke zargi da satar yarinyar nan har da ƴaƴanki. Ko ƴan sandan nan idonsu kema na'a kanki. Amma kin kasa fahimta. Ko shi mijin naki badan mun danne masa kai ba tuni kina ganin bake zai zarga ba ne? Shin wai rayuwa babu siyasa ta yiyu haka ne?”.
“Wai Mama sai kice siyasa, siyasa. Dan kawai ina son na birge wani sai na dinga nunawa wanda bana so so. Nidai a bar wannan maganar, kawai ki faɗa min abinda zanyi na gaba dan na fara ƙosawa da halin tsohuwarnan, zan karta mata rashin mutunci wlhy bazata zo cikin gidana ta hanani rawar gaban hantsi ba”.
“A'a ban aikeki ba nikam. Ki bari anjima kaɗan zan zo gidan. Dama ga ƴar uwarki nan tazo itama babu jimawa. Kuma ni abinda nasa a raina kofa auren nan akai sai munyi duk yanda zamuyi basu zauna lafiya ba. Dan yanda ta rabashi da takwarata itama bazata taɓa jin daɗin ba. Na fara ji kuma a raina wannan tsohuwar duk itace ke ƙulla komai, maybe ma itace ta amaso asirin da aka juya kan yaron nan. Shiyyasa sam ban sonta tun aurenki da Imam. Amma idan sun san wata su basu san wata ba ai. Daga su har ita zasu ci ubansu ne da ni suke zancen. Yanzu dai ki cigaba da kwantar da hankalinki bana son jin wata fitina. Bari na ƙarasa aiki mu fito”.
“To Mama dan ALLAH kuyi sauri”.
Suna ajiye wayar zama tai jagwab a bakin gado, ita kaɗai tasan irin ƙunar da take ji a ranta game da auren nan. Ji take kamar ta sakama yarinyar nan shinkafar ɓera a abinci ta mutu kowa ya huta, dan tafi sauran ƴan uwanta tsaya mata a rai, shegiya ga ƙyawu kamar wadda ta tashi a rayuwar hutu, duk baƙar izayar da take mata kullum zaka ganta fes-fes ga shegen Musaddiq ɗin can kullum cikin saya mata suturu yake. Tanada plans daban-daban da zata iya bi ta wargaza auren nan dama rayuwar yarinyar nan duka, amma Mamanta na hanata. Amma yau kam tana ji in har Mama bata iya tayi komai ba itafa zatabi ɗaya daga cikin plans ɗinta ne. Dan bazata taɓa yarda a ƙwacema ƴarta da tafi so abinda ke nata ba. Sai dai ko duk su rasa, ko kuma ƴarta ta samu ita.......✍️


_Humm Mom to bari muga yaya wasan zai kaya 🚴_.
    


_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_


.......Bayan nayi wanka nayi sallar Azhar da tayi ina zaune ina ɗan tsakurar abinci zuciyata fal tunani. Zantukan mutumin nan kawai ke min kai-kawo a rai. Dan tun jiya nake son fassarasu amma na gagara hakan. Ina son na sanar ma Mansoor da Yaya Musaddiq gaskiya amma ina jin shakkun abinda zai je ya dawo. In har zai iya saceni harna tsahon kwanaki goma sha bakwai, kuma ya dawo dani gida batare da wani ya gani ko yaji ko gano shine ba har jami'an tsaro wane makami kuke tunanin zan iya ɗauka domin kare kaina?. Bily ina da taurin kai da kafiya. A wasu lokutan harda tsiwa ma. Amma fa babban weakness ɗina a rayuwa sune ƴan uwana guda biyu. Zan iya bada rayuwata a wajen karesu kamar yanda nasan suma zasu iya hakan. Dan su ɗin garkuwa ta ne. In dai hakane kenan ya kamata na kwantar da hankalina na nutsu waje guda har a gama bikin nan na koma ƙarƙashin ikon Mansoor. Na tabbata zai taimaka min da duk irin gudunmawar da nake buƙata game da bama ƴan uwana garkuwa batare da hatsabibin ya farga ba. Na kuma tona asirin sa ta hanyar da bai zato ba. Tunda yanada wayo shima ya kamata a tabbatar masa da TSUNTSU mai WAYO ta baki ake kamasa. Hakan kuma bazai yiwu ba har sai na nutsar da hankalina waje ɗaya na shirya nima tsaf ta yanda zan zame masa tamkar kifin tarwaɗa da baza'a taɓa iya kamashi da santsin kalkashi a hannu ba. Dan a yanzu ni kaɗai nasan inda video ɗin yake. Dan abinda Mansoor bai sani ba ni da kaina na goge na wayarsa, badan kuma ban yarda da shi nai hakan ba. A'a ina tsoron a masa barazana dani ne a amsa wataran. Shiko Yaya Musaddiq dama bai tura ba kwata-kwata. Dan haka na ciresa daga tawa wayar nima na maidashi a flash drive dana sayo na adanashi inda daga UBANGIJINA sai ni muka san inda yake.....
       “Oh Amarsu irin wannan zurfin tunani haka?”.
   Aunty Zakiyyar Gwaggo da bamma san lokacin data shigo ba ta faɗa cikin katseni ta hanyar taɓani na kawo nannauyan numfashi. “Har kin fara tunanin rabuwa da gidan ne raguwa? Sai bakin tsiya kuma”. Ta sake faɗa cike da tsokana. Murmushi na sakar mata ina duƙar da kaina. Na ce, “Kai aunty yaushe kika shigo bamma sani ba”.
     “A taya zaki sani kin lula duniyar tunani. Yaya jikin naki dai to?”.
    “Alhamdullah Aunty, dama babu inda ke min ciwo, allurar da suka min ce kawai ta sakani wannan dogon barcin”.
         “ALLAH sarki to Alhamdullah ai haka akeso. ALLAH kuma ya kiyaye gaba. Ya tona asirin duk wanda keda hannu a kan hakan. Damma dai Alhamdullah addu'a tayi tasiri ƙwarai da gaske. Kuma da alama duk ma wanda suka kamakin ba mugaye bane. Dan masu amsar kuɗin nan sunfi haɗari. Amma waɗan nan da alama suna da tasu manufar ne a kanki gaskiya. Na kuma fi ƙyautata zaton akan auren nan ne kamar yanda kowa ke zargi, musamman akan wannan maman taku da Baby. Kowa yafi dangantasu da al'amarin nan wlhy, dan zuciyarsu babu ƙyau komai zasu iya aikatawa tunda sun gagara ɓoye hassadarsu”.
     “In sha ALLAHU Aunty bazasu ci nasara ba kuma. Tunda gashi ma ALLAH ya kuɓutar dani cikin sauƙi, dan tabbas addu'ar ce tai tasiri a kansu suka sakeni batare da sun shirya ba, amma kuma ni bana danganta al'amarin da su Mum da dalalin auren nan kamar yanda kowa ke kallo, dan in dan auren ne ai kinga babu yanda za'ai su sakeni haka da sauƙi da sai lokacin bikin ya wuce ko”.
     “Tabbas hakanne kam Samraah kema kinzo da batun dubawa. Amma dai ai zaki iya ganesu? Dan naga angon nan naki da gaske ya shirya ɗaukar mataki, a yanzu haka suna ƙofar gida da ƴan sanda da Musaddiq da Yaya Imam.”
    Idanu na zuba mata kawai, sai kuma na nisa a hankali na ce, “Aunty bazan iya gane su ba. Saboda abinci kawai suke kawo min sau uku a rana. Kuma komai nasu a rufe hatta da hannayensu ma. Kuma basa mun magana sai dai su ajiye kawai su juya su fita. Ko'a ranar dana samu damar kiran Yaya Musaddiq ma kwato nayi, sai kuma suka kamani bayan sun amshe wayar suka shaƙamin abu suka ɗaukeni da ga gidan sai farkawa nai na ganni a wani sabon waje. Hakama yanzu sai da suka min allura sannan suka kawo ni ƙofar gidan nan.”
    Aunty Zakiyya na shirin yin magana dai-dai nan Yaya Musaddiq yay sallama. A tare muka amsa masa. Batare da ya shigo ba yace nazo. Miƙewa nai na ɗauki hujjab ɗina na saka sannan na fita. A falon baƙi na samesu shi da d.c.o da Mansoor sai Gwaggo Gudidi da Abba. Daga can gefe Baby ce ta masifar zubama Mansoor ido kamar zata cinyesa. Shiko sai wani cin magani yake tamkar an aiko masa saƙon mutuwa. Sai da muka haɗa ido ya ɗan sauke numfashi tare da sakar min murmushi. Murtani na mayar masa nima ina duƙar da kaina ƙasa. Gaisar da d.c.o nayi cikin girmamawa, shima ya amsa min da kulawa tare da tambayata ya jikina. Kaina a ƙasan na ce, “Alhamdullah bana jin ciwon komai Sir”.
      “Masha ALLAH, Alhamdullah haka muke son ji ai dama. Samraah wannan zuwan naki ne. Muna fatan zamu samu haɗin kai domin son sanin komai daya faru dake tun daga fitarki a gida a waccan ranar har zuwa yau da ALLAH ya maido mana ke bisa ƙarfin ikonsa”. 
      Babu musu na jinjina masa kaina tare da faɗin, “In sha ALLAHU ranka ya daɗe zan faɗi abinda na sani”.
     Zamansa ya gayara sosai yana fuskantata. Kafin ya furta, “Yauwa Ina jinki”. Bayani na fara masa tiryan-tiryan tun daga shirin fitata. Kiran dana samu daga MD har zuwa fita cikin layi da tare napep. Jefamin handkerchief da wanda na samu a napep ɗin yayi bayan ya kira sunana tabbacin ya sanni ko yana son tabbatar da ni ɗin ce, har zuwa buɗe ido na ganni a wani waje daban. Yanda na rayu a gidan farko har zuwa kiran wayar Yaya Musaddiq da nayi da wayar ɗaya daga cikin mutanen da kuma canja min gida da sukayi. Sai dai na samu kaina da kasa faɗar wanda ya saka akai kidnapping ɗin nawa kamar yanda ya nuna min kansa da buƙatar na bashi abinda ke a hannuna da yayi, hakama dalilin ɗaukar tawa duk ban faɗa ba. Maidoni gida da sukayi da kuma kiran da yayma Nurse a asibiti ta bani. Kawai dai na sanar musu kamar yanda na sanarma Aunty Zakiyya ne. Sosai falon yay tsitt suna saurarena. Yayinda d.c.o ya kafeni da idanu ko ƙyaftawa bayayi. Jinai duk na tsargu, amma na dake abina kun dai san mutuniyar taku ai. Dan kansa ya gaji ya janye idanunsa a kaina. Cikin sauke numfashi ya furta, “Kin tabbata iya abinda ta faru kenan Samraah? Dan bana son ki ɓoye mana komai, kar kiji tsoron barazana ma idan sun miki babu abinda zai faru”.
      “Iyakarsa kenan yallaɓai. In har na ba mance wani abu to bashi da muhimmanci ne”.
    Kansa ya jinjina cikin nuna gamsuwa, kafin ya kalla yaronsa dake rubuta duk abinda nake faɗa, sai kuma ya maida idonsa kansu Yaya Musaddiq. “Inaga fa dole ne mu sake gayyatar MD ɗin nan nasu, dan komai idan aka tattara ya ta'allaka ne akansa. Amma bawai ina tabbatar da shi ɗin ne ba. Dan ita shiri'a saɓanin hankali. Kuma tunda har ta dawo gida cikin ƙoshin lafiya Alhmdllh, koma minene zai zo mana da sauƙi. Yanzu dai inaga sai a kiyaye gaskiya. Fita anyhow dole ta jingine ta. Mukuma duk inda ta saka ƙafa idan ma har ta fitan zata kasance a ƙarƙashin kulawarmu ne.”
        “In sha ALLAHU babu damuwa ranka ya daɗe. Dan ko batun zuwa aiki ma dama zata ɗan dakata, in ma zata cigaban ne sai bayan bikinta idan mijinta ya amince sai taje ɗin”.
    “Wannan ma dabara ce kam mai ƙyau sosai. Amma taron bikin nan fa dole ayisa da kulawa. Koda yake zamu haɗata da jami'ar mu mace domin ta kasance da ita ama duk inda take like handbag ɗinsu na mata. Hakan zai sauƙaƙa mana aikin mu insha ALLAHU.”
     Kowa a falon yaji daɗin zancen nasa kuwa. Dan har fuskokinsu sun gagara ɓoyewa. Ni dai kaina a ƙasa kawai abubuwa da yawa nata min kai kawo a zuciya. D.c.o ya ɗan ƙara tattaunawa da su Yaya Musaddiq kafin suyi mana sallama su wuce. Tare da jaddada min duk sanda suka buƙaci gani na zan iya ganinsu a gidan, ko kuma su aiko a ɗaukan zuwa office ɗinsu. Da to kawai na amsa musu ni dai. Gwaggo Gudidi sai jera musu godiya take. Mansoor da Yaya Musaddiq kuma suka tafi musu rakkiya waje. Muma miƙewa mukai muka koma cikin gidan. Dan Aunty Zakiyya ta tabbatar min da yau babu fashi zata fara min gyaran jiki. Ban musa ba, dan nima ina son zuwa fadar masoyina fes tamkar wata ɗan daren sha biyar.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*








*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_




_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_


........Tun daga shigowar ƴan sanda har fitarsu a gidan Mum ta sani, amma batako leƙo ba. Sun tafi ma babu jimawa sai ga Mamanta da ƙanwarta dake aure a Bauchi. Acewarta tazo ne bikin Samraah domin yima Mom Kara. Bata bari sun zauna a falo ba ta shige dasu bedroom ɗinta. Da kanta kuma ta fito ta haɗa musu abinci takai musu. Ko kunya babu yanda ƙanwarta ta cire mayafi ta fara lodar abinci haka itama Maman tayi. Kai bakace a gidan suruki take ba. Bayani ta sake ma ƙanwar tata akan duk yanda aka samo Samraah, dan ita Mamansu tasan komai. Ƴar uwar tata kai ta jinjina. Sai kuma tai ɗan jimm alamar tunani, kafin ta sake ɗagowa tana kallonsu bayan ta gama ƙulla abinda take ganin zai fanshi yarinyar nan tsakaninta da ALLAH. Dan magana ta gaskiya ita su Samraah sun jima suna bata tausayi, sai dai bazata iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login