Showing 60001 words to 63000 words out of 88219 words
masa yay magana da d.c.o ɗin ta waya, gashi nan zuwa ma su jirashi. Dole sukai zaman jiran dawowarsa duk a ƙage. Sai bayan kusan mintina sha biyar kuwa sai gashi ya dawo. Ganin yanda suke hankali a tashe ya buƙaci fara ganinsu. Suna gaya masa kamar yanda Attahir ya sanar masa tun a waya, shiyyasa ma ya katse abinda yake acan ya taho, ya amshi wayar Musaddiq tare da kiran yaronsa yace ya kwashe number ɗin yanzun nan ai masa tracing. Amsa yaron nasa yay ya kwashe number ɗin ya fita da hanzarinsa.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_
......A matuƙar hanzarce cikin tashin hankali yake bin umarnin ogan nasa. Ita daya shaƙama abu ya fara kinkima ya kai mota. Ya sake dawowa ya tattara duk abinda ya shafeta ya fita da su suma. Hatta kayan data jiƙa domin wankewa bai bari ba. Bedsheet da komai ya tattare katifa kawai ya bari a ɗakin. Cikin abinda bai wuce minti goma ba ya bar gidan da ita da komai nata. Cikin uban gudu ya nufi hanyar inda ogan nasa ya sashi maidata. Yayi nisa a tafiyarsa saƙo ya shigo masa. Sanin wayar da mutum ɗaya take da alaƙa ya sashi taka birki da sauri ya ɗan gangara gefen hanya. Titine da bai cika yawan kai kawon motoci ba saboda sabuwar anguwace sosai kuma a gefen gari ne ma. Idanu ya waro matuƙa sakamakon ganin saƙon da ogan nasa ya turo masa, tare da sauri ɓalle murfin wayar kasancewar ƙarama ce dama ya cire batteryn shima ya zare layin. Karyashi yay huɗu yay cilli da shi yana mai kwanciya akan steering ɗin da sauke nannauyar ajiyar zuciya mai ƙarfi. Yayi kusa minti biyu a haka sannan ya ɗago. Samraah dake kwance a baya tamkar gunkiya ya kalla, cikin cije baki ya ɗauke kansa. Motar yay ƙoƙarin sake tadawa akai knocking glass. Da wani irin bala'in sauri ya kalla gefen nasa, dan motar tinted glass ne da ita shiyyasa. Yasan wanda yake ta wajen bai ganinsa, amma shi yana ganinsa. Ganin kamar babu wani alamun kasancewar sa jami'in tsaro ya sashi sauke gilashin a hankali. Matashin saurayi da bai wuce sa'ansa ba ya ɗan sake duƙowa da faɗin, “Barka oga. Badai wata matsala bace ba ko?”.
Murmushi yay shima cikin sauri ya ce, “Barkanmu. A'a babu komai na ɗan tsaya amsa kiran waya ne kawai. Nama gama yanzu zan wuce”.
“A to masha ALLAH, dama ina tunanin ko akwai matsala ne. ALLAH ya tsare hanya”.
Godiya ya masa yana ƙoƙarin maida gilashin kawai yaga an buɗe murfin gefensa an shigo. Da sauri ya juyo nan ɗin. Mutum ne garjejen gaske gashi cikin baƙaƙen kaya kamar shi. Sai dai wannan yasan ko'a mafarki sukai wasan kokawa ɗagashi zai dingayi yana nanawa da ƙasa. Amma cikin dauriya ya ce, “Malam lafiya kuwa?”.
“Itace ta kawo haka”.
Mutumin ya faɗa a gadarance. Sai kuma ya sa hannu ya zare key ɗin motar yana faɗin, “Fita ka koma baya”.
“Na koma baya kamar ya? Ni da motata ka shigo min babu wani neman excuse kace kuma na fita na koma baya. To kai a wa kuma?”.
Uffan mutumin baice da shi ba. Sai ma ɗora masa bindigar daya zaro a jikinsa yay a saman cikinsa. Da sauri saurayin ya kalla bindigar, cikin son ɓoye tashin hankalinsa amma yana ta son bayyana kansa ya ce, “Malam miye kuma na bindiga anan?”.
Shi dai bai tanka masa ba. Sai ma ƙoƙarin saƙala yatsarsa yake akan kunamar bindiga ɗin, shima sai kawai ya buɗe motar ya fita zuciyarsa na wata irin bugawa da sauri. Turus yayi jikinsa na tsuma ganin zuƙa-zuƙan motoci har biyu baƙaƙe wulik, ga Samraah ana ƙoƙarin sakawa a ɗaya. Sai garadan maza har uku irin wanda ya titsiyesa a mota tsaitsaye da bindigu suma. Yana ji yana gani haka ya shiga bayan motar dan dolensa, saboda babu makami ko ɗaya a tare da shi. Kodama akwai ai sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi. Sannan waɗan nan kam sunfi ƙarfinsa, dan yama riga ya sadaƙar kawai jami'an tsaro ne su ɗin.
Shima abu suka shaƙa masa, a take ya sulale sai barci. Daga haka bai sake sanin a wace duniya yake ba sai farkawa yay ya gansa a inda bai taɓa sani ba. Dan ɗaki guda shima aka ajiyesa shi kaɗai. A yanzu kam hankalinsa ya fara tashi ƙololuwa. Dan ya fahimci ba ƴan sanda bane ba. To ko ogan nasa ne yasa akai masa haka? Amma mizaisa yay hakan kuma?. (Ka nema ɓata masa aiki mana) wani ɓangare na zuciyarsa ya ayyana masa. Kansa ya dafe da ƙyar, dan gaba ɗaya jikinsa yay masa nauyi. Jin kamar jiri na ɗibarsa ya ɗan zame ya sake kwanciya yana mai lumshe idanunsa...
(✿(✿(✿)(✿)✿)✿)
A ɓangaren su Yaya Musaddiq kam anyi traicing number da Samraah tai kiransa an kuma gano inda suke. A take babu ɓata lokaci d.c.o ya shirya mutanensa. Duk yanda yaso su Mansoor su zauna sun dage da roƙon son binsu, ya fahimci koda ya hanasu zasu iya binsu a baya, hakan kuma akwai haɗari dan haka ya haƙura aka fita har dasu. Sunyi tafiya baifi ta mintuna uku ba layin ya yanke. Da sauri yaron d.c.o ya sanar masa.
“Oga akwai matsala fa. Da alama sun farga damu dan layin ya daina aiki. Hakan na nufin an ciresa a wayane, dan da yana kan wayar ko kasheta sukai zamu same su”.
Shima hankalin d.c.o ya tashi, amma sai ya dake shi cikin bada umarni ya ce, “Ku ƙarasa har inda layin ya dakata da aiki”.
“Okay sir”.
Ya faɗa yana yanke wayar. Su Mansoor basu san halin da ake ciki ba. Dan suna a ɗayar motar ne. Gashi kuma an cigaba da tafiya kamar yanda aka faro. Cikin abinda bai gaza mintuna talatin da biyu ba suka iso dai-dai wajen, dan gefen gari ne sosai. Sun sami mota kaɗai, amma babu alamar mutum. A take duk suka fito, sauran da basu san mike faruwa ba duk sun zagaye mota da bindiga. Wanda dai yake kamar ogan tafiyar ne ya sake kiran d.c.o ya sanar masa cewar gafa mota sun samu, sai dai basu sani ba koda mutum a ciki ko babu. Nan ma umarnin bincikawa ya basu, dan haka suka fara aikinsu, sai dai an hana Mansoor da Musaddiq zuwa kusa da motar duk da yanda suke a zalame.
Cikin kulawa da ƙwarewar aiki aka buɗe motar, sai dai me babu kowa a ciki sai kayan Samraah harda jiƙaƙƙun nan na botiki, sun cigaba da bincike motar tako ina, har suka samu nasarar ganin layin wayar a gefen titin an karyasa. Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga kwaranyoma Musaddiq, hakama Mansoor ya duƙar da kansa jikin motar ƴan sandan kawai da alama shima dai kukan yake yi. Dan ba sai an faɗa musu ba komai ya tabbatar musu da mutanen nan sun sake samun nasarar tserewa da Samraah kuma.
Komai an tattara har motar aka wuce da su station. Wasu a cikin ƴan sandan kuma suka watsu a wajen ta cikin jejin har ma da cikin ƙauye dake ata wajen bisa umarnin d.c.o. Dan yana zargin wanda suka ɗauke tan ko dai sun shiga jejin, ko kuma sun shiga cikin ƙauyen domin tsira tunda har aka samu motarsu anan. Sauran ƴan sandan da suka wuce station nata ƙoƙarin kwantarma da su Musaddiq hankali. Dan a take sun nema bayanai daga companyn layin wayar da Samraah tai kiran Musaddiq. Za'a binciki dukan abinda akai da layin a kwanakin da suka gabata. Kai tunma daga randa aka sayesa. D.c.o ya tabbatar musu da in sha ALLAHU za'a dace tanan. Badan dai sun gamsu ba suka haƙura suka tafi, dan bayanan sai zuwa gobe za'a samesu...
(✿(✿(✿)✿)✿)
Tunda na farka daga nannauyan barcin dana kasa tuna lokacin farawarsa rufin ɗakin da nake kwance kawai nake iya kallo. Rufine dake tabbatar da ba'a ƙaramin gida nake ba. Dan yanayinsa da fentin bangon ɗakin kawai ya isa ya tabbatar da haka. Na jima a hakan kafin na motsa da ƙyar. Saman gado nake, tabbas hakan ne, na ayyana a raina cikin tabbatarwa da kaina. Komawa nai na sake kwantawa batare dana ƙarasa tashin ba. A take komai ya shiga dawo min dalla-dalla. Na zare wayar wanda ke gadina na kira Yaya Musaddiq, bayan ya ƙwace ya shaƙa min abu, daga haka ban sake sanin komai ba. Kenan dai ɗakkoni yay daga can gidan ya maidoni nan saboda gudun tonan asirinsa. Hakan na nufin babu rana balle watan komawa ga zuri'ata. A hankali wasu hawaye suka shiga silalo min masu zafi. Yau saura kwanaki takwas aurena, na tabbata duk hankalin wani masoyina ba'a kwance yake ba zuwa yanzu. Musamman Yaya Musaddiq, Mansoor, Hafizzullah... Wani murɗawa da marata tai ya katse min dukan tunani na. Faɗuwa gabana yay, Dan kuwa lallai lokacin prioud ɗina ne. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Aiko akwai matsala, idan na kasance a wannan halin anan waye zai kula dani? Dan ba ƙaramar wahala nake sha ba har sai an mun allura, wani lokacin ma ai allurar taƙi sauka. Shiyyasa har shan magani nake a ɓoye dan kar jinin yazo. Abinka daba uwa ba balle ta gani ta kwaɓa, sai babu wanda yasan ina hakan har yanzu, kuma na jima inayin hakan, dan ko yanzu kusan watana na biyar kenan banyi ba saboda bana wasa da maganin a duk sanda nasan kwanakin period ɗina sun gabato, yanzu ma da ace akwai shan kawai zanyi shike nan bazai zo ɗin ba. Jin yaɗan lafa min na sake buɗe idanuna tare da yunƙurawa da ƙyar na tashi zaune. Ɗakine babba, sai dai babu komai a cikinsa sai iya katifar da nake kai, ashe ba gado bane, irin ƙatuwar katifar nan ce irin wadda ba'a sakawa a gado. A hankali na miƙe da ƙyar, windows ɗin ɗakin nabi na lalleƙa, sai dai bana iya gane komai sai dai ina iya jiyo magana mutane ƙasa-ƙasa. Hakan yasa na nufi inda nake ƙyautata zaton ƙoface. Bugawa na shigayi babu ji babu gani ina kuka. Sosai nake ma ƙofar bugun hauka da nasan dolene ya damesu. Amma ƴan iskan nan kamar kurame, ga wani irin murɗi da marata kemun na azaba, tun ina ƙarfin hali har na sulale ƙasa jikin ƙofar na zube. Tuni nayi sharkaf da zufa na azaba, ga jikina dake rawa, sai kuma uban kuka da nake ina kiran sunan ALLAH da fatan Yaya Musaddiq ya zo ya ɗaukan.........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_
.......Dukkanin bayanan da d.c.o ya buƙata an kawo daga companyn layin wayar mutumin. Dan haka yay zaman dubawa daki-daki. Sabon layi ne, an kuma buɗesa wata ɗaya daya gabata. Sai dai ba'a taɓa waya da kowa da shi ba sai number Yaya Musaddiq da Samraah ta kira. Sai kuma number ɗaya jal da sakwanni kawai aka dinga tura masa da ita. Dukannin sakwanin kuma a gajarce ne. Babu kuma wata ma'anar da za'a fahimcesu sai su da suka yi abinsu. A yanda kuma sakwannin suke kamar babu sanayya tsakanin wanda ke amfani da layin da mai tura saƙon da alamu suka tabbatar shine ya saka akai kidnapping Samraah ɗin. Abin ya tsayama d.c.o a zuciya. Amma dai ya sake bada number da ake tura saƙon itama a basu bayani a kanta. Nan ma sunce sai washe gari. Hakan yasa d.c.o sakawa ai masa traicing number ɗin kafin su kawo bayananta. Sai dai me sam layin babu shi akan network kwata-kwata ma. Hakan na nufin shima mai shi ya karya shi ɗin kenan ko ya yarda ko ya sauke. Wani irin dukan ɓacin rai d.c.o ya kaima desk ɗinsa. Dan ya fahimci wannan al'amari gaba ɗaya akwai rainin wayo a cikinsa. Duk kuma wanda ya shirya ɗauke yarinyar nan yana da basira ƙwarai da gaske. Dan bai ɗauketan ba sai da ya gama tsara dukkan hanyoyin ɓullewarsa daki-daki ta yanda gano wanene shi zai yi matuƙar wahala. Amma babu komai, ai dole ne ko yaya yayi kuskure. Da kuma wannan ɗan ƙaramin kuskuren kaɗai zasu iya kama shi in sha ALLAH..
Ranar da kansa ya zo gidan Abba ba yaransa ba. Lokacin kuma anyi sa'a duk suna gida. Hatta Nabil yazo weekend bai koma ba dan shi a hostel yake zama. Hafizzullah dai ya koma bisa tirsasawar Yaya Musaddiq. Da farko kicin-kicin Mum tai da fuska. Dan ita fa magana ta gaskiya zancen Samraah ɗin nan ya fara isarta. Zirga-zirgan da ƴan sanda ke musu kullum a gida yanzu ta fara cimata rai. D.c.o dake ta binta da kallo cikin dakewa ya ce, “Ina ganin muna gab da ganin Samraah in sha ALLAHU”.
Mum data gama cika taf cikin ɓacin rai ta ce, “Yo dama kune ke wahalar da kanku, duk ma inda take ai itace takai kanta. Dan ni nasan abokan iskancinta tabi wani garin kawai suke zaman shashancinsu a wani wajen. Amma yallaɓai duk kunbi kun tadama kanku hankali muma kun gagara barinmu mu huta. Haba, Samraah dai Samraah dai kamar wata allura ko sarƙar gwal ko diamond”.
“To amma Hajiya duk kin san da haka miyyasa baki sanar mana ba tun farko?”.
“Ni! Rufamin asiri na mutu maza su kaini ba mata ba. Taya zan sanar muku kuwa yallaɓai. Ace kuma na laƙa mata sheri. Kadai san ɗan riƙo komi zaka masa ba tsira kake ba. Amma tun yaushe wannan yarinyar ke bin maza suna barin gari. Wane hotel ne bata san da zamansa a garin nan da wajen garin ba. Ai ni bana raba ɗayan biyu wannan yarinyar ta zubar da ciki sama da sau bakwai kuwa. Tunda nan zata dinga mana ihu da murƙususu wai mararta na ciwo, haka zakaga jini na binta, in ba zubda ciki ba kuwa mi tayi?”.
Kai kawai d.c.o ke faman jinjina wa. Yayinda Abba keta hararar Mum da mata alamar tai shiru amma matar nan sai da takai aya ta haɗiyi yawu bakinta kamar an ɓarka zani. Kallon Abba d.c.o yayi bayan ya gama ɗan rubuce-rubucen sa. “Amma Alhaji matsayinka na uba duk kasan da hakan baka taɓa ɗaukar wani mataki ba?”
Kafin Abba yay magana caraf Mum ta sake amshewa. “Matakin mi zai iya ɗauka a kanta yallaɓai. Bayan duk gidan nan babu wanda take shakka ko tsoro tafi ƙarfinmu. Sannan ɗan uwanta duk da saninsa take komai tunda shine kawalinta.....”
“Amma Hajiya ina magana da mijinki ne. Shi kuma nake son ya amsa min wannan tambayar.” kai Mum ta ɗauke gefe tana laɓe baki. D.c.o ya sake maida hankalinsa ga Abba da yanayinsa ya nuna sam baya jin daɗin abinda Mum ɗin keyi, amma ya gagara tsawatar mata. “Kai nake saurare Alhaji”.
“To yallaɓai ni mizance. Al'amarin ne gaba ɗaya akwai ruɗarwa. Amma ina yin iya bakin ƙoƙarina, sai dai kasan mu maza koda yaushe kana waje ba zaman gidan kake ba, shiyyasa ita ta fini sanin abubuwan”.
Shiru kawai d.c.o yay tare da zubama Abba dake ta ƴan kame-kame ido. Yaya Musaddiq da idanunsa suka cika da ƙwalla cikin sarƙewar murya ya ce, “Ranka ya daɗe Samraah bata taɓa aikata fasiƙanci ba. Sannan inba akan aikin nan nata ba zan iya rantse maka bata taɓa shiga hotel ba. Sannan ciwo da takeyi tana yinsa ne duk wata sakamakon al'adarsu ta mata. Amma inaga abar maganar nan, duk kuma inda take in sha ALLAHU addu'armu na biye da ita. ALLAH ya bayyanata, ya kuma bata kariya daga sharrin duk wani mai sharri”.
Maganganun Yaya Musaddiq sun sake saka Abba shiga wani yanayi, dan sai zufa yake kamar wanda ya haɗiyi kunama. Yayinda Mum keta ƙunƙuni ƙasa-ƙasa tana jin kamar ta rufe Musaddiq da duka. Sai dai babu damar hakan kodan d.c.o dake zaune. D.c.o ya gamsu da zancen Musaddiq, dan haka bai sake cewa komai ba ya miƙe. Miƙewar shima Musaddiq ɗin yayi batare da ya sake kallon inda su Abba suke ba ma, dan bai taɓa jin ɓacin rai mai tsanani akan abinda suke musu ba irin yau. Wani irin zafi yake ji a zuciyarsa game da su matuƙa....
★💫★💫★💫★💫★💫
Ciwo ne sosai yaci ƙarfina. Harma nake ganin ya ninka wanda nakeyi a baya. Ko hakan nada nasaba da yanda nasha magani wata na biyar kenan ma banyi ba. Sama-sama nake jin ana buɗe ƙofar. Daga haka ma nai ɗiff alamar hankalina ya gushe daga gangar jikina.
Da sauri wanda ya shigo ɗin ya koma baya ganin Samraah ta suma. Cikin tashin hakanli yake sanarma sauran ƴan uwansa, “Kai yarinyar nan fa kamar ta mutu”.
“Mutuwa fa?”.
Suka faɗa a tare suma